Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
suka ci karo ta Riko Zaina sun Fito daga Tiolet kamar Wanka Ta Taimaka mata Tayi da alwala Tunda dai Wasu masallatan Har sun Fara Kiran Sallar mngariba.
Atare Umma da Zaina suka kai Dubansu kan Haddir da Nene Cikin mamaki Umma ke binsu da kallo har suka kariso Cikin Dakin,Haddir ne ya Fara gaisheta Cikin ladabinsa Lokaci Daya yana karema Zaina kallo ganin Tayi wani Fari fayaut kamar bata da jini ajiki kuma Ta Rame bakinta ya Bushe akallon Farko sai yaga kamar Tayi wani Danye Danye kamar wata mai Shigar Sabon Ciki Ita kuma Sau Daya Ta kalleshi kawai ta kauda kai kan Gado Umma ta zaunar da Ita Tana Fadin"Zauna ki Huta kafin ki shafa mai ki saka kaya sai kiyi sallah kici Abinci ko..?
Kallon Umma kawai Tayi batare Da Tayimgana ba Umma ta maida Hankalinta kan Haddir tana amsa gaisuwansa Nene ta kalli Zaina Tana Fadin"Sannu Halima Ya Karjin Jikin..?
Bata amsa ba illah kanta Data maida kasa Daman bata saka Rai zata amsata ba Domin Tunda Abun nan ya Faru Bazata ce taji mganar Zaina ba ko sau Daya ba sai dai in da Ummanta,Umma ce ta kalli Nene Tana Fadin"jikin nata da Sauki ba zazzabi sai dai Rashin karfin Jiki Shi kuma wannan Rashin Cin Abinci ne Tunda ko Taci sai ta amayar dashi..?
Nene tace"Toh yanaga Idanuwanta sun kumbura ne bata bar kukan bane..? Umma ta Rausayar Dakai Tana Kokarin Daukan man Vaseline saman Madubin Dake dakin Tace"Bata bari ba..Kuma Harda ma da Rashin barci Da Rana tana samu tayi kadan ammh Da Daddare bata barci Kwana Take kuka.."
Umma Ta Fada Fuskarta na Sauyawa Haddir ne ya sauke Numfashi yana Fadin"Allah ya Sauwake ya kamata Taga Likita Gaskiya.."Umma tace"Bata so..Bazata asibiti ba tace..Ni kuma bana som matsamata Na kyaleta Ko Taje asibiti Basu da mganin Damuwarta Hadiru.."
Haddir yace"Hakane Umma..Ammh Kuka ma da Amai Da Rashin barci ai Wata Cutan ne na Dabam ko..?Umma batayi mgana ba illah mika ma Zaina Man Data Dauko mata Datayi wacce ke sanye da Hijabi Dogo na wajen zainab ne Umma ta Dauko mata Karba Tayi Ita kuma Umma tace"Ki shafa.."
Haddir ne yaga Umma na Shirin Shiga Tiolet yace da Sauri"Umma wajenki fa nazo.."Dakatawa Umma Tayi Ta waigo Tana kallonshi kafin tace"Wajena kuma..? Allah sa lafiya..?
Haddir yana kallon Zaina wacce Ta Dago Tana kallonsa da Rinannun Idanuwanta yace"Lafiya lau..Dama mganar Zaina ce Umma"
Umma Ta Juyowa Gabadaya Tana Fadin"Ina Jinka.."Tafada Tana kallon Nene wacce ta marairaice mata Tun Daganan Ta gano Inda suka Dosa Sai dai bara Ta katse musu Hanzari ba gwara Taji Daga bakinsu lalle zasu ga Fushinta nan take kuwa.
Idanuwan Umma sun ma Haddir kaifi ya kasa mgana sai da ya Sunkuyar dakai kana ya iya Fadin"Dama..Dama..Umma mganar Komawar Zaina Gidan Mijinta ne kinga Zain yanachan kwance ba lafiya kuma Yana Bukatarta ayanzu gaskiya.."
Har ya gama mganarsa Umma na Jifansa da wani kallo na lalle nema kun Raina mutane Zaina kuwa Tun mganar Haddir Taji Dan Jinin Jikinta ya Daina Gudu Bata Sha"awar kara ganin Ya zain ma Ita acikin Idanuwanta ammh akasan Ranta Tsausayinsa Sonsa Sun Hanata Sukuni Kamar Daga sama Taji Umma na Fadin"Ok Shi ya aiko ka kenan...? Shine kuma Da zaka zo Fada ka Dauko Uwarsa kuka zo Tare ko..?
Nene tace"Eh yazo yagamin komai..Nace yazo muje mu Taru mu Roke ki Umman Zareena Hannunka fa baya Taba Zama Cuta gareka,Bamu da yarda zamu yi da wannan kaddaran kuma Hana Zain matarsa kamar kara Tabarbara komai ne,ki barta ta koma Gidan Mijinta Suyi Jinyan Juna Ya bata Hakuri sai Kiga komai ya Daidaita.."
Umma Ta Tsuke Fuska Tana Fadin"lalle nema..Wato yanzu ne Take da kima da Daraja acikin Idanuwansa ko..? To kaje ka Fadamai Wlh Tallahi kunji Rantsuwan Musulmai yata bazata Je ko"ina ba.."
Daga Haddir Har Nene kasa Mgana sukayi jin Umma ta Rantse,Cikin Jan karamin Tsaki Umma tace"Ina Dadiron nashi ko nace karuwan nashi Da bai Kirata tazo Tayi Jinyarsa ba Ko nace Uwar Shegen nashi..? Sai yata Zata Dinga Wahala kansa ko..? Hadiru ka Fita idona karka kara Zuwarmin da wannan mganar Banzan Daga kai har Uwarsa Wacce bazata ga Illah Da Abun Tir din da D'anta ya aikata ba.."
Tafada Cikin Bacin rai Da Sauri Haddir ya Rankwafa yana Fadin"Don Allah Umma..Ko Sau Daya ki bani Dama nayi mgana Da zaina kila ita ta Fahimceni.."Kamar Umma zata mareshi Haka ta taso mai Tana Fadin"Anki abaka Daman..? Nace an ki abaka daman..? Ba inda Zata ka wuce ka bamu waje kafin Raina ya baci Na Tsinke ka da mari Hadiru.."
Jin Haka yasa bai yi gaddama ba ya Juya yana Fadin"Allah Huci Zuciyarki Ummah.."Da Sauri Tace"Ameen.."Nene bata ma yi mgana ba ta kada kai ta Juya Tabi Bayan Haddir kawai Umma Ta Rakasu da Harara Tana Fadin"Kaji min iskancin banza iskancin Wofi..Wani wai Ta koma Gidan Mijinta..? wato ta koma Taje Chan ta Cigaba da zama Dashi karshenta ya Auri Karuwarsa Tasa tazo Tana Tayasu Renon Shegen nasu Rayuwarta Ta kare Cikin Bakinciki Wlh bazata sabu ba indai ina Numfashi Halima Ta bar Auran Zain har Abada.."
Zaina Dake zaune bata san Sadda Karshen kalmar Umma ta saka Kukanta Fitowa ba Cikin wani Takaichi Umma ta Isa Gareta Tana Fadin"Rufemin baki Sakara mara wayau...Ana Neman yadda Zaki Rayu Cikin salama kina ma wanda ya ci Amanar zaman tare da irin Soyayyar da kika nuna mai kuka..? Ki Min Shuru yanzu ko na Kikkifa miki Mari yanzu yanzu nan.."
Jin yadda Umma ke Sababi ne yasa Zaina Tayi gum da bakinta bata kara Bari kukanta ya Fito ba ma Ta Dinga Hadiyeshi Tana Sauke ajiyar Zuciya kamar wata karamar yarinyar da Uwarta Ta Tsigeta Tana Cikin Shan Nono Tsaki Umma Taja ta Nufi Hanyar Tiolet tana Fadin"Kafin na Fito ki Saka kaya ki Tada Sallah in kina so mu Shirya.."
Da Sauri tace"Toh Umma."Tana Kokarin Goge Hawayenta da Danne kukanta Sai Lokacin Umma Taji Tsausayinta ammh kuma Dole ne tayi mata haka In ba Haka ba Haka Zatayi ta zama Cikim Kuncin zuciya har wani Cutan ta kamata Kofar bayin ta Bude ta Shiga Ta bar zaina na Kokarin Mikewa Lokaci Daya tana saka Hannu tana Danne bakinta kada kukanta ya Fito Umma Taji ta Fito taci kaniyarta.
_Godiya Ta musamman ga Dimbin Masoyan ZAINAZAIN,Ina ganin Tarin Sharhinku da Comments Dinku Musamman yan Group din ZAINAZAIN 1&2 ,da Gidajen Janafty Shakira,Duka ina gani Kuma ina Jin Dadi Sosai kuke sakani Nishadi Kuyi hakuri bana samun Lokacin Maida muku martani Abubuwan ne sai a Hankali ammh ina gani kuma ina Godiya Da ku da yan Wattpadians Fans dina suma Ina ganin Sharhinsu Alhamdullahi kawai Zance Allah ya bar Zumunci Ameen..!_
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣3️⃣
"Haddir ne kan gaba Nene na Biye Dashi Zuwa Falo,Zareena na ganinsu Fuska ba walwala Tasan ba"a Dace ba Domin Taga Umma Ta Dauki Fushi Sosai kuma Bata ma da Niyar Barin Zaina Ta koma Gidan Mijinta a Take takenta Datake gani.
Cikin Kallonsu Tace"Ba"a Dace ba ko..? Nene ce ta zauna Gefenta Tana Fadin"taki ma Sauraranmu...Naga Bacin rai naga Tsausayi na Soyayyah da Jinkai duka acikin Idanuwanta na Farko Tana Tsausayin Zain Tana kuma Tsausayin Halima Tana kuma Jinta kamar yarta Data Haifa Da Cikinta,Wannan Dalilin yasa Ta nuna bacin Ranta Sosai wanda ban Taba gani ba.."
Nene Ta Fada Cikin karaya,Zareena Tace"Hm...Allah ya kyauta nagaba.."Haddir ya amsa da Ameen yana Fadin"Bari naje na samu Alhaji Tsoho muyi mgana in anci Sa"a ya saka Baki mgana Ta kare.."Nene tace"Shima din bana Jin zai ce wani Abu awannan Lokacin Hadiru.."Haddir yace"Zan Jaraba Dai na gani yadda mukayi Dashi ko ban Daawo ba zan Kiraki awaya na Shaida Miki.."
Nene tace"Shikenan..Sai na Jika.."Zareena kuma tace"Ka gaida Zain din sai nazo.."ya waiwayo yana Fadin''Ke ina zaki da Daddaran nan..? Baki bari sai gobe..?
Nene tace"Nima Abunda na gayamata kenan.."Jin Haka yasa Zareena tace,"Shikenan bari na Bari sai goben Dama zan Jira in Zainab Ta Dawo Daga makaranta Direban Abba ya kaimu ne ammh Bari dai na bari sai gobe da safen.."Haddir ya wuce yana Fadin"Yadai kamata kam...Ni na wuce.."Suka Rakashi da Allah kiyaye Hanya.
Yana Fita Haraban Gidan yaci karo da Zainab Ta Dawo Daga Makaranta Cikin Ladabi Ta Ramkwafa Tana gaisheshi ya amsa Sama sama ya Fada Motarsa ya Fice Daga Gidan Ta Bishi Da kallo Bata samu Fuska bane Taso Ta Tambayeshi Ya Ya Dakta yake ne..? Sai dai baima saki Fuskan ba Ballatana ta Tambayeshi Tana Shirin Shiga Cikin Gida ne sai ga Motan Abba ta Dawo Daga Dauko su Saudart Daga Islamiya bata ba Tsaya ba Taja Jakarta Ta Nufi Cikin Gida Domin yau din agajiye ta Dawo Wuni Tayi Cikin Makaranta Suna Kokarin Fara Test din Zangon Karatunsu na Farko ne.
Haddir kafin ya isa gidan Alhaji Tsoho sai da ya Tsaya masallacin Kusa da Gidan yayi Sallar mangariba kana ya karisa,Alhaji Tsoho Na cikin Dakinsa saman Kujeransa yana Karatun wani katon Littafi da Siririn Gilashinshi mai kara mai karfin gani,Gabansa Haddir ya Zube bayan sun gaisa Ya Shiga Rarrafomai Abunda ke Tafe Dashi na game da Fushin da su Abba suke da Zain da kuma Halin Da yake ciki da kuma Yadda sukayi da Umma yau din..
Har ya kamallah maganganunsa Alhaji Tsoho na kallonsa bai ce komai ba,Ganin Alhaji Tsoho yayi Shuru ne yasa Haddir yace"Nazo na gayamaka ne Tsoho Saboda ka saka baki Abba ya Janye wannan Fushin Da yakeyi Ko Zain zai ga Daidai Arayuwarsa..Umma kuma ka mata Mgana Ta bashi matarsa Tunda dai mai afkuwa ta Riga ta afku Sai dai muyi kokarin kada Hakan ya kara Faruwa..!
Mirmishi Alhaji Tsoho ya saki kafin ya Ijiye littafin Hannunsa Saman wani karamin Tebur Dake gabansa Lokaci Daya Yana Fadin"Toh ni yanzu da kazo kana Gayamin me kake so nayi maka..?
Cikin Mamaki Haddir yace"me nake so..?kaifa Tsohon nan ka iya Nuna ma Mutane Boko fa..? Ai nayi maka Bayanin komai.."Dariya Ta kama Alhaji Tsoho wanda Tun Faruwar Al"amarin nan bai yi Dariya Haka ba baki Sake Haddir ke kallonsa kafin ya koma kawaai ya Hade Ransa sai da Alhaji Tsoho yayi Dariyansa Son Ransa kana yace"Yaro yaro ne...Yaro Man kaza bai san Wuta ba sai ya Taka.."
Cikin Haushi Haddir yace'"Ammh dai bani kake Nufin yaro man kazan ba ko..?Alhaji Tsoho yace"A"a Ba da kai nake ba...Karin mganace tamu ta Hausawa.."Yafada yana Dariya Lokaci Daya yana Daga Hannu Alaman yayi saranda Mirmishin Lebe kawai ya saki Yana kallon Alhaji Tsoho Daman ya sani Alhaji Tsoho so yake ya Hukuntashi Shida Zain alokaci Daya.
Ganin yadda Haddir din yasha Kunu ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakata da Dariyan Dayake ya Fuskanci Haddir yana Fadin"Kasan abunda kai baka Fahimta ba Hadiru..!? Bai bashi Zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Duk Cikin ya"yana Usmanu Yafi kowa Hakuri da kawaici Sai Mahaifinka Aliyu..Sai Rukayytu..Dama masu Zafin Da Zuciya Sai Babana da Hannatu uwata Daman kuma so Gado sukayi wajen Uwarsu Amina ka gantanan nayi Fama da Ita Tun Lokacin muna da Kuruciya.."Yafada Cikin Zolaya Murmusa kawai Haddir yayi batare Da yayi mgana ba Shima bai Damu Daya Tanka din ba ya Cigaba Da Fadin.
"Tunda kaga Usmanu yayi irin wannan Fushi Ka Tabbata Babban Abu ne...Mutun ne mai kawaici da Boye damuwa Naji matukar Tsoro Lokacin Danaji Labarin Damuwar da Zainullahi Ya sakashi Ta kaishi Har kwance bai iya zuwa aiki Daganan nasan Zainullahi ya Gama Raunana Zuciyar Usmanu na Wanda banta gani ba Tunda na Haifeshi Saboda Hakurinsa da Kawaicinsa..!
Ya fada Idanuwansa na kan Haddir wanda ya natsu yana Sauraransa Cikin Takaichi Alhaji Tsoho ya Cigaba Da Fadin"Me kake so nayi akai Hadiru..? Karka manta Usmanu Shine Mahaifin Zainullahi Shine Babban D'a Namiji cikin ya"yansa Wanda ya Dorama Son Duniya da kuma Burin Watarana In Bashi Shi zai Gejesa ya Rike Iyayensa da kanninsa..? Ya bashi yarda yana ganin Ya Sauke Nauyin Dake kanshi Wajen Bashi Dukkan Tarbiya da Ilimi na Arabi da na Zamani Saboda Watarana ya Tsaya Da Kafafunsa bayan Gama Dukkan wananan bai ga Sakamakon komai ba sai wannan aikin da Zainullahi ya aikata na Ijiye karuwa suna zaman Haramci Harda Tsaraban Ciki,Ni na isa na Hanashi Nuna Fushinsa da Damuwarsa akan Abunda ya Haifa..?
Ya Fada yana kallon Haddir Wanda kalaman Alhaji Tsoho suka Sanyayamai Jiki Kai ya Girgiza Cikin Mutuwar Jiki Kafin Alhaji Tsoho ya Cigaba da Fadin"Toh ka gani bani da wani Abunda zan iya yi kan wannan Lamarin Hadiru Zainullahi ya gama Bamu kunya gabadayanmu..Na Riga nayi iya Abunda zanyi sauran kuma sai mu bar ma Ubangiji mganar ita yarinyar ma Mahaifinta ya Kirani yace nayi Hakuri Dayake ya karbi Lambata Ranar kafin su Wuce kan Gobe ne Suke sa Ran Zuwan ita Uwar yarinyar Daga Sudan in tazo yayi mata Bayani Insha Allahu zasu zo da mai Dakinsa su kawo ta Wajena kamar yadda nace..Sai godiya yake min abun gwanin ban Tsausayi..!
Haddir bai samu Damar mgana ba yaji Muryan Hajiya Mama Dake Kokarin Shigowa Dauke da Farantin Kololin Abincin Alhaji Tsoho tace"Nifa wannan Hukuncin naka baimin ba Sam Taya za"a ce kuma tazo ta zauna Cikin mu Har ta Haihu ai sai in muna ganinta Bakinciki watarana ya Nemi kashemu daka sani Ta tsaya chan gaban Uban nata ta Haife Shegeen..'
Tafada Cikin bayyana Takaichinta Da Sauri Haddir ya mike ya karbi kayan Hannunta yana Fadin"Kamar kin Shiga Raina Hajiya Mama..Wlh nima Haka nace..!
Yafada yana Sauke Farantin Gaban Alhaji Tsoho wanda ya murmusa yana Fadin"Mata mata..Sai abarku..Nan din Shine mafita ai Aminatu..Mahaifinta Dan Siyasa ne zamanta gabansa akwai mtsala Gwara tazo nan ta Haihu sai a Daura musu Aure suje chan su Cigaba da Renon Abunda Suka Hadu suka samar baShikenan ba.."
Hajiya Mama na zama Gefen Haddir Tana Fadin"Bafa Shikenan ba Mallam..Su mun Rufa musu asiri mu kuma mun Tona namu kana Tunanin mganar nan bazata Fita bane in Har yarinyar ta Dawo gabanmu da wannan Abun kunyar..? Alhaji Tsoho yace"Zai fita mana...Alheri ke Buya banda Sharri Aminatu..Kuma Wanda ya rufama wani asiri Allah Shima zai Rufamai Duniya da Lahira,Muma ai ya Rufamana Tunda bai kai mu kara Kotun musulunci ba Inda chan yakai Allah Jikanki jefasa za"ayi har ya Mutu Tunda da Auransa yake Zina.."
Hajiya Mama tace"Ita fa sai a kyaleta..? Alhaji Tsoho yace"In ta Haihu ita kuma Bulala 80 za"ayi mata Tunda ita batayi Aure ba.."Hajiya mama Tayi Tagumi Tana Fadin"Ba wacce nake jin Tssusayinta Har Raina sai Yarinyarnan Halima Dazu mukayi mgana da Fatima Take Fadamin komai taci sai Ta Dawo dashi kwana Take kuka Ga Rashin Barci..'
Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Nima Wlh Aminatu..Kamar kin Shiga Raina da Yarinyar nan marainiyar Allah nake kwana ina Tashi..Ina Fatan Allah yasa ya zame mata kaffara.."Gabadayansu suka amsa da Ameen,Kafin Alhaji Tsoho yace"Mganar da Hadiru yazo min da ita kenan kam in saka Baki Takoma Gidan Mijinta Shima yana chan kwance ba lafiya Hadirun ma ke Kwana chan yana Kula Dashi..".
Hajiya Mama tace"Oh ni Amina...Allah ya kyauta na gaba..Me kace kan mganar..? Alhaji Tsoho ya sauke Numfashi yana Fadin"Me kuwa zan ce..? Bazai yuyu Ta koma yanzu ba saboda Halin Datake Ciki Gwara ta zauna anan Uwarta na Kula da ita Zuwa akara kwana Biyu ni dakaina zan saka Fatimar tazo Da ita nan na kara mata Nasiha Da Lallashinta Mganar Usman kuma Shima sai zuwa bayan an kwana Biyu zan mai Mgana kan ya Sausssauta Fushinsa Hakan bai da wani amfani Kai kuma Hadiru in ka koma Wajen Zainullahin in Jikinsa yayi sauki gobe ka kawomin shi nan ina son mgana Dashi.."
Haddir yace"Allah ya kaimu.."Daga Haka ya kalli Hajiya Mama yana Fadin"Me kuka Dafa ne Tsohuwa..?
Cikin Haushi Hajiya Mama tace"Uwarka Safiya ce Tsohuwa don kaniyarka.."Baki ya Rike yana Fadin"Me yayi zafi Kika sako Sunan uwata Gatse haka..? Karkace kai Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"Don ma Bance Aliyu Kai Tsaye ba..?
Baki ya kama yana Mikewa Lokaci Daya yana Fadin"Kirashi mana ai ke kika Haifi Abunki ni miye nawa..? duk Tsiyarki dai baki haifeni balle kice zaki Dakeni Ni kinga ma Tafiyama basai kin ga mutum bama ballatana ki gayamai mgana.."
Yafada yana Bayyana yadda yaji Haushin Kiran sunan Mamarsa Datayi,Alhaji Tsoho na Gefe yana Mirmishi Cikin Tura Haushi Hajiya mama Ta Rakashi Da Fadin"Kwarai na Haifeka kuwa..Tunda na Haifi Uban daya kawoka Duniya kaga kuwa bama Duka ba zanyi sakaka Cikin Daki nayi maka Dukan Tsiya sai na barka kwance.."Ko Tankata bai yi ba ya Fice yana Fadin"Sai kuma kiyi..Ji dai da wannan Rudadden Tsohon Mijin naki.."
Da karfi Tace"Bana ga Rudadde ba..Rudadde ya wuce Ubannanka Bashir ko Aliyu.."Yana Jinta Daga Falo kai ya Girgiza yana Fadin"Gaskiya Tsohon chan ne Daya ce Rigimarki su Baban kaduna suka kwaso.."Abayyane yayi mganar Dakinsa ya Shiga Wanka yayi ya Sauya kaya kana ya Fito Kitchen ya Shiga wajen Tabawa suka gaisa Cikin Sanyin Murya Take Fadin'Ya zainullahi yake ne Hadiru..?
Tura baki yayi yana Fadin"Kai Tabawa..Wai kema Hadirun nan Har dake.."Dariya Tayi Tana Fadin"Eh mana wannan Shine zamu kira namu na Mutan Da..Ko Bakin ku na yan zamani ne Hadiru..'Kai ya Rausayar yana Fadin"Ba wani kuna dai Batamin suna kuma ba kowa yaja ba sai Tsohin chan Da matarsa.."Tabawa Tayi Dariya kawai Haddir yace"Zain yana nan Lafiya..Bai dai jin Dadi ne yanzu ma Shi nazo samar ma wani Abu Allah yasa kinyi Tuwon nan naki mai Dadi Tabawa..'Cikin alhini tace"Allah Sarki..Allah bashi Lafiya Jarabawa ce Allah ya bashi ikon Cinyewa damu gabadaya..!
Haddir ya amsa da Ameen Kafin Tabawa tace"Akwai Tuwon Shinkafa Miyar Danyan kubewa Wanda nayi ma Alhaji Tsoho ne.."Da sauri Haddir yace"Alhamdulillah..Saka mana Cikin Kula nayi gaba Dashi Daman na Dade banci Tuwon ki ba Tabawa.."Tana Dariya tace"Na Dumaman Alhaji Tsoho ne fa ko nayi muku wani ne..?
Da Sauri Haddir yace"No..Samana wannan Tafiya zanyi na bar zain Shi kadai..Yaci yanzu banda Hadama yace harda wani Dumaman Safe..? In yayi mgana gayamasa Manyan Jikokinsa na Bukata kin basu.."Tabawa na Dariya tace"Shikenan kuwa..!
Saka musu Tuwon Tayi Cikim kula Miyan ma Haka wacce Taji Kashin Rago da manshanu Dauka yayi ya Fice yana mata Godiya Ta Rakashi da Allah kiyaye Hanya da kuma sakon Gaisuwarsa ga Zain ko Dakin Alhaji Tsoho bai kara Lekawa ba Saboda yadda hajiya mama Ta gama bata mishi Rai abayan Motarsa ya Jera komai ka fin ya Shiga ya Tasheta ya Fice Daga Haraban Gidan Bayan Maigadi ya wangalemai get.
Yana Bisa Hanya Dadyn Abuja ya Kirashi sukayi mgana ya kara gayamai Halin da ake Ciki