Chapter 15 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 43

42K to 45K   out of 126.5K words

wani Abu Jalal.

Cikin Farinciki Da Jin Muryan Dan"uwanta Tace"Aboki Zainullahi Yauwa..Ashe ka samu Labari..? Yana Shafa Sumar kansa yace"Eh yanzu Mukayi Mgana da Firstlove Take Fadamun Ta Fara Rigiman sai Taje nace ta bari na koma Gida sai Muyi mganar.."Zareena na Dariya Tace"Wlh da gaskiyanta ita da Zafira ba wanda ya Taba zuwarmin gwamma kai da Haddir kun Rakoni Lokacin da Umma zata maidani Wannan Karon Tunda ba Gida na Haihu ba Ina Bukatar ganin Duka Ahalina.."

Zain yace"Insha Allahu karki Damu Abokiya Zareena ga Ummamki zata yi Kokari Taga Ta isa kan Lokaci.."Ya karishe Fada yana Dariya Zareena tace"Fadi ka kara Gobe Abba yace Min Umma zata tafi Lagos yama Mijin Inna Hannatu mgana zai nema mata Flight din da zai Tashi Da Daddare da Safiyar jibi zata iso nan din..'

Zain yace"Uhm kaji masu Umma...."Zareena Tace"Kwarai wanda Bai da Umma kuma Sai Jin Haushi.."Zain yace"A"a Fadi ma wanda bai Dashi Ni ina Da Neneta.."Dariya Ta saka kafin Tace"Yanzu muka gama mgana da Aboki Haddir yace min ya kiraka ka Baka Daga sai nace bari na gwada kiranka nagani sai gashi kuma ta Shiga..Gamu asibiti ammh yanzu za"a bamu sallama mu koma Gida.."

Zain yace"Eh naga Kiransa Ban Kusa da wayar ne..Allah Sarki Abokiya Zareena Allah ya Raya Jalal yayi kanwa kenan Ina angon Karni mijin Zareena.."Tana Dariya Take kallon Mijinta Lokaci Daya Take Fadin"Gashi a gefena..Ga Jalal mana yana gaida Uncle Zain,nidai Har kai da Aboki Haddir ku Taho Don Allah Kila sai ya samu Wata Yar Baturiya anan su Daidaita Tun Da naga alaman ya Fara zama Tazuru ba Aure.."

Zain ya Saka Dariya Yana Fadin"Wlh ai yama zama Tazuru kawai ya jira in Wannan Jaririyar ta Girma Sai ki bashi Ita ya Aura..."Zareena ta saka Dariya Harda Jawaad Dake gefensa Tunda Wayar a amsa Kuwawa aka sakata Zareena Tace"Kai mugu ne Aboki Zain Sai na gayamai.."Zain yace"Gayamai ko yaji Haushi nan da Wata Biyar musha Biki..Haddir fa ina jin Ko Budurwa bai da ita.."Zareena ta kada kai Tana Fadin"Zai yi ne in Lokacinsa yayi da yardan Allah.."

Zain yace"Allah ya yarda..Ba Angon karni Wayar mu gaisa..Nan ta mikama Jawaad wayar ya karba suka gaisa da Zain ya yi mishi Barka Daganan sukayi Sallama Bayan sun gama wayar ne Sai ya Kira Nene nan take Shaidamai Haihuwar zareenan yace sunyi mgana Daganan ya tada Motarsa ya Nufi Gida,Koda yaje chan Rigimar Zainarsa ya tashi kan ya barta Taje sunan Zareena ba yadda ya iya Dole ya amince Sai da ya koma Gida sukayi mgana da Haddir inda yace Daman Zareena ce tace ta nemi Wayarsa bata samu ba,Cikin Dakile Zencen Yace mai Sunyi mgana Daga Haka ya katse Kiran Saboda Bayaso Haddir din ya Jefomai Tambayan Ina yaje har ya Kirashi bai Daga ba.

Washegari da Safe kan ya Tafi aiki ya Biya Gida Ya gaida su Nene nan yaji Tafiyar Umma yau zata Bi Jirgi zuwa Lagos,Bai sani ba kawai Umma tace mai Tare da Zainarsa zata tafi mamaki ya kamashi Yace ma Umma"Umma na Dauka sai Zuwa Suna Sauran kwana Biyu Lokacin Jirgin da wadanda zasu Tafi Sunan ya samu..?

Umma Ta kalleshi Tana Fadin"A" a Tare Da ya'yana zan Tafi...Ta kano zamu Tashi Zuwa Lagos Zafeera nachan na Jiranmu."Mamaki ya kama zain kawai sai ya Fara Tura baki yana Fadin"Nifa Umma ban amince Tatafi yau ba gaskiya.."Umma bata kulashi ba Ta kalli Nene Tana Fadin"Nene Gayama D'anki Da yata zan Tafi Yaji da wai ma.."Daga Haka Tayi Shigewar Daki Ta barsu nan Nene ta Lallabashi ya yarda,Dole ya Kira Zaina yace ta Shirya zata Bi Umma Ta Fara Murna tana Tsalle Ta Fara Shirya kayanta ta Kira Laila ta gayamata Ta kuma ce ta Dinga saka mata Atendence kafin ta Dawo Da haka sukayi Sallama,Saboda Zumudi Ko Ta Jira Zain din ya Dawo batayi ba ta Hado kayanta zuwa Gida,Sai da tazo Taji Labarin Harda Zafira zasu Tafi ta fara Murna Nene da Umma na Musu Dariya Zain yana asibiti Halima ta Kirashi kan zasu Tafi Suna Gidan Alhaji Tsoho baro asibitin yayi yazo Sukayi sallama Daga Halima sai Umma Direba ya Tafi Dasu kano,Wajen La"asar suka isa,Salloli kawai sukayi suka Nufi Airport Dama sun ci Sa"a sun samu Jirgin Azman wanda zai yada Zango a Birnin Ikko Suka Shiga Bayan Inna Rukayyah ta Rakasu har Airport din Tana musu Fatan Dawowa lafiya Domin bazata samu zuwa ba Inna Hannatu ce Zata tafi.

Jirginsu ya yada Zango A Murtala Muhammed International Airport Dake Birnin Ikko,da Misalin 7pm na yammah Direban Gidansu Inna Hannatu yazo ya Daukesu Zuwa Gidanta Dake Victoria island,Nan sukaci Abinci sukayi Sallah Ba zencen zama Domin Jirgin Karfe 11:30pm na Dare zasu bi Zuwa U.s Babban Birnin America.

Koda 11pm Tayi a Airport Tayi Musu Daman Mijin Inna Hannatun ya Riga yayi musu Bucking Tunda Tafiyar Harda Ita Lokaci nayi kuwa Jirginsu ya Daga Basu isa ba sai Washegari da Hantsi Dama Tun Suna Lagos Sunyi waya Da Zareena sun gayamata Lokacin Hawan Jirginsu ita kuma sai ta Kin Taci Lokacin Saukarsu Suna Sauka suka ga Jawaad da Dansa Jalal Sunzo Daukansu a Filin Jirgin nan suka Rankaya sai Jerin Estate din da Ma"akatarsu su Jawaad ta basu Umma ce kadai Ta Taba Zuwa Lokacin Da Zata maida Zareenar Bayan Jawaad din ya kawota Gida Ta Haifi Jalal Lokacin ya samu Hutun Karshen Shekara ne sai suka Tattaro Gabadayansu Zuwa Mahaifarsu Sai bayan Ta Haihu Tayi Arba"in kana suka Dawo Da Rakiyar Umma da na Mama Safiya Matar Dadyn Abuja,Tunda Daman Tun Dawowarsu kasar ba wanda ya Taba Zuwar mata sai wannan Zuwan Wanda Bakin Zareena yaki Rufuwa Saboda Murnan ganin Ahalinta.









*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️


*BOOK 1*
   

             1️⃣1️⃣

"Sai da su Halima suka kwashe Wajen kwana Goma a kasar ta U.S kafin su Dawo,Kwanansu Hudu da zuwa akayi Suna Yarinya taci Sunan Umma Wato Fatima,Suna Kiranta little Umma Washegarin Suna sai ga Baban Kaduna da Mom Ikilima Sun Biyo Sun ga Zareena da Bby kwana Daya sukayi suka Wuce Cyprus Wajen Sadiq karami Chan Yake Degree dinsa Yana Shekara ta uku achan.

Tafiyar Halima Ta saka Dina Tayi amfani Da Wannan damar Kusanci ya kara Shiga Tsakaninta da Zain wanda take iya bakin kokarinta Koda yaushe suna tare acikin asibiti ne gidanta ne,Ita take Dauke mai Kishiruwan Zainarsa,Duk da baya Jin Dadin Hakan dayake yi Ammh kuma bashi da wani Zabi,Haddir kuwa Ransa ba karamin kuna yake ba in yaga Zain da Dina suna Tare Saboda ya sani Shedaniya ce Kuma bawai ya yarda da kalaman Zain Din bane bama Shi kadai ba Mutane Da Dama suna Dora musu Zargi,Ganin Abun nasu yayi yawa ne yasa ya yanke Shawaran zai yi ma Zain din mgana Tunda yanzu har Fita Suna Tare da Dinar Wani Lokacin da Motarta wani Lokacin da Motarsa Cin Abinci kuma Tun Farkon Tafiyarsu Umma yake zuwa Wajen Nene yana Ci ammh yanzu sai dai Dina Ta jashi Zuwa Waje Su je chan suci Abinci ko kuma ta Jashi Gidanta Su je chan suyi Watsewarsu in Sun gama ta Sulala musu Ko Indomie ne Suci Su Dawo Cikin asibiti Abubuwa dai gasunan ba Tsari Wanda Haddir din yake Tsoron Faruwar waani abu.

Ranar sun Dawo Daga Resutarant Cin Abinci Bayan sun Faka Motarsu a parking Space,Sun Fito Motar Dina ce ita ke Driving Din Motar Dukkansu Sun Fito Suna Dariya Fuskarsu na Bayyanar da Annurin Da Suke Ciko karo Suka ci Da Haddir ya Fito Daga Cikin asibitin zai Fita da kallon Mamaki ya Bisu Dashi Daga Zain Din Har Dina,Zain kuma kallon kallo Sukama Juna kafin Zain din ya kauda kai Dina kuwa Data gaida Haddir Kin amsata yayi sai ma kallon Tsana Daya watsa mata yana kallon Zain Lokaci Daya Yana Fadin"Zain ina son mgana Dakai..!

Yafada Cikin Kakkausan Murya Juyowa Zain yayi yana kallonsa Kafin ya kada kai ya kalli Dina yana Fadin"Shiga ciki gani nan Tafe.."Daga haka ya Juya ya Bi bayan Haddir wanda ya karisa Wajen Motarsa yana Bin Dina da wani kallon Tara saura kwata Ita kuma kai kawai ta gyada kafin ta wuce zuwa Cikin asibitin Tana wani Takun Isa.

Zain na karisowa Kusa da Haddir ya karkace Kai yana Fadin"gani Lafiya ka ke son ganina..? Ido Cikin Ido Haddir yace'"Meka yi kenan Zain..? Kasan Ma"nar haka kuwa..?

Gyara Tsayuwa Zain yayi yana Fadin"Me kenan..?bangane inda ka Dosa ba Mallam.."Haddir ya Murmusa yana Fadin"Karka Raina ma kanka Hankali Zain..Kagane inda na Dosa ina mgana ne kan Wanchan yarinyar Dina,miye yake Hadaka Da ita..? Muharamanka ce..?na lura dakai kwana Biyun nan kun wani kulle ne wanda kuma Nake zargin Ba ta alheri bace..!

Zain ya wani Cije baki kafin ya fara mgana"Bangane Kaga mun kulle ba..?wannan wata irin mgana ce Karfa ka manta Dina Bayan Abokiyar aikina Abokiyar karatuna ce kuma Kawata ce akwai illah ne Don kaganmu Tare..? Kuma wani irin Ba alheri bane kake Fadi Me kake son Fadi...?

Kai Tsaye Haddir yace"Kafini sani..Ina Zargin kun koma Ruwa Kaida Ita kuma Faruwar hakan kamar Barazana ne ga Zubewar mutumcinmu Da naka gabadaya.."Da sauri Zain ya Tareshi Yana Fadin"Tsaya mallam kasan kuwa Zaton Zina... ? Ko kutu akaje Sai ka kawo Sheda Hudu suma sai sun ganin ma Idanuwansu Turmi da Tabarya kana da wannan Shedar ne..?Mganarka kawai kake wanda kuma Ra"ayinka ka Fada mallam Ni babu komai Tsakanina da ita sai na abokiyar aikina ce Fakat.."

Ya karishe Fada Cikin Son Nuna Bakomai Haddir yace"Hmm koma miye kai ka sani Nidai ina Fadamaka nan ba London bane Bauchi ne Wlh Zain ina Jiye maka wani Tsoro ka dawo Cikin Hayyacinka Nidai nagaya maka Tuni nace ka sallami yarinyar nan Ta kama gabanta Ammh kaki In banda kana da Manufa miye na gayyato ta nan Tayi aiki Damu..? In gaya maka ina jiye maka Mtsala Ne..'

Karamin Tsaki Zain yaja yana Fadin"Zato Zunubi Dai koda ya kasance Gaskiya ne..Kuma Hadisi ne guda Ka Rika kyautatama Dan"uwanka Musulmi Zato.."Daga haka ya wuce Ya bar Haddir nan Tsaye yana Binsa da kallon Tsausayi kuma Har acikin Ransa ya yarda da Zarginsa akan Zain ganin yadda yayi wani Wiki Wiki Dashi kada kai kawai yayi ya Bude Murfin Motansa ya Shiga acikin Ransa yana yima Zain Fatan Shiriya

Zain kuwa har ya isa Office dinsa yana Juya Mganar Haddir Tabbas yasan gaskiya yake Fadamai ammh Taya zai iya yakice Dina..? Yayi iya bakin Kokarinsa wajen ganin ta bar Rayuwarsa ammh Abu ya gagara Shi kanshi yana Tsoron Wani abu ya Faru ya Tabbata Cikin Ahalinsa ba wanda zai mai Uzuri uwa uba kuma Zainarsa da wani ido zai Kalleta..? Haka ya wuni Sukuku kamar mara lafiya La"asar ya bar Cikin asibitin zuwa Gida Yaje yayi wanka ya kwanta yana ganin Kiran Dina yaki Dagawa sai ma ya Lalubi Zareena yace ta bama Umma wayar,bayan an bata sun gaisa ya Fara Complain din cewa Matarsa yaushe zata Dawo Umma tace suna Tafe Dole ya Hakura ya maida Wukar ammh Shi kanshi yasan yana Bukatar Matarsa ta Dawo Hakan nan Tunda Sukayi aure Bai Taba bari Taje wani Waje ta kwana Fiye da Biyu ba Shiyasa yake Jinsa Wani Iri.

Ranar asabar su Umma suka Dawo Ta lagos suka Sauka nan Suka kara kwana Washegari Umma da Halima suka Bi Jirgi zuwa Bauchi Ita kuma Zafeera ta Hau Jirgi zuwa kano Taso Binsu Umma zuwa Bauchi Gabatowar Test dinsu yasa ta hakura ta koma kano sai sun samu Hutu,Zain bai ma san Ranar zasu dawo ba sai da ya Dawo Daga asibiti yaji Gida na Tashin kamshi,sai ga Zainarsa tazo ta Rumgumeshi Tana Murnan ganinsa Shima kamkameta yayi Yana Bayyana mata yadda yayi kewarta Ranar dai kwana sukayi Suna Bayyana ma Juna yadda Sukayi kewar Juna.

Washegari kuma Monday ta koma makaranta Ranar kuma suka Fara Test ba zama Sai Hankalinta Duk ya koma kan karatunta Tunda Suna Tun karar Exams Din Second Semister ne,Don ma Allah ya Taimaketa Laila tayi mata Wasu Assigment din Da Data samu Gibi da yawa ba kadan ba.

*****

Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai adade ba"a je ba Gashi Har Su Halima Sun kamallah Test dinsu na makranta Haka ma Su Zafeera,Shiryen Shiryen Fara Jarabawa suke yi nan da Sati Daya Gabadaya Hankalin Halima ya koma kan Makaranta da karatu bata ma samun Lokacin kanta hatta Gidan Umma da Gidan Alhaji tsoho Sai Ranar Sati Take samun Zuwa Saboda karatun Jarabawa bata da wata Natsuwa.

In Ta Shiga Cikin makaranta sai yammah Take Dawowa Suna Chan Libarary ita da Laila da Sauran mates Dinsu Suna karatu,Hakama in ta Dawo Gida Zata Dukufa Sallah kadai ke Tashinta,Sai kuma wani aikin Daya Shafi Mijinta Shi kanshi Zain Din Tsausayamata yake yanzu ganin Ta saka Karatu acikin Ranta Sosai Shiyasa Girki ma sai Weekend take yi Musu Sai Breakfast kafin su Fita daSafe Da Rana kowa Wani Abu yake nema yaci Da Daddare kuma Kafin Zain ya Shigo Gida yake Biyawa wani Restaurant yayo musu Takeway suci Su kwanta Wani Lokacin Har sai ya kwanta ita bata kwanta ba Tana Falo Tana karatu Har sai ya Farka ne in ya Laluba yaga bata sai ya Fito Falo ya Tattara ta zuwa Ciki Toilet yake Turata Yayi mata wanka Wani Lokacin ma abinci sai ya Zaunar da ita ya bata take iya ci Ta Riga ta saba Da Abinci Shi yake Ciyar da ita da kansa Shiyasa Dagashi Har ita In Kowanne ya Tafi Laluransa Da Rana ba wani Abincin Kirki Suke zama su Ciki ba Saboda sun Riga sun Saba Da Ciyar da junansu.

Bangaran Dina kuwa Ta Yarda da plan din Da Zakiya ta kawo mata Duk da Tana Tsoron Zubewar Mutuncin Mahaifinta ammh Zakiya ta Nuna mata Daga Mahaifinta har iyayen Shi Zain din bazasu zo mganar ta Fasu Waje Ba Tunda Dukkansu Suna da kima a idon Mutane zasuyi Abunda zai zama Rufun Asirinsu ne kuma Shine Aure Tsakaninta da Zain,Ta yarda da Shawaranta Sosai Shiyasa Ta Kudura acikin Ranta Six Month Din Datayi Alluran Planing Din Datayi yana karewa Bazata karayi ba In Allah ya Taimaketa Tsarinsu ya Tafi Daidai kamar yadda Suka Tsara,Acikin Zuciyarta Batason Faruwar hakan ammh ya zama Dole ne Tunda Tana son Son Zain kuma Tana Son Kasancewa Tare Dashi Har Abada Har yau har gobe In Tayi mai mganar Aure sai ya kara Maimaita mata bazai Taba Auranta ba Tunda bai Taba Cewa yana Sonta ba ya gayamata ba tun yau ba Mace Dayace Matarsa itace Zaina bazai iya Auran wata mace ba bayan Ita da irin Wadanan kalaman yasa Ran Dina ya kara Baci Batare da wani Dogon Tunani ba ta amince da Shawaran Zakiya ammh Bayan ta sun kara zuwa Wajen Bokan Zakiya na Hanyar kaduna Daman Zakiya ta kaita wajensa Shi yake mata aiki kan Alhazanta ta samu alheri akansu Yake kuma mata aiki in Taga wani Alhaji mai kudi a Tsaida mata Shi ta wanki Rabonta Da suka je mai da Bukatarsu ya Buga kasa yace musu in Sukayi Haka Auran nasu zai Tabbata sai dai yaga Duhu sosai acikin al"amarin Kamar yadda yagaya musu a Farko Suka ce bakomai Kowani Duhu suna Maraba Dashi Sun karamai Zubemai kudi kan ya kara Sakama Zain Din Fitinaniyar Sha"awar Dina Wanda bazai iya kwana bai Kusanceta ba Ko zasu samu Hakkansu ya cimma Ruwa yace karsu Damu anyi an gaba su Jira sakamako kawai Sai Dina tana Koran Zain ammh yana manne mata kamar wani Tsohon Maye mara Zuciya.

Cikin Ikon Allah su Halima suka Fara Zana Jarabawar Karshen Zangon karatunsu na aji Daya,Chan ma Kano Zafeera suma sun Fara,Duk wani Masoyansu yana Tayasu ga Addu"an Fatan Nasara da Sa"a,Sannu sannu kamar yau suka Fara sai gashi Sun kamallah Zafeera sun Riga Halima gamawa a kuma Ranar bata kwana agarin Kano ba Sai Bauchi sai dai su Umma suka ganta Kwatsam Murna wajen su Zainab ba"a mgana Ita Tana gida Ta Rubuta jamb sai Farkon zango karatu Zata Fara zuwa makaranta itama Din ATBU bauchi Abba yace Zatayi bayason Tayi Nisa da Gida,Su Halima kuwa sai Da su Zafeera suka gama da kwana Uku kana suna Suka gama Farinciki Kamar me bakinta yaki Rufuwa,Sai da ta kai Laila Gida kana ta Wuto Gidan Umma Direct Daman Tunda Zafeera ta Dawo basu Hadu ba aikuwa tana Zuwa Suka Rumgume Juna Suna Murna kamar Wasu yara kananan Umma na Dariyan Farinciki Tana Fadin suyi a Hankali Nene kuma na Fadin Yaranki Umma basu Girma sai na Jikinsu.

Bayan gaishe gaishe Dakin su Tun na yamatanci Suka Kule Ciki Inda yake matsayin nasu Har yanzu Tunda Zafeera batayi Aure ba,In tazo Hutu nan take Sauka Itama Halimar nan take wasu Abubuwan nata in tazo Ko Dakin Umma ko Dakin Nene Duka Basu da Shamaki da Dakunan Iyayen nasu.

Hira ce ta Barke Tsakaninsu Cikin Hiran ne Zafeera ta kalli Halima Tana Fadin"Wai Ukti ba wani Bayani ne..?kusan fa Shekara kadan bashi a auranku keda Yaya Dakta..!

Halima Ta gyara zama Tana Fadin"Bayanin me kuma Ukti..? Zafeera tace"Dillah na Haihuwa nake mgana Tun ina kano nake so nayi Miki Tadin munji Shuru ba wani Bayani me Dadi ko matar Likita Tana planing ne..? Halima Ta Daka mata Duka a Cinya Tana Fadin"Uwar planning Din kema kin zama Hajiya mama ko..? Haka wanchan Satin da muke je gaishesu ni da Firstlove take mana Fadan wai ko muna Tsarin Iyali ne Sa"o"in Auran mu Duk sun Haihu Har fa Tsohon can yana mana Nasihan Muji Tsoron Allah.."Zafeera tace"Wlh da gaskiyansu...Yadda Alhaji Tsoho ke Bala"in kaunarku keda Yaya Dakta Zai zo Ganin Ya"yanku kafin ya bar Duniya..'

Tagumi Halima Tayi Tana Fadin"Wlh Nima ina so Ukti...Allah ne bai kawo ba Kinsan Allah ban taba Shan kowani kwaya ba kuma ban Taba Allura ba Firstlove ma baazai bari ba kinsani.."Zafeera Tace"To wani Taimako kuka nema..? Ta Sauke Tagumin ta Tana Fadin"Wani Taimako kuwa Kwanaki Dana Fara mai mganar sai ya Fara min Fada yaushe Duka Duka mukayi Auran Ballatana ace bamu Haihu ba..shi bayason Irin Haka Haihuwa Lokaci ne, in Lokacinta yayi Komai zai Wuce Daga Lokacin yace na bar mganar Babu Komai Dukkanmu lafiyanmu Lau Tunda Daga kowani Bangaran mun gaji Haihuwa.."

Zafeera Na Dariya tace"Kuma fa Hakane mganarsa...In Lokacinta yayi Burum zamu ji Ukti na Faman Laulayin Ciki ana Tsirtar da yawu.."Ta fada tana wani yamutsa Fuska

15 / 43