Chapter 27 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 43

78K to 81K   out of 126.5K words

Shiga Wani Hali Uwa uba ga Yarinyar nan Abun Tsausayi Wlh.."

Hajiya Mama Ta jinjina kai Tana Fadin"Allah Miki albarka Safiya...Naji Dadin mganarki Fatima da Aisha Don Allah ku bar wannan kukan..Ke kuma Zareena Ji da yarinyar nan Sai kukanta nake ji Tun dazu ku kuma kuzo mu tafi yana Jiranku.."Daga haka ta Fice Daga Dakin Inna Rukayyah da Inna Hannatu suka Rufa mata Bayan Sun iske Alhaji Tsoho nata Lallashin Ya"yansa da Nasihu Sai gashi Lokaci Daya Sun Warware sun kuma ji Damuwarsu ta Ragu Suma Su Inna Rukayyah suka nemi Waje suka zauna suna Sauraransu Cikin Mganar Alhaji Tsoho ya kallesu Yana Fadin"Kun gano Inda muka Kuskure kan wannan Al"amarin..?

Gabadayansu kai suka Girgizamai alaman A'a Cikin Hikima Yacigaba da Fadin"Kuskuran mu kadan ne .Bazan ce Saboda mun kai ya"yanmu kasashen Ketare karatu ne ya Jawo mana wannan Abun ba A"a Abun ba Haka yake ba Duk da wasu Dalilin Haka Suna Lalacewar ammh Hakan ba zai zama Hujja ba Tunda Nima nayi wayon Kashashen Ketaren kuma Wlh Allah ban yi wannan Lalacewar ba Kuma gaku kunyi kuma har yau wani Abu mai kama Da haka bai Faru ba..Nayi Tunanin Sakacinmu da kuma Rashin Bibiyar ya"yanmu akan lokaci Ko kuma nace Rashin Saka Ido Inda ace muna Kokarin Saka ido Sosai koda basa gabanmu Achan Kasar da suke mu Samu wani mai amana wanda zai Dinga Kula da Shige da Ficen ya"yanmu na Tabbata in da Muna Haka zamu samu labarin wani Abun kafin ya Girmama kun gane Abunda nake nufi..?

Gabadayansu suka ce'Hakane Tabbas..Alhaji Tsoho.."Mirmishi yayi Cikin Jin Dadi yana Fadin"Yauwa..Tunda mun gano haka Sai muyi Kokarin Kiyayewa Yanzu akwai Ragowan Yaranmu da Basa gabanmu Bana jin Ta zafeera Tana Gaban Rukayyah ne kuma nasan ita da Shitu bazasuyi Sakaci Da Tarbiyansu ba.."

Da Sauri Inna Rukayyah Tace"Insha Allahu Alhaji Tsoho muna iya bakin Kokarinmu.."Alhaji Tsoho yace"Yauwa sai Abubakar karami ko..? Yana ma wata kasa ce .?Da Sauri Daddyn Abuja yace"Shi yana Cyprus ne Alhaji ammh ya kusa kamallawa.."Alhaji Tsoho ya gyada kai yana Fadin"Masha Allah...Sai mai sunan Manya Umaru Faruq shima yana Chicago ko..?

Baban Kaduna ya gyada kai yana Fadin"Hakane..! Alhaji Tsoho yace"Allah ya tsare su..Dukkansu zamu saka musu ido.."Baban kaduna ya Jinjina kai yana Fadin"Insha Allahu Alhaji Tsoho.."Kallonsu yayi Dukkansu yana Fadin'"Mganar Hamdiya kuma inda yafi Sauki za"a Daura auran.."

Daddyn Abuja ya Kada baki yace"Nan za"a Daura Alhaji Tsoho.."Jin haka yasa Kowa yayi Na"ama Da mganar,Alhaji Tsoho yace"Sai Mganar Zafeera Zan bata Lokaci Zuwa bayan Bikin Hamdiya in bata kawo wani ba zan bama yaro nan Ahmed Dama.."Kowa yayi Na"am Da mganar nan sukaci ba Da Tattaunawa,Kafin Alhaji Tsoho ya Hada kan ya"yansa sukaci Abinci Suka koshi suka Sha Ruwa Su Inna Rukayyah kuma suka koma Dakin Hajiya Mama Kowacce Tana hada Kayanta Gobe zasu wuce.

Sai Gabda Mangariba Zaina ta Farka Daga Barci Tana kuma Tashi Da kuka ta tashi kamar yadda Ta kwanta Dashi,Mganar Duniyan bata Tanka kowa ssi Umma da ita kadai Take mgana Dakyar ta Lallasheta Ta Rakata Tiolet tayi alwala tazo Tayi Sallolin Dake kanta azaune Tana Sallah Tana kuka Domin kamar Magiji Haka Abun ke Dawo mata.

Abunci kuma Umma Tayi Tayi ammh Taki ci Zareena Ta kalli Zaina Tana Fadin"Kici Abinci Zaina..Don Allah.."Tana kallon Cikin Idanuwan Zareena Sai Hawaye ta kasa Mgana ganin Haka yasa Handiya Taje ta Kira Hajiya Mama tazo Tana ta Fada kan Zaina Taci Abinci ammh Sai Taki ci sai da Tayi mata jan Ido kana Ta yarda Ta karbi Abincin Daga Hannun Umma ta Tusa Ko Loma Goms Batayi ba Zuciyarta Ta Fara Tashi sai Amai Tun Tanayi da karfinta Har ta kasa Umma da Mama safiya suka Riketa ganin Bata da karfin Jiki yadda Take kuka ne Tana Hawaye yasa Tsausayinta ya kara Shiga Ransu Ruwa aka kawo Umma ta wanke mata baki Hamdiya kuma ta Tsaftace Wajen kafin kace me Jikinta ya Sake Daukan zafi Ta kwanta Jikin Umma Tana Rawan Sanyi.

Abba ne ya aiko kan su Umma su Fito su Tafi Gida,Dole Nene da Umma suka Mike Kowacce Fuska akode,Hajiya Mama Tace Umma ta Kwantar da Zaina kan Gadonta su Tafi sai dai me Tana Mikar da ita ta makalkaleta Cikin kuka da Rauni Karo na Farko Datayi mgana..

"Umma...Zan...Zan biki..!

Tafada Cikin Fitar kwallah gabadayansu da kallo suka Bita Lokaci Daya Ta maida kanta Jikin Umma Tana Sauke Numfashi Ganin haka yasa Hajiya Mama taje ta gayama Alhaji Tsoho Halin Da Ake ciki Cikin Nazari yace"Barta su Tafi da ita..Taje gidan ta Huta na wani Lokaci Shima ai zainullahin baya cikin Natsuwarsa yanzu haka zuwa gaba in komai ya Daidaita za"a samu Masahala.."Da haka Taje tace Umma su Tafi da Zainar gida Inji Alhaji Tsoho.

su Mama Safiya da Mom Iklima suka Taya Umma Kama zaina suka Rakasu har Haraban Gidan Inda Direban Abba ke jiransu,Zareena ma Ta Goya yarta Tabi su Umma,Su Baban Kaduna Duk suna Waje nan sukayi sallama Kowane ba Farinciki ammh Da Sauki ba kamar Dazu ba,Abba ya kalli Umma yana Fadin"Fatima Har yanzu Jikin Halimar..?

Kai Umma Ta Dagamai Tana Jin Taruwan kwallah Saman Goshinta ya Taba wanda yasa Ta Bude Kodaddin Idanuwanta Tana kallonsa Cikin Tsausayawa Yake Fadin"Sannu Halima..Sannu kinji ko..? Nima Hakurin zan baki Allah ya kiyaye kawai.."Yake Fada haka su Baban Kaduna Sallama sukayi Suka Shiga Mota Nene dai ba Baki sai dai kaga Tayi Shuru Kawai Tana kallon Mutane Abun ya Daketa Sosai..

Koda su Umma suka Koma Gida sun iske Sadiq ya koma Labari kuma Tuni yakaima Zainab Tunda Sadiq daya Dawo yake Fadamata itama taci kuka bata ma Kara Jin Wani kukam ba sai Da Taga Shigowarsu Umma haka Tazo ta Rumgume Nene Tana kuka Gefe Daya kuma Tana kallon Umma Dake Rike da Zaina wacce ke Kuka kasa kasa.....

Dakinsu Ita da Zafeera Umma ta kaita ita da Zafeera da Nene Abba kuma ya wuce Dakinsa,Kwantar da ita sukayi suna Mata sannu Jin Jikinta yayi zafi Zareena ce ta Dago Tana Fadin"Umma ko zan kira Aboki Haddir ne yazo ya Dubata..? Wannan zazzabin yayi yawa ajikinta..!

Numfashi Umma ta Sauke Tana Fadin"Kirashi in zaki sameshi.."Tafada Tana kallon zaina wacce ke kara Shiga Cikin Bargo Tana Kudundune kanta Jin za"a Kira Haddir yasa ta Dago kanta da Idanuwanta da suka Kumbura Tace"A"a Umma..Kada ki kira kowa..Ki bani panadol kawai .Domin wannan Ciwon Da nake ji acikin Kirjina Bashi da mgani Har Abada..!

Tafada wasu Tagwayen Hawaye na Zubomata kafin ta koma ta kwanta Tana maida Numfashi Umma Ta Dade Tana kallonta Batayi mgana ba Nene ta kada kai Tana Fadin"Dole azo adubaki Sa"adiya Dare muke gudu..Dama ba mganin Damuwarki zai baki ba, na lafiyarki ce Domin Damuwa ko Mu bamu da mganin Tamu sai Hakuri kawai.."

Zareena Ta Ijiye Jakar Zaina Wacce Ta tattaro mata Daga Gidan Alhaji Tsoho nan Gefen Gado Jakarta ta Dauko Tana Laluban wayarta Cikin karamar Jakarta Take fadin"Kuma Nene Zazzabin yayi yawa fa..!

Hannu Umma Ta Dagama Zareena Tana Fadin"Kyaleta Zareena Ayi mata Abunda take so..Ina Jin Tsausayinta Fiye da yarda nake jin Tsausayin kaina Bari nayi sallahr Mangariba nazo na Taimaka mata tayi sallah Tayi wanka sai na Bata mganin Ta kwanta.."Ba suyi mata gaddama ba Suka Fice Daga Dakin Umma dai Kofar Tiolet ta Tura ta Shiga ta Dauro alwala Tayi sallah Ta Tada Zaina wacce Zazzabin ya karayin zafi Ta kaita Tiolet Ta Taimaka mata tayi wanka Tazo Ta Taimaka mata ta zura mata wata Doguwar Riga Umma Ta kasa Daina Jin wani iri game da Kukan da zaina keyi ta kasa ma Lallashinta,Dakyar ta sakata Tayi sallah azaunr kamar ta Kife

Fita Tayi zuwa Kitchen ta Iske Zainab na Hada Fruit Salad shi ta Diba Ta kai ma zaina Dakyar ta iya Bata tayi Cokali Biyar ta kauda kai Allah yasa batayi Aman ba wannan karon Ta Balla mata panadol Ta bata tasha Ta koma ta kwanta Fadi Take"Umma Rufamin Bargo..Sanyi..Sanyi.."Hakoranta na Haduwa Rufamata Tayi Tana Tofa mata addu"a bata barta ba sai Da taga kamar makyarkyatan ya Ragu kamar zatayi Barci kana ta Fita Zuwa nata Dakin Tayi wanka Lokacin ana Kiran Sallar Isha"i Tayi Kan sallayar ta zauna kawai Domin Gabadaya Gidan yau ba Dadi Nene ma na Dakinta Haka ma Abba Zareena ma Tana Dakin Datake sauka ita da Jalal Zainab Kuma dasu Saudat suna Falo duk da su Yara ne basusan Komai ba Sun Fahinci gidan Ba kamar yadda yake ba Sadiq ma yana Dakinsa bakajin Motsin kowa.

Babu Wanda ma ya Nemi Wani Abu Zainab ce Tayi Tunanin Hada Fruit salat Saboda Ruwa Ruwa ne zai yi Dadin sha Toh banda Wanda Umma ta bama zaina Ko Kitchen din ba wanda ya kallah Zareena ko Tana Dakin Datake sauka Bayan tayi Wanka Tayi sallah Ta Kira Haddir Sai da tayi mai Kira Biyu ya Dauka Sama sama suka gaisa Take Tambayanshi yana ina..? Yace mata yana cikin asibiti..Cikin Jimami tace ina zain Ya bata amsa da bai sani ba Tunda ya Fita da Mota Dazu bai kara ganinsa ba,Kuka ne yaci karfinta ta yanke kiran Shi kanshi Haddir kukan yake Tun Dazu yazo cikin asibitin ya kulle kanshi Cikin Office dinsa yana ta kuka Kukan Tsausayin Iyayensu da Zain din Shi kansa da kuma Uwa Uba Zaina wacce Yake Tunanin wani Hali Take ciki yanzu..? Shi kanshi yayi kuka kan wannan lamarin Ballatana ita.






*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
  

*BOOK 1*

             2️⃣0️⃣

"Zain kuwa Tunda ya koma Gida ya Shiga Cikin Bedroom dinsu ya kulle kansa ya zauna akasa ya Hade kai da gwiwa ya Dinga Rafzan kuka Kukan Daya Dade baiyi kamarsa ba bama zai iya Tuna Rabonsa Daya Zubar da Hawaye ba Duk da ya kasance mai Taurin zuciya BA Abu bane karami bane zai saka kaga yana kuka ko Lokacin Suna yara Haddir yafishi Rauni ko Rashin Lafiya Zareena Take ya Shiga Tashin Hankali kenan Har kuka yana yi ammh bandashi iya wutar Rauninsa Sai dai idanuwansa su kada suyi Jajir Jijiyoyin kansa Su Tashi Radau kamar mai wani Cuta yau gashi Rana tazo Daya zauna Yana ta kuka Kukan Tsausayin kansa Dana kunyar Iyayensa uwa uba kuma kunyar Zainarsa da wani ido zai kalli Firstlove ya gayamata Duk wadananan Abubuwan sun Faru..?ya sani yanzu Lokaci ya Kuremai Karyansa kuma Tagama karewa.

Haka ya kwana cikin wannan Halin bai iya cin komai acikinsa ba Wayarsa kuma Rashin Chaji yasa Ta mutu,Ruwa Kadai yake sakama Cikinsa,Kafin safe wani Mugun zazzabi ya Rufeshi Ga Ciwon kai Dakyar ya iya Tashi yayi sallar asuba ya koma ya Kudundune kan gado yana Rawar Sanyi.

****

Dina na kwance kan Makeken Gadonta,Misalin karfe 9:30am na Safe Tun barcin Jiya bata Tashi ba Sallah ba sai Wajen 7am Tatashi Tayi ta itama Din Domin Hajiya Batula tazo ta matsa mata ne,Kasala Take ji da kuma Tsinkewar miyau Don ma Allah ya Taimaketa Cikin bai Mata Laulayi Sosai ba ballatana ta Wahala ko amai ba sosai Take yi ba sai Taji yunwa in Taci Abincin sai ta Dawo Dashi..

Hankalinta kwance Take Barcinta Ringing din wayarta Ya Tada ita Daga Barcin salama da Farincikin Datake yi Dagowa Tayi Lokaci Daya da karamin Tsaki Kafin ta Jawo wayar Dake gefenta Domin Dazu da asuba sunyi mgana da Ummi maimuna,Tana ganin Zakiya ce ke Kiran Ta Daga da Sauri Tana Fadin"Yanzu fa nake cewa in na Tashi zan kiraki..!

Dagachan Bangaran zakiya ta saki Dariyan Nishadi Tana Fadin"Kaga manya manyan mganin kanana...Mrs Zain Usman Abubakar saulawa Barka da safiya.."Mirmishin Jin Dadi Dina ta saki kafin tace"Barkanmu..Ya gajiyan Jiya... ? Zakiya tace"Gajiya Tabi Jiki..ya Karfin Jikinki..? Ki Dinga kula da kanki Dina Kinsan Ayanzu wannan cikin Shine fa makamin mu..'

Dina Ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wai yanzu haihuwansa zanyi..? Allah ban Shirya Haihu yanzu ba zakiya.."Zakiya tace"Ya zama Dole kuwa Hajiya..Kina ganin ba Domin Cikin nan ba akwai wani uzurin da Danginsa zasu karba ne ballatana Har su Dubeki..? Kima Dawo cikin Hayyacinki.."Dina Ta Kauda zencen da Fadin"Hmmm kawai..!

Zakiya Tace"Na kiraki ne na Gaya miki na cikama Dr.Imran alkawarinsa Daran Jiya Duka nashi ne Bai ma jima da Tafiya ba..Gaskiya zan Dan Raka da Gayen ya san Harka yafi Wadanan Tsoffanfin da Dama chan Basir da girma ya gama Cutar dasu.."Baki Dina ta saki Tana Fadin"Kai zakiya Don Allah ki bar wannan mganar...Ni da nake so kema ki Fidda wani ki aura Duka mu bar Rayuwa barikin nan.."Zakiya Tace"Wa zai yi Aure..? Wai ni..? A'a Wlh ko Baba yagaji da mganarsa ya kyaleni Ba yanzu zanyi Aure ba Dina Domin har yanzu ban samu Wanda yayi Daidai Dani ba nafi son na Auri Ustaz Wanda bai san komai ba na Auresa muyi ta Shan Soyayyarmu.."Dina ta Rike baki Tana Fadin"A ina zaki samu..?

Zakiya Tace"Acikin gari mana..Kina mamaki ne..?karki manta Bawa baya cire rai da Rahmar Ubangijinsa.."Dina Tace"Tsiya na Dake Sani..Ammh kina Take sanin naki.."Zakiya Tace"Mutane nawa ne acikin Duniyanan Suna sani kan Abu kuma Suke Takewa... ? Ke duniyar nan fa cike da Mutane Dabam Dabam masu aikata Laifin ma sun fi kowa sani Ni kyale ni Nafi jin Dadin Rayuwata ahaka kin ganni nan Kedai Da kika ga zaki iya Auran Shikenan.."

Dina Tace"Allah ya Shirya.."Zakiya Tace"Ameen..."Har zakiyan Zata kashe wayarta Dina Tace"Wai ni ya matsayin Matarsa ne yanzu..? Nifa tafi Tsayamin arai kuma Tayaya zan koma Gidansu da zama kina ganin ba mtsala..?

Zakiya Tace"Ai yanzu bai da Wata mata bayan ke..Agaban idanuwanki Kika ga Abunda ya Faru..Na Tabbata ko Waye zai saka baki bazata Saurareshi ba..wannan Firstlove din ya kare Daga Jiya Ina gayamiki..Mganar zuwa Gidansu kuma yayi Daidai..Kinga kin samu Hanyar kusanci da Zain kenan da Duka Ahalinsa Kuma Bashi da wani Ikon Wulakantaki Tunda kina Gaban Iyayensa ne Uwa uba kuma Alhaji Tsoho bazai bari wani ya Tozartaki ba..'

Dina Tace"Hakane....Da Farko ina Jin Tsoron Haduwa da Zain..Gabana nata Faduwa.."Zakiya Tace"Babu Abunda ya isa yayi miki..Yanzu ma Bata ke yake ba..Yana ta kansa ne ki Sharesa karma ki Kirashi In kin koma Gidansu Dole ku Hadu kuma Lokacin bashi da wata mafita.."Dina Ta gyada kai alamun gamsuwa Da sauri Zakiya tace"Sai mun sake mgana..!.

Daganan suka yanke Kiran Mika Dina Tayi kafin ta yaya Bargon Dake Jikinta ta Zuro Kafarta Waje Silafis Din Dake bakin Gadon Ta zura Ta Fada Tiolet Da Farko Tana Ciikin Damuwar Taya zata iya Rayuwa awani gidan da ba nasu ba..? Ammh Mganganun Zakiya yasa Duk wani Fargaba ya Gushe mata.

*****

Zuwa Safiya sai zazzabin Jikin Zaina ya Ragu Taji Sauki Sosai Har Tatashi Da kanta Tayi wanka Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Umma adakin Ta kwana Tare da ita Dukkansu Suna Jere kan Darduma Bayan sun Idar da sallah Kowanne acikin Ransa Abubuwa Dadama yake sakawa.

Umma Azkar takeyi ammh Rabin Hankalinta baya Jikinta Tatafi Duniyar Tunani in Ta Tuna Abubuwan da suka Faru Jiya sai Taji Tsinkewar Zuciya da kuma Raunin Rai,gabadaya Abun ya Faru ne wanda basu Taba tsammani ba,Tunda Take bata Taba kawo ma Zain wannan Lalacewar ba Ta sani ita Ta Haifi Zain Kuma Soyayyar Uwa Da Danta na musamman ne Ammh ko afili Bata Taba Nuna wata alaman da za"a Fahimci Zain Danta bane bata Taba Damuwa da Sha"aninsa ba komai nashi Nene ne,Ita Halima itace yarta Domin Ita ta Riketa Tun tana karamarta har zuwa yau Tana Jin Dacin Damuwar Datake ciki Domin Wata Shakuwa ce tsakaninsu Kamar ta Uwar Data Haifi yarta da Cikinta ayanzu Tafi Dora Duka Laifin kan Zain ne ayayinda Gefe Daya kuma Take matukar Tsausayin Zaina,ayanzu ma Haka Ita Take Tunani Tana Tunanin wani Hali kuma zata Shiga agaba..? Tana Tsausayinta Domin Tafi kowa sanin yadda zaina Tafi yarda da Zain Fiye da kowa aduniya Ta soshi Tun bata san kanta ba Tana Fatan Allah yasa Zuciyarta Tayi Juriya wajen Daukan wannan al"amarin.

Kallonta Ta maida kan Zainah Wacce ta Kurama Gabanta ido Ga Carbi a Hannunta Tana ja ammh bawai Tasan Abunda Take Fada bane Hawaye ne wasu na Koran wasu suke zubomata gani Take kamar a mafarki Abubuwan suka Faru in ta Runtse ido Da ta Bude kuma sai Ta Gasgasta Abunda ya Faru yau wai Firstlove ne yayi ma Wata Mace ciki ba Ita ba macen ma ba Wata mai Daraja ba karuwa wacce ya ijiye sunan zaman Dadiro Wannan Abun yafi komai yimata Ciwo da Nauyi akirjinta Ji Take kamar Zuciyarta Zata Fashe Tana Jin wani Zafi Zafi yana Fitowa Daga kasan Ranta,Tana jin aduniya kuma wa zata kara bama yardanta..? Tunda wanda tafi kowa yarda dashi yau yaci amanarta Wanda yafi kowa saninta da sanin Rauninta yau yayi sanadiyar da Rauninta ya bayyanata Tanajin kamar ta Mutu ta Huta da wannan Bacikin Daya Ziyarceta Daga Jiya zuwa yau.

Umma ce ta Dafa Kafadarta Lokaci Daya Tana Fadin"Zaina..."Cikin wani yanayi na karaya da Tsausauyi Juyowa Tayi Tana kallonta Idanuwanta na Zubar da kwallah ganin Umma yasa Rauninta ya Karu kawai sai ta Fada Jikinta Tana sakin kukanta Umma ta Riketa Tana Lallashinta Itama kukan Zuccin Take ammh Tana Kokarin Dannesa Saboda kada Ta kara Raunamama Zainar zuciya.

Sai Da Tayi kukanta ya isheta kana ta Dakata,Umma ta Dago ta Tana Share mata Hawaye Cikin Sigar Lallashi Take fadin"Kinga baki da lafiya ki Daina wannan kukan kinji ko..? Jikin ki da zazzabi har yanzu kada ya kara Daukan zafi.."Tana kallon Umma da Rinannun Idanuwanta Tace"Umma Don Allah a zamana da ya zain akwai Abunda na Rageshi Dashi ne..?Ko kuwa akwai wani Abunda nake mai wanda baya Burgeshi ne..?ko kuwa Daman chan Baya sona ne Umma alfarman na Tashi agabanki yasa ya Aureni..?meyasa Firstlove zai min Haka..?Umma Meyasa bai ce min yana son ya kara Aure ba..? Wlh bazan Hanashi ba Zan barshi ya kara aure indai zai Cigaba da zama Dani a matsayin matarsa,Da kuma Kare kansa da aikata zina...!

Ta karishe Fada Cikin wani Gunjin kuka Tana Sulalewa Jikin Umma ita kanta Umman kukan Take Cikin Zuciyarta dago da Fuskarta Umma Tayi Tana Girgiza mata kai Lokaci Daya Tana Fadin"A' a Diyata ki Daina kuka..Bari kuka.."Take Fada Tana Share mata Hawaye Cikin Wani irin Dacin Zuciya Zaina Tacigaba da Fadin"Umma Dadiro fa Firstlove...Dadiro ya ijiye har yayi mata ciki..? Zuciyata Tana zafi kamar zan mutu Ina jin kamar bazan kara Rayuwa ba..Bani da kowa Umma mahaifana Duka sun Rasu wazan Tunkara wa zai Tsayamin ga wannan Jarabawan Rayuwan Data Fadamin Umma bani da kowa.."

Take Fada Tana kuka kamar Ranta zai Fita,Umma Tayi mata Kuri

27 / 43