Chapter 12 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 43

33K to 36K   out of 126.5K words

Tace"Dama ai bazaki Rabu Dashi ba sai mun kai ga Nasara.."Ido Dina Ta sakarmata kafim Tace"Taya..ya..? Help me kaina ya Dunkule waje Daya baya wani Motsi...!

Mikewa Zakiya Tayi Ta kariso Kusa Da ita Lokaci Daya Ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Alluran planning din da kikayi na How many Month ne..! ? Kai Tsaye Dina Tace"Harkin mata..? Tare fa mukayi na Six Six Month ne..!

Zakiya Tace,"Ban manta ba So nake na kara Tabbatarwa..In ban manta munci Almost 4 month kenan Tana mana aiki ko..? Kai kawai Dina Ta Dagamata alaman eh Cikin Sauri Zakiya Tace"So ina so Indan Ta gama aikinta ajikinta karki sakeyi mujira mugani...!

Da mamaki Dina ta Dago Tana kallonta Cikin som karin Bayani Lokaci Daya Tana Fadin"Kar na sakeyi kuma.? Kinsan me Hakan ke Nufi..? Zakiya Tace"Yes naasani..Ba Ciki kike Tsoro ba..? Kai Dina ta gyada mata Tana Fadin"Eh mana..Kinsan Zain ya gargadeni akan Hakan Tun Farko...!

Wani Mirmishin Mugunta Zakiya Ta saki kafin tace"Toh ai da Cikin zamu Amfani mu Razani shi..Tunda na Lura yana Tsoron Danginsa Da Matarsa Wacce yafi so baya so Taji Labarin yana Tarraya da wata mace awaje..Duk Shaidar da zamu Tanada Bata kai Shedar ki Mallaki Kwan Haihuwarsa a maranki ba Dina Kuma Dole in Mgana ta kai kunin Manyansa su Zauna su sassanta mganar Domin na Tabbata baza su so wannan mganar ta Fita ko Domin kada kimarsu da Darajansu ta Zube akan Idanuwan Duniya ba..!

Ta karishe Fada Lokaci Daya ta Juyo Tana kallon Dina Wacce tayi Shuru Tana kallon Zakiya kafin Zakiya tace"Ya kika ga wannan Salon..? In yasan wata bai san wata ba Tawan..Kuma kin manta Boka daman ya gayamana kafin Auranku yaga Turniku da Duhu..? Toh ai wannan yakin da zai Faru Shine Duhun Tabbas za"a kai Ruwa Rana Rayukan wasu zasu baci..Wasu zasu Raasa kimarsu Dayawa ammh mu bamu damu ba Koda mun Rasa namu kimar Daman chan ba wata kimar garemu Wajen Allah ba Indai Burinki zai Cika na mallakan Zain na yarda Duniya ta Shaida bamu da Wata Cikakkiyar kima Kura ce Lullube Daman da Fatar akuya..!

Tafafa Tana wani kada mata Hannunta Ajiyar rai Dina Ta Sauke kafin tace"Hakan kina ganin bazai Taba Siyasar Mahaifina da kujeransa ba..? Zakiya Tace"In Macijin yayi mana Taurin kai ne Mganar zata Fasu saboda bamu da Zabi..Ammh in ya nuna yana son Sulhu zaku Sulhu iya ku Biyu ammh kuma ki Tuna Hakan bamai yuyuwa bace Dole ne Shima yarasa kimar Dayake Takama Dashi in ko Hakan ta Faru Dole ne Labari ya Fasu...indai kin Zabi Kujeran mahaifinki To ya zama Dole ki Yi Hakuri Da Cikar Burinki Dina..!

Shuru Dina Tayi tana wani Tunani kafin ta Sauke Tagwayen Numfashi Tana Fadim"ammh kada muyi Saurin Datse ma Macijin kai Zakiya..Gwara mu Fara Datsan ganganar Jikinsa koda mu Rabasa da Kansa ne batare da Mun kashesa ba.' !

Zakiya Ta saki Dariya Tana Fadin"Wato Dai mu Fara Sare Macijin kafin mu Sare kansa kenan.? Kai Dina ta Gyada mata Kafin Tace"Haka nake Nufi..!kai kawai Zakiya Ta Jinjina kafin Tace"Shikenan komai na Hannunki..'

Daga haka suka Cigaba da Tattauna mganar sun Jima Kafin Dukkansu su Shirya su Fita Tare Dina cikin asibiti Ta koma Ita kuma Zakiya Gida ta wuce Zatayi wanka Ta Shirya Tana da Bako.

*****

Gabda Kiran Sallar mangariba Halima Tagama Komai Zobo Take Hadawa Taji Kiran wayanta Daga Falo Mirmishi Ta saki Sanin Firstlove ne ke kiranta Zobon Tagama Hadawa kana ta Dauka ta saka Cikin Fridge yayi sanyi Abincin Datayi kuma Farar Shinkafa Miyar ganye Mai kifi sai Ferfesun Pepe Kitchen wanda Tayi Saboda Firstlove nan Kitchen din ta bar komai Saboda Tana so Sai ta koma Daki Tayi wanka Tayi sallah kana sai Tazo Ta jera komai kan Dinning ta goge Kitchen Din Inda ta bata.

Da Sauri ta Fita Daga kitchen Din Zuwa Falo Katon Talabijin Din Dake kafe Shi yake ta aiki Shi kadai kan Center Table Din Dake Tsakiyar Dakin Ta Hango Wayarta Da Sauri ta karisa ta Dauka kenan wani Kiran ya kara Shigowa Fuska Ta bata ganin Sunan mai kiran *UKTI ZAFEERA..*!

Cikin Tura baki Ta Daga Kiran Tana Fadin"Dillah ji yarinyar nan ta sakani gudu nifa da naji Kiranki na Zata Firstlove ne....!Tafada Tana wani Tura baki kamar Wata karamar yarinya Dariya Dagachan Bangaran Zafeera Ta saka kafin Tace"Ehhe..Kaji masu Firatlove...Mu da bamu Dashi Allah ya bamu Ukti..!

Halima ta saki Dariya Tana Fadin"Ameen Ukti kefa kikayi sanya Ina Barrister Ahmed yake..?Meyasa baki bashi Dama ba yana Sonki Wanchan Satin Alhaji Tsoho ke Fadamin yaje ya gaisheshi Da wani aiki ya Shigo Dashi Garin..'!

Tabe Baki Zafeera Tayi Dagachan Bangaran Tana gyara Zaman System din Dake gabanta Cikin Basarwa tace"Yayi kokari..Ukti ya gida..? Ya kuma Yaya Dakta yake..? Naga Kiranki Dazu ina Cikin makaranta ne Shiyasa na bari sai na Dawo Gida na Kiraki..!

Halima Tace"Komai lafiya Ukti to ya karatun.? Ya su Inna Rukayyah Ina Shema..? Zafeera Tace"Shema ta Shiga wanka..Nima yanzu na Fito Dayake ko Mintoi Ashirn bamu yi da Shigowa Gida ba.."Halima Tace"Allah ya Taimaka Ukti nayi kewarka yaushe zaku samu Hutu..?

Zafeera Tace"Nima ina matukar Kewarki Ukti..Wlh sai nan da 2 Month inaga domim ko Test bamu Fara ba.."Halima Tace"Muma bamu Fara ba..Kuma ina ta ma Firstlove nacin yakai ni kano Wajenki yaki Maida kai akan mganar..!

Zafeera Tace"Dama ai bazai barki ba Ukti..Kim manta Tun muna Gabansu Umma Sai inda ya Zabar Miki..? Dariya Suka saka atare kafin Zafeera Tace"Ahki Faruq na gaisheki Ukti Dazu ina School ya Kirani mukayi Vd call.."Tsalle ta Buga Tana Fadin"Don Allah..? Kice kinga Mutanen Chicago..!

Zafeera Tace"Wlh..Kinga yadda ya zama ya kara Kiba da Fari.."Halima Tace"Allah Sarki Shine ni bai kirani ba.."Ta fada Cikin Shagwaba Zafeera Ta Saki Dariya Tana Fadin"Ho..Ni kuma Kishiyarki ba..Toh Yace ya Kirani bai sameki ba ya Kira Yaya Dakta kuma yace kina Gida Shi yana asibiti..!

Halima Tace"Shikenan ya Fita...Nima zan Kirashi mu gaisa Wajen wata Biyu Rabon da muyi mgana Dashi.."Zafeera Tace"Nima kinsan yanayin karatunsu na lauyoyi Tunda ya Dage sai yagaji Dadyn Abuja.'Dariya Halima ta saki Kawai Lokaci Daya kuma suka Sarke Hiran Jin ana Kiran Sallar mangariba ne yasa Halima tace"ke wai hala baki Sallah ne..?

Dariya Zafeera ta Sheke Dashi Tana Fadin"Au da kin zauna ne..? Nifa Shehi yayi min Tawa.."Halima tace"Banza Allah ya isana.."Dariya Zafeera ta kara sawa Tana Fadin"Dama Ai chan Allah ya Isa mana.."Halima Tace"Naji ni ba wannan ba Ukti Dama ina Son ganinki mgana nake so nayi Miki.."

Zafeera Ta natsu Tana Fadin"Ko..? Toh ina jinki ko sai kinyi Sallah ne..? Halima Tace"Bari mu Fara mganar Tunda naji yanzu Wasu masallatan suke kira...!

Jin Haka yasa Zafeera ta Ture Laptop Din gabanta ta mike Tsam Ta Fice ganin Shema"u ta Fito Daga Tiolet,ita kuma Zafeera macece mai Zurfin Ciki bata yarda kowa yasan Cikinta in ba Umma ko Halima ko Faruq ba,Koda Shema ta kasance Diyar Inna Rukayyah bakomai nata ta sani ba Fita tayi zuwa Falon ganin Duka yaran Mazan sun Tafi massallaci Matan kuma sum Shiga Dakumansu yin Alwala Inna Rukayyah ma Tana Dakinta kan Daya Daga Cikim kujeran Falon Ta zauna Tana Fadin"Ina Jinki Ukti..Na Fito Falo ne..!

Mirmishi Halima Tayi kafin tace"Kan mganar Barrister Ahmed ne meyasa bazaki Bashi Dama ba Zafeera..! Naga yana sonki kuma Naga Dadyn Abuja da Alhaji Tsoho suna yabonsa Sunce Dan Gidan mutumci ne kuyi Auranki Ukti na Tabbata zai barki ki Cigaba da karatunki..!

Numfashi Zafeera Ta saki Kafin Tace"Uhm..Ukti Nifa ba wai ina kin Ahmed bane..Kawai dai Mazan wannan zamanin ne baka gane kansuu baka san abunda ke cikinsu ba kuma Abun ke ransu dabam Abunda bakinsu ke Furtawa Dabam.."Da Sauri Halima Tace"Bangane ba..? Zafeera Ta gyara zama Tana Fadin"ina Nufin Acikinsu Dai dai ku ne keda Amana..Sai mace Ta gama yarda dasu Daga baya su Ci Amananta Ukti zuwana Kanon nan naga Casess na mazan da sukaci Amanar Matansu Daga Karshe suka bar matansu da Ciwon Zuciya Da Damuwa Shiyasa Maza suka Fita kaina na ke musu kallon Duka Halinsu Daya..!

Da Sauri Halima Tace"Ammh banda Firstlove dina ko? Na Tabba Kin Shaida Bazai taba Cin Amanata ba.."Zafeera Tace"Ba zan iya sani ba Ukti bar ganin Yaya Dakta na yayana kema yar"uwata ce ta Jini Dole na gaya miki Gaskiya bansani ba Tunda Nidai Zahiransa nake gani ba Badini ba..Ammh dai karki saka komai acikin Ranki Ki kyautatamai Zato..'

Jikin Halima yayi Sanyi Cikim Rauni Tace"Yanzu kina so ki gayamin kema kina Tunanin Wata Rana Firstlove zai iya yin wani Abu nacin Amana agareni Ukti..? Da sauri Zafeera Tace"A"a
Ni wlh bance ba Ba kuma Haka nake Nufi ba..Nace bansani ba..Ammh Mu kyautamai Zato Ukti ni na Shaida Kaunar Yaya Dakta agareki Insha Allahu makamanciyar cin Amana bazai Taba gitwa tsakaninku ba.."

Jin Tayi Shuru yasa Tace"kinji Ukti Don Allah karki Damu plz..! Ajiyar Rai ta Sauke kafin Tace"Shikenan...Zan kiraki zuwa gobe mu karisa mganar bari naje nayi wanka da Sallah Firstlove na Kan Hanyar Dawowa.."Kai Zafeera Ta gyada kafin tace"IS ok..Akulamin da Yayana Dakyau.."Dariya kawai Tayi ta katse Kiran Tsaye kawai Tayi Tana Tattara maganganun Zafeera gefe Daya kuma tana gamashi Dana Laila sai take ganin Kamar Abu Daya suke Nufi gabadaya Jikinta sai yayi sanyi Dakyar ta karisa Cikin Bedroom Dinsu ta Fada wanka bata Fito wanka ba sai da Ta Dauro alwala tazo Ta shafa Lotion Dinta Ta Zura Doguwar Riga ta Tada Sallah bayan ta Idar ne ta karisa gaban Wardrope Ta bude ta Dauko Riga da Sikat dinta na wani Atamfa mai kalan Ja ta saka ta karisa gaban madubi ta kashe Dauri ba wata kwalliya tayi ba sai dai kayan sun kamata kwarai sun Fitar mata da Sirrin kyanta,Turare ta saka a ko"ina na Jikinta kana ta Fito Daga Bedroom din.

Karo suka kusa Yi da Zain wanda ya Sawo kanshi Cikin Bedroom dinsa Dauke da Suit dinsa a Hannun Dayan kuma yana Rike da wayarsa da Key din Motarsa Baya Taja Tana kallonsa Shima kallonta yake Cikin mamaki bai samu Zarafin mgana ba tace"Yaushe ka Shigo..?

Kai Tsaye yace mata"Yanzu na Shigo..! Ido ta Rausayar Tana Fadin"Kwata kwata banji Bude get ba da Shigowarka ba."Cikin mamaki ya sakamata Ido kafin ya Fara taku zuwa gareta Cikin Tsare ta ido yace"Meke Damunki ne Firstlove..?

Kai Ta Dago Tana kallonsa Tace"Me ka gani...? Cikin Sauri yace"U look so Silent Ba yadda nasan ZAINA ta ba.In taji Dirin Motatana zata Fito da Gudu ta kamkameni Abunda tasan yafi komai Sakani Farinciki kenan Fara Tozali da kyakyawan Fuskarta da kuma jinta acikin Jikina."Sai da ya Fada Taji Tayi wani Gibi Daga Abunda ta saba Cikin Sanyi Jiki kawai Ta Fada Jikinsa Batare da tace komai ba Shima azuciyar Zuciya ya saki kafin ya Saka Hannu Daya ya Rumgumeta yana Fadin"I Love u Firstlove In kika Bar Rayuwata Wlh zan lalace ne..!

Tana Jinsa Saboda Jikinta a sanyaye yake bata iya cemai komai ba Sun Dade haka kafin ta Dago Daga Jikinsa Rigar Hannunshi ta  Karba Tana Fadin"Muje kayi wanka..Daman ban gama Jera abincin saman Dining ba..'

Tayi gaba yana Binta abaya Cikin mamakin ganin yanayinta ayau kuma da Safe lafiya Kalau suka Rabu Har Tailet ta Shiga Ta Hadamai Ruwan wanka kana Ta Fito Ta Tayashi Ciro kayan Jikinsa Ta Daura mai Towel ta Rakashi Har Cikin bayin kana ta Fito Shidai da kallo yake Bita yana so ya karanci meke Damunta taki bashi Dama,tana Dawowa ta Tattara kayan Daya Cire Zuwa Cikim Wardrope dinta Bangaran inda Take Tara kayan wankinsa,Ta Rufe ta Fice Daga Bedroom Dim kichen ta koma ta Dauko komai ta Jera Bisa Dining kana ta koma ta Gyara Kirchen din ta Fito kenan sai gashi ya Fito da wata Bakar Jallabiya mai Gajeren Hannu Mirmishi ya sakar mata Itama ta maida mai Kafin ta karisa ta Riko Hannunsa Zuwa Saman Dinning Din Taja mai Dayan Daga Cikin kujeran ya zauna Ita Tayi Sarving Dinshi Har sai da yace Ta barshi haka kana ta koma Kujeran Dake kallonsa ta zauna itama Taja Filet ta zuba Daidai Cikinta.

Cikin mamaki yakura mata ido Ganin Haka yasa ta Lamgwabe kai Tana Fadin"Bai yi Dadi bane abincin Firstlove..?

Kai yaGirgiza kafin yace"Ko Daya....Kawai naga wani Chanji Tare Dake ne Firstlove wanda Banta gani ba..!

Ido kawai ta sakamar Batare da Tayi mgana ba Shi kuma ya cigaba Da Fadin"Na Dawo ba"asan na dawo ba..Na biyu kuma Tunda mukayi Aure indai ina Gida baki da wajen zama sai kan Cinyata ni nake Ciyar dake Da Hannayena Firstlove ammh yau sai naga kin samu Kujera kin zauna kin kuma Dibi naki abinci ke kadai zaki ci..Sai na Fara Tunanin wani irin laifi ne mai Girma na aikata miki..? Wanda ni acikin Raina ina jin da na Bata miki gwara ke kin batamin Firstlove..!

Ya karishe Fada yana Tsareta da mayun idanuwansa kai ta Kauda gefe bata iya Juran kallonsa Kanta na kasa ta Dago Tana Fadin"Allah bakomai Firstlove karka Damu..!

Cikin Mamaki ya ijiye cokalin Hannunsa yana Fadin"Kinga bana son gaddama ban gane kada na Damu ba.? Ya bazan damu ba alhalin ga damuwa nan ta bayyana atare dake..?ki gayamin Abunda ke Damunki Firstlove in har kin Daukeni Abokin Rayuwarki..!

Yafada Cikin Nuna Ransa ya baci Kai ta Rausayar kafin Tace"Babu Abunda ke Damuna Firstlove Belive me..!

Fuska ba walwala yace"Na yarda Dake Fiye da yarda na yadda Dakaina..Ammh Damuwar Dake Fuskarki ta macece..?

Ido Cikin Ido Ta Dago Tana kallonsa ba Zato ba Tsammani yaji tace"Firstlove don Allah zaka iya cin Amanata watarana..? Zaka iya barina Watarana saboda Wata.?

Karishe Fada kai Tsaye Tana kallonsa wani irin Dam! Dum! Yaji gabansa ya amsa Cikin Waro Ido yake kallonta Tuni kuma yaji zuciyarsa ta sake Ta fara Tunanin kodai Tasan wani Abu Dake tsakaninsa Da Dina ne..? Daya shiga goma bama uku ba...!




*Yan group din ZAINAZAIN BAND1&2 Bakwa sharhi kalilan ne masu Comments kuma gashi Kun cika Groups din duka ko ku gyara ko kuma Duka na kakkabe ku nayi Sabbin Zubi...*




*Shakira...*











.
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️

*BOOK 1*

          0️⃣9️⃣

Cikin In ina da Tsoro da kuma Fargaba Hade da Faduwar gaba Zain ya Tattaro mganar da take Kan Harshen Bakinsa yace"Wa...n..wannan Wata irin Mganace ko nace Tambaya kuma Firatlove..? Waya gaya miki Watarana Ni Zainullahi zan Guje ki saboda wata...?

Yafada kai Tsaye yana kara Tsareta da manyan idanuwansa Itama Shi take kallo Cikin Son karantar yanayinsa Ganin yadda mganar ta Dakesa ne sai yasa Ta saki Wani Kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Kaima kaji Dukan Zuciya ko..! Kaji ka Razana da mganar ko...? Nima Haka naji Firstlove Lokacin da Laila Take Fadamin na Rage Sonka na Rage yarda Dakai saboda kai Namiji ne Watarana Duk Yadda ka kai da Rashin Son ganin Raunina zakayi Sanadiyar bayyanarsa..!

Ta Fada Manyan Idanuwanta na kawo Cikar kwallah mamaki ya kama Zain da maganganun Zainarsa Cikim Mutuwar Jiki yace"Laila kuma..? Dama ita ta gaya miki Watarana Zan iya barinki Saboda Wata..? Ya karishe Fada yana wani Hade Rai Cikin Karaya da Rauni Tace"Bata ce bane....Misali Ta bani Da kuma jin Tsausayina kada Hakan ya Faru dani Watarana..!

Cikin zafin Nama ya Daga mata Hannu yana Fadin"Kaji min Yarinya da Gulma..? Da ina kallonta yarinya mai Hankali Shiyasa na barki kike kawance da Ita Banta Zatonta Zatayi Sanadiyar Tsarwatsamin yardanan Danayi Shekaru ina gina ta ba Firatlove..! Ya karishe Fada yana wani karya mata Wuya Cikin Wasa da Spoon Din Hannunta Tace"Ba ita kadai Ta gayamin Haka ba..Ukti Ma na Tambayeta kan tana ganin zaka iya Cin amanata Watarana..? Kasan wata amsa ta bani..?

Zuwa Lokacin maganganun Zainar Tasa Sun Fara Bashi Tsoro Cikin Tsoro da jarumta Duka Lokaci Daya ya Girgiza mata kai alaman bai sani ba Cikin Mutuwar Jiki ta Cigaba Da Fadin"Wai itama cemin Tayi bata sani ba..Zahirinka ta sani ba Badini ba ammh Tana da kyakyawan Shaida akan ka..Firstlove kalaman Laila dana Zafeera suna min amsa kuwwa acikin kunnina sun sakamin Raunina ina Ji ajikina in Hakan Ta Faru wani Hali zan Shiga..? Wlh zan iya kashe kaina indai na Wayi Gari Zaka barni Saboda Wata Firslove..!

Ta karishe Fada Cikin kuka kamar Wata karamar yarinya kana ganin yadda Take kukan zaka san Daga karkashin Zuciyarta yake Fitowa Da Sauri Zain ya mike Daga Inda yake ya Isa gareta ya saka Hannu ya Dagota Tsaye Cikin Wani Sanyi Jiki dana Zuciya yake Fadin"Kinga Firstlove..Stop Craying..Kinga Mganar Zafira Data Laila Hasashe ne kawai Zainata Bazai Taba Faruwa ba..!

Yafada yana Dauke mata Hawayenta Da Tafin Hannunsa Cikin Tsuramai ido Tace"In Hasashensu ya zama gaskiya fa Firstlove..? Tafada Cikin Kuremai Idanuwanta masu Cike da wani Rauni da neman Tallafi Jikinsa ne ya kara Mutuwa Sai kawai ya kauda Kansa Lokaci Daya Ya Jawota jikinsa ya Rumgume ya kamkameta yana Sakin Zuciya kamar wani karamin yaro Itama Jinta acikin Jikinsa yasa kawai ta Kara sakin kukan Dake Cin Ranta Tuni Shi kuma sai aukin Shafa bayanta yake Cikin Sigan lallashi kafin ya Dagota ya Share mata Hawaye yana Fadin"Kin yarda Dani..?

Kai Tsaye Tana kallonsa Tace"Sosai ma Fiye da yadda na yarda Dakaima ma kuwa Firstlove..! Cikin wata murya yace mata"To indai kin Yarda Dani ki saka Ranki Har Abada ni Zainullahi bazan Taba barinki saboda wata ba..Duk Duniya mace Daya nake so kuma kece..Bayan ke ba Wata Firstlove mganar Laila da Zafeera kuma Suna Dora mizanin Haka kila sun ga Wani Abu ya Faru achan wani waje da Nisa wanda bamu da alaqa da Hakan Ki daina Kokwanto akaina Kinji Insha Allahu ko Mutuwa Tare zata Daukemu..!

Ya karishe Fada yana Sakar mata manyan Idanuwansa Sun Dade suna kallon Juna kafin ta kada kai Tana Fadin"Na yarda Dakai Firstlove...Ina Sonka Abun alfaharina..! Rumguma ya kaima ta Cikin Wani yanayi yake Fadin"nima ina Kaunarki Zainata...! Yake fada yana Shinshinar wuyanta itama makaleshi Tayi Sun Dade ahaka kafin ya Dagota yana Fadin"Kuka ya kare ko..?

Kai ta gyada mai bai yi Wata Wata ba ya Dagata Cak yana Fadin"Muje muci Abinci....nagode ma Allah dana iya Shawo kan wannan Matsalan da Zafeera da Kawarki Laila suka so su kunnomin acikin gidana..! Yafada yana yar Dariya itama Dariyan Take kan Cinyarsa ya zaunar da ita bayan ya zauna ya Jawo Filet din Abincin da Cokali ya Fara bata tana karba Har sai da tace ta Koshi kana ya bata Zobo da Ruwa Tasha kafin Shima ta Ciyar Dashi Har sai da ya Koshi suna kamallawa ya Tashi ya Tayata suka kwashe komai suka maida Kitchen jin ana Kiran Sallar Isha'i yasa ya

12 / 43