Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
mai kyau ce ko Batayi kwalliya ba kyanta yana Haskawa Ita kuma Zakiya Doguwar Atamfa ce ke jikinta wacce ta kamata sosai Daga mazaunanta,Kanta ba Dankwali Sai da ta yafa wani Vail a Kanta zuwa Saman Kafadarta Takalmin kafarta ma mai Tsini Ne sai wani Glass Data Toshe Fuskarta,Hannunta Dauke Da karamar Jaka lokaci Daya kuma Tana Kada key din Motarta akallon Farko in kayi musu sai ka kara Domin Sun amsa Sunansu na Mata masu aji da Baiwar iya Taku da isa da kuma Haiba Iya Sarrafa Jikinsu.
Zakiya Tayi ta kara ma Dina karfin Gwiwa Tunda ita ta Sare,kuma ganin Kowa nata zuwa gaishe da Alhaji Tsohon zakiya ta nuna mata in bataje Ba, Zain bazai ji Dadi ba Da wadanan kalaman Ta kara jan Ra"ayinta Ta jata suka Nufi Family Side na Cikin Asibitin.
Duk wanda ke asibitin Dr.Saulawa ya san da wannan Shashin,Shashi ne wanda Dr.Saulawa tun yana da karfinsa yasa aka samar Dashi Saboda iyalansa da yan"uwa da abokan arzuka nan ake Attempting Dinsu har su samu lafiya Shashi ne mai matukar Girma da kawatuwa,Koda yaushe Cikin Gyarashi ake da Sauyamai Fasali,Duka iyalansa ba Wanda bai da Fayel acikin asibitin Saboda Halin Rayuwa Dr.Saulawa da kansa yayi ma Shashin Lakabi da Fanmiy Side.
Daki na Mussmman Mai dan Girma ne Alhaji Tsohon ke Ciki Kofar tana Rufe ne ammh Kana jin Hayaniyar mutane kadan Kadan Daga Ciki Zakiya ce tayi Knooking Din kofar kafin ta Tura ta Fara Shiga da karamar Sallama Hannunta jaye da Hannun Dina Wacce Take jin Wani irin Faduwar gaba kamar ta arce ta gudu,Suna Shigowa Dakin Gabadaya kallo ya Dawo Garesu Sai da suka kariso Tsakiyar Dakin zakiya Taja ta Tsaya Itama Dinar sai ta Tsaya cak,wanda yaji kayan alfarma kamar ba asibiti ba kama Daga Cafet,Kayan kallo kujeru Da kuma Abun Sanyaya Daki A.C,Fridge, Sai gadon Mara lafiya Dake gefe chan Shima din Wani Tsararra ne,Wanda ba Daya yake da Sauran gadajen Dake Cikin Asibitin ba Daga gani na Musamman ne kamar yadda Barayin Ko Shashin yake na Musamman.
Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba Usman Suna zaune kan kujeran Dake Gefe,Yayinda mai kallonsu kuma Mom Iklima da Mama Safiya sai Nene ke zaune akai,Daga gefe kuma kan Wata Farar kujera Inna Rukayyah ce zaune,Daga Saman Cafet din kuma Umma ce da Inna Hannatu,Daga saman Gadon da Alhaji Tsoho ke Kishigide Bayan an karamai Filo abayansa kuma Hajiya Mama ce ke zaune gefensa Itama Daga gefenta Zain ne zaune ya yada Kafadarsa Bisa Kafadarta Suna mgana kasa Kasa Daga Tsaye kuma Haddir ne Wanda ya coge Hankalinsa kaco kan yana kan Wayarsa ne,Daga tsakarwajen kuma ga manya manya kololi nan Baje na Abinci sai manya manya Ledoji na kayan Marmari,Daga yanayinsi zaka Fahimci Tabbas Ahalin ya Cika Ahali kuma Ahali ne na Girma Da Dattako.
Da yin Sallamarsu Dama Wajen yayi Tsit duk da Farko Hira na Tashi Sama sama,Gabadaya ido Suka zuba musu suna kallonsu Sama sama da kasa Duk da Baki sun Ta shigowa wasu ba saninsu sukayi ba wasu Likitoci Asibitin ne wasu kuma Nurses ne da Sauran Harda ma"aikatan Asibitin Ba"a barsu abaya ba,ganin Sun Coke ne sun kasa karisowa yasa Inna Hannatu ta Washe bakinta mai Dauke da Hakorin makka Tana Musu Maraba sai Lokacin Dina ta iya Dago kanta ta Kare ma Jama"ar Dakin Kallo Daidai Lokacin da Zain ya Dago kansa Daga Kafadar Hajiya Mama suka Hada Ido Hudu Da Dina.
Wani irin yanke gabansa yayi ya Fadi Lokaci Daya ya zaro Ido yana kallonta ita kuma sai ta lamgwabe mai kai ta wani Rausayar da idanuwanta,Zakiya ce ta Damke hannunta Lokaci Daya tana Sakin Mirmishi ganin Gabadaya idanuwansu yana kansu ne,Zain kuma da Sauri ya kauda kai yana kokarin Daidaita Natsuwarsa Haddir ne ya Dago kansa ya Sauke su kan Su Dina da mamaki yake kare musu kallo bai samu Zarafin mgana ba Yaji Alhaji Tsoho Dake Kishingide Cikin Wata Farar Jallabiya Muryansa ta Dan Shake alamun Mura yace"Maraba sannunku da zuwa..Ke Hannatu ku basu Wajen zama mana.."
Yafada yana kallon Inna Hannatu dake Zaune kasa,Bata mike ba illah kafanta Data jaye Tana Fadin"Ai maraban nake musu Alhaji Tsoho Sannun ku da zuwa ga waje ku zauna Duka iyayan naku sun zaune kujerun.."
Tafada Tana yar Dariya Da Sauri Zakiya Tace"La bakomai..Dama munzo Duba mai Jiki ne.."Tafada tana jan Dina zuwa Gaban Gadon Alhaji Tsoho Cikin ladabi Ta Rankwafa ta gaisheshi da Alhaji Tsoho da Jiki ya amsa Ganin haka yasa itama Dina Tayi hakan ya amsa Cikin Sakin Fuska yana ta saka musu albarka Zain dai Gabadaya bai da Natsuwa Hajiya Mama dake gefensa Tace"Kai kuma lafiyarka sai Hada Zufa kake Kamar wanda yake jin kashi..!
Tafada Tana kallonsa Dariya ta Kubcema Haddir ya saketa har yana Dukawa yana kallon Zain wanda ya Hade rai yana wani Hura Hanci Cikin Son Basarwa yace"Ina Ruwanki kedai ji da wannan Tsohon Mijin naki gawa taki Rami kawai.."Haddir sai Dariya yake Hajiya Mama na Tayashi Dina kuwa sai nacin kallonsa Take yaki yarda su Hada Ido Zakiya kuwa kowa awajen take karema kallo su Baban kaduna dai suna ma Hirnsu ne haka ma su Nene Gwara ma Inna Hannatu da Umma hankalinsu na kansu Suna Nazaratansu.
Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Yau kuma Aminatu Keda Megidan naki ake jin kanku..? Haddir yayi Saurin Fadin"Tsoho Daman ai Megidan na Bugi ne..Nine kadai Megidan gaskiya.."Hararansa Hajiya mama tayi Lokaci Daya Tana maida Hankalinta kan Zain wanda ya Fito da wayarsa yana Dannawa ji yake kamar Ahalinsa sun san Abunda yake aikatawa Shiyasa ya kasa Sukuni Sai Hada Zufa yakeDafoshi Tayi Tana Fadin"Kaji Juyo gareni Megidana Zainullahi kyale Hadiru ni kam Bani son Shi baya Cefene."Saurin Ture hannunta yayi yana Fadin"Jeki na Sakeki..Ko ki koma wajen Tsohon Mijinki ko kuma ki koma Ma Haddir din."kwabe baki Tayi Tana Fadin"Au ni zaka watsa ma kasa a ido..?
Fuska ya Hade yana Fadin"An watsan wa ya ja.."Yafada yana matsawa kusa da ita nesa kadan Haddir da Alhaji Tsoho suna ta musu Dariya Dina dai da Zakiya suna Tsaye suna kallon Tsabar Shakuwa Tsskanin Jikoki da kakaninsu,Alhaji Tsoho ne ya an kare dasu,Dasauri ya kallesu yana Fadin"Af..Kunga mun Sha"afa da Baki..Sannunnku an gode ko..? Ammh Daga ina kuke ne...?
Yafada Cikin Muryan Tsufa Lokaci Daya yana gyara zaman Farin Gilashin Idonsa Zakiya ce ta Murmusa bata samu Zarafin mgana ba Haddir yace"Wannan anan asibitin Take aiki...Wannan kuma ina jin kawarta ce Domin ba'anan take aiki ba"Yafada yana kallonsu Zakiya Tayi yake kafin Tace"Eh ni Kawarta ce.."Tafada tana wani kallon Haddir din Kasa kasa yana Lura da ita ammh sai ya basar da ita,Alhaji Tsoho yace"Allah Sarki Sannunku fa Nagode Allah yayi albarka.."Sukace Ameen Cikin Dattakonsa ya kallesu yana Fadin"Duk wanda yazo gaisheni Ko daga ina ne baya Tafiya sai na san Sunanshi ko Sunanta.!
Zakiya ta Murmusa kafin Tace"ni Sunana Zakiya Nuhu Daga Jahar kano.."Tafada tana kallon Dina Wacce take nacin kallon Zain Shi kuma yaki kallonta Cikin Sadda kai Tace"Dina Gaddafi Sheerif Nima Daga Kano.."Alhaji Tsoho ya kalleta Sosai bama Shi kadai ba Hatta su Baban kaduna sai da suka Dago Suna kallonta kafin Alhaji Tsoho ya samu Zarafin mgana Baban Kaduna yace"Gaddafi Sheerif Dai da muka sani kwamishinan kudi na Jahar kano.."
Haddir ne ya gyada kai yana Fadin"Shifa Baba..Diyarsa ce.."Baban kaduna da Daddyn Abuja suka Hada baki wajen Fadin "Ikon Allah.."Shiko Alhaji Tsoho Mirmishi yayi yana Fadin"Masha Allah..Sannunki naji Dadin yadda kika Dogara ga kanki ba wa mukamin Babanki ba kika Tsaya kikayi karatu Domin Taimakon Al"ummah Allah yayi albarka.."Kansu na kasa Suna amsawa Da Ameen Alhaji Tsoho ya sake kallon Dina yana Fadin"Ammh yata Baki da wani Suna ne..? Naji kince Sunanki Dina kuma a sanina Sunan Kiristoci ne wannan Sunan domin in bazan manta akwai wata wacce mukayi aiki da ita a asibitin Dana Fara aiki a Bongcuf,Itama Likitar kwakwalwa ce Sunanta Dr Dina itama.."Dariya ta kama su Umma da Inna Hannatu Hajiya Mama tayi karaf tace"Yo in ban da Abunka Alhaji Yanzu yandda zamanin nan ya lalace Sunan ma Da zakaji an saka bashi da wani Ma"ana ayi ta kwaikwayon Arna wajen saka Sunaye Allah dai ya kyauta kawai.."Haddir da Alhaji Tsoho Suka ce Ameen Dina kuwa sai Taji ta Muzanta Kallonsu Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Nagode kwarai Allah yayi albarka..!
Zakiya ta Rankwafa Tana Fadin"Allah kara lafiya da Nisan kwana.."su Inna Hannatu suka amsa da Ameen Ameen juyawa sukayi suna ma su Nene sallama Mama Safiya ce kadai ta amsa Mom Ikilima kallon TaraSaura kwata tayi musu Tana Fadin"Kai Nene wadanan yan mata basu da kamun kai kalli Shigarsu.."Nene ta Tabe baki Tana Binsu da wani kallo Haka Kurum Taji basu Burgeta ba,Suna Gabda Fita Daga Dakin aka Turo Kofa aka Shigo Zainab ce kan gaba ita da Maryama Din Inna Hannatu,Dauke da manyan Kololi a Hannunsu,Sai Zafeera da Zaina da suka Shigo Daga Baya Zafeera na Rike da Filet da cokali ita kuma Zaina na Rike da Katon Jug,Dukkansu basu ma Lura dasu ba Zafeera har Tana bangazan kafadan Zakiya kuma ko ta waigo Saboda Hankalinta ya tafi kan iyayenta Dake Dakin ne,Zakiya ta Juyo Tana kare ma Zafeera kallo Cikin baki isa ba ita kuma Dina Zaina ta kura ma ido ganin ta ta kara Kiba da Haske Alhaji Tsoho ne ke ta Fadin"Maraba da Amaryata Halimatu Sa'adiya mai Hali Dubu...Maraba da Zafeeratu Farar mace alkyabban Mata maraba da Zainabu Abu mai Tagwayen Suna Maraba da Maryama Allahu Akbar Allah yasa Ki yi koyi da Hali Irin Maryama Uwar Rikon Haddir da Zanullahi da Zareena uwa Shakikaya wajen Halimatu Sa"adiya Allah ya mata Rahma Ita da Abdullahi Da Mallam Umaru da Atine Allah ya Hadamu a Aljannah Firdausi.."Ya karishe Fada Cikin Alhini Duka Dakin suka Hada baki Wajem Fadin "Ameen Ameen ya Allah...Allah ya Haskaka kabarinsu.!
Gaban su Umma suka yada Kololin Gabansu suna gaida Iyayen Nasu Daddyn Abuja ne yace"Sa"adiya me kika Dafo ma Tsohon naki ne?ya fada yana kallon zaina dama Sa"adiya yake Kiranta da Shi,Baban Kaduna ne kan kirata Halimatu su Mom Iklima kuma Dukkansu Zaina ne,Tana Dariya Tace"La..Daddy Tuwon Semo nayi muku miyar Kubewa Bushashiya Dukkanku Domin nasan Duka iyayen nawa sun yi Gado Wajen Tsohon nan na kwance.."Ta karishe Fada Tana Dariya Suma Dariyan Suka saka Mama Safiya tace"kwarai..Duka gidajenmu Gidan Daura Tuwo ne..Allah dai ya karama Alhaji Tsoho Lafiya..!
Suka amsa da Ameen gabadaya Alhaji Tsoho yace"Dama ai kyan ya"ya su gaji Tsohonsu...Kunga wannan Tuwon Shi ke kara Muku Lafiya da karfin gani ba Ciyen Ciyen kayan Turawan nan ba.."Zain yace."Hakane Tsoho...Ina mamakin zamowarka Likitan kwakwalwa Ba Likitan Sanin Mutum har hanji ba.."Dariya suka sakamai Gabadaya kafin Hajiya Mama tace"Ke ta kwacen Miji zuboma mijina Tuwon yaci yasha mgani Tun Dazu yaki cin komai yana Jiranki.."Tafada Tana Hararanta Dariya kawai tayi ta Duka ta Fara zubamai Tuwon Zafeera na Tayata Zain na Daga gefe ya Dago kansa yana Fadin"Kinga Firstlove Da kin Sakama Tsohon nan Zubomin Ina jin yunwa.."Haddir ya kallesa yana Fadin"Lalle ne ma.Su Abban fa..?
Harara ya Zabgamai zai yi mgana kenan suka Hada ido Da Dina Dake tsaye har yanzu basu Tafi ba Ido yazaro yana kallonta ganin Haka yasa Zakiya Taja Hannun Dina suka Fice su kansu basu san meya Tsaidasu ba ammh Ahalin na Gidan Saulawa Abun kallo ne Suna Da Fahimta Da kuma Kaunar Juna basu samu Zarafin mgana ba sai da suka Dangana da Office din Dina Zakiya kafin ta zauna sai da taKwankwadi Ruwa kana ta koma tazauna Tana maida Numfashi Dina kuma Takaichi ne Fal acikin Ranta da kuma Kishin Zaina Daya yi mata katutu.
Dina kuwa zama Tayi kan kujeran Dake kallon na Zakiya Tana Fadin"Tsohon nan ya Cika Tambaye Tambayen Tsiya..'Zakiya tayi Mirmishi Tana Fadin"Likitan kwakwalwa ne fa...Tsohon Daga gani Lokacin Da yake kan ganiyar kuruciyarsa anyi Jajirtattace.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya kafin ta Dora da Fadin"Baki mamakin yadda Shekarunsa sukaja Haka ba ammh kallesa Hutu da Jin Dadi Sun Boye tsufansa..?
Dina Ta Tabe baki Tana Fadin"Ke ni bama Wannan ba..Wai kiji fa Cemin yayi Sunana irin na Kiristoci ne..? Da gaske ne sunana ba na Musulmai bane.'? Ta fada Tana kallon Zakiya Ido Cikin Ido Wacce ta saka Dariya Tana Fadin"ina zan sani.? Ammh Tunda kikaji ya Fada gaskiya ne..Sai kiyi Hakuri Tunda Babanki ya Riga Da ya saka miiki baki da yarda zakiyi kuma..!
Baki Dina Ta Bude Tana Fadin"Bangane ba.? Zakiya Tace"dama ai bazaki gane ba....Ke wai wata yarinyan ce ta Bangajeni Da zata Shigo Din nan.? Baki Dina Ta Tabe Tana Fadin"Ina zamnsanta..Banga Fuskarta ba Matarsa kadai na iya Ganewa Sai Haddir sai Shi kanshi zain din gabadaya Cikin Dakin Banda su ban son kowa ba..!
Zakiya tace"Soon zaki sansu Kawata...Nadai san na kan gadon nan Kakanininsu ne,Sai kuma Mazan Dake gefe sukuma iyayansu ne,Kin manta an gayamana Ya"yansa Biyar uku Maza Biyu mata,Kana ina kyautata zaton bayan Matan ya"yansa akwai ya"yansa mata Biyu a wajen."Dina tayi Tagumi Tana Fadin"Hmmm..Kina Nufin Harda iyayen Zain awajen..!?
Zakiya tace"eh mana Surukan ki na Wajen..Kilama sune Wadanda da zamu Tafi mukayi musu Sallama sukabi da kallon Wulakanci.."Dina ta waro Ido Tana Fadin"Topha..Kada fa hakan ya bata mana Shiri fa..?
Mikewa Zakiya Tayi Tana Rataya Jakarta Lokaci Daya Tana Fadin"Basu isa ba....Ki kwantar da Hankali Wlh bazan Taba Natsuwa ba sai naga wannan aikin namu ya tafi Sussufull ba wata matsala.."Dina ta sakar mata ido kafin tace"Kin Tabbata..?
Taku Zakiya ta Farayi gabanta Lokaci Daya Tana Dafa Kafadarta Tana Fadin"Kin manta da kudinki kika Biyamin nayi Rigisteration na Shiga Jami"a Lokacin da Babana ya nuna Aurar Dani zai yi..?ni kuma nace karatu zanyi na Tssayu ga Kafafuna..? Ko kin manta Kina London kin Sha Turomin da kudin Abinci Dana Makaranta Har sai da na Shiga Aji Uku na Fara Raba ma maza Jikina Suna Bani kudi..?
Ta fada Tana kallon Dinar wacce tayi Mirmishi Tana Fadin"Ni na manta...Bakuma nasan kina Tuna Baya.."Dariya Zakiya Tayi Tana Fadin"Zaki iya mantawa ammh ni bazan Taba Manta wannan Alherin naki gareni ba Dina..Shiyasa nayi Miki alkawarin bazan Runtsa ba sai naga Kin mallaki Zain kamar yadda kike Buri..! Ke baki Hango Yadda Fuskokin wasu zai sauya Daga Farinciki Zuwa Bakin Ciki ba..? Na Tabbata zasu Girgiza in sukaji labarin Abunda Dansu mafi Soyuwa garesu yake aikatawa Wlh inda ace Nasan inda zan samo Wasu Daga Cikin yanmatan Dayayi Hulda Dasu Har dasu zamu Saka Cikin plan din mu sai dai Kash..Bai yarda yayi Hulda da Ira iranmu bane Shiyasa Daya gane baida wayau..'
Dina ta Saki Numfashi Tana Fadin"Na samu Natsuwa yanzu..Yaushe plan dinmu zai Tabbata kuma Wa zamu Fara.
Tunkara.? Zakiya tace"Karki Damu...Komai na Tsarashi Daki Daki zan zo Gidanki Da Daddare akwai aikin da zan sakaki kiyi mana Shima yana Daga Cikin plan dinmu...Ni na Wuce sai nazo.."Da kai Dina ta amsa Kafin Tace"Shikenan sai mun Hadu.'Juyawa kawai Zakiya tayi ta Fice Daga Office din Tana wani Takun Daya Bayan Daya Dina ta Bita da kallon Tabbatar da mganarta.
Bangaran Su Zain kuwa Duka nan suka wuni Cikin asibitin sai Dare kana suka Watse Hajiya Mama aka bari da Haddir zasu kwana da Alhaji Tsoho,Inna Hamnatu da Inna Rukayyah da su Baban Kaduna da Matansu Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Daman nan suke sauka Iyalan Abba kuma suka Wuce Gida Zaina kuma da Zain suka ce Gidansu sai da safe kana suka Dawo yau ma Zaina ta Dafo Abinci Farar Shinkafa da Miyar Ganye mai Kifi,da aranar Alhaji Tsoho ya matsa zai koma gida Dakyar su Abba suka Lallabashi ya kara kwana Tun Safe kuma yace sai Gida Dole aka bashi Sallama suka Tattara Zuwa Gida Tunda yaji Sauki Muran ma Tayi Sauki Ta Sakeshi.
Washegari Kuma Inna Rukayyah Ta koma ita da Zafeera Inna Hannatu dai sai da ta kara kwana ta Jira Megidanta yazo ya Duba Jikin Alhaji Tsoho suka koma Tare nan dai suka bar Maryama Gidan Abba Tunda Sa"anin suke da Zainab itama sai wannan Shekarar zata Shiga Jami"a suma su Baban kaduna Duk Aranar suka koma Gidajensu su da iyalansu ganin Jikin na Alhaji Tsoho yaji Sauki kuma ga Zain da Haddir suna Kokaron Kula dashi Shi da kanshi ma yace Kowannensu ya Dauki Iyalansa ya koma Bakin aikinsa Shi ya samu Lafiya da wannan suka samu Natsuwan Tafiya su ma Su Nene sai Ranar suka samu Natsuwa agida.
********
*Bayan wata Biyu..*
Bayan Wata Biyu da kwanaki Tuni Zaina sun Dade da Komawa makaranta sun Fara karatu ba kama Hannun yaro Tunda yanzu Suna aji Biyu ne,Zafeera ma Tana kano Tana Cigaba da Karatunta sai dai suna Waya Lokaci bayan Lokaci da Zainar.
Bangaran Dina da Zain kuwa Tana iya bakin Kokarinta Wajen bata ga wani Baraka ya Shiga Tsakaninsu ba,Duk domin don plan dinsu ya Tabbata ammh Har Zuwa wannan Lokacin Shuru ba wani Bayani mai Karfi Zakiya Ta kagara kullum Cikin Zuwa Take ko Kiran Waya Tana Tambayan Dina bataji Wani Chanji Daga jikinta ba Tace Mata ita dai bataji Komai ba Har ta Fara Tunanin ko Zain yana amfani da wani matakin kare kai ne Daga barayinsa Ita Dina Tace bata sani ba ammh kusan kullum Suna Tare da Juna ya cita ya kuma Koma yaci Matarsa kamar wani Bunsuru.
Har zakiya ta Fara sarewa da al"amarin ta Fara Tunanin nemo Wata Hanyar ita Aranta Take Tunanin kila Zain yana amfani da wani Abu agabansa na Tsikan Sparm kafin ya Shiga Mahaifar Dina ya Lalace,Ta riga ta gama Sanyi da Al"amarin ta kuma Fara Nema musu Wata Hanyar ganin wannan Taki Bullewa har yanzu.
Yau din Dina ce takai Ziyara gidan Zakiya suna zaune Suna cin Abinci A Saman Cafet din Dake Falon zakiya Indomie ne da kwai suke ci,ita Zakiya Dafa nata tayi Na Dina kuma Ta Soya mata sanin bata son Cin Dafaffen kwai Ammh Abunda yafi bata mamaki ganin yau Dinar tace bata ma son warin Soyayyah Dafaffen taci Ta barma Zakiya taci Soyayyah,Ita dai Zakiya sai kallon Dina Take Tunda Ga samam kanta Har zuwa kafarta ammh bata ga wani Chanji ba sai ta watsar da Lamarin kawai suka gama cin Abinci suka koma samam kujera suna Cigaba da Hiransu Ranar ma Gidan Zakiya Dina ta kwana sai da Safe ta koma Gidanta.
Sakamakon yadda aiki yayi ma Zakiyar Yawa a office sai Suka kwana Biyu basu Hadu da Dinar ba,Sai da suka kwana Wajen Biyar kana Dina ta Kira zakiya Da