Chapter 30 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   30 / 43

87K to 90K   out of 126.5K words

Sadiq yayi yana Fadin"Eh...Jiya nan Abba ya gama Tara su Umma da Nene yace bai yarje musu In kazo Gidan suyi maka mgana ba ballatana Har su Saurarekaba Daga karshe yace harta Anty Zareena na bai yarje mata ba kuma Umarni ne ba Shawara ba Daga Karshe yace Shi da kanshi zai gayamaka kada ka karo Tako mai Gida Tunda ba Da kudinka ya Siya Gidan ba..!










*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️

*BOOK 1*



              2️⃣2️⃣

"Ba Zain kadai ya kad'u da jin Mganar Sadiq ba Hatta Haddir Shima sai da ya nuna Kad'uwarsa a Zahiri,Zain kuwa K'asa kasa Daukansa Tayi Domin Wani irin Jiri ne ya kwasheshi ya Tafi luu zai Fadi Atare Dukkansu Sadiq da ya watsar da Jakar Hannunsa ya Nufeshi Sai dai Haddir ya Rigashi isa Gareshi Tunda Shi yafi kusa Dashi Cikin Ikon Allah ya Tallafeshi ya Fado Jikinsa Cikin Fitan Hayyaci yake Fadin"Abba...Ne Abba ne yace kada na kara Shigomai gida .?

Yafada wasu zafafan Hawaye suna Biyo Duka kuncinsa Atare Sadiq da Haddir suka Rikosa Zuwa Bakin gado ganin yadda Duka Jikinsa ke Rawa suna Zaunar Dashi Haddir ya kalli Sadiq yana Fadin"Jeka Kitchen ka Dauko Goron Ruwa mai sanyi a cikin Fridge..ka Hado da karamin kofi plz.."

Jin Haka yasa ya Fita Da Sauri ba"a dau wani Lokaci ba ya Dawo da Ruwa a Hannunsa Da karamin Kofi ya mikama Haddir Shi kuma ya karba ya Tsiyaya Ruwan Fin Rabi acikin Kofin ya Mikama Zain yana Fadin"Karbi kasha..Zuciyarka Zatayi sanyi ta kuma Daina Bugawa Da Sauri Da Sauri.."Idanuwansa da Suka Sauya kala ya Watsama Haddir Dake mikamai Kofin Ruwan Cikin Bugun Zuciya da wata murya Cikin yanke Tsammani yake Fadin"Taya kake Tunanin zan iya Shan Ruwa ya Tsirgamin Haddir..?Kanaji fa Abba Da kanshi yace kada kowa ya Saurareni kuma Shima zai Fadamin kada na kara Takamai zuwa Gida..? Kaichona Haddir Wlh ban Taba jin na Tsani kaina ba Irin Jiya yau kuma kalaman Abba Gareni sun kara karyamin Duk wani Sauran kwarin Gwiwata yanzu ina zan saka kaina Duka iyayena da yan"uwana Suna Fushi Dani kuma suna kallona a mutumin da bai da wata kima..? taya zan kara samun Damar da Duka Ahalina zasu yarda dani..?Ga Firstlove itama Zata barni saboda wannan Bakin Fentin da na Saka ma kaina Allah na Tuba Allah ka yafemin Astagafurullah...!

Yake Fada Cikin Kuka Lokaci Daya yana saka Fuskarsa Cikin Tafukan Hannayensa yana wani kuka mai cin rai Harda Sheshsheka kamar zai Shida,Sadiq baya ya koma Shima yana Sharan kwallah Domin Zuciyarsa bazata iya Juran ganin Jajirtatacen Yayansa na irin wannan kukan,ba Haddir kuwa kansa kawai ya Dukar yana Sauraran Duka maganganun Zain din Shima Ya gaji da kukan zuccin Da yake yine,Dagowa yayi yana kallon ZAIN Din kafin ya sake mikamai Kofin Ruwan yana Fadin'"Duk naji...Karbi dai kasha Ruwan ko bakomai zai Saka ka Natsuwa..!

Bai yi gaddama ba ya karba ya kafa kai Domin gabadaya makoshinsa ya Bushe ne kamar bai Taba Shan Ruwa ba sai da ya Shanye Duka Haddir ya karamai kana yaji Bushewar makogwaransa ya Ragu Da Kofin da Ruwan Haddir ya mika ma Sadiq yana Fadin"Fita dashi Sadiq.."

Ba Gaddama Sadiq ya maida Komai Kitchen din kana ya Dawo ya Iske Haddir ya zauna Kusa Da zain yana Fadin"Zain Dago kanka ka Saurareni..'Dole Zain ya Dago kansa daya maida kasa yana Sharan kwallah Cikin Sanyin Murya Haddir ya Dafashi yana Fadin"Abunda Muke Gudun fa ya Riga ya Faru..Fake gaba kawai zamu yi sai Abu na gaba yadda zaka Shawo kam iyayenmu su yafe maka da kuma yadda zaka Gyara Mu'amalanka da Matarka Domin fa mai afkuwa ta Riga ta afku bamu da yarda da zamu yi wannan koke koken naka bazai kaika ko"ina ba Wlh Gwara Tun Wuri ka Ijiye wannan gefe Tunda komai ya Faru kai ne Sila Tun Muna London nasha Fada Maka kabar wannan Muguwar Dabi"an Bata Dace da Dan Musulam kwarai ba Zain kaki jina Na Dauka Da muka Dawo Gida zaka Daina Abunda kakeyi Ko Domin Tsoron Allah da kuma Darajan Mutumtakan iyauyenmu ammh baka Daina ba ka Biyema Yarinyar nan Dina Wacce Tun ganin Farko Dana yi mata na gayamaka ka Rabu da ita Shedaniya ce kaki jin mganata,Wlh na Tabbata ba sai nayi kaffara ba Da gangan ta bari Ciki ya Shigeta Saboda ta Fallasaa ka Aureta Tun Farko sai da na gayamaka in Sonta kake ka Aureta mana ka Hadasu ita da Zaina da kabi Shawarata Hakan zata Faru..?

Kamar karamin yaro Haka Zain ya Girgiza ma Haddir kai alaman A"a,Haddir yaci gaba da Fadin"Toh ka gani ka kijin mganata Lokacin ma Saboda ina Gaya maka gaskiya gaba ka Farayi Dani Da auranta kayi Da Duk Abunda ya Farunan bazai Faru ba Gashi yanzu Dalilin Son Zuciyarka da kuma Shedan din Daya Dinga kawata Maka aikata zina yasa ka Cikin wani Halin Ka samu mumaa Damu da Duka Yan"uwanka da makusantanka Don Allah ina Dadinsa..? Ni babban Damuwa ta ma Fushin iyaye akan ya"yansu Bala"i ne Uwa uba ayanzu bamai Shiga mganar nan Tunda kowa ma yana Cikin Bakincikin Abunda ka aikata ga Zaina Ka saka yarinya karama Dandanan Dacin Bakincikin Cin Amanar Da Namiji ni kaina ina Jin kunyar mu Hada ido da ita bansan me zan ce mata ga Ga Babban ma Tashin Hankalin Cikin Da ke Jikin Dina kuma Alhaji Tsoho yace sai ta Haifeshi yanzu haka Acikin Zuru"armu zamu samu Dan gaba da Fatiha..?Kai son Zuciya bai yi ba sam Wlh.."

Ya karishe Fada yana Dafe kansa Sadiq Dake gefe kai yake Jinjinawa alamun gamsuwa da kalaman Haddir din Shi kuwa Zain Kansa kawai ya Tusa Cikin Gwiwoyinsa Yana Kuka kamar wani karamin yaro Mikewa Haddir yayi yana Fadin"Nasan Damuwa ta zama Dole Gareka ammh u Hv To become Very Strong Tunda daman kasan Duk Abunda kake aikatawa watarana asirinka sai ya Tonu kuma Wannann Lokaci zai zo,ina Jiyemaka Hawan jini Ko Ciwon Zuciya yazo ya kamaka Domin Duk wanda zai ji wannan mganar kukan ka bazai Taba bashi Tssusayi ba Illah ma ya karama da kalmar Allah kara kai ka jawo ma kanka komai miye yake Faruwa Dakai."

Ya karishe Fada yana Sakin Numfashi kafin yace"Zan je Gidan Na Duba Abba da Jiki Daganan zan Biya Gidan Alhaji Tsoho na gayamai nagani ko zai iya Saka baki Abba ya sauko ammh Shima din ba yanzu ba saboda Kaga Halin Daya ke Ciki Yanzu ba"a son yasa ka wani Damuwa aransa kaima ka sani.."Da Sauri Zain ya Dago yana Fadin"'Don Allah Haddir ka Tayani Lallashin Firstlove kace mata Tazo ta ganni muyi bankwana na Roki gafaranta kada na Mutu ka Shaidamata Wallahi Summa Tallahi Duk Duniya Ita ce macen da nake so Kuma Itace in ta barni Rayuwata zata Lalace ka Fadamata Ta Dawo Gareni Don Allah ka Tahomin da Firstlove na Rumgumeta akirjina Nayi kukan da Haryanzu ya kasa Fitowa Daga Cikin Kirjina.."

Yafada yana Runtse Ido Saboda yadda yakejin Zuciyarsa na Bugawa Daga Sadiq har Haddir sai da suka kusa mai kwallah Cikin Muryan Lallashi Haddir ya Dafashi yana Fadin"Karka Damu I Will Try my Best Insha Allahu naga komai ya Daidaita..Yanzu ka kwanta ka Huta ka Cire komai aranka da Izinin Lahi Tunda kayi Tuban gaskiya Komai zai zo ya wuce kamar ba"ayi ba zan je nyi mgana Dasu Umma itama Zaina zan yi mgana da ita komai zai Daidaita kaji ko..?

Kamar Haddir yamai Gafara Haka yakeji Cikin Gyada kai yace"I Trust u...Kuma Wlh da Gaske na Tuba...Nama Dade da Tubam ma Allah Dina ita ce Ke maidani Ruwa Shiyasa na Tsani Jin Sunanta ma na Tsaneta na Tsani mai kaunarta Tayi sanadiyar Jefani Cikin Bala"i Tsakanina da ita sai Allah ya isa kawai zence Shegiya macuciya..'Haka kawai Zain yake Sambatu yana Zagin Dina Haddir ya gyada kai yana Fadin"Koma miye ya Faru da Taimakon wannan Shedaniyar kawar nata...Shiyasa akomai kada kayi mu'amala da Mutumin Banza Domin Aiyukansa Watarana zasu iya Shafanka..Bari Naje ka kula Da kanka kafin na Dawo in Tabawa Tayi Tuwo nazo maka Dashi..?

Da Sauri ya gyada kai yana Fadin"Allah yasa ta bada in Taji ance ni za"a kawo mawa.."ya fada kamar yayi kuka Mirmishi Haddir yayi yana Fadin"Zata baka mana...Har yau har Gobe kanan nan amatsayinka na Zain Usman Abubakar Saulawa Babu Abunda ya Sauya wannan kuma Abunda ya Faru Jarabta ce kuma Allah ya bamu ikon Cinyeta Watarana zata zama sai Labari Insha Allahu.."Cikim Karfin Hali Zain yace"Allah yasa.."

Fara Tafiya Haddir yayi yana Fadin"Da yardan Allah...Kai Sadiq in ka Tashi muje na ijiye ka Tasha naga ma kamar kayi yammah.."Sadiq ya Fara Tafiya Wajen Jakarsa ya Dauka ya Rataya yana Fadin"Yauwa Ya Haddir nako gode....Banyi ba ko agida Abba yagaji Da Fada ya kyaleni nafi son Tafiyar Dare.."

Haddir na Barin Bedroom din yana Fadin"Tab lalle...Yarinta ke Damunka Allah ya Shiryeka muje.."Daga haka ya Fice Shi kuma Sadiq ya Tsaya gaban Zain yana Fadin"Ya Dakta Allah kara Lafiya zan koma Zaria sai an kwana Biyu kuma.."Cikin Rinannun Idanuwansa ya Kallesa kafin ya mike ya Riko Hannayensa Duka Biyu yana Fadin"Sadiq kai kanina ne Ka ga Dai Abunda ya Faru dani ko..? Ina baka Shawara karka yarda ka Kusanci aikata Badala Kai ko mata ma kadaina sakar musu Fuska Da yawansu Shedanu ne sai sun kai ka sun baro su kyaleka Cikin Bala"i ka Tsare Kanka Don Allah.."Yafada Cikin Fitan Hayyaci Tsausayinsa ya kama Sadiq ya murmusa yana Fadin"Insha Allahu Ya Dakta..Ni Bana Shiga Harkan mata Mazan ma ni ba Shiga Harkansu nake ba Allah ya Tsaremu Daga aikata Abunda zamu zo muna Dana sani Daga baya.."

Da Sauri Zain yace"Ameen Ameen Nagode..Allah ya kiyaye Hanya.."Ya amsa da Ameen Har Falon ya Rakosa kafin ya koma Shi kuma ya Fita Zuwa Haraban Gidan Inda Haddir ke Jiransa bai ma kai ga Shiga Motar ba Tanimu maigadi ya Tsareshi Da Tambayan ina Gimbiyar Dakta ko Tayi Tafiya ne bata Dawo Gida ba..? Shidai Haddir cemai kawai yayi bata lahiya Tana Gra Shine fa ya Fara kwararo Addu"o'i wata addu"ar ma baisan me yake Fadi ba Mirmishi kawai Haddir yayi ya zaro 1k ya bashi yana ta Godiya kana ya Bude mota ya Shiga Sadiq ma ya Shiga Gidan Gaba Yayi Hon Tanimu ya Bude Get suka Fice Daga Gidan.

Sai da yakai Sadiq Tasha kana ya Wuce Gidan Abba Sadiq din kuwa yayi Sa"a yana zuwa Motar Zaria Ta kusa Cika Saura mutum Biyu yana Shiga sai ga wani Shima ya Zo Basu Dade ba Suka Tashi Haddir kuwa Koda ya isa Gidan Abba  ya iske Har Abba yaji Sauki ma ya Farka yana Cin Abinci Bayan ya Gaisheshi da Jiki Su Umma da Nene Duk suna Dakin Abba ya Kallesa yana Fadin"Ka koma bakim aikib ka ko..?

Cikin Ladabi Haddir yace"A"a sai zuwa gobe Abba..Jikin Zain din Har yanzu ba Dadi.."Zaro Ido Nene Tayi Lokaci Daya Tana Dafe Kirji Cikin kaduwa Tace"Na Shiga uku me ya sami Zain din..? Kafin Haddir ya Bata amsa Abba ya maka mata Harara yana Fadin"Na manta ban Fada muku ba ko Sunansa na Kashe ambatonsa acikin Gidan nan..!

Wannan Karon Har Umma sai da Ta kalli Abba kamar zatayi mgana sai kuma ta Fasa,Nene kuwa Idanuwanta Ne suka cika da kwallah ammh batayi mgana ba Abba ya kalli Haddir Fuskarnan nashi ba Annuri yace"Ka koma wajen aikinka ka Rabu Dashi..Babu jin kai ga wanda baya jin kunyar aikata Abunda yaso..!

Kan Haddir na kasa yace"Kayi Hakuri Abba...Nasan Zain yayi Laifi matuka ammh.."Ammh me..? Me zaka Fadamin wanda ban ji ba kuma ban Fahimta ba..?

Abba ya katse Haddir Lokaci Daya Da Dagamai Hannu sai Haddir yaji Gwiwansa Tayi sanyi Cikin Dauriya ya Dago kansa yana Fadin"Nasani Abba ammh In ka Lura da komai yadda ya Faru Zain ya Hadu da Shedaniyar mace ce ita ke Ribantanshi koda ya Tuba kan Abunda yake aikatawa.."

Abba ya Dade yana kallon Haddir kamar bazai yi mgana sai kuma ya Murmusa kafin yace"Kaji wata mgana..? Ai Shine Babban Shedan din Hadiru.."Haddir ya Bude baki zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Kaga Hadiru Tashi kaje sabgoginka nagode..Ammh Matukar mganar Zainullahi zai kara kawo ka kaima na Yanke maka zuwa Gidan nan Allah bada lada.."

Daga Haka ya Mike Daga kan gadon Bayan ya Ture Filet Din Abincin Daya gama ci Ya Taka ahankali ya wuce Tiolet,Dukkansu suka Bishi da kallo Cikin Tsausayawa ganin Duk ya Rame ya Fada Kada kai kawai Umma Tayi Tana Fadin"Komai ya Faru Zuciyarsa Data Rinjayensa itace Silan komai.."Daga haka ta Fice tana Kokarin Boye Damuwarta Dakin zaina ta Wuce Domin ta Dubata sai ta Iske ta samu Barci Hamdala Tayi ma Allah Domin Jiya Tana Jinta kwana Tayi bata yi Barciba Tana kuka Yanzu ko Hakkin Yarinyar nan Allah ya kama Zain Dashi zai ga Daidai arayuwarsa..?

Nene kuwa Umma na Fita ta kalli Haddir Tana Fadin"Hadiru ya Jikin Zainullahi din..? Fata dai da sauki ko..? Bai mata mgana ba Jin kamar Abba na Shirin Fitowa Daga Tiolet Da Sauri Nene ta wuce Gaba Tana Fadin"Biyo  ni muje Dakina Hadiru..Alhaji ya Riga yayi Fushi Da Zain kuma Fushin da bamu Taba ganin yayi kamarsa da wani ba.."

Ba Musu ya mara mata Baya zuwa Dakinta suna Shiga Ta Rufo Kofar Tana Fadin"Hadiru ba dai wani Cutar ne ta kama min D"ana bako..? Haddir ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Bata kamashi ba ammh in ya Cigaba da saka Damuwa zata iya kamashi Har tamai illah.."

Salallami Nene ta Fara kafin ta zauna Gefen gado Tana Fadin"Oh ni Aisha..Ina zan saka Raina Wlh Hadiru Tun Shekaran Jiya Rabona da samun Barci mai Dadi agidanam Hankalina na wajen yaron nan babu Kowa awajensa bamai Sauraransa sai kai Ba Domin Alhaji yana mana iyaka ba Da Tuni naje naga Halin Dayake Ciki.."

Haddir ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Haka sadiq ke Fadamana yanzu Daya Biya kafin yanzu mu Fito Tare nakai shi Tasha ya Hau Motan Zaria,Zain din ne ma ya matsa bayan yaji Sauki kan zai zo gida da na Hanashi yaki Hanuwa Shine Sadiq yake Fadin Abunda Abba yace..Abun bai yi Dadi ba Nene Kinsan Fushin Iyaye kan ya"yansu fa Ba kyau sam.."Nene na Sharan kwallah Take fadin "Na sani Hadiru ya zanyi..? Wlh ni kam bana Fushi da zain sai dai in na ganshi zan mai Fata fata na Nuna mai Bacin raina kan Daukan Tarbiyan da ban Taba mai Shi ba..Ya na iya Alhaji yayi Fushi sosai wanda kuma sauko Dashi kan wannan Fushin sai Alhaji Tsoho kuma Shi din na Tabbata ba zai saka baki yanzu ba kuma Fushin Alhaji Duk da Yarinyar nan Halima ita ke kara Sakashi Jin Takaichin Zain Wlh Domin Kuka fa Take kwana yi Ta Wuni Yi Tunda Abun nan ya Faru.."

Haddir yace"Ai da wuya ma Alhaji Tsoho yace wani Abu yanzu..Mganar ma Zainar  Duk da ita ta kawoni Nene,Ku saka Baki ta koma Gidan Mijinta Wlh Zain yana Bukatarta Sosai kuma Abu ya Riga ya Faru ai sai Hakuri Bawa bai isa ya kaucema Kaddaransa ba.."

Nene tace"Hakane...ammh kam banajin Hakan zai yuyu gaskiya..'Haddir yace"Saboda mene Nene..? Nene tace"Saboda Ba wanda zai ce Dole Sai Halima ta koma Gidanta..Alhaji kuma bazai yi mgana ba Alhaji Tsoho kuma yasan Tana nan gidan ammh bai ce komai ba Uwarta ce kuma Bazata Yarda Ta baka ita ba.."

Cikin Sauri yace"Wai Umma..? Nene tace"Eh..."Haddir ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"Bari naje nayi mata mgana in tayarda ta bani ita shikenan Abba da Alhaji Tsohi basu da yarda Zasu yi indai sukaji Ta koma Wajen Mijinta ai ba wanda ya isa ya Raba Tsakaninsu sai Allah Nene.."

Nene Ta Mike Tana Fadin"Kwarai mganarka Haka Take muje Dakin Halimar Umman Tata tana Chan Tunda Ita ke kwana da ita.."Daga haka ya Fita itama tabi Bayansa Sun Fito Falo kenan suka ci karo da Zareena Tana Zaune afalo Tana bama Takwaran Umma Nono Jalal na Gefenta yana Game acikin Tap dinsa,Ganin Haddir yasa Ta saki baki Tana Fadin"Aboki Hadiru Tazuru kuma kanina Yaushe kazo gidanan..?

Tafada Tana yar dariya Ba laifi Itama Ta Fara sakewa ba kamar Jiya ba Tunda Har tayi wanka Zataje gidan Alhaji Tsoho ne Hararanta yayi yana Fadin"Ni sa"anki ne wai Abokiya Zareena..? Kin Raina ni ko..?
Cikin Shakiyanci Tace"ji wannan yaron..? Ban girmeka bane nifa yayarka ce ko kaki ko kaso.."Haddir yace"Wata Hudun da kika bani Shine kin Girmeni..?Ki sake Tunani yarinya akwai malaman da suka ce komai kankantar Namiji shine Shugaba akan mace saboda Haka ki Dawo Cikin Hayyacinki Maza Bisa kanki yarinya.."Yafada yana Kashe mata Ido Daya Bata rai Zafeera Tayi Tana Fadin"Da aurena da ya"yana kake cemin yarinya..?

Yace"Au Ai harta wanda ya ijiyeki Engnear Jawaad din yaro ne..."Duka Zafeera Takaima ya kauce yana Dariya Nene ta Tayasu Sai ga Jalal ya Saka Dariya ashe Tun dazu yana Kallonsu kumatunsa Haddir ya Kama yana Fadin"Ai gaskiya na Fada ko Son..? Da sauri yace"Is Truth Uncle.."Dariya ta kama Haddir har Sai da ya Bashi Hannu yana Fadin"Dat my Son Plz Give a Five.."Yako bashi Hannu suka Kashe Zareena tacika kamar ta Fashe Nene sai Dariya Takeyi Haddir da Jalal na Tayasu.

Kukan Little Umma ne ya katse Zareena ta koma ta zauna Ta Cigaba da Bata Nono Tana Fadin"Ka samu sa"a ne Aboki Zaim baya nan Da shi zai Taremun Tunda kafini baki.."Ambaton sunan Zain Da Tayi ya Dauke duka walwalansu Cikin Damuwa Haddir yace"Yana Gida ba Lafiya Abokiya Zareena.."

Cikin Damuwa Itama Zareenan tace"Ayyah..Allah ya bashi lafiya..Zan je na Dubashi ammh Nene Kada Abba yaji labari.."Nene tace"Wa..? Ba wanda zai ji kinji na Rantse Miki anjuma kije ki Dubamanashi Don Allah kice ya kwantar da Hankalinsa Nenensa na Tare dashi komai zai Wuce.."

Zareena Tace"Insha Allahu...Zan Tafi Gidan Alhaji Tsoho na kai mai mai Sunan Umma Shi da Hajiya Mama da Tabawa Daganan sai na Biya na Dubashi..Allah sarki wannan Kaddaran bata kyauta mana ba sam Nene..'"Haddir yace"Uhm...Bari dai na ga Umma kam mganar Zaina.."

Zareena Ta kalleshi Tana Fadin"Tab...Anya kuwa..? Da kun bari zuwa akwana Biyu Lokacin Abun ya saketa.."Haddir ya kama Tafiya Zuwa Dakin Su Zaina yana Fadin"A"a Barin zuwa Wani Lokacin ta wannan bangaran abun kara Tabarbarewa zai yi..Zain na Bukatarta ahalin Dayake Ciki.."Zareena Tace"Allah yasa ku dace..'

Nene Tace"Ameen Ameen..."Daganan Itama ta mara ma Haddir Baya zuwa Dakin Da zaina Take,Haddir ne kan Gaba ya Tura Kofar ya Shiga Nene na Binsa abaya Da Umma

30 / 43