Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ki yi Ta Cizona indai zaki Huce kuma ki biyoni mu koma Gidanmu.."Yafada yana Mikewa Kamar zai kamota Tayi Saurin Ja baya Tana wani irin kuka Kura mata ido Yayi kafin ya mika mata Hannu yana Fadin"Taho...Taho Firstlove don karki kiki Tahowa gareni..Taho mu koma Gidanmu..Na Yarda Muna Zuwa Gidanmu ki kulle ni acikin Dakina kiyi ta Dukana Har sai kin Huce indai zaki Barni kuma Ki zauna dani na yarda na amince.."
Yake Fada kamar yayi mata kuka,Tana Kallonsa Tana ja da Baya Cikin Kuka Da Tsausayinsa Take Fadin"Aah....Bazan iya ba..ba zan iya ba.."Tafada Lokaci Daya tana Juyawa Ta Bude Kofar Tiolet ta Fada da Sauri ya Bita sai dai yayi Rashin Sa"a Ta Riga ta Saka Makulli Jikin Kofan ya tsaya yana ta kwalamai Kira tamai Banza ta Sulale nan Kasan Tiolet din Tana sakin kukanta Bazata iya Binsa ba Ba saboda Laifinsa ba sai domin Umma uwa wacce Tayi mata Dukkan Hallarcin Duniya bazata iya watsa mata kasa acikin Idanuwanta ba.
Tana Jinsa ya gama Kiran Nata da Buga Kofar Ya Taka ya Fice Kuka ta kara sakawa Tana Jin kamar ta Bude Kofar ta Bishi sai ba Hali,Kukanta tayi ta Sha abunta Kuka ne na Soyayyah kauna da kuma yanke kaunar duk Lokaci Daya.
Shi Kuma zain yana Fita Cikin Wani irin kasala ya Fara Taku zai bar Falon,Yaji Kiran Nene Daga Bayansa ya waigo Cikin Saurin Basar da yanayinsa Kura mai Ido Nene Taayi kafin Tace"Me ya sameka..?
Yana Shafa kafansa yace"Bakomai Nene..na shigo kina Kitchen.."Nene ta kada kai Tana Fadin"Eh...Naga Zaka Fita baka Shiga ka Duba yarinyar nan ba.."Cikin yamutsa Fuska yace"Wata yarinya kenan Nene..? Cikin Takaichi Nene Ta mai Dakuwa Tana Fadin"Bansani ba...Toh wacce ka Kakabamana Dole mana Ai kana sane jiya iyayenta suka kawo ta.."Sosa keya yayi yana Fadin"Nene don Allah kyaleta..ina da aiki asibiti Na Tafi.."Baki sake take binsa da kallo Har ya Fice bata samu zarafin mgana ba sai da ya Fita kana Ta kada kai Tana Fadin"Uhmm..!
Nene bata koma Dakinta ba sai da Ta gama Kulla Duka Tuwonta cikin leda ta saka Cikin Wata katuwar Kula,Jin ana ta Kira kiran sallah yasa ta koma Dakinta ta watsa Ruwa Tayi sallah sai taga Zaina na sallah sai Lokacin ma ta iya Tunawa da ita Kada kawai tayi ta Shiga Tiolet tayi wanka Koda ta Fito Zaina ta bar Dakin Nene ta Murmusa Tana Fadin"Ta gudu Dakin uwarta kenan.!
Umma kuwa sai da Zaina ta koma Dakin kana ta Tashi kan ya Saukar mata Ta Shiga ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan Ta Idar ne ta Zura ma Zaina ido ganin Tana ta wani Dukar dakai kuma Fuskarta ta kumbura kamar tayi kuka Cikin Mamaki tace"Meke damunki..?
Da Sauri Zaina Tace"Ba...Bakomai Umma.."Kuri Umma Tayi mata da ido Tana Nazartanta kafin ta mike tana Fadin"Ke dai kika sani..In ma Kukan nace zan rabaku ne Wlh sai dai kiyi tayi har Hawayenki ya kare bazaki Koma gidansa ba.."
Daga Haka Umma ta Sabule Hijabinta ta Fice ta bar Zaina na Kokarin maida Hawayenta acikin Ranta Tana Tunanin da Umma ta gansu yau ai da ta kade har ganyenta.
*****
*Bayan Sati Daya..*!
Haka abubuwan sukayi ta Faruwa,Acikin sati Dayan bangaran Dina kuwa iskancinta sai Karuwa yake yi kayanta Data Zube sai dai Nene ta saka Zainab ta gyara mata ta Shiryamata kowanne ta ijiye abangaransa,Banda Nene kuma bamai Biye mata ballatana ya san da zamanta Itama Dinar bata Fitowa kullum Tana Daki Taci mai kyau tasha mai kyau sai Abunda ta Zaba shi Take ci Nene ta Daure mata Gindi Bangaran Umma kuwa basu kara ma Haduwa ba kuma kafarta bai Taka Dakin ba ballatana Abba Da bama yasan ganinta Ballatana mganarta Ragamarta komai yana Hannun Nene ne Shi Kanshi Uban gayyah bai Tana Zuwa Inda Take ba,itama Dinar bata Damu ba Saboda Zakiya tace ta bashi Lokaci Zai Dawo gareta.
Dina Tana waya da Daddyta da Kuma Hajiya Maimu wacce ta koma Sudan kuma Tayi ma mahaifiyarsu bayanin komai har mgana sunyi da Dinar ta waya ta kara yi mata Fada da Nasiha Wanda bai wai Domin Dina ta Jita bane Yadai Shiga kawai ya Fita,Hajiya Batula kuwa bata Taba Kiranta ba itana ba Damuwa Tayi da ita ba Wayarta Daga Daddy sai Hajiya Maimun sai Zakiya take Doguwar mgana Dasu bayan su Bata da wannan kwaramiyan sai dai Shiga Kafafen yada Labarai Tana Chart dinta Hankalinta kwance Babu Abunda ya Shalleta Nene Bata Taba ganin inda Dan Shege ke zama ado ba sai Wajen Dina Alfahari Take da wannan Cikin Jikin nata wanda Allah ya Taimaketa Bai sakata Laulayi Sosai yanzu Damuwar Dina Daya Rashin sanin makomar Auran Zaina da zain kuma gashi bata ma Jin Motsinta acikin Gidan Fargavanta Daya kada ace Ta koma Gidan Zain dinta wanda bata Fatan haka Zakiya ce ta Lallashe da cewa ta bi komai a Hankali kuskuran kadan Zatayi zata Lalata Duka plan dinsu ta bari zata samu Lokaci Tazo koma miye Sai ta ganoshi kafin Tatafi da wannan mganar ta Saurara da har taso Ta Tambayi Nene Kan Zaina sai kuma Ta Fasa Tunda Zakiya ta kwabeta.
Bangaran Zain kuwa Yasha Zuwa gidan in ya Daidaici Abba ya Tafi office Umma kuma Tana Daki ko Tana Kitchen sai ya Rutsa Zaina yayi ta mata magiya yana kwakwumarta,Nene dai ta sani kuma batayi wani abu ba Dagani Tana so ayi ma Ummi Shigo Shigo ba Zurfi ne bata Sani ba Haka zai zo yagama Nacinsa in bai ci Sa"a ba Ranar zaina ko mgana Batamai sai dai ma Ta Hadashi da kokenta,Duk da Haka bai Hakura ba sai ya latsata Don ya nuna mata bazai yarda arabasu ba Wajen kwana Hudu yana yin haka Ranar na Biyar Dubunsa ya Cika Umma Na Kitchen zaina na Dakinta Ta Fito Zata koma Daki Suka ci karo ya Riko Hannun Zaina zai Kaita Dakin Nene Daman nan ne Deport dinsa Daya ga Umma sai ya Dake ammh Zaina kamar tayi Fitsari saboda Tsoro wani mugun kallo Take watsamai Kafin ta Saka Hannunta Ta Fizge Hannun Zaina Ta Bishi Da katon Dundu Sai da Nene Ta Shiga Tsakani Haka Umma ke Fada ta Inda Take Shiga bata nan take Fita ba aka bar Nene da ban Hakuri
Zaina kuwa Hannunta ta Fincika Zuwa Daki Cikin Tuhuma Ta kalleta Tana Fadin"Tun yaushe ya Fara zuwa yana Janki aboye ban sani ba..? Cikin Inda inda da Tsoro Zaina Tace"Tun...Tun..Ranar ne Wlh Umma bana so.ya.."Bata gama Rufe baki Umma ta make bakin Tana Fadin"Rufemin baki in baki so zai miki Dole ne..? Daukan ki yayi..? Wato kema munafuka ce bansani ba ko..? In gaskiya ne meyasa baki Taba gayamin ba..?
Zaina na Hawaye Ta Bude baki Zatayi mgana Umma ta Sakarmata Dundunaye har guda uku agadon Bayanta Tana Fadin"In kuna Takaman ku yaran Zanani ne nima Uwar zamani ce..Bazan barki ya kara Cutanki ba Tunda ke kam baki da wayau Shashasha mara Tunani kawai.."Daga haka ta Fice ta barta Tana kokenta.
Umma Taki barin mgana Ranta ya Baci Har Abba sai da ta gayamawa Tace yajama D'ansa kunni ya daina zuwa ya Horema yarta kunne agabanta ya Daga waya ya kira zain wanda Tun bayan Faruwan lamarin Abba bai Taba Kiransa ba Jiki na rawa ya Dauka ko amsa gaisuwansa Abba bai yi ba ya Sauke mai nashi Jidalin da Fadan Yace ya Daina Zuwar mai Gida ashe bai ji ba..?hala da kudinsa ya Gida gidan..? Daga Karshe yajamai kunni kada ya kara Zuwa gidan Ballatana Har yazo kusa da Zaina Daya na sonta da bai aikata wannan Shanshancin ba ya Dai Jira in wannan Cutar da yayi ma Mutane ta Haihu aka musu Aure ya Dauketa zuwa Gidansa Su Huta.."
Ranar Zain yaga Fada iri iri Umma Tayi nata Abba ma Haka Numfashi kawai yake ta Saukewa washegari daya bama Haddir Labari sai da ya kwanta Saboda Dariya Shi kuma bai ga Abun Dariya ba wannan Abun a Tsausayamai ne gashi Firsrlove ya kasa gane kanta ya bata Hakuri kamar ya kwanta mata ammh Daga Dukkan alamu Tana son Goyon Bayan mamarta ne Shi kuma bazai bari haka ta Faru ba,yaji Fadan Abba ya Dauke kafa na kwana Biyu.
*******
Yau da Bikin Hamdiya ya Rage saura kwana Biyar Dukkan wasu Shirye Shirye sun kamkama,Tuni an kawo Lefe nan Abuja Dangin Mama Safiya suka je suka karba Achan,Sai Zuwa Gobe zasu iso Yan Chan Abujan Dukkansu Inna Hannatu dai ta iso Da nata gayyar Inna Rukayyah kuma sai Gobe Zafeera ma ta Dawo Duk Yau din Gidan Alhaji Tsoho Suka Tafi Harda Umma da su Saudart Zainab ma bata Shiga makaranta ba Tare suka Tafi.
Nene ce kadai agidan sai Zaina wacce Take cikin Damuwa Dazu sunyi mgana Da goggo Halima ta wayar Umma tace tana ta Kiran wayarta bata samu Ta Kira Zain Shine yace Tana Gida Wajen Umma,Shine ta Kira Toh itama Umman ahaka ta bari a Zaina bata da Lafiya Domin bazata ce komai ba yanzu Ta Kira sun gaisa da Zaina kana suka Cigaba da mgana da Umma Har take gayamata Bikin Hamdiya Tace zata zo Insha Allahu Daganan ta Duba Halimar Shine zaina ta Damu bata so Umma Ta tari Goggonta da wannan mganar ko bakomai Ita Mai Rufama Firstlove Sirrinsa ne ba kuma Tasan ya Goggon zata Dauki Lamarin ba Gefe Daya ga Laila Data Dameta Da zuwa kan Ta koma makaranta Ta Fadamata Ta Hakura da Karatu har Abada Tundai Gashi zata Rasa Firstlove.
Tana Cikin Dakin Umma Kishin Ruwa ya Fito Da ita Har ta Shiga Kitchen din ta Dauko Ta Fito Tayi Mugun gani Dina ce ta Fito Falo Ta Rako Zakiya zata Tafi Daman dazu Taji Nene na Fadin Wannan kawar Dinar tazo Wajenta,Dina sanye Take da Wando Plazo sai wata karamar Riga Kallo Daya Zaka mata ko ba"a Fada maka kasan tana da Ciki Saboda yadda ya Budeta ba kamar Zaina da Cikin Jikinta ya saka Rama ba sai Laulayi don ma yanzu Yayi sauki ko aman ba sosai take yinshi ba Bata kara yarda ta kwanta bata lahiya ba saboda Umma kada ta Mtsa sai sunje asibiti asirinta ya Tonu wanda kuma Bata Fatan hakan
Ruwa Take Sha alokacin da suka Hadu Sai da ta Dawo da Ruwa ta kware ta Fara Tari Dina ta kalleta sama da kasa Hakama Zakiya kafin su saka Dariya su Tafa Cikin Shakiyanci Zakiya tace"Topha ita wannan Daman Ta na gida nan..?na Zata ganin Matar so ta bayyana Tuni An koma Kauyen Tsoho da Tsohuwa..?
Tafada Cikin wani Wulakantattacen kallo Datake Bin Zaina Dashi Wacce Taji har ta Fara Hawaye ga kuma wani Mugun kallo da suka Jefanta Dashi cikin Kishi Dina tace"Kema kya Fada Ba Zuciya Namiji ya gama nuna maka baka da wani amfani awajensa ammh ka manne..! Duk kukan Banza ne bata iya Rabuwa Dashi Tunda gashi Ta kasa ta Dawo Gidansu Ta Tare kamar gidan Ubanta.."
Zakiya tace"Ayya yi mata Uzuri Matar Zain..Kinsan ba"a saba zaman kauye ba..Kuma da kike Fadin Ta Rabu dashi Toh in ta barshi wa zata kama..? Daman ai Taimakonta yayi ya aureta ammh Ita kanta taasan Wutsiyar Rakumi Tayi nesa da kasa..Kuma mganar gida kamar Gidan Ubanta Haka take gani mana kin manta nan Tsohouwa Tayi aikatau Tsoho ma yayi gadi Kinsan Dattakon iyayanmu na Baya Rikon Dan wani ba wani Abu bane..Kema ki barta Ta Raba agidanku ko yayane ta Rika Cin Jan miyar kar Abun yayi mata yawa ga Rabuwa da Zankadaden Miji ga kuma Komawa Kauye zaman Zawarci."
Cikin Shakiyanci Dina tace"Allah ko Tawan..?
Zakiya tace"Keda kikasan komai kuma..adai Daga mata kafa.."Dariya suka Sheke Dashi Harda Tafawa Lokaci Daya Dina na Fadin"An barta Tawan.."Zaina Da gabadaya kalamansu Zakiya yasa ta Jike da Hawayen Bakinciki da Takaichi Mganganunsu sun sakata ta Tuna Abunda ta manta,Kuka take so ta Fashe dashi ammh sai ta Danne Bata kara kallonsu ba ta Juya zuwa Dakin Umma Ko gani batayi suka Bita Da Dariyan Shakiyanci.
Ko gani Batayi ta karisa Dakin Bata ma kai ga Haawa gadon ba ta Sulale nan ta Saki wani marayan kuka ita kuwa Dina sun Dade da Xakiya nan Suna Ta Mganganunsu sai ga Nene ta Fito ganinta ne ma yasa Sukayi sallama da Juna zakiya ta Juya ta Fice tana ma Nene sallama Ita kuma Dina ta Koma Cikin Dakin Nene ta Bita da kallo acikin Ranta Tana Fadin"Allah ya Shirya.."!
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣8️⃣
"Kuka kawai Zaina Take kuka mai Cike da Bakinciki Da Takaichi Gefe Daya Mganganun su Dina na kara mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta,Dafe kanta kawai Tayi Tana jin yana Sara mata kamar zai Tsage gida Biyu.
Hawayenta kuma Suna ta Zuba Suna Diga saman Cinyarta.
Hakikanin gaskiya Su Dina gaskiya suka Fada mata Ita wacece..? Ba kowan kowa bace Eh gaskiya suka Fada ita din Diyar maryama Wacce tayi aikatau ne anan gidan kuma Diyar Abdullahi wanda ya zauna matsayin Megadi Kuma Ita Jika ce ga Mallam Umar gada Wanda Shima Gadin ne Sana"arsa,Itama Kakar nata Atine itama kamar mahaifiyar nata aikatau tayi sai dai me..? Sun yi Dacen Iyayen Gida irin Iyalan Alhaji Tsoho Tunda Gashi Basu Hada komai da ita ba Suka Dauketa suka maida Tamkar yarsu suka Kula da Rayuwarta suka bata Ingantattacen Ilimin zamani Dana addini Daga Karshe suka aura mata D'ansu mafi Soyuwa garesu Ita kuwa me zata ce ga wadanan Bayin Allah..? Dame zata saka musu..?
Wani kukan Ta kara sakawa Tana Tuna kalaman Dina akanta na Cewa bazata iya Rabuwa da Firstlove bane ammh yaci ace Bayan haka yasa Ta gane cewa ita din ba kowan kowa Bace Tabbas mganrta na kan Hanya Inda Baya sonta bazai Fara Mu"amala da ita ba Har yayi mata Ciki ba me hakan ke Nufi..? Tayi kuskuran Yarda da Duka kalaman Bakin Firstlove Domin Duka ba gaskiya bane,ammh ba Laifinta bane Laifin Zuciyarta ne Data ke matukar Kaunarsa kuma ta Soshi da Zuciya Daya Kodomin Mganar Dina bazata yarda ta watsa ma Umma kasa a ido ba zata Nuna mata ko Babu Shi zata iya Rayuwarta..!
Wata Zuciyar ta Tambayeta Zaki iya Zaman jura wannan Zaina..? Koda Tana Tunanin bazata Jure ba ya zama mata Dole Ta Jura hakan kuma Lokaci yayi da Zata Sam me take ciki nan fa ba Gidansu ba Tasan ina ne Tushenta Gada Ammh kuma Taya Tun abaya bata koma Musu ba sai yanzu da komai ya kare zata koma musu Babu Auran Tare da ita kuma Harda Tsaraban Ciki Domin in Ta Jure Rabuwa da Firstlove bazata iya Juran Rabuwa da Abunda ke Cikinta ba.
Ta Dade Tana kuka Tana kuma Saka da warwaran makomar Rayuwarta kafin ta tashi Ta Fada Tiolet Tayi wanka Ta Dauro alwala jin ana kiran sallar La"asar yasa Ta Tada Sallar Ta idar kenan Sai ga Nene ta Leko Cikin Shirin Fita Tana Fadin"Diyar Umma na Shirya Zan wuce gidan Alhaji Tsoho..ki Shiyar Ummanki ta barmin Sallahun na Taho Dake chan.."
Cikin Sanyin Murya Zaina tace"Bazan samu zuwa ba Nene sai gobe kaina ke dan Damuna.."
Cikin Tsausayawa Nene ke Fadin"Ayyah sannu kinsha mgani..?kai ta gyada mata alaman Eh Nene tace"Shikenan Allah kara sauki ni na wuce..Keda Dina ne agidan ki kula kinji ko..? In Abban ku ya Shigo Abincinsa na Kitchen ki mikamai.."
Cikin Ladabi tace"To Nene adawo Lafiya.."Daga Haka ta Fice Kafin Nene ta wuce sai da Ta Shiga Dakin Dina ta Isketa kwance kamar kullun Tana cin popcorn Tana ganin Nene ta gyara Zama Tana kallonta kafin ma Tayi mgana Ta Riga ta da Fadin"Zan Fita....Bakowa agidan Sai Halima zani gidan Alhaji Tsoho Saboda Sha"anin nan Daya Karato.."
Cikin Mamaki Dina Tace"Sha"ani..? Nene tace"Eh...Daya Daga cikin Jikokin Gidan ne zata yi aure kanwar Haddir ne yar wajen Daddynsu na Abuja Shine Zasu zo nan ayi Bikin Daganan za"a wuce da Amarya Gidanta Dake kaduna.."Kai kai kawai Dina Tayi Kafin Tace"wai ni Nene haka zan Ta zama ba Fita..! Ina som komawa wajen aikina fa.."
Nene taJuya Tana Fadin"Ina zaki da wannan Abun kunyar kuma..?koda yake ke ado ma kike da Ita ai ko cewa akayi ki Fita zaki ce bazaki Fita ba saboda kaucema Idanuwan Mutane gashinan Cikin ki har ya Fara Bayyana ko bama Haka ba Duk wanda ya kalleki yaga mai Juna Biyu.."Baki Dina ta Tura kawai Kafin Tace"Ai Duka Da Haihuwa ce..Kuma Yana da Uwa Da Ubansa.."
Nene na gyada kai tace"hakane ba Shakka..Kinga Tafiyata.."Daga Haka ta Fice Dina Ta rakata da Harara,Nene bata ma Jira Direba ba Tunda yana Office Tare da Abba Da kafarta Ta taka Zuwa Gidan Alhaji Koda Taje duk an Hadu Falon Hajiya Mama ana ta Kira Hira Itama ta Shige Cikinsu Ganinta ita kadai yasa Umma ta Tace ina zaina Nene tace Tana Gida tace bata jin Dadi Umma Tayi Shuru tana wani Tunani Har ma Inna Hannatu ta kada baki Tana Fadi su daina barinta Tana zama ita kadai Ta Riga zama cikim Mutane ko Abun zai saketa,Hajiya mama ta kada baki Tace Tunda Uwarta Ta na Kokarin Raba auranta ai Damuwa yanzu suka kulla Inna Hannatu na jin haka tace Wlh itama Tana Bayan Umma abar Zain din ya zauna da Dina Tunda ita ya zaba nan fa Nene ta saka baki Tana kare zain kan yayi Nadama don Allah su karbi Tubansa Inna Hannatu tace har ga Allah komai ya wuce ammh fa Tana Bayan Umma yarinya karama Bakincikin yayi mata yawa ko ita Babba wannan Abun ya Faru da ita ya zatayi ganin sun Dake ne yasa Nene ta sakarmusu ammh fa tace su bazasu saki ba Sai dai ayi wacce za"ayi.
Umma dai Zainab ta Nema kan Ta koma Gida ta zauna da Zaina Tsoronta Kada wani mgana ya Shiga Tsakaninta da Dina kana kuma Bata son yaudaranta Da Zain yake yi yana Zuwa yana Hore mata kunni,Dole Zainab Ta Shirya ta koma Gida koda Taje ta Iske ma Har Abba ya Dawo Zaina ta kawo Abinci nan Falo Ya zaunar da ita yana kara bata Hakuri da kuma yi mata Nasiham Hakuri da Takwalli Dawowar zainab din yasa ya barta suka koma Daki Tare Dina kuma na cikin Dakinta ko Motsinta ba"a ji.
Sai Umma sai Dare suka Dawo Umma dai Haddir ya Dawo da Ita da su Zareenaa dasu Saudarta Nene kuma Zain ya Daukota Tunda Bayan ya Tashi Daga asibitin chan ya wuce,Inna Hannatu ta Kebe dashi