Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Abun kauna da Tattali Irin Zareena Shiyasa Dr Salauwa Ya sakamata Umman Zareena sai kuma ya Bita har ya"yan suka kama Maryama kuma Mama maryama Abdullahi kuma Suna Kiranshi da Baba ne ayayinda Suke Kiran Alhaji Usman da Abba Tun Suna yara.
Duk da kowa ya Fahimci mahaifiyarsa ammh yarintarsu bai Hana Sun Fahimci inda suka Fi Samun kulawa ba,Kowanne sai ya fi Nuna Doki ga inda akafi Jansa ajiki,Zain yafi Son Nene Saboda itace komai nashi Sai ko Mama Maryama Umma Zareena kuwa komai ta samu yarta ce Zareena Ko ta kan Zain bata Bi Tana mai alkunyar dan Fari da kuma Kawaicin Nuna ita Zareena ce yarta Da Farko Zain Din ya Fara nuna Damuwarsa Sai kuma Daga Baya da Nene itama Ta Tare komai nashi Sai Shima ya koma Tamkar itace ta Haifesa ba Umma ba.
Mama maryama kuwa Tamkar Uwa Haka Suka Dauketa Domin Itace Komai nasu Sun Taso Sun ganta ne Ita da Baba Abdullahi sai suke kallonsu kamar wasu iyayensu kuma na Dabam Tunda Watarana ma nan Shashen Maryama Suke kwana In Tatashi aikinta Daga Cikin Gidansu zata Shashenta sai su makale mata Sai Sun Bita su kuma iyayen suce Tatafi Dasu Haka zasu Bita suje chan suyi ta Kirniya Abdullahi na Biye Musu Har barci ya Daukesu Maryama ta kwashesu zuwa kan gado ta kwantar Dasu bayan tayi musu addu"an Barci Cikin so da kulawa.
Gidan Dr Saulawa kuwa Suna yawan Zuwa Musu Weekend ko Hutu Duk su nasu baya Wani Dadewa Suna kusa da gidan iyayensu Haddir ne kulafunci Zuwa Hutu Bauchi Saboda Su Zain Wadanda Tun Suna Yara mafarin Abotansu ta Fara Su ukun Haka mafarin Rayuwarsu Ta Fara Da Shakuwa da kaunar Juna Barin Ma Zain da Zareena Tamkar yan Biyu haka suke wanu bai isa ya Taba Wani ba acikinsu Hakama Haddir sunfi Shakuwa da Zain sosai kan Zareena,ita Suna yawan Fada Tunda Tana ganin yana so ya nuna yafita son zain sai suyi ta Fada Sai Maryama ta Raba Fadan ko kuma Chan Gidan Hajiya Mama ko Atine su Raba Tsiyan Da karfi da yaji Haddir ya Dawo Bauchi yaki Abuja Dr.Saulawa yace su kyaleshi cikin yan"uwansa Dole suka barshi Alhaji Usman ya Dauki Haddir ya sakashi makarantar da su zain suke zuwa mai Suna International School Bauchi,Iyayensa basu wani Damu ba Tunda Lokacin Safiya Tana Goyon yarta mace Da Ta sake Haihuwa mai Suna Hamdiya.
Kwatsam Megadin Gidan Alhaji Usman yazo ya sameshi kan Zai ijiye aikinsa yana so ya koma Garinsu Mahaifinsa bai da lafiya karfi ya karemai zai koma yayi Jinyarsa Hakika Alhaji Usman Yaji ba Dadi Saboda Sun Saba Da Yusha"u megadi ammh Uba ya wuce wasa Hakanan yayi mishi Fatan samun Lafiya ga Mahaifinsa kuma ya Hadamai Sha Tara na arziki Suka Rabu Faruwar haka sai Alhaji Usman ya Fara Tunanin Samun wani Megadin Jin haka yasa Maryama ta Shawarci Mijinta kan me zai Hana Shi ya karbi Gadin Yayi Tunda dai ba wani aiki yake yi ba karamcin Su Alhaji Garesu yasa Ya amince mata kuma ya samu Alhaji Usman din da mganar da Farko yaso yaki Tunda ya Nuna Tamkar kani ya Dauke Abdullahi Shi kuma ya Dake sai yayi mgana dai Har ta kai ga Dr.Saulawa Da Mallam Umar Shi Mallam Umar shi ya kashe mganar inda yace Sai dai In Usman bai yarda da Abdullahi ba Ammh in ya yarda Dashi ya barshi yayi mai gadin Tunda Ba wani Abu yake ba Dole Alhaji Usman ya Amince ammh Har Cikin Zuciyarsa baya Kallon Abdullahi Da maryama wasu Bare yana kallonsu nr amatsayin Wasu Shakikan yan"uwansa..
Faruwar Haka da wasu Wattani Ciwon Daji mai Tsanani ya kwantar da Mallan Umar da Farko Abun kamar Ba Ciwon Daji ba Sai da Dr.Saulawa yayi ta Shige Da Fice dashi a asibiti kana aka Fahinci Ciwon nashi Duk da kokarin da Dr Saulawa ya Dinga yi Bai Hana Mallam Umar Rokon alfarman Su barshi ya koma ga Ahalinsa yayi Jinyar achan ba,Yana Tunanin Ciwonsa bana Tashi bane Da Farko yaki Sauraransa ammh ganin yadda ya dinga Rokonsa sai bai ki ba Lokacin da Mallam Umar da Atine zasu koma Gada da Zama Gabadaya Ahalin Dr.Saulawa Sun Girgiza Sakamakon Sabo Ammh ba yadda zasu yi Tunda Mallam Umar ya nuna musu ko basu ga Abdullahi da Maryama nan Tare dasu kuma in da Rai ba"a Rabu ba.
Suna ji suna gani Haka zamansu ya yanke a garin Bauchi Ashe kuma ta Har Abada ne,Da komawarsu Garin Gada da Rasuwar mallam Umar Kwana Ashirin ne yace ga garinku ne hakika ba Yan"uwan Mallam Umar kadai sukai Rashi ba Hadda Dr.Saulawa da Duka iyalansa,domin dasu akayi zaman gaisuwar har akayi bakwai Saboda Atine wacce Tunda Taji Mutuwar Mijinta ta yanke jiki ta Fadi ko da ta Farfado ba Baki Ance Jininta ne yayi bala"in Hawa.
Bayan addu"ar Bakwai su Hajiya Mama suka Dawo Bauchi Harda Abdullahi da Maryama Saboda Yara,Wanda Suna Gida Tare da iyayensu sai dai suna Ta Kuka da kiran sunan maryama din Da Abdullahi,Allah mai Gagara Misali Rasuwar mallam Umar da Wata Biyu itama Atine ta Bisa kuma ta Rasu ne Akarkashin Kulawan Likitocin asibitin na Dr Saulawa Tunda yaje garin yaga Halin Datake Ciki ya Daukota ashe bazatayi Tsawon Rai ba Duka Duka kwanta Biyu a asibitin tace ga garinsu nan.
Duka Chan suka Tafi Gada Tunda Dangin nata sun Nuna Chan suke so ayi mata Sutura Hakika Hajiya mama tafi kowa jin Mutuwar Atine awannan karon sai kuwa Abdullahi Daya Dawo Maraya Sadakar uku kawai Sukayi suka Dawo ammh Sun bar Abdullahi da Maryama achan sai da akayi bakwai suka koma Cike da alhinin Rasa Iyayen nasu Domin Ita kanta Maryama Bayan yayarta Halima bata da kowa sai iyayen Mijinta Abdullahi.
Bayan Dawowarsu ne kuma Umma Zareena ta Fara Laulayin Ciki wannan karon ita kadai ce Sai kuma Matar Bashir itama Iklima da ta Fara Nata laulayin Cikin,Kwanci Tashi ba wuya a wajen Allah Umman Zareena ta Haihu Da kwana Uku iklima ta Haihu kuma Duka maza Suka Samu Bashir sai ya maida ma Dansa Sunan Dansa na Farko Daya Rasu Abubakar hakama Abba Usman Shima Abubakar din ya saka ma nashi Suna Kiranshi Sadiiq Babba Yaron Wajen iklima kuma Suna Kiranshi Sadiq karami.
Wannan karon ma Nene tayi Ruwa Tayi Tsaki kan Abata Sadiq Babba Har Dr.Saulawa da Jikokinsa ke kira Alhaji Tsoho yayi mata Lakabi da Nene Uwar Maza Domin Allah ya Doramata Son Haihuwan ya"ya Maza Sai dai kuma Allah bai bata ba Shiyasa,Zain da Sadiq babba Suka koma Tamkar sune ya"yanta Ita kuma Umman Zareena Dama Uwar matace Domin Itama Tafi son ya"ya mata Sai aka Raba kowa yaja Nashi Cikin zaman lafiya da kwanciyar Hankali.
Sadiq Babba nada Shekara Daya da wani Abu Ciki ya Bulla ajikin Maryama Murna Wajen Nene da Umman Zareena Ba"a mgana kamar su Za"ayi ma Haihuwan,Ita kanta Maryaman Tana Farinciki Domin Sosai Take son ganin kwan ta adunya koda Kwara Daya ne,Duk da Su Zareena Sun Debe mata wannan kewan komai Mama Maryama kinga Haddir ko.? Mama maryama Kinga Zain ko..? Mama maryama kin ga Xareena ko..? Aikinta kenan Cikin Rabon Fada da alkalanci.
Tunda Cikinta ya Fito yaran suka Fahimci Tana da Ciki suka kama Murna Kada ma zain yaji labari Domin Tun Sanda yaga Cikin Mama maryama yayi Girma ya Tambayeta ya yaga Cikinta yayi kato ko Bata da lafiya ne..? Lokacin Tana Shashen Su Umman zareena ne Nene ce Ta bashi amsa da Cewa kani za"ayi musu ko kanwa Yana jin Haka ya Bata Rai yace Shi Gaskiya Mata yake so Mama maryama ta Haifamai Kowa sai da yayi mamakin kalaman yaro Dan Shekara Takwas da Wani Abu sai dai Ba Abun mamaki bane sanin Halin manyance irin ta Zain kamar wani Babba Kowa ya Bude Baki Yana kallonsa Sai Mama Maryama Taja Jikinta Tana Fadin"Karka Damu D'ana zain...Nayi maka alkawarin in mace na Haifa Na baka Ita matsayin mata Ko da bana Raye in kuma Namiji ne zan baka shi a matsayin Karamin kani Wanda zai iya ma Yayansa Biyayyah Har karshen Nunfashimsa..!
Kowa ya Dauka kalaman Maryama da Zain amatsayin Wasa ne Har da Alhaji Usman ya Dawo Matansa ke gayamai yana ta Dariya,Ashe a Bangaran Maryama Da Zain ba Haka bane Shi da Gaske yake Cikin yarinta ita kuma Da gaske take Cikin Son Cikamai alkawarin Tana jin Babu Abunda zata mallaka wanda ba zata iya mallaka ma Iyalan Dr.Abubakar Saulawa ba.
Tunda ga Lokacin Komai Zain ya samu sai yace na Matar sane wanda Mama Maryama Zata Haifamai ko makaranta yaje baya kashe kudi wai yana Tarawa zai Siyama Matarsa Babyn Wasa,Komai dai ya Samu ko naci ne sai ya Tsakura yace na Matarsa Wacce Mama maryama Zata Haifamai ne,Tun ana Daukan Abun Wasa Har dai aka Fahimci Zain Da gaske yake Labarin kuma yakai ma Kowa,kowa kuma sai Dariyan Kuruciyar Zain yake da Shirmensa Lokacin da Cikin Maryama ke Wata na Shida Umman Zareena itama ta samu Ciki kuma kusan Lokaci Daya Suka Fara laulayi da Nene Wannan karon ma.
Cikin kwanciyar Hankali Duka Suka Cigaba da Rainon Cikinsu Har Cikin maryama ya Shiga Watan Haihuwarta sai Yayarta Halima tazo akan Tana son Tafiya Da maryama Chan Gida taje ta Haihu ammh Sai Alhaji Usman ya Hana yace Maryama Tamkar kanwa take garesa Saboda Haka anan zata Haihu Karamci Irin nasu yasa Halima Batayi Gaddama ba Ta Tsaya ta kwana Biyu Ranar Datayi Shirin komawa aranar Maryama Tatashi Da naguda aka kwasheta Zuwa asibitin Mallakin Dr Abubakar Saulawa.
Suna zuwa aka karbeta Sai Dakin Haihuwa Duka Gidan aka Tafi Umman Zareena da Nene,Sai Halima da Baba Abdullahi Da Direba Hajiya mama Tana Gida bata Taho ba Sai Dr.Saulawa Wanda Dama yana Cikin asibitin Alhaji Usman Daga baya Yazo Asibitin ganin Har Wajen Yammah Maryama Bata Haihu ba Sai Aka yanke Shawaran yimata aiki Zuwa Lokacin Hajiya Mama ta iso Ita dasu Zain Wadanda Tunda suka Dawo makaranta aka kaisu Wajenta Suke mata kuka Suna ta Kiran Sunayen iyayensu Dana Mama maryama ganin Haka yasa Ta lallashesu Ta Fada musu suyi ma Mama maryama addu"a Tana asibiti zata Haifa musu kani ko kanwa Jin Haka yasa Zareena da Haddir suka Fara Murna Shi kuma Zain sai ya Fara kuka yana Fadin Shi ba kanwa za'a Haifamai ba Mata da kuma kukan sai an kaisa yaga Mama Maryam Dole Hajiya Mama ta Tarkato su suka Taho Tare Duk da Dr.Saulawa Nata Fada ammh ganin yadda Yaran suka Sha kuka ne sai suka bashi Tsausayi.
Cikin Ikon Allah ana Kokarin Saka ahannu akan Takardan da za"ayi ma Maryama aiki Allah ya Sauketa Lafiya Inda ta Samu Haihuwar yarta Mace mai kama da Ita sak,sai Kuma Duhun mahaifinta Data Debo Saboda Maryama Faraace Sosai Sabani Abdullahi Dayake bakin Fata Sai da aka gama gyarata ita da Abunda ta Haifa kana Nurse Ta Fito da Jinjiran a Hannunta Da Halima ta Faracin karo Zata mikamata Zain yayi azamar Mika Mata Hannu yana Fadin Ta bashi matarshi Tsaye Tayi tana kallonsa Cikin Mirmishi Dr.Saulawa yace ta mikamai Tako mikamai ya karba kamar zai Fadi Halima ta tareshi suka koma Suka Zauna kowa ya Kura mishi ido ana kallon yadda ya kurama Jinjiran ido yana kallonta da wani Mirmishi Kafin ya Dago yana kallon Abbansa Cikin Yarinya yace"Abba me sunanta...?
Kafin Alhaji Usman ya bada Amsa Abdullahi ya bashi amsa da Fadin"Maryama Ta gayamin in ta Haifi mace Sunan Yaya Halima Take son asakamata Saboda Haka Alhaji Dakta kayi mata Huduba da HALIMATUS SA"ADIYA..!
Gabadaya Murna Ta kama Halima wacce ya"yanta ke Kiranta Goggo Halima Cikin Jin Dadi Take fadin"Masha Allah..Allah ya Raya Halimatu.."Zain kawai akaji yace"Ba Sunanta Halima ba Abba..Ni Matata irin Sunana gareta..!?
Cikin mamaki Nene tace"Irin Sunanka Da'n Nene..? Wani Suna kenan..?
Cikin Kura ma Jinjiran ido yace"Tunda Sunana ZAIN ita kuma Sunanta ZAINAH daga yau ba Halima ba...Kunga Zainazain kenan..!gabadaya al"ajabi da Mamaki ya kama kowa Dr.Saulawa yana kallon Zain da wani Farinciki acikin Ransa kafin ya Dafa kansa yana Fadin"Allah ya maka albarka...Karka Damu Sunanta Halima ammh Kai mijinta me kuma ka zaba mata Suna ai Shikenan kowa ya Shaida Sunan Matar Zain Zainah ko..?
Yafada yana kallonshi Washe baki yayi yana Daga sai Abun ya basu Dariya Dakyar Dr.Saulawa ya iya karbanta Suka Dunguma Dakin da aka maida Maryama Suka Iske ta Farfado agabanta yayi ma Jinjiran Huduba da Halima ya Dago Yana Fadin"Allah ya Raya Halimatus Sa"adiya..!
Karaf Zain yace"Ba Sunanta Halima ba Sunanta Zainah nace muku..!Maryama ke neman karin Bayani Nene ta Koramata yadda akayi Dariya Tayi Tana Fadin"Gaskiya ne Yarona..Sunan da aka Zabamata yayi Daidai da..Sunanka ina Fatan ko bayan Raina zaku Tabbatar da Halima amatsayin matar Zain..?
Tafada Tana Tsare Duka yan Dakin da Ido Kowa sai yaji Abun Wani iri Baba Abdullahi ne yayi Mirmishi yana Fadin"Kema yarintar Zain din zaki mana..? Kai ta girgiza Tana Fadin"Ba yarinya bace..Ku kalli Idanuwansa Tsabar gaskiyansa yake Fada..Nidai Nayi alkawarin Tun Kafin Ta Fito Duniya na Bama Zain ita amatsayim Mata Har Abada Ko Bayan Raina Abdullahi ka Tayani Sauke nauyin Dana Dauka..!
Kowa adakin Sai da Jikinsa yayi Sanyi Dr.Saulawa ne yace"Karki Damu Maryama...Insha Allahu da kanki zaki Hada Hannun Zain da Halima amatsayin ma"aurata."Wani Sanssayar Miemishi Tayi kafin tace"Allah yasa Ina Fatan Haka.."Daga Haka bata kara cewa komai Suma ba wanda ya kara mgana sai aka koma Raba Rigima Tsakanin Zain da Zareena Inda Take Rigiman sai ta Dauki Halima karama ammh Zain ya Dafe gadon da Maryama ke kai yace bamai Taba mai Mata Tun Abun nashi na basu Dariya Har suka zo suka Tabbatar ma kansu zain Da gaske Acikin Ran Dr.Saulawa kuma yana Ta auna Abubuwa afili ya Furta Haka Allah ke al"amarinshi Daman.
Kwana Daya Maryama Tayi a asibiti Aka sallamota ta koma Gida aka cigaba da karban yan Barka Gabadaya Kulawanta ya koma Karkashin Nene da Umman zareena Duk da suma Suna Fama da kansu Goggo Halima Sai dai kallo Domin ko Tace su barshi Sai suce sai sunyi ai maryama Tamkar kanwa Take garesu Hakama Hajiya Mama Tana iya bakin Kokarinta,Zain kuwa ansha Fama Dashi Domin Tunda akayi Haihuwan sai Ansha Fama Dashi yake zuwa makaranta sai ya Fara kukan Sai dai ya Tafi da ita da Dubara yake Tafiya yana Dawowa kuwa Shashen Maryama yake yada Zango Daga ma Karshe chan ya koma da kwana Saboda Zaina Ba Wanda ya Damu da Hakan Domin Kowa yana ganin Maryama da Mijinta yanzu Suna Cikin Ahalin Dr.Saulawa Tsudum.
Dr.Saulawa da ya"yansa sun ma Maryama kara Sosai Da Abun arziki Sai wanda ya gani Musamman ma Alhaji Usman da Matansa Sunfi kowa Rawan gani Haka da yan Gada suka zo Suna suka koma da Fadan Irin Dimbin karamci da Dattako irin na Iyalan Dr.Saulawa Goggo Halima ma Bayan Suna Ta koma Itama da Sha Tara na arziki Tana Ta Godiya Aka bar Maryama da yarta Halimatu Sa'adiya wacce Taji Tudu Biyu Sunan Goggo Halima kuma Sunan Baba Atine na gaskiya.
Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah Zaina nada Wata Shida Aduniya Nene ta Haifi Yarta mace Wacce taci sunan ZAFEERA bayan Haihuwanta da Kwana Hamsin Ita kuma Umman Zareena ta Sauka Wannan karon ma Namiji ta samu Yaci Sunan Mallam Umar suna Kiransa Faruq,kamar dai yadda Tsarin yake Nene uwar Maza Taja Nata itama Umman zareena Uwar mata taja nata Tunda Lokacin Zareena ta Girma Suna Cikin Shekaru na Goma da Haihuwa sai Tattalin ya koma kan Zafeera Yadda kukasan kwai haka Umman Zareena ke ji da Zafira kamar Tsoka Daya amiya Zain kuwa da karfi Da yaji ya zama Dan Shashen Maryama Saboda zainarsa Reno kuwa Tare sukeyi da Maryama Tun baya Iya Daukanta Har sai da ya iya Haka zai zauna yana ta mata wasa Tun Kafin ta isa Cin Abinci Zain ya Fara bata kayan zaki Ko Iyayen nashi na Fada Maryama Ta kanyi Mirmishi Tace su kyaleshi Mutum da matarsa Saboda Hakama Ta Riga ta ganeshi Da Taji muryansa zata Fara wuntsila kafa Tana Babban Dariya irin na Jarirai yana Daukanta kuma Shikenan Haka zasu yi ta Rigima da Zareena kan sai ya bata ta Dauketa In Kuma akaci Sa"a ya bata Zareena na Daukanta sai ta Fara kuka Sai Zain ya Fara Dariya Haddir dai yana Gefe Shi baima Cika cewa zai Dauka ba Ganin yadda Zain din ya mamaye komai Sai dai yayi tama Zareena Dariya ita kuma Taji Haushi Ta Fara kuka Maryama Ce mai Raba Fada ta kuma Shiga Ciki Tayi alkalanci.
Shekaran Halima Daya da Wattani Maryama ta kara samun Ciki Sai dai kuma yazo da matsala Tunda Tayi ta Ciwo sai da akaje asibiti nan aka gano Tana da Cancer Mahaifa Hankakula Suka Tashi barin ma Abdullahi,Ammh Dr.Saulawa da Alhaji Bashir sukayi Tsaye sai da akayi mata aiki taji Sauki Bayan an Fitar da wanchan Cikin,Dalilin wannan Ciwon sai Dawainiyar Halima Ya koma Hannun Umman Zareena Tunda Allah ya Doramata kaunar Yarinya Ta Hadasu ita da Zafeera Tana Rainonsu Tare Zain na Tayata Domin Dakyar ma ya bari Umman Zareenan ke Daukan Halimar har ta goyata Ganin Mama Maryaman Bata da Lafiya ne Shiyasa.
Bayan Taji Sauki ma Hakan bata Chanza Zani ba sai dai in Tana kuka akaita Maryama Ta bata Nono a maida mata Ita,Cikin ikon Allah ba Dadewa Maryama ta Sake samun Wani Cikin Wannan karon Da Sauki Abun Sun dai koma asibitin anyi Gwaje gwaje aka Tabbatar da Maryama zata iya Haihuwa ba Matsala Da haka tacigaba da Rainon Cikinta Gefe Daya kuma Dawainiyar Halima yana Hannun Umman zareena Cikinta na Shiga wata na Shida Ta Yayeta Ta Damkama Umman Zareena Ita,wacce ake ma Lakabi da mai Rainon Yan Biyu Sakamakon Zafeera akwai Girman Jiki Har ta kamo Zaina a Girma Ita har ta Fara Takawa Halima din ce Take Ta Rarrafe.
Acikin Wannan yanayin ne Wani al"amari ya Faru wanda iyalan Dr.Saulawa suka kasa mantawa Dashi Shine Wata Ranar Asabar da Misalin karfe 2:00pm na Dare yan Fashi Suka Shigo Gidan Alhaji Bashir da Manyan makamai Lokacin da Suka shigo Gidan Abdullahi ya Tashi gaban get ya Shiga Gidan Wajen Maryama Dama Hakan yake yi sai asuba kuma yake Dawowa,Duka ya Kulle get Din Haurowa sukayi suka Shigo kamar Wasa Dama Tunda ya Shiga Ciki bai kwanta ba,Alwala ya Dauro ya Fara Sallar Nafila yakai Raka"a na Biyu yaji motsin Takun