Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Daddyn Abuja ya Sauke Numfashi yana Fadin"Yanzu muka gama mgana Dashi ya Usman Din..Dama na sako mai nganar Zain din kashe wayarsa yayi ya Riga yayi Fushi Dashi ne sosai na kuma Kira Ya Bashir namai mganar Shima ya nuna Ma Ya Usman din yayi Daidai ne bazai saka baki ba..!
Haddir acikin Ransa yace"Daman ai wannan haka zai ce.."Haryanzu bai manta zafin marin Dayayi mai ba Cikin Damuwa yace"Daddy meye Abun yi Kenan..? U hv to do Something fa..'Daddyn Abuja yace"Karka Damu...Muna ta Shiryan Shiryan Dawowa nan Bauchi Dukkanmu gabadaya Har sai an gama Bikin Kanwarka Hamdiya kafin mu koma Insha Allahu i will Tary may Best naga komai ya Daidata kaji ko..?
Ajiyar rai Haddir ya Sauke Kafin yace'"I Truth u Daddy...."Daddyn Abuja yace"Tanque Son..Ina zain din bani shi a waya nayi mgana Dashi..?Haddir yace"Yana Gidansa yanzu haka ina kan Hanyata ta zuwa ne naje na Karbomai Tuwo Gidan Alhaji Tsoho..'"Jinjina kai Daddyn Abuja yayi kafin yace"Alrigh in ka isa Call me Ina son nayi mgana Dashi.."Haddir yace"Ok Daddy..Ka gaida Mom..!
Daga Haka suka yanke Kiran Shi kuma Haddir ya Cigaba da Driving Dinsa Bai jima ba ya isa Gidan yaji Dadin ganin Zain yaji Sauki Har ya sake yin wanka ya Fito Falo Har ya Shiga Kitchen ya Dafa Ruwan Coffea,Haddir ya Nuna Jin Dadinsa Sosai ganin Zain din ya Taahi da kafarsa ba kamar kwana Biyu nan Dayake Wuni Kwance ba Tare sukaci Tuwon Suna santi kafin Haddir ya maida Sauran ya saka Cikin Fridge,Shima irin na Alhaji Tsoho zai yi Dumame kenan Bayan ya wanko Hannu ne ya Dawo ya Kira Dadyn Abuja yabama Zain sukayi mgana Sun Dade yana ta Fada Cikin Hikima da Salama yana kuma Nuna mai Kuskusaransa kana ya bashi Tabbacin zai zo Bauchi bazai koma ba sai komai ya Daidaita Zain nata Godiya yana kuka kafin Wayar nasu ta kare sai alokacin ne Haddir ke Fadamai Sakon Alhaji Tsoho Duk da Zain yaso yaji me ya Faru Dayaje Tahowa da Firstlove..? Ammh sai yaki gayamai komai Illah cemai Da yayi Zareena da Nene na Gaisheshi Cikin mamaki yace"Ashe Har yanzu suna Sona..?
Dariya Haddir yayi yana Fadin"Ai ba"a sauya ka ba..Kanan nan amatsayin Yaya Daktan ka.."Sai da Zain ya Murmusa da kalaman Haddir Cikin Sanyin murya yace"Ya jikin Abba..? Haddir yace"Yaji Sauki Shima.."Daga haka ya yanke mganar ya Dauko wayarsa ya Fara Latsawa Shi kuma Zain ya koma ya Jingina da Kujera ya Fada Zurfin Tunani yana so ya Tambayeshi Zaina kuma sai ya kasa Domin baya so yaji wani Labari mara Dadi akanta,Shiyasa yayi Shuru da bakinsa Ammh Abun nacin Ransa da Zuciyarsa..
*****
Washegari kuma Tun Wajen karfe 10am na Safe Zareena da Zainab da Little Umma da Jalal suka zo Gidan Zain sun iskeshi Shi kadai Haddir baya nan ya Fita Zuwa Cikin asibiti,Yaji Dadi da kuma mamakin ganinsu Domin bai taba tsammanin Wani Daga Ahalinsa zai zo Dubashi ba Karban Little Umma yayi yana Kallon Zareena yana Fadin"Ammh Abba bai san kun zo ba ko..?
Kai ta gyada mai Tana Fadin"Bai sani ba..Gidan Alhaji Tsoho nace zani..Umma ma bata sani ba Nene ce kadai ta sani tace na Gaisheka kwarai ita tabamu ma wannan Ferfesun Kayan Cikin Tace mu kawo maka.."Idanuwansa suka Ciko da kwallah yabi kulan Dake Hannun zainab da kallo kafin yace"Allah Sarki Neneta..Na Saka Zuciyarta Ta Raunana saboda ni..Allah na Tuba Allah ka yafemin.."Suma cikin Tsausayawa sukace Ameen Jalal ne ya Hau gadon yana Fadin"Uncle baka da lafiya ne..?
Kumatunsa ya Shafa yana Fadin'"Eh Sojan Jaawad...Ina Babanka.? Zareena ne tace"Yana katsina ya samu Hutu ne...Daman kuma akwai Bikin Diyar yayarsa Jibi ma zai zo yaDaukemu mu Tafi Chan Family House dinsu sai an gama Biki zamu dawo insha Allahu.."Yana Mika mata little Umma yana Fadin"Allah ya kaimu ya kuma kaiku lafiya.."
Ta amsa da Ameen Shuru ya Biyo Baya Kafin ya Dago yana Fadin"Ya Firstlove take..? Tabar yin kukan...?
Zareena tace"Tadai Sauki kam..Nadai jita dazu ita da Umma Tana ta yi mata Fada kamar zata Dageta kan Kukan Da takeyi..'Cikin karaya da wani Irin Soyayyarta Dake Cikin Zuciyarta yace"Bazan iya kwana ban je na ganta ba.."Da Sauri Zareena tace"Ya zakayi da Abba..? Umma ma bazata barka ka ganta ba Domin Jiya marin Aboki Haddir ne kadai batayi ba kan yace yazo Tafiya da ita.."
Ido ya sakarmata yana Fadin"I know.."Yafada Cikin wata Murya Kamar yayi kuka kafin yace"Zan je koda zai Koreni ne..Zan je na Duka na Bashi Hakuri..Shi da Umma na kuma Dukama Firstlove na kuma Roketa Data Yafemim.."Zareena Tace"Shikenan ammh karka kaje kai Kadai..Ku Tafi Tare da Aboki Haddir.."
Kai ya gyada mata yana Fadin"Eh Tare zamu..Yanzu ma Shi nake jira zamu je gidan Alhaji Tsoho yace yana son ganina Ko bama Haka ba ni da kaina Zani Shima na Rokeshi Gafaran Abunda na aikata da kuma Kuncin dana sakasu Shi da Hajiya Mama..'Cikin Sanyin Murya Zareena tace"Ya kamata..Allah daidaita komai.."
Ya amsa da Ameen basu wani Dade ba suka wuce Zasu Biya School su kai Zainab Da Zareena Ta Fadamai haka ne ya Kalli Zainab yana Fadin"Zee Kun Fara Test ne...? Kai ta Girgiza mai kafin tace"Bamu Fara ba mu..Ammh wasu Duk sun Fara Yaya Dakta ina Jin ma Harda su Anty Zaina Domin na Hadu da kawarta Anty Laila take cemin yanzu zasu Shiga Test ne.."
Cikin Karfin Gwiwa yace"Dole zan je na Roki Firstlove gafara..Na Dawo da ita Gida ta koma makaranta bazan yi Sanadiyar Ruguza Burinta nayin karatu mai Zurfi ba.
******
Su Zareena basu kai awa da Tafiya ba sai ga Haddir ya Dawo Daman Zain ya Riga ya Shirya Cikin Riga da wando na Wata Blue Din Shadda Fitowa kawai yayi suka Wuce,Suna Hanya ne Haddir ya juyo yana kallonsa yadda Duk yayi Zuru Zuru ga Kasumba Tayi mai yawa Cikin Damuwa yace"Ko zamu Biya Shagon aski ne ka Rage wannan Gashin..?
Kai kawai Zain ya Girgiza kafin yace"Bashi ne agabana ba Haddir...Muje gidaanmu Dagachan sai mu wuce Gidan Alhaji Tsohon
Da Sauri Haddir ya kalleshi kafin yace""A"a ba yanzu ba Zain..Abba nacikin Fushi bazai Saurareka ba.."Zain Cikin Takaichi yace"Banga Laifinsa ba..Ko Bazai Saurareni ba Zanje na Duka na nemi gafaransa Koda zai min Koran karene..'
Haddir zai yi mgana Zain ya Dagamai Hannu yana Fadin"Komai ya Faru ninaja..Abaya Abba yamin haka..? Amsa ita ce A'a Saboda Naji na Dauka zan Tunkarin wannan Yakin Insha Allahu da Tsarkakken Zuciya Allah na Tuba ka yafemin.."Yafada yana Jin Taruwar kwallah acikin Idanuwansa Haddir bai kara mgana ba yayi Shuru yana Fatan in sun isa Allah ya Kwantar da Zuciyar Abba.
Allah kam bai amshi Addu"an Haddir ba Domin Suna Shiga Falon suka ci karo da Umma da Nene,Dukkansu Mikewa sukayi suna Bin Zain da ya Shigo abayan Haddir da kallo Cikin wani yanayi Umma kallonsa Take Tundaga sama Har kasa ganin yadda ya Sauya Cikin kwana Uku kachal,Nene kuwa Har ta Fara Hawaye ganin yadda yayi wani Baki ya Rame kamar bashi ba Cikin Dimuwa da Tsausayi ta Nufeshi Tana Fadin"Zain...!
Bata karisa Gareshi ba Shima ya Taho da Sauri Zuwa gareta Da Murnan ya samu kafadan da zai Kwanta yayi kuka Yaji Muryan Abba yana Fadin"Kul...Aisha karki Sake ki karisa kusa Dashi..Kinji ma nagaya miki..!
Yafada Cikin Kakkausan Murya,Gabadayansu suka waiga suna kallonsa yana Tsaye Daga Gaban Korodon Dakinsa Cikin Bakar Jallabiya Shi kanshi ya Rame din ganinsa yasa Zain ya Zura mai ido yana Jin Tahowar kwallah Cikin idanuwansa cikin Takun Rauni ya Fara Taku Zuwa gareshi Sai dai mai Cikin Tsawa Abba yace"Kul..Karka kuskura ka kara somin nan...Bana son ganinka..!
Yafada Cikin Tsawa da Fushi Wanda Harta Zaina Dake kwance Ta Fara Barci Ta jita Ta tsshi afirgice Tana Raba ido Shi kuwa Zain Cak ya Tsaya Idanuwansa Sun Fara Zubda da kwallah Cikin Raunin murya yace"A...Abb...!
"karka ka kara Kirana da wannan Sunan Kirani kai Tsaye da Usman Dina zai fin Dadi da naji kana Kira da Sunan Ubanka Zainullahi."Ya fada bayan ya Tarema Zain din Numfashi,Yanayin yadda yake mgana zaka Fahimci Ransa kuna yake Domin Shi kanshi Idanuwansa sun kala sun yi Ja Cikin Sagewa Gwiwa Zain yaji Kafafunsa sun kaisa kasa ya Zube Bisa Gwiwoyinsa yana kuka kuka mai Cin ran Mai Sauraro Cikin Fada Abba ke Fadin"Wama ya baka izinin Shogomin Gida...?baka ji Sakona bane..? Na sallama maka na Nace ka Tafi Chan ka zauna da karuwarka Dadironka Domin Ita ce Rayuwarku ta Dace da Juna bamu ba..!
Yafada Jijiyoyin kansa na Mikewa yana Numfarfashi Da Sauri Haddir yace"Abba kayi Shuru hakanan Saboda lafiyarka.."Abba ya juya kallonsa kan Haddir yana Fadin"Kai da ka damu da lafiyata..Toh in kana so nayi Shuru kace ya Tashi ya Fitarmin Daga Gidana Tunda bada Kwabonsa aciki na Siya Gidan ba.."
Jin haka yasa Zain ya Fara Rawan baki yana Fadin"Zan...Zan Fita Abba ammh sai na Rokeka Gafara..Don Allah Abba Don Annabi ba Domin Halina da Tarin Laifuka na ba..Ka yafemin Wkh Abba na Tuba bazan kara ba Na Tuba nabi Allah Abba bazan kara ba..."yake fada yana wani kuka mai Cin rai Nene da Gudu ta karisa Kusa Dashi itama ta Zube Cikin kuka Take Fadin"Don Allah kayi Hakuri Alhaji ka yafemai..Shifa Bawa ne kuma Bawa zai iya aikata Kowani irin Laifi Alhaji Don Allah karka Koresa Daga Gidanka in ka koresa ina zashi..?...
Itama Ta Fada Cikin kuka Ganin Haka yasa Haddir ma ya Isa Kusa da Zain Shima ya Duka yana Fadin"Don Allah Abba kayi Hakuri..ZAIN yayi Laifi kuma ya Gane Kuskuransa Don Allah Abba ka yafemai.."Umma Dake Tsaye Kai kawai ta Kauda Tana kuka Zaina kuma Dake Kofar Dakinsu k'asa Kasa Daukanta Tayi Sai da Ta Jingina da Bango tana wani kuka mai Cin rai Lokaci Daya Da Tushe Bakinta kada Kukanta Ya Fito.
Abba kuwa kai ya kauda Cikin Tsawa yace"Ya tashi ya Fice Daga Gidana nace..? Zan kira mai Jami"an Tsaro Wlh in bai Fita ba."Ganin Zain Bashi da Niyyar Tashi ne yasa kawai ya Fara Laluban wayarsa Dake Aljihun Jallabiyansa Ya Zarota Ya Fara Kokarin Kiran waya Nene da Haddir sun ma kasa Mikewa Ballatana Zain da kansa ke Duke ya Hada Hannayensa alaman Roko Idanuwansa na Zubar da kwallah
.
Cikin Bazata Suka Ji Abba ya Daga waya yana Fadin"Dpo....!Bai Karisa ba,ZAINA ta bayyana Afalon Tana Dingishi Lokaci Daya Tana Dafa bango Tana Fadin"A'a ABBA...DON ALLAH KADA KA KIRAMA DA'N DA KA HAIFA DA CIKINKA YAN S A.N.D.A..'Tafada Cikin Rarrabe mganarta Saboda kuka Cak Abba ya Tsaya da mganar Da yake yi ganin Zaina wanda Ya kwana Biyu bai sakata a ido ba.
Haka ma Zain Cak Kukansa ya Tsaya Nene da Haddir ma suka Dago suna kallonta Haka ma Umma Ganin Abba ya Tsaya ne yasa Zaina ta isa Gabansa ta Zube Tana kuka Tana Fadin"A"a Abba Hakan bai kamata ba...Duka Abun na Cikin Gida ne Don Allah kayi Hakuri kada ka Koreshi Daga Gidanka Da jikinka Gabadaya..!
Tsura mata ido Abba yayi Cikin Tsausayamata yana Ganin itace ma Abun Tsausayi Wayarsa ya kashe ya maida aljihun gaban Jallabiyansa Ya Saka Duka Hannunsa ya Tallabo kafadunta Ya saka Kuma Hannunsa Duka Biyun ya Daukemata Duka Hawayenta Yana Fadin"Naji bazan kiramai Jami"an Tsaro ba..Ammh ya Tashi ya barnin gida..!
Zatayi mgana ya Hanata Da Daga mata Hannu Lokaci Daya Ya Kai kallonsa ga Zain wanda ya Kura musu Ido Shi da Zaina wacce yake jin kamar yaje ya Rumgume Zaina ya Fashe mata da kuka Ta Fahimci Nadamarsa Da Yadda yayi kewarta.
Cikin Kakkausan Murya Abba ya kalli Zain yana Fadin"Wlh Tallahi Ko Saboda Cutar da wannan Marainyar Allah da kayi Zainullahi Allah bazai barka ba..Kuma nima bazan Taba yafe MAKA BA...!!!
Kowa Abba yabi da kallo Wanda ya Juya yana Tafiya Yana Fadin"Aisha Ki gayama Dan'ki ya Fita yabarmin gidana..In na kara Fitowa na ganta Abun bazai mana kyau ba.."
Ya Fadin haka ya Shige Dakinsa ya Banko Kofarsa,Kawai sai Zaina Ta Sulale nan ta Fashe da kuka Zuciyarta na wani Rawa Saboda ita Abba bazai yafe ma Zain ba..? Ta Shiga uku Kar tayi Sanadiyar Raba D'a Da Mahaifinsa..? Ina zata saka kanta In haka ta Faru..?
Zain Da ya Fara Rarrafe kamar karamin yaro yana kuka zuwa ga Zaina sai da Taji kawai Numfashin Mutum Gabda da Ita Tana Dago Fuskarta Datayi Jabe Jabe da Majina Da Hawaye suka Hada Ido Hudu, da Zain Kowa tsayawa yayi yana Kallon Kowa..Kuma kowa da Abunda Yake Sakawaa cikin Ransa,Yana kallonta yana Zubar kwallah itama Tana kallonsa Hawayenta na Bulbulowa kamar an Bude Famfo.
*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣4️⃣
"Ita Zaina Tana Kallonsa ne Da Dukkan Zuciyarta Mai cike da Soyayyarsa Kaunarsa da Kuma Tarin Tsausayinsa da kuma yardansa Idanuwanta na Fidda Hawayen karaya da Rauni Ganin yadda ya Rame ya Fita Hayyacinsa Cikin kwana Uku Kachal.
Shi kuma ZAIN yana kallonta ne Cikin Raunin Zuciya,Karaya da Ban Hakuri da kuma Soyayyah da kaunarta Hade da Tarin Tsausayinta ganin yadda ta koma Kamar wacce bata da Ishashan Jini ajikinta,Gabadaya Jikinsa Rawa yake wajen Saka Hannunsa ya Riko Nata Hannu Cikin Rawan baki Dana Murya ya Furta..
"FI...rsT....LO..ve...'Ya fada Gabadaya Jikinsa na Daukan Rawa Dukkansu sai da Zukatansu suka amsa Cikin Fitan Hayyaci da wani irin Muradi mai Girma da kuma Nenan sauki da Waraka ga Halin Dayake Ciki Taji ya afka Jikinta kawai ya Rumgumeta da wani irin karfi Wanda ba Domin Ta saka Dayan Hannunta ta Tallafe kasan Cafet din ba babu Abunda zai Hanata batayi Bayaba ya Bita sun baje atsakar Falon ba Saboda Tsabar irin Karfin Rumguman Da yayi mata.
Da karfi ya matseta Har sai Da Taji bata iya Fitar da Numfashi,Kansa yake Tusawa Saman Kirjinta Lokaci Daya yana sakar mata wani marayan kuka wanda Sai ya Tada Hankalin Mai Imani Nene da Haddir kuwa Wani irin Abu Suke ji akansa Ransu na Tsausayin Duka Zain din da Zaina,Ita kuma Umma Kuka take kawai Batare ma Da tasan kukan Me take yi ita ba,ta dai sani Zain ya kasanace mafi soyuwa acikin Ranta Tun yana karaminsa Bata iya Juran kukansa Sai dai ta Boye ko kuma ta kauda kai Saboda Nene.
Jin yadda yake kukan ne yasa Raunin Zaina ya kara Bayyana Cikin Wani irin azama ta Dago Hannunta zata Rumgumeshi,Sai kuma ta Fasa Domin Alokacin Hotunan Zain da Dina ne Cikin yanayin Da ita kadai ta sanshi yake Gilma mata Gefe guda kuma Tana Tuno mganarsa na Yarda da cewa Cikin Jikin Dina nashi ne da Sauran mganganu,Gabadaya Jikinta ya Fara karkarwa Cikin Sarewa Da Duk wata yarda da Tsausayi kawai Ta Janye Hannunta Lokaci Daya ta Fara ja da baya Tana Kokarim kwace Jikinta,Ganin Tana Mutsu mutsun kwace kanta ne yasa ya Dago Da kansa Fuskarsa Duk Ta baci Da hawaye yana kallonta Itama Shi Take kallo Cikin mamaki yaga tana ja da baya Hannu ya mika zai Rikota da Sauri Ta kara matsawa Baki ya Bude yana Fadin"Firstlove...!
Kai ta girgiza mai Tana Fitar da kwallah,Sai kuma ta Fashe da kuka kawai Tana Girgiza mai kai tama kasa Mgana Zain ya Duka Hannu Bibbiyu ya Riko Kafar zaina yana kuka yana Fadin"Firstlove...Matata Farincikina...Halimatu Abdullahi Gada..My Firstlove my World,Kece Rayuwata Zaina In baaki bazan iya Rayuwa ba..Naji na yarda naci amanar Soyayyarmu naci Amanar yardan Da kikamin ki Taimakeni ko ki kara bani Dama ta Karshe Don Allah..Ni zainullahi Abubakar Saulawa nayi Miki Alkawarin bazan kara Dabi"ata ta neman mata ba,ammh Plz Don"t Leave me i Can"t do Without u..!
Ya karishe Fada yana Kife kansa Jikin Kafanta yana kuka,Itama kukan Take Lokacin Har Jikinta ya Fara wani irin Tsuma Umma ce Ta Lura da haka da Sauri Ta Share Hawayenta ta isa Garesu Cikin Fushi ta saka Hannu ta Fizgo Zaina ta Mikar da ita tsaye wanda yasa Zain ya Dago Idanuwansa Jajir yana Kallonta Cikin kaifin Idanuwan Uwa da Danta Take kallonsa Shima haka Cikin Karaya yace"Ummmaa..!
Kai ta kauda Kafin Ta Kama Hannun Zaina kawai ta Nufi Hanyar dakinta da ita Cikin Murya wacce ba Sauti yace"Don Allah Umma ki yafemin...Ki yafemin ki bani Matata itace Rayuwata.."Cak Umma ta Tsaya sai kuma kawai ta Cigaba da Tafiya Har gadon Ta kai Zaina ta Zaunar da ita ganin Tana Neman Shidewa ne Saboda Kuka yasa Ta Zura mata ido Cikin Takaichinta Tana Fadin"Ko Na barki zaki Bishi ne..?
Da Sauri Ta Girgiza kai Cikim Kuka kwafa Umma Tayi Tana Fadin"Toh ki kiyayeni Da min wannan kukan mara amfani..."Daga Haka kawai ta Fice Daga Dakin Harda Turo mata Kofa kan gado kawai Zaina ta Malale tana Sakin kukanta Zuciyarta ta Kasu kashi Biyu ne na Farko Kaunar Zain da Tsausayinsa na Biyu kuma Kishinsa da kuma Bakinciki Wanda yaki barinta Ta Kalleshi Lokacin Dayake kuka yana Rokonta Gafara.
Umma kuwa Falon Ta koma ta Iske Nene Rumgume da Zain yana kuka Tana Lallashinsa Mirmishi Takaichi Tayi kafin tace"Nene ki gayama D'anki...Ba yata bace Rayuwarsa wannan Dadarion nasa Uwar Dansa ko yarsa itace Rayuwarsa Ita zai je ya Dauko tamai Duk Abunda Mata kema mijinta Dama ai sun saba.."Daga Haka kawai ta kada kai Zuwa Dakinta Zuciyarta kamar Tayi Bindiga in ta Tuna da Abun kunyar da zain ya Jawo musu.
Zain ya gama Sarewa da almarin Umma cikin Karaya da Zubar kwallah ya Dago yana kallon Nene Lokaci Daya yana Fadin"Nene Umma ta Tsane ne kamar yadda Abba ya Tsaneni.."Kansa ta Shafa Tana Fadin"A"a kadaina Fadin Haka ka Tabajin Inda Uwa ta Tsani Abunda Ta Haifa da Cikinta?ko kuma Uban daya Tsani Dan sa wanda ya kasance mafi Soyuwa Garesa..?
Da Sauri Zain yace"Nene yana Faruwa..Tun Ballatana Yaron in ya kasance yayi watsi da Tarbiyan da suka bashi da yardansu..."Yafada Yana Runtse Idanuwansa Cikin Kunar Zuciya Kansa Nene Ta Shafa Cikin Son Kwantar mai da Hankali tace"Ko Daya..Koda Ya kasance Haka yarona zasu mai afuwa Domin Shima Dan adam ne wanda Baya Wuce Kuskuransa..Basu Tsaneka ba Bacin Rai zai sakesu Lokaci Kadan Insha Allahu kaji ko..?
Kura mata ido Cikin Samun Salama da kalamanta yace"Zasu yafemin Nene..? Kema zaki iya yafemin Abunda na aikata gareku naja muku Abun kunya Nene ni kaina ina Jin kunyar kaina da Abunda na aikata ."Yafada yana kokarin Durkusa mata da Sauri ta Dagoshi Tana Fadin"Basai ka Dukamin ba Ni Dama uwace mai afuwa gareka ammh kuma mai Kokarin Doraka hanyar gyara..?Meyasa ka zabi Yin Tarayyah da matar da ba taka ba yarona..? Wannan Dabi"ar Ba ita na Koya maka Tun kana karami na Karantar dakai Kallonka iya Halas Dinka ne ba Haram ba yarona.."Cikin