Chapter 39 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   39 / 43

114K to 117K   out of 126.5K words

Ta karamai Fada sosai da Nasihan Gudun Duniya ya Tabbatar mata Daya Tuba kuma yayi Nadama,Ammh yana Rokonta Ta saka baki Umma ta maidamai da Matarsa yayi ma Alhaji Tsoho mgana Shi kuma yaki Cewa komai,Inna Hannatu tace Itama Tana Goyon Bayan Umma wannan Shi ya sagar mai da Gwiwa har suka Iso Nene baki Take bashi kan kar ya Damu Umma Fade kawai Take,Bai Shiga Gidan ba yana Sauketa ya juya zuwa Gida Tunda Abba na Gida,Haddir ne ya Shiga Har suna Hira da Zareena sai chan dare ya koma Gida.

*****
Washegari Bakin Yan Abuja Suka iso Mama Safiya da Hamdiya da kawayen Hamdiya Guda Biyu sai wata yayar Mama safiyar Amina,Daman Mama Safiyar yar Kano ce,Sauran Dangin suna Tafe gobe,Chan kuma sai ga Inna Rukayyah da Zafeera da Maryam yar wajen Inna Hannatu Daman Taje kanon Hutu sai Shema"u sun Dira Su Asma"u sai zuwa Gobe Gidan Alhaji Tsoho ya Cika ba Matsaka Tsinke Chan zuwa yammah kuma sai ga Mom Iklima ita da Takwanran Hajiya Mama Wacce suke kira da Hajiya Harda Amin aka zo Duk da basu samu Hutun makaranta ba Baban kaduna yace azo Dasu Saboda Yan"uwa kowa zai Hadu su ga yan"uwa da abokan arziki Mazan dai basu Riga sun iso ba sai Ranar jumma"a Duka zasu Hallara Harda Tawagan Angwaye.

Su Zafeera suna Zuwa Gida Suka Wuce ita da Shema Harda kayansu,Nene da Umma daman tun safe suka Tafi Harda Zareena Zainab ce agidan sai Zaina sai Kuma Dina Hakima Zaina Tayi Murna da ganin Zafeera suka Rumgume juna Daman Umma tace Zafeera Karta bar Zaina agida Ta matsa mata su Taho Tare Sai da sukayi sallar suka ci Abinci suka sake wanka kana sukayi Shirin komawa Gidan Alhaji Tsoho Zafeera kuma ta matsa ma Zaina ta Shirya su Tafi da ta Fara Nokewa kan bata da kayan sawa tafarayi Zafeera ta Bata nata tace sai ta saka Dole Kanwar naki ta Shirya Ta saka kayan Zafeera Doguwar Riga Duk da Daman Zafeera Tafita Jiki ammh abaya Kayanta na yi mata Saboda ita tayi Cikar aure ammh yanzu Rigan Tayi mata wani Burum sai Dan Wuya,Zafeera ta Daukota mata mayafin kayan ta Bata Da Farko tace bazata saka ba Zafeera Ta Rantse mata sai ta Saka Dole ta saka Sun Fito Falo zasu Tafi sai ga Shigowar zakiya Wacce Dina ta Kirata kan tazo Ta Tayata zama Duka gidan sun Tafi sun barta ita kadai kallon kallo Sukayi ma Juna Daman Daga Zafeera har Shema yan Bana bakwai ne suma awulakance suka kalleta suka Dauke kai zaina dai Tana Rike da hannun Zainab Jikinta na Rawa Ita kuwa Zakiya mamakin yaran Take Shema cikin Kallon Tara Saura kwata tace'Wannan itace uwar Shegen..? Wacce tazo Goyon Ciki Gidan iyayen abokin Farkan nata..?

Da Sauri Zafeera Tace"A"a ba ita bace..Abokiyar Shanshancin nata ne.."Shema Tace"Ko Daga gani Daman ba kima.Mudai an Hadamu da Bakin Gaddara.."Zainab tace"Wlh kuwa.."Kafin Zafeera ta Ja Hannun Shema da Zaina Tana Fadin"Let go.."Suka wuce Zakiya Data kame Tana Binsu da kallon Mamaki har suka fice Daga Falon.

Kada kai Zakiya Tayi ta karisa Dakin Dina ta sameta Ade ade kan gado Tana Dannan waya Cikin wani irin Isgilanci Zakiya tace"Wasu Kwalayen yan iska kuma kuka samu agidan..? Nagansu tare da Kodaddiyar Kishiyarki Wacce Duk ta Rame ta Kode kamar Kudin Guzuri...!

Dina Tace"Hmm Waya sani..Kila yan Biki ne nidai ina ta jin Hayaniyarsu.."Zakiya na zama Gefen gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Lalle..Kam...Naji sunata mganganu ni Dariya ma suka Bani Dukkansu kananan yan Iska ne basu san me ake Kira Bariki ba Ballatana Iskaci.."Dina Tace"Nidai bar wannan mgana Cikin nan ya Fara isata na kosa na Haifeshi yamin Katanga da Abun kaunata Tunda fa nazo Gidanan ko Inda nake Zain bai Taba kallah ba ballatana na saka Ran wani kyakyawan kallo Daga Barayinsa.."

Zakiya Tace"Karki damu...Sauran wata Biyar ki Haife Abunda ke Cikin ki Daga Lokacin kuma ai bashi da yarda zai yi zai saba mganar kakansa ne bayan Tarin Laifukansa Kisha Kurumin ki kin Riga kin zama Matar zain Ta har Abada.."

Dina Ta washe baki Tana Sakin Dariya,Zakiya kuma Tana mata Mirmishi Cikin Tsausayamata yadda Ta Kwallafara akan Zain Wanda ita bata Fatan hakan ya Faru da ita,tafi son Rayuwar yanci Da kuma Sakewa nan Ta gyara zama suna ta Hira da Dina Rabi Duk Labarin Shanshancisu ne Da kuma Mafarkin Dina na Auran Zain.

****

Umma Taji Dadin ganin Zafeera Ta Taho da Zaina Kowa ya ganta sai ya koka Ramarta Inna Rukayyah da Mom Iklima sai da sukayi mganan kan Ramar Zaina suka kuma yi mata Fadan Ta Cire damuwa aranta Ta kuma Dinga cin Abinci Tace Toh,Sai Ranar Alhaji Tsoho Ya ga Zaina Tun bayan Faruwar Lamarin Alhaji Tsoho Shi kanshi Yaga Ramarta Sosai ammh sai bai yi mata mganar ba Ya dai mata wasan Dayake mata Tunda yaga bata wani maida kai ba yasan Har yanzu Abun bai saketa ba,Daganan sai yan matan suka kebe kansu Dakin Hajiya mama Harda Hamdiya da kawayenta,Duk da Sauran kawayen suna Tafe gobe,Duka suna Tare ana ta Hira Zaina na gefe sai dai in Su Zafeera Sun sakota ta Dan Murmusa nan suka kai Dare sai Wajen 9pm na Dare suka koma Gida Taga dai Haddir ammh Bata ga Zain ba,wanda kuma ya ZO gidan Bai Kawo Cewa Zaina Tazo ba kuma yayi Tunanin Binta Gida sai yaga pass 6 Abba ya koma Gida sai ya Fasa Bayason Ran Abba na Baci saboda shi!

Sai washegari  alhamis ya ganta Dayake sunyi Sister Day nan Filin Gidan Alhaji Tsoho akayi komai bayan anyi Hayan Konofi da kujeru Baki na Nesa Dna kusa sun kariso Dangin Mama Safiya Mota Biyu suka yo Daga kano Banda na Sauran garuruwa,Wasu ma suna Hanya basu kariso ba manyan ya"yan Inna Hannatu dana Inna Rukayyah duk sun kariso Da nasu Tawagan,Daddyn Abuja ma ya Iso aranar Baban kaduna ne sai Zuwa Gobe Suma Daga Barayinsu sunyi gayyah Sosai,Domim Katin ma Guda100 Suka Bugo wanda Abba ya Daukin Nauyin buga katin Gayyata Daga Gidan Saulawa Harta da chan katsina yan"uwan da suka Rage duk Hajiya mama ta Kirasu awaya ta sanar dasu Ganin gidan ya Cika ne yasa Haddir ya Tattara Inashi Inashi zuwa Lowcost wajen Zain wanda yaji Dadin haka Sosai,Yan matan kuma Ranar ma Gidan Abba suka yada Zango chan ya Cika da Iyayensu.

Kowa ya maida komai bakomai ba an manta da Abunda ya Faru..Zaina ce dai suke Tsausayamawa Kowa yana nan nan da ita Bangaran Dina ba wanda ya Damu da Tambayarta ma Domin kowa haushinta yake ji Gwara ma Inna Rukayyah Tayi mganarta Tace chan gida suke Barinta Don karta Fito Labari ya Yada gari,Nene tace Tana Gida Ko Su Shema da suke kwana agidan ba ganinta suke ba,Tana Dakinta Bata Fitowa komai sai dai ayi mata Tana Daga Cikin Daki Nene ce ke wannan Wahalar Suna Gidan suna Sha"aninsu basu ma Damu da ita ba Itama bata Damu dasu ba Sai dai in Zakiya Tatashi aiki Sai ta Kirata tazo Ta Tayata zama,Su Wuni suna Shakiyansu wani Lokacin sai su Umma sun Dawo Take Tafiya.

Ranar Daya ganta ana Tsaka da Sister Day din ne Sun yi Shigar Jallabiya baka,Wanda Zaina bata ma san Umma ta Siya mata Har taso ta Zuke zuwan Taga Umma ta Dauko mata Dole ta saka Zafeera Tayi mata Rolling Da Vail Din Harda Shafa mata Hoda da Man baki sai gashi Ta Fito kamar ba ita ba sai dai Rigar Ta bayyana Ramarta Sosai ,Abunda yasa ya ganta Daddyn Abuja ne ya aike su Shida Haddir suka je gidan Buredi suka Siyo Buredi mai yawa Cikin Booth Daga asibiti suka Biya suka Siya sai Suka Wuto Dashi Gida suna zuwa suka Iske ana Taron,Ganin mata sun yawa bai ma Tsaya gane kowa ba sai Haddir ne ya Tabashi Yana nuna mai Zaina wacce ke zaune kusa da Zafeera Ido ya kura mata Yana kallonta Cikin wani yanayin Ganin yadda Rigar Tayi mata kyau ne Sosai Tabbas ya sani Firstlove ta Rame sosai ko kula da matan Dayake wajen bai bi yi ba ya isa inda Suke zaune Tun kafin ma yayi mgana Umma Tazo Taja Hannun Zaina ta maidata Kusa Da ita Tana Hararan Zain wanda yayi kasake kawai yana kallon Umma Inna Rukayyah ce matayi ma Umma mgana kan ta Sausasauta ammh Taki mgana sai ma Hade rai Datayi ita kuwa Zaina Tama ji Dadin haka Domin bata kaunar Kara Haduwa ko Kebencewa da Zain.

Jiki ba kwari ya Juya ya Tafi Ko Cikin Gidan Bai Shiga ba Haddir ne ya Shiga Ciki Buredin kuma yara suka kwashe Zuwa Ciki,Har suka Tafi Umma na makale da Zaina Bata matsa ma,sai Gabda Mangariba aka gama Sister Day din Aka koma Cikin Gida Ba Wuta katon Genenrator Din Gidan Alhaji Tsoho aka kunna Haske ya Gauraye ko"ina Dama su Zafeera da Shema da Zaina da maryama Haraban Gidan suka Shimfida Darduma katuwa Tun bayan da aka kwashe Kujerun,nan sukayi Sallar Mgariban kana suka Nufi Cikin Gidan Inda Hamdiya Take da Bakin kawayenta Yan wajen aikinsu da abokan karatunta da suka Sauka Dazu Da Rana.

Koda suka Shiga Falon sun Tarar da Duka iyayen nasu suna Falo Inna Rukayyah,Inna Hannatu,Mama Safiya da yan"uwanta Mom iklima Umma,Nene da Sauransu sai Hira ake ana Dariya sai gasu Zafeera sun Shigo sannu da gida suka yi musu kafin su Wuce Zuwa Dakin Hajiya Mama Mom Ikilima ce ta Kura ma Zaina ido kafin Ta Daga baki ta Kirata Ta Juyo tazo Tana zuwa ta kara kallonta kafin tace mata Ki dinga cin Abinci kinji ko Sa"adiya Da Toh ta amsa kafin Tace Tatashi Taje Tana Tashi Mom Iklima Ta kalli Umma Tana Fadin"hmm wai ke Hajiyar Allah da kike kokarin Raba wannan Auran ina zaki kai Cikin Jikin Sa"adiya..?

Gabadaya Falon sai ya koma kan Mom Iklima Cikin mamaki Umma ke Fadin"Ciki kuma..?ke Uwar Amin wata Sa"adiyan ce ke da Ciki Zaina..? Mom iklima tayi Mirmishi Tana Fadin"Toh da wace Sadiya garemu..Ita fa Wlh Ciki gareta.."Ido Umma da Nene suka kwalalo Umma Cikin Wani yanayi tace"Wai wani irin Ciki..? Badai na Haihuwa kike Nufi ba..?

Mom iklima Tace"Shima fa gareta..Kina ina baki gane ba..? Yayi Wata uku in ma bai fi ba Wlh.."Nene ta washe baki Tana Fadin"Alhamdulillah.."

Umma kuwa Tagumi Tayi Tana Fadin"Wlh bansani ba...Ban taba lura ba..Mau ciki da Rama kalleta fa ki gani.."Mama Safiya Tace"Nima Wlh mgana ne kadai Banyi ba ammh Tun Lokacin da Naganta Sai dai naga alamun Ciki Tare da ita.."

Mom iklima Tace"Ai Indai Kasan alamun Ciki kana ganin Sa"adiya kaga mai Shigar Dan Ciki ajikinta.."Umma Ta saki Numfashi Tana Fadin"Wlh ban taba Lura ba..Naga sai Uban Rama Take,ammh Nima alamomin cikin sai yanzu na Fahimta Domin Kwana Take kwanaki cikin zazzabi,Ga Amai komai taci sai ta dawo Dashi Ni ban kawo komai ba Tunanin kila Saboda Damuwa ne.."

Mama Safiya Tace"ai mata kala kala ne...Wata Zaki ga Ciki ya Sakata kiba Tundaga Farkon Laulayi wata kuma Daga Farkon zata Rame sosai sai Cikin ya Girma sai ta Murmure.."Nene Ta Daga Hannu Sama Tana Fadin"Alhamdulillah..Sai aba ma yaro na Matarsa yanzu.."

Umma Ta Sauke kai kawai Tana Fadin"Umh...kawai batare da ta kara mgana ba Su Mama safiya suka Cigaba da Tattauna mganar suna gayama Umma Tayi Hakuri kawai ta maida Zaina Dakinta Abunda ya Faru ya Riga ya Faru Mama Safiya tace"Nifa addu"ata Allah sa in Yarinyar chan tatashi Haihuwa Ma yaron ya mutu tun aciki kowa ya Huta.."Duka suka ce Ameen Wlh Umma dai na Jinsu bata kara mgana ba ta Shiga Kogin Tunani.

Dakyar Zaina Ta iya karisawa Dakin Hajiya Mama saboda Fargaba da kuma Tsoro a kunnanta Taji mganar Mom iklima Da mganganun su Umma Labe ba Dabi"arta bane ammh Jin Abunda Mom iklima Tace ne yasa Gabanta ya yanke ya Fadi Shikenan Abunda Take Boyewa ya Bayyana Shikenan Umma zata Rabata da Firstlove Lokaci Daya Kuma Ta Rabata da Abunda ke Cikinta Wasu Hawaye suka Zubomata Lokaci Daya Tana Dafe Cikinta Saurin Goge Hawayenta Tayi Ganin Zafeera Ta Fito Tana nemanta Tayi kokarin Shiga Cikin su Ta nuna komai ba komai bane ammh Cikin Ranta cike da Fargaba da kuma Tunanin Taya ya zata Tseratar da Cikin Jikinta Domin Tana Sonshi Tana ma jin aduniyar nan Shine Kadai Wani makusacinta.

Umma ma abangaranta Haka Abun yazo mata Shiyasa anayin isha"i Ta kira zaina tace su zo su Tafi Gida sai tace dasu Zafeera zata Dawo Umma Tace ta wuce su Tafi Tun a Mota Take Sharan Hawaye Domin tasan kwanan Zencen ai kuwa suna Zuwa Gida Umma ta Tusata Daki ta Tsareta da Tambayan da gaske ne Tana da Ciki..?

Tsoro ya kamata Ta Fara kuka Taki mgana Umma Ta kalleta Tana Fadin"Kukan ki ya Tabbatar min kin san dashi ammh Baki sanar dani bako..? Dalili kenan kika Hana muje asibiti ko kada ace kina da ciki naji ko..?

Da Sauri Zaina tace"Ban sani ba Umma..Ban sani ba.."Take Fada Tana kuka Umma Ta girgiza kai Tana Fadin"Miye na kuka kuma Halima..! Nifa yakin so kanki nake miki Wlh..? shi Zain din ya sanda kina da Ciki..?

Saurin Girgiza kai Tayi alamun A"a Umma Ta kada kai Tana Fadin'"Karki sake ki sanar dashi..Domin wannan cikin bazai sakani na Fasa Abunda nayi Niyyah ba Dole ya Sakeki..Cikin ma Zubar dashi zanyi.."

Umma Ta Fada Daga karshe Cikin Gatse ganin yadda Zaina ke kuka aikuwa kalmar Umma Ta karshe Ta saka Zuciyar Zaina Tayu wani Rugurugu,Da Sauri Ta Dago Tana kallon Umma Cikin Firgici da Tsoro Cikin Hararanta Umma tace"Eh haka nace..Ki bar kallona da wadanan Idanuwan naki kafin Ranki ya baci.."Dole Zaina ta maida kanta kasa Tana Danne kukanta Ranar kwana Tayi kuka Umma na jinta Tayi mata Banza Tana ganin ikon Allah Ya zama Dole ta Yi Kaffaran Rantsuwanta ta maida halima Gidanta kafin Watarana ta maida kanta Ji Daga mata gatsen Zubba da Ciki Ta kwana tana kuka,Su Zafeera basu dawo ba Chan suka kwana sai da Safe suka zo sukayi wanka,Umma Tun Safe suka koma Gidan Alhaji Tsoho,Zaina kuna sai da Zafeera ta matsa mata kana ta koma Ammh kowa ya ganta yaga Ta Rage Walwala kamar baya,Zafeera Tayi Tambayan Duniyanan Taki mata mgana Gabadaya Tagama Rudewa Tana Son Firstlove Tasana san Cikinta Bata za iya Juran Rasa Ko Daya ba Aranar har yanke Hukuncin Neman Zain Tayi ta gayamai komai ta Fito Haraban Gidan ko Zata ganshi bata Ganshi ba Ranar asibiti ma ya wuni bayan an tashi ya Tafi Gida ba Saboda baya son ganin Matarsa ba sai sanin Halin Umma Ga kuma Mutane sun Cika Gidan ammh ya Guduri Niyye Ranar Daurin Aure Sai ya saceta sun gudu wani waje sunyi sati basu nam kila Daganan Umma zata bashi Matarsa.

Washegari Jumma"a Aka Tashi Da Shirin Walima Baki kuma Duk sun gama isowa Baban kaduna ma Tuni ya iso,Basu da mataalan Wajen kwana Boysquaters suka Tare Dayake Yana gyarashi Lokaci bayan Lokaci Suma Ango da Abokansa sun sauka ammh Otel suka kama su.

Da yammah akayi Walima Wata malama aka kira anan Haraban Gidan tayi wa"azi kan Aure akaci aka Sha aka kuma yi Rabon Abubuwa Domin Zuwan Daddyn Abuja yasa mota Biyu tazo Ta Sauke Ruwan Gora da kuma Drinks kala kala Da komai na Bukata Bangaran Abinci Daman Oda akayi sai dai aka kawo shi adafe wannan aikin Abba ne shi ya Dauki Nauyin komai.

An Tashi Walima Kenan Sai ga Goggo Halima Ta iso Da matar Danta Isuhu,Zuciyar Zaina Ta kara Raunana ganin Goggo Halima Haka ta Rungumeta ta Fashe mata da kuka Dagota Tana Fadin"Ke kuma haka ake murnan sai kuka..?

Umma Dake gefe Sai Jikinta Yayi sanyi Hajiya mama ce Tace"Uwa mai Dadi tayi kewarki ne Hali Dubu.."Goggo Halima ta saka Dariya Tana Fadin"Haba dai Hajiya Mama mai uwa Irin Umman Zareena da Nene wani kewa zai yi kuma..? Ga salihin Miji Irin Zainullahi Wlh Sa"adiya bata da wata mtsala sai Godiyar Allah.."

Su Mama Safiya Da yan"uwanta da su Mom iklima suka ce"Hakane kam...Shagwaba ce kawai. "goggo Halima ta Tureta Tana Fadin"Ja chan..Banason Sarkaci Tafi wajen uwar taki kiyi Tabaran ita data Daure miki Gindi.."Umma ta Jawo Zaina Jikinta Tana Fadin"Taho nan Diyata...Ga inda ya Dace kiyi Shagwabar ki nan Bar Goggo Halima taji da Tsufanta.."Gabadaya aka saka Dariya ammh banda Zaina wacce ke Tunanin Abunda zai Faru gaba.

Nan Su Zafeera suka bar Duka iyayen yan matan kuma Harda Hamdiya da kawayenta wajen su Takwas suka Tafi Gidan Abba su kwana Sai gobe su dawo Tunda Gidan Alhaji Tsohon ya Cika da baki Goggo Halima chan suka barta Cikin su Umma sai kwamawa suke da Hajiya Mama daman abokiyar yinta ce.

Da suka koma Gida ba wanda ya Damu da Dina sai Zainab Data Shiga Wajenta Tunda Nene ta Roketa Ta Shiga ta Dubata,Tana Shiga sai da ta saka Ta Dafa mata kwai wai shi zata ci Ta isketa Zaune kan gado Tana kallo Cikin System dinta Harda cewa su rage Hayaniya Saboda Bata son Damuwa Dayake su kadai ne agidan Abba ma yana Gidan Alhaji Tsoho wajen yan"uwansa Harda Alhaji Tsoho wanda Shima yayi kaura Daga Cikin Gidan Saboda mata Zuwa nan Boysquaters.

Dakin Umma Su Zafeera suke Hamdiya kuma da gayyarta suna Dakin Nene Zaina sai da ta bari duk sun yi wanka sun yi Shirin kwanciya kana ta Zare Jiki ta Shiga Tiolet din,chan ta samu Damar yin kukanta ya Isheta da kuma Tunanin mafita Ta Dade kafin Ta yanke Shawara da kuma Hukunci Duk da Abun Da zata aikata bazai ma kowa Dadi ba ammh Shine mafitan Cikinta da kuma Auranta Uwa uba ta Gujema ganin Auran Firstlove dinta da Wata mace irin Dina...!









*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️

*BOOK 1*

               2️⃣9️⃣

Sai da Ta Tabbatar da kowa yayi Barci kana tayi wanka ta Dauro alwala Ta Fito Daga cikin Bayin Sadaf Sadaf ta iske su Zafeera sun kwanta Duk sunyi Barci Alamun gajiya nan Taga Hamdiya Amarya Itama Ta baro chan Dakin tazo ne ta kwanta Saman Cafet barci ya kwasheta Saboda Gajiya.

A hankali Ta Dauki Hijabinta Ta Zura Bayan Tunda a Tiolet din Ta maido Doguwar Rigar Abayan Dake Jikinta,Ta shinfida Darduma Ta Tada sallah Bayan Ta Idar ta Dade Tana addu"a Lokaci Daya Taji Natsuwa ya sameta,na game da Abunda Take Shirin aikatawa,Batare da wani Dogon Tunani ba Ta Mike Tanayin

39 / 43