Chapter 24 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 43

69K to 72K   out of 126.5K words

kallon Baban Kaduna Ido Cikin Ido yace.

"kiramin Zainullahi a wayarka Bashir...!







*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️

*BOOK 1*

           1️⃣7️⃣

"Gabadayansu ido suka sakarma Alhaji Tsoho Suna kallonsa cike da mamaki Baban Kaduna ne ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Nakira Zain fa kace Alhaji Tsoho..?

Gyada mai kai Alhaji Tsoho yayi yana gyara Siririn Gilashin Dake Idanuwansa yace"Eh haka nace ka Kiramin Zainullahi awaya yanzu..Ka sanar dashi Duk inda yake yazo ina son ganinshi.."Yafada Cikin Dattako da kamala Dina da Zakiya suka Rike Hannun Juna alamun Nasara.

Daddyn Abuja ne ya Mike yana Fadin"Haba Alhaji Tsoho..Ai bai ma Kamata ka Biye ma wannan Shirmanmiyar mganar ba wacce bata da Tushe ballatana makama ba.Miye Abun Kiran Yaronnmu Mu Tsitsiyeshi kan Abunda zan Iya Rantsuwa bai aikata ba wanman karya ce Tsagwaronta da Bita da kulli kawai ake so azomana Dashi Cikin Zuru"a Domin abata mana Suna.."

Yafada yana Kumfar baki Cike da Bacin Rai Baban kaduna da su Inna Hannatu kuwa Jinjina kai Suke alamun Gamsuwa da Zencen Daddyn Abuja,Abba kuwa Zaune yake kawai kansa na kasa yana Kiran Sunan Allah yama Rasa wani Tunani zai yi ko kuma ya Zai Dora Abun akan Mizani.

Alhaji Tsoho ya Dade yana kallon Daddyn Abuja kafin ya Saki Mirmishinsu na Manya kawai ya Juya yana kallon Baban Kaduna yana Fadin"Bashir kiramin Zainullahi nace ko..? Umarni nake baka ba Shawaranka nake nema ba..".

Yafada cikin Kakkausan Murya Inna Rukkaya Ta Bude baki zatayi mgana ya Daga mata Hannu yana Fadin"In har na isa Daku kada wanda ya kara mgana..Bana so ku zage da yawa Daga baya kuzo kusha Kunya..,Daga yar wajensa Har Zainullahin Duka namu ne Domin Da na kowa ne Mugu sai Mai Shi..Kuma In ba Rami me zai kawo maganar Rami..?bawai Ina da yakinin Gaskiyan Abunda suka Fada bane ammh In babu Gaskiya meyasa sai nan Gidan zasu zo..? Bauchi Tana da Fadi da sai su nemi Gidan Daya fi Namu suna da Asali,ammh kuma Kai Tsayen nan suka zo..Kuma karku manta yarinyar tana aiki Tare dasu Zainullahi a asibiti baku Hango Wani Abu Acikin Wannan Zencen..?

Ya karishe Fada yana Binsu Da kallo Daya Bayan Daya,Yana karantar yanayin Fuskokinsu Sai kuma daya Fada sai kowa Jikinsa yayi sanyi,Daddyn Abuja ya koma ya zauna kaawai yana Salati acikin Ransa,Hajiya Batula na gefe Tana kallon Komai Su kuwa Dina da Zakiya Farinciki ya cika Ransu kwamishina kuwa Nadama ce Mai Tsanani ta Shigeshi na yarda ya sake ma Rayuwarsa Da yawa haka in ba Domin haka mai zai kawosa nan da Kimarsa yana Fadar mgana ana karyatasa Kwarai yana Cikin Nadama mai Tsanani.

Baban Kaduna ya Fito da waya ya Nemo Lambar Zain ya Kira sai kuma,sai tayi kamar zata Shiga sai ta Dauke Cikin Tararradi Ya Dago yana Fadin"Alhaji Tsoho Layin Zain baya Tafi fa.."Kai tsaye yace"Kira na Hadiru kaji..ko basa Tare shi ya Nema mana shi..'

Ba musu ya juya akalan Kiran Zuwa ga Haddir wanda ana Kira wayar ta Shiga ammh har ta katse bai Daga ba Baban kaduna ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho yana Fadin,"Na Kirasa bai Daga ba.."Nan ma kai Tsayen yace"Sake Kiranshi Bashir..Insha Allahu zai Daga
Jin Haka yasa ya sake Kiranshi

Haddir kuwa Lokacin da Kiran Baban Kaduna na Farko ya Shiga wayarsa yana kan Mashin Ya Shigo garin Bauchi Suna Tafiya Sun Fita Bauchi kenan sun Dau Hanyar kano Wani karfe na Jikin Taya ya Fita Daga Motarsu.

Hankalinsu ya Tashi gashi ba Garejin Akusa sai ya bar Zain nan Wajen Motan ya Samu wani mai Mashin Ya Daukosa zuwa Cikin Gari ya Sauka adaidai Garejin da yake kawo Motarsa gyara,Ya Dauko Walet dinsa yabama mai mashin Din kudinsa kenan ya sallameshi Sai yaji Wayarsa na Ringing yana Daukota Sai da Gabansa ya Fadi Daya ga Sunan Baban Kaduna Cikin Girmamawa ya Daga Kiran.

Sallama yayi Baban Kaduna ya amsa yana Fadin"Ina ka shiga ne in kiranka baka Daga ba..?cikin Girmamawa Haddir yace"Wayar tana Aljihu ne ban ji kiran Ba Baba.."

Baban Kaduna ya Numfasa yana Fadin"Kuna Tare da Zain ne..? Na kira wayarsa bata Shiga..? Wani Rugurugu Haddir yaji Dakyar ya Fizgi mganar yana Fadin"Ehm...Ehm..Muna Tare munzo Cikin gari Daurin Aure...!ya karishe Fada yana Goge wani Zufa Dake ketomai Duk da Iskan Dake kadawa awajen

Kai Tsaye Baban Kaduna yace'"Ok Toh kuyi maza ku Dawo Gida yanzu yanzu..Alhaji Tsoho keson  ganinku.."Yafada Daidai Lokacin Da Haddir yaji Muryan Alhaji Tsohon yana kara Jadadda suyi Sauri fa ai Haddir Bai san sadda ya samu Jikin Garu ya Lafe ba yana maida Numfashi Baya Duba ammh Tabbas Ranar Daya ke ta Gujema Zain ce Tazo baya Raba Dayan Biyu Dina ta Fallasa mganar Cikin ga Alhalinsu.

Har Baban Kaduna ya gama Hello Hello Dinsa yaji Shuru ya katse Kiran Haddir bai sani ba Zufa kawai ke ketomai Tuni yaji na Maransa ya Daure maimaita Salati kawai yake acikin Ransa yasan kuma ba wata Dubara sai ta Allah Dakyar ya iya Karisawa Cikin Garejin sukayi magana da Mai Garejin Dayake sun saba Yana kawo gyara wajen bayan ya gayamai Matsalan Nan ya bashi Cikin Yaransa guda biyu Daya yana Da Mashin ya Dauki Haddir su biyun suka koma Wajen Motar.

Suna zuwa Haddir ya kalli Zain wanda ke jingine Jikin motan Kallo Daya zakamai ka Fahimci baya Cikin Natsuwarsa,Cikin Tsausayawa yace"Bakaniken nan zamu bari anan..Zan bashi Key din Motar in ya gama gyaran motar zai Tukata zuwa Garejinsu Daga baya zan zo na karba.."Cikin Rashin Fahimta Zain yace"Bangane ba..?motar haya zamu samu Zuwa kanon..?

Bazai iya kallonsa ba Shiyasa ya Juya baya yana Fadin"Gida zamu koma..Na samu wayar Baban Kaduna kan cewa Alhaji Tsoho na neman mu dagaggawa.."Gum Zain yaji kamar an Bugamai Guduma asaman kansa Cikin Rashin Fahimta ya isa ga Haddir ya Juyo Da Fuskansa yana Fadin"Me kake son Fada Haddir..?
Cikin karaya Haddir yace"Banda...Tabbas ammh ina Bakincikin Sanar dakai Dina ta Rigamu...Ina Zargin mganar Cikin nan takai ga iyayenmu..!

Girgiza kai Zain ya Farayi kamar wani Zararre yana Fadin"Kai ina..? Karya ne Wlh bata isa ba...Kila dai Kiran na Taron nan ne,kasan Alhaji Tsoho ya matsa fa.."Yafada Cike da kwarin Gwiwa,Cikin son yarda da Mganarsa Haddir ya Gyada kai yana Fadin"Allah yasa hakan.."Zain cikin karaya da Rauni yace'Ameen

Daga haka Haddir ya Fara Taran musu Mota sai dai basu samu ba Wajen Minti goma sai bakaniken yace su Jira gyaran bai da yawa yanzu zai gama,sai gashi Cikin Ikon Allah ko Minti Talatin baiyi ba ya gama gyaran Haddir ya Hau ya Bata wuta yaga Komai Daidai 5k ya bashi yace yakai ma ogansu su kuma ya basu 2k,Daganan suka Hau Mashin dinsu Su kuma su Haddir suka Hau tasu Motar suka Juya zuwa Gida Zuciyoyinsu Kowanne yana Saka Abubuwa Dadama.

Gudu Haddir yayi sosai Cikin Lokaci sai gasu sun iso Haraban Gidan Alhaji Tsoho Suna Fitowa Daga Motan su da Jeep din da su Kwamishina suka zo da ita suka ci karo Sai kuma Excort dinshi Guda Daya da Mamaki Haddir da Zain suka kalli Juna cikin alamun Tambaya,ganin basu da masaniya Dukkansu yasa suka Nufi Hanyar da zata Sadasu da Babban Falon Gidan na Alhaji Tsoho.

Haddir ne agaban Gaba Zain na Biye Dashi abaya cike da karfin Gwiwa koda suka ga Takalma akofar Falon Basu Tsinke ba sanin Duka iyayensu yau suna gidan na Alhaji Tsoho Shiyasa suka Shiga da karfin Gwiwansu Musamman ma Zain,gwara ma Haddir Tsoro ya Shiga Zuciyarsa.

Akusan Tare suka yi sallama akuma Tare Duka Jama"ar Falon suka Daga suna kallonsu Lokaci Daya suna Amsa Sallaman nasu Atare yadda Duka iyayen nasu suka Zuba musu ido ne yasa Jikin Haddir kawai yayi sanyi sai kaawai ya samu kansa da kwarema yan Falon kallo Daya bayan Daya zuciyarsa ta Tsaya Cak ne sanda yaci karo da kwamishina da Hajiya batula bai gama Mamaki ba sai da ya sauke ganinsa kan Dina da kawarta Zakiya suna kallonsa Cikin Wani yanayi ai sai Haddir yaji kamar an Dasashi lokaci Daya kuma Yaji kansa ya Sara wanda yasa ya Dafe kansa Lokaci Daya yana Kiran sunan Allah Cikin Rawan Zuciya da Rawan kafa

Zain kuwa Da zuciya Daya bai Fahimci Halin da Haddir ya Shiga Ko domin Shima bashi da Natsuwar ne,Wucesa yayi ganin ya Tsaya bai ma Lura da Su Dina ba Idanuwansa kawai iyayensa kadai suke nunamai acikin Falon kai Tsaye Alhaji Tsoho ya Nufa yana zuwa ya Zauna agefensa yana Fadin"Kai Tsohon Likitan nan ka cika Takura Miye kake ta kiranmu baka ya"......!

Sauran Kalaman Bakin nashi Sun makale ne sanda ya Dago zai Nuna su Baban kaduna kawai karaf Suka Hada ido Hudu Da Dina Wacce Daman Tunda ya Shigo Take nacin kallonsa Taga in ya ganta ya zaiyi aikuwa yana ganinta sai ya Fara Tunanin Gizon ta ne ya gane da Fari kafeta da ido yayi yana kallonta Cikin Bushewar Miyan Baki kafin ya waiga yana kallon Alhaji Tsoho irin kana kallon Abunda nake gani Sai dai kuma..? Kawarta Zakiya Dake gefenta Dukkamsu suna Jifansa da wani manufukin Mirmishi Kamar wani wanda Wutar Lamtarki taja Haka ya Mike Jikinsa Ko"ina ba inda baya Rawa Idanuwansa ya Rufe Cikin Nuna ta yatsa yake Fadin"Dina..!

Kallonsa Tayi Ido Cikin Ido Kafin Tace"Na"am Zain..."Tafada tana wani karkatamai kai Idanuwansa gabadaya sun Rufe ya manta da Wadanda ke Falon ya fara Taku zuwa Gareta Kowani Taku kuma Kirjinsa na wani lugude kamar amafarki Yaji Muryan Alhaji Tsoho yana Fadin"Kai Zainullahi ina zaka..? Maza dawo nan ka zauna..!

Yafada Cikin Kakkausan Murya,Cak ya Tsaya sai Lokacin kuma Ya Fara dawowa Cikin Hayyacinsa ya Lumshe Idanuwansa ya kara Budewa yana Bin Kowa Dake falon da kallo So yake ya Gani Da gaske ne Dina ya gani ko Gizon ta ne..? Yakuwa kara ganin Gaskiyan Harda karin Kwamishina da Hajiya Batula,Gabadaya Falon Shi aka zuba ido ana kallonsa Idanuwansa ya Sauke kan Dina kyam kamar an Dasashi Wani Irin Hajijiya ce da wani Taurin Abu yake taso mai kamar zai kadashi Rufe ido yayi ya sake Budewa Still Dai gaskiya ne Tuni yaji Numfashinsa ya Tsaya Cak ya Daina aiki.

Cikin Bacin Rai Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fada'Ko baka jina ne..? Cewa nayi ka Dawo nan ka zauna.."zuwa Lokacin Tuni Jikin Su Umma ya gama yin Sanyi da Abunda zain yayi wannan ya nuna akwai wata akasa atsakaninsa,,Nene kuwa kai kawai ta Sadda Tana jin Duk Wata gabarta na Saki Haddir ne Daya ga Ran Alhaji Tsoho ya baci ga Zain kamar baya Cikin Hayyacinsa yasa ya Daga kafarsa Da yayi masa Nauyi ya isa ga Zain din ya Rikosa yana Fadin"Muje Alhaji Tsoho na Kira..!

Kamar wani karamin yaro ya Juya yana kallon Haddir lokaci Daya Yana Fadin"Kaga Abunda Idanuwana suke ganemin kuwa afalon nan Haddir..? Cikin Wani irin kunya da Nadama Hade Tsausayi Haddir ya gyada mai kai yana Fadin"Eh nagani Zain..Yanzu ba Lokacin mgana bane muje ka amsa Kiran Alhaji Tsoho.."

Karyansa kuma ta karse yau..Haka Zain yake Fadi acikin Ransa Har suka isa Gaban Alhaji Tsoho wanda ke Binsu da kallo Cike da Nazari Cikin Dakiya Haddir ya Zaunar da Zain Kusa da kafafun Alhaji Tsoho Shima ya koma ya zauna Gefensa kansu suka maida kasa Haddir Nata Kiran Sunayen Allah ayayinda Zuciyar Zain Tana Daina ma Bugawa bakinsa kuwa Motsi yake ammh kuma baisan me yake Fada ba.

Gyaran Murya Alhaji Tsoho yayi kafin ya Daga Dayan Takardan Dake Hannunsa yana Fadin"Wani Likita ne ya baku wannan Shedar acikin asibitin Saulawa Spealist..?ya fada yana Kallon Dina Wacce Cikin Ladabi ba alamun Damuwa tace"Dr.Imran ne Ranka ya Dade.."Atare gaban Haddir da zain ya kara Bugawa kuma atare suka Dago suna bin Takardan Dake Hannun Alhaji Taoho Da kallo Sai dai Daga nan Basa Fahimtar komai Zain Dai kafe Dina kawai yayi da ido yana kallonta da Tambayar ni zaki ma Haka Don Kutumar Ubanki..?

Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Kai Hadiru kasan wani Dr.Imran a asibitinku..? Cikin Sanyin murya ya Daga kai ba mgana Alhaji Tsoho yace"Toh Tashi..Kayi maza ka Dauki Mota kaje asibitin ka Taho min Dashi nan yanzu.."Daga shi Har zain sai da suka kara kallon Alhaji Tsoho aammh ganin yanayinsa yasa Basu kara marmarin kallonsa ba Da Sauri Haddir ya mike yana Fadin"Toh Insha Allahu.
!

Da Hanzari ya Fice Daga Falon Har yana Hada Hanya yana Fita Baban kaduna ya Kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Alhaji Tsoho zaman me meke haka ne..? In zain ne gashi ya iso ka Tambayeshi ya gayamaka gaskiyan mgana Atashi wannan Taron mara amfani kowa ya kama gabashi.."Wani Mirmishi Takaichi kawai Alhaji Tsoho yayi kafin yace"Yaro Yaro
ne...Yaro man kaza ne.."

Yana Fadin Haka ya koma ya Gintse Ransa kawai yana Bin Zain da kallo Cikin Takaichi Da Bakinciki Wanda ke Fitowa Daga kasan Ransa Duk da bai da Wani Sheda kan Zain bai aikata wannan Fasadin ba ammh kuma alamun Rashin Gaskiya da Kamshin Gaskiya sun bayyana Garesa sai dai kuma Koda Hakan ta kasance yayi alkawarin kamanta gaskiya ga Duka Shashen Insha Allahu.

Har Haddir yaje asibiti ya Dauko Dr Imran Alhaji Tsoho bai kara mgana su Inna Rukayya ne ma ke Cecekuce,Dina kuwa da Zakiya Zukatansu kamar Farar takarda Saboda Fari,Zaim kuwa Tunda Haddir ya Tafi yana nan zaune inda yake Motsi mai karfi ma Bayayi kansa na kasa Baya ma Marmarin Dagowa saboda yadda Kowa na Falon ke jifansa da Wani irin kallo wanda ke kara Tsinkamai ya"yan Hanji.

Shigowar Haddir da Dr.Imran ne yasa Falon ya Dau Shuru gaban Alhaji Tsoho Suka Rusuna Dr Imran ya gaisheshi ya amsa Cikin kulawa kafin Dr.Imran yace"Ina cikin Office Dina Sai ga Dr.Haddir yazo ya sameni da cewa Ka umarceshi Dayazo ya Daukoni kana Nemana..Allah yasa Lafiya Ranka ya Dade..?

Alhaji Tsoho Ya muskuta yana Fadin"Eh hakane...Karbi nan.'ya fada yana Mikamai Takardan Dake Hannunsa wanda keda Tambarin asibitinsu wanda kuma Dr Imran din ya basu Sakamakon Cikin Dina ajiki Da Sauri ya Gani na wasu sakwanni kafin ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho bai samu Zarafin mgana Alhaji Tsoho ya katseshi da Cewa"Ka gane wannan Takardan..?.

Dr Imran Dagowa yayi yana Bin Mutanen Falon da kallo sai alokacin Yaga Dina da Zakiya Cikin mamaki ya ke kallonsu da Neman karin Bayani Ido Kawai zakiya Ta kadamai Cikin Takaichi Inna Hannatu tayi Tsulum Tace"Kai Shashasha...Tambyarka akayi bawai an ce ka juya kana kallon wasu ba..!

Tafada Cike da Takaichi Cikin Wayancewa ya waiwayo yana kallon Alhaji Tsoho Lokaci Daya ya gyada kai yana Fadin"Eh Tabbas..Ni da kaina na bada ta  ta Shekaranjiya da yammah..'

Alhaji Tsoho yace"Kai kayi Test din..? Nan ma kai ya Girgiza yana Fadin"A"a Bani keda alhakin wannan ba nidai Dina da kawarta Zakiya  gasunan sunzo sun Sameni kan Dina Bata da lafiya na Duba Toh Bisa Tambayoyin da nayi mata ne sai na Fahinci kamar Gwajin Ciki ne ya Dace da ita nan kuma take na Dibi Jininta na kai Lap dinmu na Basu suka Gwada kuma suka Fitar da wannan sakamakon.."

Yafada Cikin Fargaba da kuma Tunanin meyake faruwa..? Kowa yaji Abunda ya Fada Cikin Hikima Alhaji Tsoho yace"Ka Tabbata wannan sakamakon na gaskiya ne..? Kai Tsaye Dr.Imran yace"Wlh Allah kenan..Wannan Sakamakon Gaskiya ne..In ma baku yarda ba sai akoma asibitin akara gwadawa a gani"Alhaji Tsoho ya Dagamai Hannu yana Fadin"A'a Ba Bukata ai ka Rantse..In ma karya ka Fada kai da Allah..Mungode..Kai Hadiru bama Abubakar Key din Motarka ya maidashi..'

Ajiyar rai ya Sauke yana Fadin"Nagode Ranka ya Dade.."Daga haka ya mike yana Tafiya yana waiwayansu su Dina kamar zai Fadi Dina kai t kauda zakiya kuma Fari kawai ta mai ido alamun zamu gamu,Yana Fita Sadiq Daya karbi Key din Mota hannun Hadir yabi bayansa Ya Daukesa ya maidasa Har suka isa Dr.Imran kansa na Kulle ya Tufka ya warware ammh yakasa gano Bakin zare yaso ya Tambayi Sadiq  sai dai Rashin Samun Fuska yasa Ya kama Bakinsa..

Dr Imran na Fita zakiya ta Fito da wayarta Tana ma Dina Rada Tana Fadin"Yanzu Wasan zai Fara Daukan Dadi..Bari na Karisa Dayan aikimn."Mirmishi Tayi mata Cikim Kwarewa Ta Shiga Wsop dinta bayan ta Bude Data Ta Lalubo Lambar Zaina wacce Dina Ta Sato mata awayar Zain Tunda Wayarsa bata da matakan Tsaro,wasu Bad pics Take Turamata wanda Dina ta Daukesu ita da Zain cikin yanayi mara Dadin kallo Wajen guda Goma ta Tura mata Sai da Ta Tabbatar daya Shiga kana ta Fita Taje Bangaran Sakoninta ta Lalubo lambarta ta Tura mata sako Kamar haka...!

*Kina Bukatar sanin wani Abu game da wanda kika bama Amanarki Da Duka yardanki..? Toh in dai kin Ci karo da Sakon nan ki Bude Data dinki ki Shiga Wsop zaki ga na Tura Miki da sako..!*

Na Farko kenan na Biyu kuma sai Tace *Nasan zaki Shiga Rudu da Dimautuwa ko..?Kina kuma neman Karin Bayani..? Toh zaki sameshi Cikakke Harda ma wadanda baki sani ba..Kiyi Hanzari Kizo gidan Kakanin Mijinki zaki samu Duka Amsoshinki yanzu yanzu...*

Tana Gama Tura mata da Ta Tabbatar da ya shiga sai ta Kashe wayar Dama Sabon Layi ta Siya Kuma saboda wannan amfanin Tana gamawa ta Taka Kafar Dina Tana Fadin"All D Plan Done..Sai Abu Daya kawai ya Rage Tabbatar da Auranki da zain.."Tafada tana wani Juya ido Dina batayi mgana ba ammh Ranta kamar Farar Takardan Saboda murna

bangaran Alhaji Tsoho kuwa Dr Imran na Fita Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina yana Fadin"Kayi Hakuri fa...Bawai don ban yarda da Abunda Kazo min Dashi bane..A"a ko Daya sai Domim kada mu zama Wasu Mutanen da Marabansu da Dabbobi kadan ne..Ko miye ya Tunkaromu mu Maida Hankalinmu mu Bincika in mun Gano Gaskiya kada mu Fusata..Mu Natsu mu yanke Hukunci Yadda ya Dace.."Kwamishina na jinjina kai yake Fadin"Hakane...Tabbas na yaba da Hikimarka.."Yafada yana jinjina ma Kaifin Basiran Alhaji Tsoho.

Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Dina yana Fadin"Diyata...Wani Shaida gareki da zai Tabbatar mana Da cewa Zainullahi ne Uban Cikin Jikinki..?

Yafada yana kallonta kai ta Dukar kasa ganin Falon kallo ya Dawo kanta Zain kuwa Tunda Yaji Abunda Alhaji Tsoho yace kansa ya kara kasa kamar wanda zai Kifa Saboda Tashin Hankali,Zakiya ce ta Rike Hannun Dina tana Daga mata kai Shiya Bata kwarin Gwiwan Dagowa ta Fara mgana"Saboda Shine kadai Saurayina..Kuma Tunda Nake Shine kadai Namijin Danake irin wannan Mu"amalan Dashi.."

Dam...Gaban Kowa ya Fadi,Kowa sai ya saki baki yana kallon Dina Alhaji Tsoho ya Cije Abunda yake ji acikin Ransa yana Fadin"Ai bamu san haka ba Diyata..? Cikin Dakiya da Rawan Murya Dina Tace"Shi ya sani..Shi yasan komai...Yafi Kowa sanin Bayanshi bana Mu"amala

24 / 43