Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
yaji kamar ya Dawo Cikin Duniyar.
Gabadaya aka Zubamai Ido ana kallonsa ganinsa yana Nuna Hannu yana so yayi mgana ya kasa Runtse ido yayi wasu Zafafan Hawaye suka zubomai Cikin Rawan murya kamar mai In ina yace"First...L..O..v..e...Ta..tafi...Ta..barni.Kuma..Ta...na...Da...Cikii...naaaa...!bai ida karisa mgarsa ba Kawai ya Sulale ya Fadi nan da Karfi sai kaji Tim nan da nan Idanuwansa suka kafe ba Numfashi Cikin Tashin Hankali su Abba dasu Daddyn da Baban Kaduna da Haddir suka Rufu kansa Cikin Rudewa da wani Tashin Hankali Haddir da Baban kaduna Suka Tallafeshi suna Kiran Sunansa ammh ko Motsi Abba Dake gefe ya Rikice Hakama Su Umma sai kuka ya kara Tashi Dina Dake gefe ganin Zain baya Motsi ya Tada hankalinta Ta nufi Wajenshi Tana Zuwa Ta ture Haddir Dake Rike da kansa Baki ya saki yana kallonta Cikin Tashin hankali ta Rike Hannunsa Tana Fadin"Na Shiga uku plz zain don"t do this to me..Kada ka Tafi ka barni da Cikinka.In ita bata Sonka ni ina Sonka Zan zauna dakai nayi maka Duk Abunda take maka Don Allah ka tashi.."Sai kuma ta saka kuka Galala kowa ke kallonta sai Lokacin ma Su Umma suka ganta Cike da mamaki Wadanda basu san Labarin Dina ba suka saki baki Cikin mamaki irin su Goggo Halima.
Kowa ya kasa mata Mgana Sai Baban Kaduna ne ya Fizge Hannun Zain din yana Fadin"Ke miye haka..? Wannan wani Rashin Hankali ne..? Baki ganin Halin Dayake ciki..?
Ya Fada Cikin Takaichi kamar ya maketa Kuka ta kara sakamai Zatayi mgana Zakiya tazo Ta jata Tana Fadin"Kuyi Hakuri Don Allah..Ta saka Control din kanta ne Da Halin Dayake Ciki ne.."Inna Hannatu Dake Gefe ta Lailayo Ashar Tana Fadin"Kaza kazan Halin Data ke ciki.. Duk son data kemai Takai mahaifansa ne..? Nace baga uwarsa nan da Ubansa ba Me kika ga sunyi..? Sai ke karan kada Miya Matsa ki bamu Waje Maras kunya"Sumi Sumi Zakiya Taja Dina Dake kuka suka koma Gefe Zakiya Ta kalli Dina Cikin Takaichi Tana Fadin"Ki Natsu Dillah..Kina da mtsala wani Lokacin.."Dole Dina Ta natsu ammh hankalinta na wajen Zain wanda Daddyn Abuja yace aje asibiti Alhaji Tsoho ya Dakatar dasu yaje su kawo Ruwan zamzam Hajiya mama ta kawo yayi addu"a ciki ya bama Baban kaduna yace su Shafamai afuska Cikin Ikon Allah yana Shafamai sai gashi Ya sauke ajiyar Zuciya Kafin kuma ya Fara Bude Idanuwansa.
Ganinsa Akan Cinyar Haddir gasu Baban kaduna sun zagayesa Gefe Daya gasu Umma komai ya Dawo mai Zumbur ya Mike su Abba na Rikoshi Yayi Saurin Cire Baban Rigan jikinsa yana Fadin"Ku sakeni naje na Nemota..Wlh bazan iya Rayuwa bata ba...Bazan iya ba"Yake Fada kamar wanda ya Zare Baban kaduna da Haddir ke Rikesa Abba kuwa Da Daddyn Abuja kwalla suke dama sune masu Raunin ganin yaki yarda ya zauna yasa Alhaji Tsoho ya Daga baki ya Kirashi Sunansa.
"Zainullahi...kai Zainullah yaka nan."Jin Alhaji Tsoho na Kiransa yasa ya Dakata da Neman Fitan Dayake ya Zubamai Ido yana Hawaye Cikin kuka yake Fadin"Alhaji Tsoho kagani ko..? Zainata Tatafi ta barni sai da nace ku bani matata aka ki bani..Ku barni na Taje na Nemota.."Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru zaunar Dashi.."Haddir ya zaunar Dashi Kan Kujera Dakyar sai Sambatu yake,Kana Alhaji Tsoho ya kalli su Umma da Nene dasu Zafeera Dake kuka yace"Kuyi hakuri kubar kukanan..Aminatu Tafi Da Goggo Halima Dakinki ki gayamata komai Ya kamata tasani yanzu.."Ba musu goggo Halima Tabi bayan Hajiya Mama Daman Ta kosa Taji me ya Faru Ga kuma Tashin Hankalin Data ke ciki na Takardan Zaina,Suna Tafiya Alhaji Tsoho ya juya yana kallon su Mama safiya Lokaci Daya yana Fadin"Hannatu da Rukayyah da Wasu Cikin yan"uwanki su Dauki Hamdiya Zuwa Dakinta Saboda kunga suna Waje suna Jiranku ba Dadi..Ku Tafi ku kaita Dakinta Allah basu zaman Lafiya.."
Suka amsa da Ameen Jiki a sanyaye kafin Alhaji Tsoho ya Juya Ya kalli Haddir yana Fadin"Kai kuma Hadiru ka kara Komawa ka Dudduba Hanya da kuma Tasha..In Allah yasa batayi Nisa ba Shikenan in kuma Tayi Allah ya Tsareta aduk Inda zata je...Kaddaran Data Fadamana kenan sai Hakuri.."Haddir ya gyada kai yana Fadin"To Alhaji Tsoho.."Ya mike kenen Zain Shima ya mike yana Fadin"mu tafi Tare Haddir..!
Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a Koma ka zauna..Ina zaka Cikin wannan Halin..? Cikin Karaya da Muryan kuka Zain yace"Taya Zakacemin na zauna alhalin Matata Ta bace ba"a ganta ba..? Bazan zauna ba din sai naje Wlh.."Yafada Harda Rantsuwa Cikin Fada,Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Kai Bashir kamasa ya zauna..Ba inda zaka nace Zainullahi.."
Zain zai kara mgana Baban kaduna ya Hanashi Da Fadin"Kaga koma ka zauna Jiri fa kake gani koma ka zauna.."Zain ya koma ya zauna yana Fadin"Baba Firstlove ce Fa tace wai Tatafi..? Ina zata..? Kuma fa Tace Tana da Ciki Baba Bata da inda zata Baba kabarni naje na Nemota.."Abba ya kauda kai yana Sharan kwallah Daddyn Abuja ne ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Karka damu za"a ganta da ikon Allah.."
Shuru kawai Zain yayi ya maida Fuskansa Kan Tafukan Hannuwansa yana Rera Siririn kuka,Haddir yamike zai Tafi Zafeera Ta Mike Tana Sharan kwallah Tace"Zan bisu Alhaji Tsoho.."Da Sauri Umma ta mike Tana Fadin"Nima zani.."Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a ke Fatima ki zauna..Kai Hadiru ku Tafi da Zafeera.."Kuka Umma Ta saka Zareena ta Riketa Tana Lallashinta.
Haddir da Zafeera suka Fice da Sauri Suna Fita Yan Kai Amarya suka Fara Fita Zuciyoyi ba Dadi ba wanda yabi Takan Dina Da Zakiya inna Rukayyah da Inna Hannatu sai Dangin Mama Safiya,da Mom iklima Suka Tafi da Hamdiya Kawayenta Tun dazu wasu abokan ango suka yi gaba Dasu Inna Halima kuma Tana Dakin Hajiya Mama tana ta Sharan kwallah Bayan Hajiya Mama ta gayamai komai Tana Fadin"Wauta ne ke Damun Halima in banda Sarkaci Data saka kafa Tatafi ina zata..?Tana da Inda yafi nan ne..? Allah Sarki Hajiya Fatima kin cika uwa Nagari.."Take Fada Tana kuka Hajiya Mama na bata baki Su Umma na Falo suma suna nasu Kukan Domin Zain banda kuka da sambatu ba abunda yake,Jin kiran salla yasa Alhaji Tsoho yace kowa yaje yayi sallah Su Umma suka koma Ciki su Abba suka Fita Zuwa sallah Harda Zain din wanda Baban kaduna yake Rike Dashi Gabadaya baya gani Sosai In ya sakesa zai iya Fadi Sambatun ambaton Firstlove kadai yake gwanin Tsausayi da kuka, Mama Safiya kuma Sauran yan"uwanta suka Fara Shirin Tafiya Alhaji Tsoho Dakinsa ya koma Cikin Damuwa Domin yayi sallah.
Dakyar Umma Tayi sallah sai kuka Take Tana Rokon Goggo Halima Kan ta yafemata itace Sillan komai ita kuma Goggo Halima na basu hakuri Nene da zainab har sun Share Hawayensu Kowa kagani Cikin Damuwa Mama Safiya sai Fadi Take Allah ya bayyana wannan yarinyar,Dina kuwa da zakiya ba wanda yasan Fitansu Sai dai aka ga basu Ashe Zakiya ce Taja Dina suka bar Gidan ganin Tana kuka Tana neman kara ja musu Abun mgana Gidanta ta kaita Tana Mata Fadan meyasa Ta cika Mtaala ne..? Yadda yau gidan Ya Rikice Daman gashi ana Jin Haushinta sai ace itace ma Sanadiyar Tafiyar ma Halimar.
Bangaran su Haddir kuwa haka suka Dawo ba wani Labari mai Dadi Wannan Labarin ya sa sai da Zain ya kara Suma Cikin Daukewar Numfashi Hankula suka kara Tashi an Daukesa Zuwa asibinsu Kenan Ita ma Umma ta Suma sai da aka sakamata Ruwa Gida ya Rikice ko abinci ba wanda yabi ta kai Dangin Mama Safiya ganin ba Lafiya suka yi sallama suka wuce bayan Sunyi Fatan Allah ya bayyana Halima.
Zain ya Shiga Doguwar Suma ne Dakyar aka Daidaita Numfashinsa aka sakamai Oxygen su Dr.Imran ne sukayi Attending dinsa Domin Dr.Haddir ya kaasa Tabuka komai Saboda Tashin Hankali Daki na musamman aka kai Zain Su Abba Duk suna asibitin Tare da Zain harda Zafeera kowanne kagani Hankali atashe acikin Zukatansu kuma Rauni ne Da kuma Fatan Allah bayyana Halima Abba kuma Yaji Tsausayin Zain dayasani da Tuni ya yafemai inda yasan haka zai Faru Daya saka baki Umma ta bashi Matarsa da Duk haka bai Faru ba addu"a kawai yake Allah Tada kafada Baban Kaduna kuma wani Abokinsa ya Kira Dake aiki nan Gidan Tv na garin Bauchi Ya gayamai Bacewar Halima Bashi da Hotonra Haddir ya saka ya Turamai Hotonta da kayan Dake Jikinta da kuma Cikakken Sunanta,Shima bai da Hoton nata awayar Zain dake Hannunsa ya Cira ya Turamai da Cikakken Bayanin Zaina din ko Allah yasa za"a dace yadai ce yanzu zai saka Duka Cigiyan In da Rabo za"a dace ko kuma wani yazo yabada Bayanin ya ganta.
****
Bangaran Zaina kuwa Tana Ta Tafiya sai da Taga tayi Nisa da GRA kana ta Tsaya Tana Haki Domin ta Dade batayi Tafiyar kasa haka ba,waige waige ta Farayi saI kuma Lokacin Tunanin ina ta Nufa yazo mata Tana Tunanin Bayan Gada da kano Bata Taba zuwa ko"ina ba sai ko Lagos kuma yanzu bai kamata Taje ko Daya Daga Ciki ba Tana wannan Tunanin ne Taji mai adaidaitan Daya Tsaya gabanta yana Fadin"Hajiya Tafiya ne..?
Kallonsa Tayi Sai kuma ta Juya Bayanta Tana tsoron kada ayi Saurin ganin Takardan nan abiyo Sawunta Sai kawai Taji bakinta ya Furta"Tasha zaka kaini inda zan samu Motar barin garin nan.."Bai damu da yanayinta ba Yace ta Shigo ya kaita da Sauri ta Shiga yaja suka Tafi,Tun acikin adaidaitan TaFara Kuka Tanayi tana Sharan kwallah basu Dauki Lokaci ba sai gasu Cikin Tasha Suna Zuwa mai Adaidaitan yace"Gamu Tasha Hajiya ina zaki ne Hada..?
Cikin Muryan data Shake da kuka Zaina tace"Ina zani kuma..? Nima bansani ba.."Da sauri mai adaidaitan ya waigo Yana kallonta kafin yace"Topha..Baki sani ba kuma..? Cikin Sharan kwallah Zaina Tace"Eh ammh nan Motocin ina ne..? Mai adaidaitan yace"Motocin Lodin Bauchi Zuwa Fambeguwa da garuruwan Dake wajen har Zaria sai kuma na Bauchi Zuwa Zaria da kuma ta Zuwa kano.."
Cikin Wani Sanyi Zaina Tace"Zaria..? zaria ta kaduna State.."? Mai adaidaitan Cikin mamaki yace"Kwarai Hajiya.."Zaina na kara Kallon Kudin Hannunta Tace"Bari na Hau ta Zarian.."Da sauri mai adaidaitan ya Fito yana Fadin"To muje na sama miki Motar.."Jin haka yasa ta Fito Tana Bin Tashar da kallo Tunda Take bata Taba zuwa tasha ba yau ga Dalili ya kawota Dankwakinta Ta warware ta kara Nanndawa aka Ta Rufe Fuskarta Dakyau Tabi mai Adaidaitan zuwa wajen da Motocin ke fake suna zuwa wani Dan Union mai adaidatan yayi mao mgana Shi kuma yace mai Motar zaria Ko me yaceme.?sai ya juyo ga Zaina yana Fadin"Kinji yace Ba Motar da Zata Zaria Direct sai dai ki Hau Ta kano in kinje chan zaki samu ta Zarian Direct.."
Zaina Bata da Zabi Sai kawai Tace"Shikenan.."Mai adaidaitan Ta kallah Tana Tambayanshi Kudinsa yace"Dari uku ne.."Dubu Dayan ta Dauka Ta bashi ya Fasa ya bata Chanji yana mata Allah ya kiyaye Hanya tace Ameen ta Wuce Tabi Bayan Dan Union din yana Fadin ko Tana da kaya ne..? Tagirgiza kai kawai Har wajen Mota sukaje Kiran Sharron Ta kusa Cika Sauran Mutum Biyu Ta Cika akace ta Shiga ta zauna Ta Shiga Ta zauna Tana jin wani Hawaye na cika idanuwanta Tana Shiga sai ga Wani yazo Ya Shiga Ba Jimawa kawai suka Tashi Sun Fara Tafiya kenan kwandasta yace kowa ya Hado kudin Mota Cikin kasala lokaci Daya Tana kara Rufe fuskata tace"Nawa ne kudin Motan..?
Cikin Sauri kwandastan yace"Dubu Biyu ne Hajiya kudin Motanki zuwa Kano."Waro Ido Zaina Tayi Gabanta na Faduwa Lokaci Daya tana kara kallon Kudin Hannunta Dubu Daya da Dari bakwai,kallon Kwadastan tayi Shima yana kallonta yace"Yadai Hajiya..? Cikin In ina Zaina tace"Don...Allah...ka..min hakuri...Kudina bai kai ba Dubu Daya da Dari bakwai gareni na zata iyakarsa 1500 ne.."Cikin kallon Sannu ko Kwandastan ya Bita Dashi kafin yace"Lalle nema kaji wata yar rainin wayau oga..?
Direban Dake gaba yana Driving ya waigo yana Fadin Lafiya nan kwadastan ya kwashe komai ya gayamai Direban daman Dan Shaye Shaye ne yace"Bari na Tsayamu Sauketa..Karya Take Yanzu haka irin yan iska nan ne Masu Zuwa bariki bada kafar Dama ba.."Kwasdastan yace.." Daga ganinta kuwa oga."Yafada yana kallon Zaina wacce ta Dukar dakai Tana Hawaye Gabadaya hankalin yan Motan ya koma kanta kowa sai Tofa albarkacin bakinsu suke Tun alokacin Zaina Taji ta Fara Nadaman Wannan Fitowar Datayi ganin Direban na shirin Tsayawa ne yasa wani Dake zaune agaba Tun Dazu bai ce komai ba ya ciro 300 ya mika ma Kwadastan ta baya yana Fadin gashi nan ya cikamata Suje Allah ya kaisu lafiya Sai Lokacin Kwandastan da Direba suka yi Shuru ya karbi kudin yace Zaina ta kawo na Hannunta ta mikamai sai Hararanta yake maida kanta Tayi kasa kawai Tana Hawaye Lokaci Daya Tana Share Hawayenta da Gefen Damkwalinta.
Cikin Ikon Allah Wajen 3:00pm na Rana suka isa kano Saboda Rashin Mutumcin Direban Nan ko Tasha bai kai Zaina ba ya Sauketa nan Bakin Hanya Da yan Motan suka mai mgana yace Shi haka kurum bai yarda da ita ba Tunda dai an zo kanon Shikenan Zaina Taji ta Muzanta Sosai ko Tsayaawa ma Batayi ba Ta Juya ta Fara Tafiya yan Motan suka Bita da kallo wasu na Fadin gaskiyan Diraben ne Suma basu yarda da Zaina ba kamar wata mara gaskiya nan dai suka wuce suka Barta Tana ta Tafiya akasan Abakin Titi Motoci nata wucewa da Adaidaita Tafe take kawai Tana kuka da Nadaman Fitowarta Tana Tunanin ko Ta koma gida ne..? Ammh ina Taga kudin Mota..?
Ina zata..? Wa zata Nufa..? Inda ma take bata ma sani ba Kuka kawai take Tana Sharan kwallah kamar an ce ta Juya sai ga Wata golf da sauri ta saka hannu ta tsaidata ta Faka agabanta Sai taja ta Tsaya Direba ne amotan sai wani a agefensa sai Wata Mace abayan Motan ita kadai ta Hakimce,Dukowa Direban yayi yana Fadin"Hajiya ina Zuwa..?
Da Kamar bazatayi mgana Ganin Abunda wanchan Direban yayi mata ammh sai tace"Za...Zaria zani.."Da Sauri yace"Ikon Allah muma ma chan muka Nufa..Hajiya Don Allah bari na kara Mutum Daya.."Daga Bayan tace"Bakomai.."
Ya Bude Ma Zaina gaban Motan yana Fadin"Kai bawan Allah gyara mata..Ta zauna ke Shigo.."Zaina tayi kwalkwal kafin tace"Ammh sai dai ka Taimaka min bani da kudin Mota.."Wani sakaran kallo Shima ya Bita dashi kafin yace"Allah ko..? Daman har yanzu akwai masu wannan Taimakon..? Gaskiya kiyi Hakuri ni Sana"a na Fito ba Taimako..".
Da Sauri Zaina Tace"Don Allah ka Taimakamin.."Ta Fada Tana Hawaye karamin Tsaki yaja kafin ya Taka Motarsa yana Fadin"Kiyi hakuri kila mai Taimakon yazo.."Yana Shirin Tafiya ne Matar Dake Baya wacce ke Kallon Abunda ya Faru Tace"Ka Dauketa..zan Biya.."Da Sauri ya juyo yana Fadin"Zaki Biya fa Hajiya..?
Ta gyada kai Cikin Washe baki yace"Shikenan Hajiya..Ke Shigo ki godema Allah hajiya ta Biya miki.."Jin haka yasa Zaina ta Sauke ajiyan zuciya ta kama Murfin Motan ta Shiga Tana Sauke Numfashi Idanuwaanta duk sun kumbura saboda kuka Sai da Ta Daidaita zamanta Tana matsawa Domin Taga kafadanta na Gogan Namijin Dake kusa da ita sai da suka Fara Tafiya kana ta waiga Bayanta Tana Fadin"Nagode Haji...!
Mganarta ta makale ne Ganin Wacce Direban ya ke kira da Hajiya Wata kyakyawan Farar mace ce mai kyau Gata Fara ga Dogon Hanci da Tsukikin baki,Tana Sanye cikin Shigar Doguwar Rigar material Buba wacce Taji Stone work Kayan Jikinta masu Tsada ne haka kunnuwanta da Hannayenta duka Sanye da Zinare,ta saka wani Jan Vail Ta yane kanta Dashi Kamar yadda Takalmin kafarta yake ja haka Jakarta ma Dake gefenta Ja ce mai Tsada Dogon Hancinta yana Sanye da Hudun Hanci,Kallo Farko in kayi mata zaka Fahinci Tana da Zubi Da Fulani,Sannan kuma karamar yarinya ce mai akallah Shekaru 25 aduniya Tana Zaune Cikin Mota ta Hakimce Kamar Wata Sarauniya.
Kara Waro Idonta Tayi Tana kallon Zaina Bayan ta Kauda Idanuwanta Daga Taba wayarta Cikin Basarwa ta kalli Zaina wacce ta saki baki da Hanci Tana kallonta Haka kurum Taji Matar ta Burgeta Cikin Sanyin Murya Tace"Bakomai..karki damu..!
Tafada Lokaci Daya Tana Cigaba da latsa wayarta Cikin Sanyin Jiki Zaina ta Daina kallonta ammh Lokaci Bayan Lokaci Tana kallonta Ta madubi kuma In Matar ta Dago suna Hada ido,Haka kurum taji Matar kawai ta Burgeta Ganin Farko Da Tayi mata Haka suke Tafiya Zaina na kallonta ta Madubi Itama in Ta Dago sai Su Hada ido Ganin haka yasa in sun Hada ido sai ta sakar mata Mirmishi Domin bata san Dalilin Yarinyar ba na yawan Nacin kallonta
Shida Saura na yammah suka iso Zaria ta Sabon gari suka Shiga Wajen Bayan gidan iya ya Sauke wannan Namijin sai itama Ta Hajiyar tace ya Sauketa nan Fakawa yayi ta Bude Mota ta Fito Tana Bude Jakarta bandir din yan Dubu Dubu Ta Fito Dashi ta zari Guda 15 ta bama Direban ya karba yana Ta Godiya,Wucewa kawai Tayi Tana wani irin Taku Lokaci Daya Tana Tsaida mai Adaidaita Baki zaina ta saki tana kallon Mace iya mace wacce ta mallaki komai na ajikin Mata,Direban ne ya katseta da Fadin"Ke wai ina zaki Sauka ne..!?
Da Sauri Zaina Tace"Nan zan sauka.."Kallon Mamaki yayi mata kafin yace"toh ki sauka mana ko kina Jiran sai nace ki Sauka.ne..?."Batama Tsaya Jinsa ba Ta Bude Murfin Mota Ta Fita Tana Kallon Kyakyawan matanan ta Tsaida Adaidaita ta Shiga Direban bai bi ta kanta ba ya Wuce yana Murnan ya samu kudi a asama.
Tsaye Zaina Tayi Tana kallo Matarnan Adaidaitan Data Hau ya Fara Tafiya kamar Wacce ta santa sai Taji in ta Bari Tatafi Zata Rasa Madafa,Kuka ta Farayi Tana Bin kasuwar da kallo Kowa sai Harkan gabansa kawai yake ba Ruwan wani ma Da ita bata Taba Zuwa Zaria ba sai yau Tana Cikin wannan Halin Taji an Dafa kafadanta da Sauri Ta Waigo Sai kawai Taga Kyakyawan Hajiyanan Ganinta yasa ta Sauke Numfashi Ta saki Mirmishi.
Cikim mamaki Tace"Lafiya..? Na shiga adaidaita mai Adaidaitan yace min ga wata chan tana kallonmu Tana kuka ko Tare muke..? Sai da nace ya Tsaya na Fito na ganki lafiya..? Ina ne Gidanku..? Wata anguwa zaki..?
Duka Ta Jero mata Tambayoyin Cikim kulawa,Da Sauri Zaina Tace"Bansan ko"ina ba..Bansan ina zani ba.."Cikin mamakinta Tace"Topha..Wajen wa to kika zo..? Sai Zaina ta Fara Hawaye Tana Fadin"Bakowa.."Shuru Tayi Tana kallonta kafin Tace"Shikenan bar kukanan ki gayamin me sunanki kuma Daga Ina kike..?
Zaina Tace"Sunana Halima..Daga Bauchi nake.."Haka kurum Taji bata son Ta gayamata karya Cikin Kallonta sama da kasa matar tace"Bazan matsa naji me ya Fito Dake Daga Gida ba...ina ganinki naji kin bani Tsausayi kuma zan iya Taimakonki ammh