Chapter 40 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   40 / 43

117K to 120K   out of 126.5K words

komai ahankali Saboda Kar Zirga Zirganta ya Tada Wata Daga Cikinsu.

Side Drower din Umma Ta Bude ta Dauko Littafi da Biron Umma wanda Take Rubuta wasu Abubuwa Gudun mantuwa Komawa Tayi saman kujeran Dake kallon Kofa ta zauna ta Yagi Takardan Ta Dora saman Littafin kana Ta aza Biron zata Fara Rubutu sai kuma Wani Sanyi Jiki da kasala da kuma Tunanin anya Abunda zata aikata Daidaine..? In tayi hakan Tayi ma Umma adalci.? Ko Tayi ma Iyalan Alhaji Tsoho Adalci Wadanda suka Fifitata Fiye da ya"yansu..? Toh ammh in fa Tana Son Cikin Jikinta da kuma Igiyar Auranta Dole sai Tayi haka Bata damu koma me zai Faru ba Ta Tabbata Watarana zai Wuce kamar bai Faru ba Hawaye Taji ya cika mata kwarmin Idanuwanta Har suna kwaranyowa da Sauri ta saka Hannu Ta Sharce Hawaye Cikin Juriya Ta Aza Hannunta Cikin kwarin Gwiwa ta Fara Rubutun.

Takai wajen Tsawon Mintina Talatin Tana Rubutun Tanayi Tana kuka,tana kuma yi Tana Tsayawa Domin wata zuciyar na sanyayamata Gwiwa ga aikata Abunda Ranta ya Rayamata ammh sai Tayi amfani da Zuciyar Dake Karfafa mata Gwiwan aikata Abunda Tayi Niyyah din har sai Da Ta kamallah Rubutun nata kana ta Ninke Takardam Tatashi Ta kaita Cikin kayan Umma ta sakata acikin Wardrope inda ma Hankalin wani bazai kai ba Umma kuma ta maida mata Littafnta da Bironta Inda ta Dauka Kana ta koma kan kujeran Da tatashi ta kwanta Kawai ba Domin Tana jin barci ba sai Domin bata da wata mafita sai na kwanciya.

Mganganun Dina da kawarta Zakiya nayi ta yi mata amsa kuwwa Gefe Daya ga Kudurin Umma,Abu Daya yafi Firgitata Rabata da Cikinta da Umma zatayi wanda Bata iya Jurewa ba Hannunta na Bisa Cikin Tana Hawaye Cikin Zuciyarta wani kunci ne,Domin Ta sani Dina Ta Rigata Daukan Kwan Haihuwan Firstlove acikin maranta kenan Gaskiya ne Ta Fita matsayi Tun Da gashi Komai ya Bayyana..? Kuka Take ahankali kada wani ya Jita takai wajen Misalin karfe 3pm na Dare bata iya Barci ba Tana Ta kuka Da kuma Tunanin Makomar Rayuwarta da Abunda ke Cikinta In har ta Yanke wannan Hukuncin Datake Shirin yankewa.

Bata san sadda wani Barci mai Nauyi ya kwasheta ba Sai da Taji Zafeera na Tashinta kan cewa Tatashi har an gama sallah Ta mike akasalance Idanuwanta Duk sum Kumbura sai da ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala Ta Fito kana Zafeera Ta Luura Da Kumburin Idanuwan Zaina Cikin Mamakinta Take Fadin"Ukti meya Kumbura miki ido Haka..?

Da Sauri Zaina Tace"Bakomai...Idona ne Jiya Da Daddare ya Dinga Ciwo shiyasa..'Cikin Tsausayawa Zafeera Tace"Ayyah..Sorry bari mu Tafi sai asiya mgani ki saka..wlh ya kumbura miki Fuska Sosai kamar wacce Tayi kuka.."Yake kawai Zaina Tayi ammh acikin Ranta Tana Fadin ai kukan ne ma.

Bayan sun Idar da Sallah Zainab da Zafeera Suka Tafi Kitchen Neman Abun karyawa Dayake su Umma Duk chan suka kwana Harda Abba su kadai ne agidan Daman chan nan Zaasu zauna sai ana Gabda Daurin Aure zasu koma Chan Gidan Alhaji Tsohon Tunda ana Daura Auran zasu Tafi da Amarya kaduna.

Bayan sun gama Hada Breakfast
Din Zafeera ta Mika ma kawayen Hamdiya nasu ta kuma Dauki nasu zuwa Dakin Umma Zainab ce ta Dauki na Dina ta Shigar mata dashi Ko Da ta Shiga Tana Cikin Bargo Tana Barci Ijiye mata kawai Tayi ta Fice Dinar ma bata sani ba Ta koma Daki suka karya dasu Zafeera,Hamdiya kuma ta koma Wajen Kawayenta suka karya Tare kana Suka Fara wanka Suna Shiryawa.

Basu yi anko ba Kowa kayansa zai saka Zafeera da Zaina da Zainab Umma Tayi musu Atamfa Da Leshi Tun Shekaranjiya aka anso Daga Wajen Dinki ko Zaina dake gidan bata san da Dinkunan da Umma Tayi musu sai da suka Gani Ko kafin zuwa 10am na Safe sun gama Shiryawa Kowa yaci kwalliyansa ya Cakare Hamdiya Daya Daga Cikin kawayenta Tayi mata kwalliya Har Tayi ma Sauran kawayen dasu Zafeera Dama kunshi Da gyaran kai Daga Abuja Tayo Abunta.

Zafeera da Zainab anyi musu makeup dan daidai Ammh zaina Taki yarda ayi mata Dakyar ta tsaya aka Shafa mata Hodo akayi mata Dauri aka kuma saka mata man baki,Dukkansu ukun less Din suka saka mai Ruwan marun,Da Pick sunyi kyau sosai sai dai kayan yafi Cika Zainab da Zafeera Saboda ya kamasu ammh Zaina sai yayi mata Rakwa rakwa saboda Ta Rame kuma Inaga Measurement dinta na Baya Telan nasu yayi amfani Dashi.

An kawo musu Abinci Daga Gidan Alhaji Tsoho Shinkafa Friderice da Alala daman Drinks basu da mtsalanshi akwai agidan,Dukkansu Falo suka Fito Kowacce ta Cakare abunta suna Hira suna Dariya wasu kuma na gefe suna Hotuna irun su Zafeera Duk Rashin Son Kada Zaina Tayi Hoto sai ta matsa mata Zainab Ta Daukesu acikin Ran zaina Tana Tunanin kila wannan Hoton Shine Abunda Ukti zata Dinga kallo Tana Tunawa da ita.

Dina Bayan Tatashi Tayi wanka Ta Shirya Cikin Riga da wando na yan kanti Breakfast din Ta Tea kadai tasha Ta Tureshi Gefe Tashi Tayi ta Bude kofan Tana kallon Abunda ke Faruwa acikin Falon Daya Bayan Daya Take kare musu kallo su basu ma Lura da ita ba,Zaina Take kallo Zainab na Daukansu Hoto Ita Da Zafeera mamaki ya kamata na ganinta ko ajikinta Har da wani kashe Dauri kamar ta Fito Falon sai kuma Ta Fasa Ganin duka yara ne kuma Batason Hayaniya yasa ta Maida Kofarta Ta Rufe ta koma ta kwanta Domin Bata Gajiya Da Barci kamar Cikin Jikin nata Yana yawan sakata Kasala da Barci.

****

Bangaran Zain kuwa ya kwana da Gudurun yau ko ana ha maza ha mata ne sai ya Dauki Firstlove sun yi Nisa da garin Bauchi Bazasu Dawo ba sai Umma ta Sauya Ra"ayinta Tun safe suka Shirya Shida Haddir Tunda Daurin Auran 11am ne saboda angwaye Zasu wuce Da Amarya kaduna.

Dukkansu Shigar Farar Shadda sukayi Harda Babban Riga wanda Daddyn Abuja ne ya Dinga musu anko Dukkansu Harda Shi da Baban kaduna da Abba,Dukkansu kuma Harda Babban Riga sai suka saka Bakar Hula da Bakin Takalmi Booth,da agogon Fata baki na kamfanin Rado Dukkansu sunyi kyau Duk da Zain ya Rame ammh yayi kyau yayi Haske sai da Ramar Jikij kawai Kuma ita ta Shafi Zuciya ne.

Koda 10 tayi na safe suna Gidan Alhaji Tsoho ana ta Shirye Shiryen Daurin Auran da zai Gudana nan da Lokaci kadan Zuwa goma Da Rabi komai ya kamallah Haraban Gidan Alhaji Tsoho an gama Tsara komai an Malale ko"ina da Manyan Cafet sun Kawata Haraban Gidan Dayake Gidan Babba ne ammh Duk da haka wasu Motocin awaje aka Fakasu Musamman ma na Abokan ango da Tawagan yan"uwansa da abokan aikinsa Sojoji,Suma Abba ga nasu gayyar na Mutanensu Hakama Daddyn Abuja da Dangin Mama Safiya Suwa Shima Baban kaduna Daga Barayinsa ko"ina ya Cika da Mutane gaisawa kawai akeyi ana Farinciki In kaga zain bakinsa kamar gonar auduga Saboda yau ya gaida Abba kuma ya amsamai Har sunyi musabaha da juna Zain ya ji Farinciki har sai da yayi kwallah Zuwa Lokacin Da Time din Daurin auran ya kusa sai Alhaji Tsoho Ya Fito ya zauna Bisa Kujeransa Daidai Lokacin kuma su Zaina Motocin da suke je Daukansu suka ijiyesu Daga Wajen Gidan,Kanwar Mama Safiya ita taje tazo da Amarya da kawayenta Haddir ta saka ya kaita Sauran kuma Motocin abokan ango ne.

Da kafa suka Taka zuwa Cikin Gida zaina Kamar ta Harde haka Take ji Sun saka mayafansu pick Zafeera da Zainab sun saka jaka kowannensu ammh Zaina Mayafin akanta ta sakashi Ta Jashi Sama saboda kada aga Fuskarta Daga Kugunta kuma Takardan Data Rubutu ne matse awajen Lokaci Bayan Lokaci Tana kai Hannunta wajen kada Takardan Ta Fadi.

Zain Dake Haraban Gidan yaga Zaina Domin koda Ga Tafiyanta ya ganeta,Sake baki yayi yana kallonta Domin Rabom da ya ganta Cikin kwalliya Tun suna gidansu baki da Hanci ya saki yana kallonta Ita kuwa bata ma gansa ba kanta na kasa Har suka Shige daman Amaryance agaba Anty Gaje rike da ita sai Kawayenta sai su Daga baya Shiyasa har suka Shige ma basu wani Daga gansu ba ganin maza sunyi yawa aharaban Gidan..

Dakin Hajiya Mama suka yada zango su kuma su Zafeera suka Fice gaida su Umma,Umma ta Dinga Kolasu Tana sun yi kyau Kowa yaji Dadin ganin Zaina ahaka Har Hajiya mama sai da tace ko kefa Hali Dubu Mirmishi kadai Tayi mata Diyar wajen Anty Zareena ta karba Tana Jijjigatamata Ganin Tana kuka ita kuma Tana Shiryawa ne,Kowa ya ganta sai yayi mgana Ita Goggo Halima bata Fahimci komai ba Tunda ba wanda ya gayamata ammh Dai ta Fahimci Halimar ta Rame sosai kamar wacce Tayi Cuta Ammh dai Ta bar ma Ranta da kila Cikin ne ya sakata Rama Domin Taga Shigar Ciki awajen Halimar Taso Ta Tambayeta Zain Sai kuma Tayi Tunanin kila zai shigo bayan Angama Daurin Aure.

Karfe 11:10am aka Daura Auran Hamdiya Aliyu Abubakar Bashir Saulawa da Angonta Hafeez Muhammad Ikra,Daurin Auran da Shedu suka Tabbatar Dashi,Wan Baban Ango Shine Waliyin Hafeez Shi kuma Baban Kaduna ya zama Waliyin Amarya Masha Allahu su Alhaji Tsoho Suna Daga Cikin wadanda suka Shaida Daurin Auran ya samu Hallartan Manyan Mutane kama Daga Lauyoyi masu zaman kansu Abokan aikin Dadyn Abuja Da Tsoffofin abokan Alhaji Tsoho Da ya"yansu wasu Tsoffin Likitoci wasu kuma sun Taka wani mukami agwammati,Sai Abokan aikin Abba Dana Baban Kaduna Dangin Mama Safiya da wasu Daga katsina,Abokan Angon Shi kanshi Da kuma Tawagar Iyayensa da Yan"uwansa,Zuwa abokan aikin su Zain da kuma Makota Da abokan arzuka Hardasu Dr.Imran da kuma Dr.peter Sun Hallaci Daurin Auran Bayan an Gudanar da Daurin auran aka Fara Fito da abinci da Lemuka ana ta Rabawa kowa yana zaune kan Cafet yana cin Abinsa da Naman kaza ga Ruwansa agefe ana Korawa da Lemu Haraban Gidan Alhaji Tsoho kamar wani Restaurant Haka ya koma.

Daga cikin Gida Kuma ana Ta Shiryen Shiryen Tafiya da Amarya Nasihu Dama Tuni iyayenta sun mata su Umma dai ke karawa Da Hajiya Mama Alhaji Tsoho Daman Tun Daran Da suka iso yayi Mata nata Sosai,Kuka kawai Hamdiya Take ganin Da gaske Tafiya da ita fa Za'ayi Adaidai Lokacin kuma Zaina ta mika ma Zareena Yarta Ta koma Dakin Hajiya Mama Jakar Zafeera na Hannunta Ta bata ajiya Suna Chan Dakin Alhaji Tsoho suna Hadama Hamdiya kayanta.

Ba kowa adakin sanda ta Shigo Duk suna Falo ana Tsaye Masu Shirin Tafiya masu Rakiya ma na Tsaye Baban kaduna da Abba Sun Shigo Har gida suna Fadan su Shirya 12 suka ce zasu Mika Hajiya mama Ta Tsara masu Tafiya Kaduna Tace Umma zata Tafi da Mom lklima da Inna Hannatu da Inna Rukayyah sai Dangin Mama Safiya kanwarta Da Diyar wan babansu Sai Ya"yan yan"uwansu yan mata Daga Barayin nan kuma Hajiya Mama tace Zafeera da Zainab da Shema da maryama duk zasu Tafi Asma"u ma da Zareena suma Duk Dasu za"a je Hajiya mama tace Goggo Halima ma Da matar Danta zasu Tafi Da Farko tace bazata ba Hajiya mama tace sai Taje Umma na jin da ita za"a Tafi Ta kuduri Niyya da Zaina zata Tafi Sai ta Fara Nemanta ammh bata ganta ba Zafeera tace kila tana Dakin Hajiya Mama Umma Ta taka Kafa zata Bita Hajiya Mama ta kirata kan da ita da Mom Iklima da kanwar Mama Safiya zasu kai Hamdiya Tayi sallama da Alhaji Tsoho da kuma Iyayenta wannan Dalilin yasa Bata koma Dakin ba suka Dunguma zuwa Haraban Gidan Kaya kuma Tuni wasu an Fara sakawa cikin Mota kuma Daman an je Tuni anyi jere chan kaduna wannan aikin Mom iklima ce.

Zaina sai da Ta Tabbatar duk sun Ragu afalon kana Ta Tashi Daga Kofar Dakin Hajiya Mama inda Ta Labe Jakar Zafeera ta Bude Ta Taga kudi 3k sai ta Dauki 2k ta bar mata Sauran Lokaci Daya kuma ta saka Takardan Data Makale a kugunta Cikin Jakar Ta ijiye mata nan Gefen gadon Ta warware Daurin kanta Ta Rike kallabin Ahannunta Ta saka mayafinta Ta Yane kanta Ta zazzagoshi yarda bamai ganeta kuka Take kuka mai Cinrai hawayenta na Zuba Tana Sharewa Sikat din yadan mata yawa sai Tajashi sama Sai da ta Leka Daga Falon Taga duk ba wanda ya santa yawancin Dangib Mama Safiya ce Sadaf Sadaf Ta Fito Tana waige zata Fice Daga Falon Taji Muryan Hajiya Mama Da ta Fito Daga Dakin Alhaji Tsoho Tana Fadin"Ke waye nan zai Fita..?

Dam!gaban Zaina ya Fadi tayi Saurin Share hawayenta kana ta Juyo Tana Fadin"Nice Hajiya mama..Zani waje naga Tafiya Amarya ne muyi sallama.."Hajiya Mama Da taci wani Ubansu Leshi Ta kariso Tana Fadin"Au Halima ce..? Eh gwara haka Kinga ke bai kamata ki Tafi ba gwara ki zauna in Uwar taki sun kaita sun Dawo sai ansan yadda za"ayi ki koma Gidan Mijinki.."

Cikin Sanyin Murya Zaina Tace"Toh Hajiya Ma..ma.."Ta Fada Muryanta na rawa ganin haka yasa ta Dafa kanta tana Fadin"Karki damu kinji ko..Ga Nene ai ba da ita za"a Tafi ba saboda kada abar gidan ba kowa ga Amanar yarinyar nan a Hannunsu Kiyi hakuri gobe zasu Dawo Dukkansu.."Tafada Cikin Sigar lallashi tana ganin kamar zaina ta Damu ne za"a Barta ita kadai Saurin kwakwalo Mirmishi Tayi kafin tace"Bari naje muyi sallama.."Hajiya Mama tace"Hanzarta.."Ko gama Rufe baki bata yi ba ta Fice har tana Tuntube sai da Hajiya Maman ta Bita da kallon mamakin ganin kamar tana Sauri kuma bata Cikin Natsuwarta.

Girgiza kawai Tayi ta koma Ciki,Achan Haraban Gidan kuwa Zaina na Fita ta Tsaya Daga Gefe,Tana Hango Hamdiya Durkushe gaban Alhaji Tsoho Da Abba Da Babban kaduna da Daddyn Abuja su Umma na Tsaye Daga Chan gefe kuma Tuni wasu ma Daga Tawagan anko sun Fara mikawa su Zafeera kuwa suna jikin wata Jeep Daga gani ita zasu Shiga Daman sun Taho Da kayansu Tun Daga Gida wajen ya cika da jama"a Shiyasa wani ma bazai gane wani ba an cika maza da mata Kamar an ce Ta kara Daga kai ta Hango Firstlove yana ma Zafeera mgana Bata san me ta gayamai ba Taga ya Nufi Wajen su Umma Kara Lafewa Tayi jikin Fulawan Dake Haraban Gidan tana kara Rufe Fuskarta Tana gani ya Rankwafa yana gaida Goggo Halima ta amsa Tana Shafa kanshi bakinta har kunni Daga gani albaeka Take sakamai Zuwa chan kuma ya mike ya Nufi Hanyar Shiga Falon gidan Sai Zaina ta kara Boye kanta Tana Danne kukanta ganin Firstlove ya Tada mata Duka wani Mikin Dake Zuciyarta,Wani irin Sonsa da kuma Raunin Rasa sa ya Bayyana Gareta Tana kallonsa har ya Shige Cikin jikinta ta Dafa Lokaci Daya wasu hawaye na Zubomata afili ta Furta"Nasan zakaji Ba Dadi in kaji irin Hukuncin dana yanke..Kada kadamu nayi hakane saboda Tseratar da Cikin ka da kuma Aurena Dake hannunka..da kuma kauce ma ganin wata Ta haifa maka D'a ko ya' ba ni ba da kuma kaucema ganin Wata a matsayin matarka..Ammh zan Dawo In da Rabo kuma nayi maka alkaawarin Kula maka da kaina da Abunda ke Cikina Insha Allahu.".

Kuka Ta fashe dashi kamar Wacce aka Duka Har sai da Ta Duke jin kamar Motsi ne Daga Bayanta yasa ta waiga Tana Toshe bakinta kada wani ya jiyota,Ido ta zaro Tana kallon Zain Daya Fito kamar yana neman wani abu Jikinta ya Fara Rawa Ta Tabbatar da ita yake nema ya kamata tayi ta Fice Daga Gidan nan kafin komai ya kwace mata,Tana ganin ya Nufi Wajen Zafeera Tayi Zuruf ta Fito Daga maboyarta Ta Bayan Mutane ta Dinga Bi Tana ta kare Jikinta kada Zainab ko Zafeera ko Umma wani gane kayan Jikinta ya Kirata,Allah ya Taimake ta har ta kusa barin Haraban Gidan bata Hadu da wani idon sani ba Tana Gabda Fita ne suka kusa cin karo da Haddir ya Shigo yana waya ganin Hankalinsa yayi gaba ne yasa sau Daya ta Waigo ganinsa yasa ta Juya da Sauri Ta na gyara Gyalanta Shi kuma sai da yace mata Tayi hakuri kana ya koma yana kallonta ganin yadda take wani Sauri kamar zata Tashi sama mamaki ya kamashi Ko dai Barauniya ce..? Ammh kuma kamar Dazu Da suka je gidan Abba yaga kamar wasu da kayan nan Dayake shi bamai wannan luran bane yasa kawai ya Cigaba da wayarsa ya Juya ya Nufi Haraban Gidan.

Hankalin Zaina bai kwanta ba sai da Taga Ta Fita Daga Haraban Gidan Alhaji Tsoho kana ta Dago Ta kalli Gidan Ta kara kallo Hawaye na Zuba acikin Idanuwanta kafin Ta Furta"Umma ki yafemin..Abba ka yafemin...Goggo Halima kema ki yafemin...Firstlove da Ukti kuma ku yafemin.."Kafin ta Fashe da wani kuka mai cin rai adaidai kuma Lokacin ne Motar Zakiya Wacce Dina ke Ciki ta Faka nan kusa da Zainar bata ma Lura dasu ba Tana kallon Gidan Tana kuka sai Da Taji muryan Dina wanda ko Mafarki Tajita zata ganeta kana ta waigo Gabanta ya yanke ya Fadi Data gansu Saurin Juyawa Tayi Tana Rufe Fuskarta Lokaci Daya kuma Tana Tsallakawa Daga chan Dayan Hannu Da kallo suka Bita Dukkansu atamfa Riga da Sikat suka saka ammh fa kayan sun kamasu Zakiya ta Zubo attch din nan Dina dai bata saka ba ammh Itama gashinta waje ga wani mayafi kamar basu basu saka ba.

Ta gefen ido Taga suna kallonta yasa ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri kamar wacce Zata Fadi Hannunta daya Damke da Sikat dinta da kudin Dake hannunta Ganin haka yasa Zakiya tace"Ita wannan fa..? Tana sauri kamar wata mara gaskiya..!
Hankalin Dina naga Haraban Gidan Take Fadin"Miye naki..? Kila barayin nan ne da suke zuwa Sata wajen Biki..Tagama Diban Rabonta Zata kara gaba.."

Ta Fada Tana kallon Bayan Zaina wacce ta Fara musu Nisa Cikin Wani yanayi kafin ta Kauda kai Zakiya ce Tace"Umh...Lalle ana Shagali kalli fa da Yadda Gidan ya cika da manyan Motoci kalli yadda Gidan ya cika fa Shine ke din acuceki sai ace ki zauna agida ke kadai.."Dina Ta saki Dariya Tana Fadin"Kyalesu...Ai na bar musu megadin gidansu yayi musu gadin gidansu..Nima sai nazo aci bikin dani nima ai na zama yar Dangi.."

Zakiya Tace"Kwarai...Kuma ai mu ai abun kunya gaba muka bashi ba Baya ba..Kuma Tunda Dansu ya bari ya Shiga Tarkonmu sai Hakuri.."Dariya suka kara sakawa harda Tafawa Kafin Zakiya ta kashe Motarta su Fara Taku zuwa Cikin Haraban Gidan Daman

40 / 43