Chapter 19 Reading Zainazain Book 1 Compelet by janafty Arewa Novels

Zainazain Book 1 Compelet by janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 43

54K to 57K   out of 126.5K words

wajen Misalin 3pm na Rana tace Tazo ta sameta agida tun Jiya bataje ko"ina bata jin Dadi Da Zakiya Taji Haka bata kawo komai ba Tana Tashi Daga Wajen aiki Ta wuce gidan Dina,Kwance Ta ganta Cikin Bargo Lokacin da suka Hada ido sai da ta zaro ido ganin yadda Dinan tayi wani Fari kamar mai Hadawa da mai jikinta Duk ya Saki da Sauri zakiya ta yarda Jaka da Takalmi ta Hau kan gadon ta Cicccibo Dina Tana Fadin"Dina lafiyanki kuwa..? Kinga yadda kika Dawo..?.


Take Fada Lokaci Daya Tana yaye mata Bargon Data Rufu dashi Daga ita sai Rigar Barci Haka take kare ma Jikinta kallo kafin ta Fizgi Tafin Hannun Dinar tana kallo Cikin Zaro Ido Zakiya tace"Dina yaushe kika ga period Dinki Last..? Yamutsa Fuska Dina Tayi Tana Fadin"Kinji ki da wata mgana Sau nawa zaki Tambayeni na gayamiki dis Month ne kadai ban yi ba ammh Last 2 month da suka wuce Duk nayi..!

Kura mata ido Zakiya Tayi kamar mai son gano Wani Abu kafin Tace"Meke Damunki..?Dina ta wani Dafe kai kafin tace"Kaina ne ke Ciwo..Tun Jiya da Zazzabi na kwana ga Kasala da Dacin Baki komai naci bayamin Dadi.."Cikin Farinciki Zakiya Tace"Zain yazo Gidanan ne... ?

Dina Tace"Yazo jiya..Wlh wani Abu yabani mamaki sam naji bana Sha"awar Sex Dakyar na bashi Hadin kai Bayan mungama Haka na Shiga bayi ina ta kwarara amai kamar zan amayar da ya"yan Hanji.."Bata bari Dina ta karisa ba Ta Fada Jikinta ta Rumgumeta Tana Fadin"Allah nagode maka our plan Was Sussefully Dina..!

Cikin mamaki Dina Tace"Bangane ba..? Sakinta Zakiya Tayi ta Mike Da sauko Daga kan gadon Tana Fadin"Tashi zakiyi zama bai ganmu ba...Ina zargin Kina da Ciki Dina.."Ido Dina ta Waro Cikin Farinciki Tana Fadin"Da gaske Ina da Ciki Zakiya..?

Tafada Cikin Sigar Tambaya Kai Zakiya ta Gyada mata Tana Fadin"Haka nake Fata kuma nake Zargin ya kasnce.."Aikuwa da Sauri Dina ta Diro Daga kan gado Suka Rumgume juna Suna Murna Kafin su saki Juna Zakiya tace"Tashi ki Rarrafa Ki Shiga wanka sanyi Jiiki ba namu bane..Zamu Shiga plan B din mu.."Dina najin Haka ta Daka Tsalle Tana Fadin"Yanzu kuwa.."

Da gudu Ta Fada tiolet zakiya ta Bita da Dariya Ita ta Fito da kayan da zata saka a gurguje Dina tayi wankan ta Fito Ta Shirya Suka Fita amotar zakiyar basu zarce ko"ina ba sai wani Private Hop,baban Likitan Dake asibitin Saurayin Zakiya ne sunyi Soyayah Holewarsu Daga Baya Ta Rabu Dashi Shi kuma har yau har gobe yana Binta da nacin in ta yarda zai Aureta ya Killaceta ita kuma tace ba yanzu zatyi Aure ba Bata gama Bariki ba Shi kuma har yanzu bai Hakura ba acewarta In Tagama Barikinta Saurayi Uztas zata samu Tayi Wuf Dashi ba irinshi Da Suka Hadu a Bariki ba.

Yana ganinsu ya Fara Rawan Jiki nan da nan Zakiya ta gayamai Abunda ke Tafe Dasu,Shi kuma ya kira wata Nurse Daga Lab tazo Ta Dibi Jinin Dina yace ta kaishi Lap yanzu yake son sakamakon Da Hanzari ta wuce Cikin Sassarfa Ita ko Dina sai Bin Zakiya Take da kallo Domin bata mata wani Bayanin Dalilin Zuwansu wannan asibitin ba Tana chan Suna Hira da Likitan Dagajin yadda suke mgana zaka Fahimci anyi kyakyawan zama tare.

Shudewar Mintina Arba"in kana aka kawo sakamakon Sai da ya Bude ya Duba ya gani kana ya Mikama zakiya yana Fadin"Kawar naki tayi Aure ne..?

Yafada yana Nuna Dina Fuska Zakiya Ta Hade kai Tsaye tace"Ina Ruwanka..? Mallam bamu Sakamako muna kan Hanya ne.."Dariya yayi kafin ya Mika mata yana Fadin"Congarulation Kawarki Tana Dauke da 5weeks and 2dys Pregant...!

Wani Farinciki ya Cika Zukatan Zakiya da Dina wanda sai da suka Rumgume Juna Cikin mamaki yake Binsu da kallo Sai yayi Tunanin kila tayi Aure ne ba kamar yadda yake Zargi Da Farko ba,Sai da suka gama Murnan kana Dina ta Juya Tana kallonsa Tace"Dacta Last Month fa nayi Mesis wannan Watan ne kadai ban yi ba Hakan ba matsala bane.?

Yana yar Dariya yace"Likita Tana Tambayan Likita game da Abunda ta sani ko Duk Murnan ne..?karki damu Normal ne Mata Wasu Daga Ciki kuna Haka kila ki Dakata daga haka kila kuma Bayan kowani Wata Daya ki Rika ganinsa yadai Danganta Daga yanayinki ne.."Zakiya ta ja Jakarta Lokaci Daya da Hannun Dina Tana Fadin"Docta sai munyi mgana.."

Daga Haka suka Fice Daga Office din Zakiya Dauke da Resuilt Din Cikin na Dina,Basu samu mgana ba sai da suka Shiga Mota Zakiya ta Ja suka Fice Daga asibitin Sai da suka Daidaita Tukin Bisa kwalta kana Dina ta waigo Tana kallon Zakiya Tana Fadin"Yanzu ina muka Nufa..?

Hankalin Zakiya na wajen Tuki Tace"Saulawa Specialist Hop..."Ido Dina ta waro Tana Fadin"Bangane ba..? Wajen Zain zamu je..?

Kai ta Girgiza mata kafin Tace"Ba yanzu ba...Wajen Saurayin naki zamu wama yake da Suna..? Wannan Bunsurun matan nake Nufi..? Cikin mamaki Dina tace"Wai Dr Imran kike Nufi..?

Da Sauri Zakiya tace"Yauwa Shi nake Nufi.."Dina tace"Bangane ba..Miye Aikin Dr Imran awannan Plan din namu kuma.."?

Zakiya tace"Bashi da wani amfani sai waje  Daya....Zamu je ne kan Baki da lafiya zaki ce ya Dauki Jininki a gwada ki kina Tunanin Maleria na Damunki....
Kinga In Sakamako ya Fito Irin na Dr.Yusuf ne,munhada Sakamako Biyu kenan Daga Mabambamta Asibitoci Ciki Harda Asibitin Dayake mallakinsu Koda zasu karyata Dr Imran zai iya zama Shadarmu.."Kai kawai Dina take gyadawa kafin tace"Daganan kuma sai yaya..,?
Zakiya ta Bushe da Dariya ta saki Sitiyarin Motarta Tana Fadin"Daganan sai Ki kira Zain ki Gayamai kina Dauke da Cikinsa..!

Dina tace"Sai kuma..!Zakiya tace"Daganan sai na Daukeki na kai ki Kano Sabuwar kofa.."

Gaban Dina ya Fadi ta kwalalo Ido Tana Fadin"Gidanmu kuma... ? Tafada Da Sigar Tambaya Zakiya ta gyda kai Tana Fadin"Eh insha Allahu..!

Dina Ta Dafe kai Tana Fadin"Miye manufar hakan..? Zakiya tana Zuba Hon abakin get din Asibitin Saulawa Ta Dago Tana kallon Dina lokaci Daya Tana Fadin"Manufa Shine Zan kai ki nace baki da lafiya..In Hajiya Batula ta Kirashi Ta gayamai Abunda ke Faru nasan zai ce akira Family Doctor dinku ya Dubaki..."

Dina Tace"Kin kasheni Zakiya zai Fada musu ina da ciki fa..?

Zakiya tace"Plan C din mu zai Fara Daga Lokacin.."

Dina tace"Wani irin plan c kuma..ya zanyi in Daddy yaji Labarin ina da Ciki Zakiya..?

Zakiya na Faka Motarta a parking space Tace"Zai ji ba Dadi mana Dina ai Duk Uba na kwarai ba zai so Gurbacewar Yarsa ba balle keda yake matukar so..Matakin da kowani Uba zai Dauka Shi zai Dauka Dina karki Damu..!

Dina na Sakin Numfashi Sama sama Tace"Nidai Don Allah ki Fitar dani Duhu Zakiya Wani irin mataki zai Dauka..? Hakan yana da alaqa da Cikar Burina ne..?

Zakiya tayi wani Mirmishin Kin Cika matsala afili sai ta Furta"Naso ki bari mu bi komai Daki Daki ne ammh Tunda kin matsa Shikenan..Matakin da zai Dauka Shine Zai Fara Tambayanki wayayi miki ciki..? Ke kuma sai ki Bashi amsa da ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA,Ki kara da cemai ya Ribace ya yaudareki da kalmar zai Aureki ya Lalatamiki Rayuwa Tun kuna London Yanzu kuma Daga karshe ya Nuna bazai Taba Auranki ba.."

Dina ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Naji sai kuma yaya..? Ta ina zamu Fara tunkarar Ahalin Zain..?

Zakiya tace"Daddy da kansa zai Dauko ki ya kawoki har garin Bauchi A gaban Iyayen Zain zai Zayyane musu Dan"su yayi ma yarsa Ciki kuma bazai yarda ba yana Neman Hakkin Yarsa.."

Dina ta Saki baki kafin tace"Kai...!

Zakiya ta Bude Murfin Mota Tana Fadin"Naki wasa ne..Komai na Shiryamai..Kinga Haka na Faruwa plan D zai Fara aiki..Yayinda Duka Zuru"arsu zasu Tattaru waje Daya Domin Yima Abun Tufkan Hanci.."ta fada Tana Dariya Jinjina kai kawai Dina keyi itama ta Bude Murfin Mota Ta Fito Tana Fadin"Burina fa Yaushe zai cika..?

Zakiya tace"Acikin plan D zai cika..Domim Daddy zai ce bai yarda ba..Zai kai kara Kotu Su kuma iyayensa zasu nemi Sulhu..Daganan kuma Za"a ce Dole zain sai ya Aureki Saboda Rufuwar Abun kar ya Hadu a Duniya..Ammh Shi kanshi Daddy Barazana zai yi musu Domin Shima ba zai so Wannan labarin ya Fita ba ko Domin Siyasarsa...!
Hannu kaawai Dina ta bama Zakiya suka Tafa Lokaci Daya Tana Fadin"Aikin ki na kyau Tawan..!

Jinjina Zakiya tayi ma Dina kawai kafin su Fara Takawa atare zuwa Cikin asibitin Zakiya na kara Gayamata Yadda Tsarin Plan dinsu zai Tafi har zuwa matakin Nasara.



*Ina Godiya da Sharhin ku kan wannan Labarin Keep it up...*





*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️

*BOOK 1*


             1️⃣4️⃣

"Shigarsu asibitin basu Hadu da kowa ba sai Dr.Aisha da Dr.Peter suma din sama sama suka gaisa Dr.Aisha ce ma ke Tambayarta Lafiya Jiya bata Shigo Asibiti ba yau ma Haka Fuska a Tamke tace mata bata Jin Dadi ne sannu kawai Tayi mata sukayi sallama su suka Wuce Office din Dr Imran ita kuma ta Wuce Femele Word Kila zata yi Dubawar yammah ne.

Dr.Imran na Tsaye acikin Office Dinsa ya gama Abubuwan Dayake Shirin Tashi ma yake,sai ga Dina da Zakiya sun Shigo mamaki ya Kamashi Da ganinsu ,Ya Riga yasan Wacece Zakiya awajen Dina Tunda kamar yadda Kowa ya san Dina a Ma"aikatan Da Zakiya take aiki Haka zalika kowa yasan Zakiya kawar Dina ce Acikin Asibitin.

Bai iya cewa komai ba har suka samu Waje suka zauna Zakiya ce Ta kalli Dina itama ta kalleta sai ta kada mata kai,Ganin haka yasa Ta Juya Ta kalli Dr.Imran wanda ya sakar mata Bunsuran Idanuwansa Cikin Wani kallon Bariki da kwarewa Cikin Basarwa tace"ah..Zauna mana..?Ko baka Maraba da zuwan namu ne..?

Cikin yake ya zauna yana Fadin"Haba..? Wane Imran yace Baya Maraba da zuwan Baki kamar Dina da kawarta...U are Higly Wlcm..."Ya karishe Fada yana wani Shafa gemunsa na yan Duniya wani kayattacen Mirmishi Dina tayi kafin Tace"Zuwa nayi yau ka dubani Dr Imran..!
Tafada Cikin Son Tabbatar da Abunda Ta Fada kura mata ido yayi yana Fadin"Topha..Meke damunki kuma.? Don naga alaman Idanuwanki sun Fada Sosai..!

Yafada yana Jifanta da wani kallo kafin Dina ta samu Zarafin Mgana Zakiya ta Rigata da Cewa"Zazzabi take Fama dashi da Ciwon kai ga kasala da Mutuwar Jiki Amai da Rashin Dadin Baki,mutuwar Jiki da tsinkewar yawun Baki.."Ta karishe Fada tana kallonsa kafin ta maida kallonta kan Dina Wacce ta zaro ido Tana kallonta kai ta gyada mata alamun karta Damu.

Maida Hankalinta Tayi kan Dr.Imran wanda ya zura ma Dina Ido kawai yana karantar wani Abu Daga bayanan Zakiya kawarta Kafin ya samu Bakin Mgana Zakiya tace"Wani gwaji kake ganin ya kamata kayi mata Dr Imran..?

Sai da ya wani Gyara zama kafin yace"Pregancy Test ya Dace da ita..Domin ina da Tabbacin Dina ciki gareki.."Yafada yana so yaga wani Reaction zata nuna sai yaga bata damu ba illah Zakiya Data kura ma ido Ita kuma kawai sai ta kada kai Tana Fadin"Zamu jira ka yanzu ka bamu Tabbaci..!

Tafada tana wani Laso Harshenta Waje,Mirmishi Dr.Imran yayi kafin ya Jawo Wata Takarda yayi Rubutu asamanta Lokaci Daya ya Mike yana Fadin"Ku jira bari naje na kira Wata Nurse ta Debi Jininta..!

Da Hannu Zakiya ta Dakatar Dashi Tana Fadin"A"a bama bukatar wani cikin wannan aikin.Kai zaka Dibi Jininta kuma Muna bukatar a Sirrinta Sirrinmu Saboda gudun ajikama aikinmu.."Tafada tana kada mai Hannunta wanda yaji jan Lalle.

Kai Tsaye yake kallonta kafin yace'"Na yarda zan Sirrinta Abun.Ammh ni miye Tukwaicina akan Hakan..? Kai Tsaye Zakiya tamike Tsaye ta Fara Taku zuwa gaban Dr.Imran batare da Tunanin komai ba ta Saka Hannu ta Shafa gemunsa zuwa Fuskarsa Tana Fadin'"In komai ya Tafi Daidai..Nice Tukwaicinka Tun Daga Farkon Dare Har karshensa naka ne.."Tafada tana wani kashe mai ido Wata Dariyan yan Bariki ya saki kafin ya kada kai yana Fadin"An gama."

Daga Haka ya fice Daga Office Din Jikinsa na Rawa da Sauri Dina Ta Mike tana Fadin"What me kikayi haka Zakiya..?.

Hannu Zakiya ta Daga mata Kafin Tace"Shiii..Ba yanzu zaki Tambayeni ba..Ki bari sai mun Fita..'Dole Dina ta koma ta zauna tana maida Numfashi Itama zakiyan zaman tayi,Cikin Lokaci sai ga Dr.Imran ya Dawo Da Sirinji da Allura a Hannunsa nan Take ya Dauki jinin Dina ya sake Fita Shudewar Mintina Hamsin Biyar suna zaman jiransa sai gashi ya Dawo Da Farar Takarda ya mikama Zakiya yana Fadin"Ga Tabbaci nan Saura nawa Tukwaicin yaushe zan karba...?

Karba zakiya tayi ta Bude Ta karanta ta gani Mirmishi ta saki ganin Sunan Dina maimakon Dina Gaddafi Sheerif sai aka Saka Dina G Sheerif kuma Sakamakon Iri Daya ne Dana Dr Yusuf Cikin Sati5 da kwana Biyu,Dagowa tayi Tana kallon Dr.Imran kafin ta mikama Dina Takardan Tana Fadin"Sai nan da kwana Biyar ko Shida zan nemeka da kaina..!

Zai yi mgana ta Dakatar Dashi Lokaci Daya da mikamai wayarta Tana Fadin"Sakamin Lambarka In baka sabamana alkawari ba nima bazan saba maka ba.."Karba yayi ya saka mata lambarsa ya mikamata yana Kallon Dina a karkace bata Bashi Fuska ba ta Mike kawai Tayi gaba Zakiya tabi bayanta tana kada ma Dr.Imran Yatsunta Har suka Fice yana Binsu da Kallo,komawa yayi ya zauna yana wani Tunanin ya sani ba Tun yau ba Dina na Harka da maza ammh bai zata Haka ta zama wawiya da wayanta da Iliminta Itafa Likita ce Taya zata zauna ta bari Har tayi Ciki..? Ya fara Tunanin anya ba wata aksa ganin Daga ita har kawar tata basu nuna wani Damuwa ba kamar ma sun san da Ciki ya Dade yana Saka Abubuwa ganin bai gano komai ba yasa ya watsar da komai Murnansa Daya zai More da zakiya Gefe Daya na zuciyarsa na kara kwaidaita masa Dina Domin Har ga Allah yana Sha"awarta kuma yana da Burun ya kauda wannan Sha"awar koda na Dare Daya ne.


Zakiya bata ma Dina mgana ba sai da Takaita Kofar gidanta kana ta Dauki Result din Da Dr.Yusuf ya basu ta mikama Dina Tana Fadin"Wannan zaki nuna ma Zain bayan kin kirashi yazo kin gayamai kina Dauke da Cikinsa..!

Dina Ta kalleta Tana Fadin"Miye Manufar hakan.? Zakiya tace"Manufofi da yawa ne Dina..Yanzu ki Sauka kije gida kiyi wanka ki Sauya kaya Sai Ki kira Zain kice yazo Kina son mgana Dashi Da Daddare in ya nuna Bazai zo ba ki Turamai Sakon ko yazo ko kuma ke ki biyoshi Gidansa na Tabbata Dayaji Haka zai zo,Sai ki nuna mai wannan sakamakon Zai Firgita kuma zai yi Challaging dinki kan kin Shirya wani Abu ke kuma sai ki nuna mai baki Shirya komai ba in ya gama Rudewansa zai nemi ki yarda azubar da Cikin,karki gaddama Ki yarda da cewa zaki Zubar da Cikin.!

Dina Tace"Na yarda fa kika ce..? Kai ta kada mata Tana Fadin"Eh ki yarda mana..Ammh na iya baki bai kai Zucci ba.Nasan zai ce ki bari da safe zai koma gida yana Tunanin mafita kuma Tabbas da Safe zai dawo yace ku Tafi wani asibiti azubar da Cikin.."Ta Dakata Tana kallon Dina kafin Ta Cigaba"Kafin yazo mu kuma mun Tsufa a kano zaki kashe Duka wayoyinki yadda bazai Taba samumki ba..Ke kuma Yau Da kinga Zain ya Shigo Gidanki ki Kirani awaya ni kuma zanyi Sauri na Daga Wayar na sakata cikin Recording Zan ji Abunda yake Fada Gefe Daya kuma ina Nadanshi a matsayin Hujja kin gane..?

Kai Dina Ta Jinjina Tana Fadin"nagane ammh baki Tunani  yaji wayata akashe bazai yi wani Tunani ba..? Zakiya tace"Zai yi mana Lokacin yana Rudene..zai yi Tunanin wani Abu ammh kafin Tunaninsa yaje mai kan plan dinmu komai ya kamallah Sai dai kawai Bom din ya Fashe Bumm...! Tafada tana Dariya Dinar na Tayata sun Dade Tana kara Fada mata mganganun da sata gayama Zain indan yazo kafin su Rabu Ta sauka ta Bude Gidanta ta Shige ita kuma ta Sakar ma Motanta Wuta ta Fice Daga Wajen da Gudu.

******

Zaune yake akan kujera mai zaman Mutum Biyu,Zaina kwance Gefensa Tayi Matashi da Cinyarsa Tana sanye Cikin Wasu Riga da wando na Barci Masu Taushi Sun lafe ajikinta,shi kuma Dagashi Sai Boxers wasa yake da gashin kanta Suna Hira Cikin so da kauna.

Lokacin Dare ne Domin Wajen 9 pm na Dare ne har ma ta wuce,Bai Dade Da dawowa Daga asibiti ba yayi wanka sukaci Abinci kana suka yada Zango a Falo suna Hiran Ma"aurata mai Dadi.

Juyo da kanta yayi Yana kallonta Ido Cikin ido yace"Firstlove kin kara Haske fa..? Mirmishi Tayi Tana Fadin"Haka kowa ke Fadi...Umma Dazu haka tacemin Dana Biya bayan na Dawo makaranta.."Kumatunta Yaja yana Fadin"Har da kiba ma kin kara kalli kumatunki kin zama Zaina bombom yanzu fa..'.

Yafada yana Dariya Itama Dariyan Take Tana Fadin"Haka Ukti tace Jiya da mukayi VD call da ita.."Kiss ya sakarmata agoshi yana Fadin"Naji Dadi..Abba Da su Umma zasu gane yanzu nafisu iya kiwo Tunda Gashi kinyi kiba.."Yar Dariya Tayi Tana Damke Hannunshi Cikin Kura mai Ido Tace"Firstlove..!

Asama yaji Sunan ya kalleta yana Fadin"Umh menene Zainazain.."Ajiyar rai ta Sauke kafin tace"Kwanakin nan ina yawan Fama da Faduwan gaba..Sai ina ji ajikina kamar zan Rasa wani Abu Daya zama mai matukar amfani agareni.!

Ido kawai ya sakarmata yana kallonta har tagama mgana kafin ya Saka Hannu ya Tadata ita Kan Cinyarsa ya Sauketa Lokaci Daya ya saka Hannuwansa ya Zagaye Kugunta Dashi yana Fadin"wa zaki Rasa Firstlove..?Nine nafi komai Muhimmanci gareki kuma Bazan Taba barinki ba Har Abada..".

Tana kallon kwanyan Idanuwansa Tace"Mutuwa fa..In mutuwa ce fa ya zakayi..? Fadin Haka yasa sai Jikinsa ya mutu,Kawai sai ya lafe Ajikinta yana Fadin"Ki daina wannan mganar Firstlove ko mutuwa ce Insha Allahu Tare zataDaukemu Wani baazai mutu ya bar wani Cikin Tashin Hankali ba Kinji ko..? In kin kara Jin Faduwar ba kiyi ta Maimaita Hasbunallahu Wani'imal wakil.."Tana Daga Jikinsa ta gyada mai kai Tana Fadin"To Firstlove na Daina kuma zan Dinga yi insha Allahu..!

Matseta yayi yana Fadin"Nagode My Wife...Allah ya barni Dake har Mudin Rai ta amsa da Ameen,Sun Dade ahaka kafin Ringing din wayarsa ta katsesu,Saussauta Rumgumar da yayi mata yayi Lokaci Daya yana jawo wayarsa Dake gefensa Sunan Dina Daya gani Tana Kira sai da gabansa ya Fadi Sororo yayi kawai ya kasa Daga Kiran ganin haka yasa Zaina ta waigo Tana Fadin"Ba kiranka ake ba..?

Yake yayi yana Fadin"Sharesu Daga asibiti ne..' Da Sauri tace"A"a bazai ayi haka ba in wani Abun gaggawa ne fa..?ka Daga ni bari naje Kitchen nayi kaye kaye na Dawo.." Tana gama Fadar haka tatashi Daga kan Jikinsa ta wuce Kitchen sai da yaga ta Shige kana ya Tashi da Sauri Dauke da wayarsa ya Shige Bedroom dinsu ya Turo Kofa yana Kokarin Kiran Dinar sai gata ta sake Kira da Hanzari

19 / 43