Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ammh ina kyautata Zaton Tana chan.."Kada kai kawai Haddir yayi Daidai Lokacin da Wayarsa ta Dauki Tsuwa yana Fito Da ita Daga Aljihu ya waro ido yana Fadin"Kai...Abokiya Zareena Ta zo Nageria..!
Da sauri Zain ya kallesa yana Fadin"In jiwa..? Wayarsa ya nuna mai yana Fadin"Gashi ta Kirani da Lambarta na Gida ba na chan U.s ba.."Dakyar zain ya iya Hadiye wani Miyau mai Daci Shi kuma Haddir ya Daga Kiran yana Fadin"Abokiya me zan gani haka..?badai kin Diro Ba Labari ba..?
Dagachan Bangaran Zafeera Dake Falon Gidansu Su Saudat sun Zagayeta,Umma na Zaune kusa da ita rike da Takwaranta Jalal kuma na Kan Cinyar Nene Bakinta Har kunne tace"Eh mana So nake na baku mamaki..Gani afalon su Umma gasu ma kusa dani Dana Sauka nayi ta Kiran Lambar Aboki Zain Tana Ringing bai Daga ba Kawai sai na Kira Abba ya Turo Direba ya Daukeni Daga Katsina nake Tun Shekaranjiya muka sauka Nida Abba Jalal yana chan sai an kwana Biyu zai Bullo..'
Haddir yace"Masha Allah..Sannu dazuwa..Zain kuma Muna tare dashi Wayarsa ya barta amota gamu nan zuwa muyi Sannu da zuwa dakyau asha Hirar yaushe gamo.."Tana Dariya tace"Yauwa Abokaina na Hakika ina Jiranku.."Daga haka suka katse Kiran Zain yana kallon Haddir bai samu Zarafin mgana ba yace mai"Zuwan mu kano yau baazai yuyu ba sai dai Mu Jira gobe..?
Cike da Tashin Hankali Zain yace"Saboda..?ammh kasa."Bai ida mgana ba wayar Haddir ta Kara Daukan Tsuwa Cikin Dafe kai yace"Innalillahi ai na Sha"afa.."Zain yace"Mun Shiga uku menene kuma..?Haddir yace"Wlh Inna Hannatu ta Kirani Tun safe tace min gata zata Hawo Jirgi nan da 12:30pm nazo Filin Jirgi in dauketa..'
Ido Zain ya kwalalo waje yana Fadin"kuma..? Me hakan ke Nufi Zafeena tazo ga Inna Hannatu ma zata zo Haddir..?Haddir na Shafa kansa yana Fadin"Bama ita kadai ba..Kowa dakowa zai zo Zain..Akwai Gagaruman mtasala kuwa indai Hasheshena ya zama gaskiya.."
Cikin Fitan Hayyaci Zain yace"Bangane kowa da kowa zai zo ba..?kai tsaye Haddir yace"Ina Tunanin gobe Asabar din Karshen wata..In lissafina yayi daidai wannan watan Shine Watan Taronmu na Family kuma kasan wanchan watan ya Kamata ayi ba"a samu yi ba ina Kyautata zaton Gobe ne za"ayi Zaman.."Dafe kai kawai Zain yayi yana Fadin"Qalu inna Lillahi..Haddir na Mutu Shikenan Asirina zai Tonu Wlh.."
Shima Haddir Yana Cikin Tashin Hankali ya kalli Zain yana Fadin "Bari muje mu Dauko Inna Hannatu Daga Filin Jirgi Allah zai kawo mana mafita.."Daga haka Haddir yaja Mota Suka Nufi Mallam Aminu International Airport.
Suna Zuwa suka iske Har Inna Hannatun tasauka sai Fada take tana Fadin Tana Kiran wayar Haddir bai Daga ba Haka ma Zain,Saboda Tana Fadan ne yasa Bata Fahimci basa cikin Natsuwarsu ba har gwara ma Haddir ya Tattaro Natsuwar Zain kuwa Zaro ido kawai yake yana kifta idanuwa Jira kawai yake ace kyf ya zura da Gudu.
Gidan Alhaji Tsoho suka kaita Suna Shirin kara Zillewa tace sai sun Shigar mata da kaya Domin kaf a Ya"yan Alhaji Tsoho da ita da Baban kaduna ne mafadata,Suna Shiga Zain yaci karo da Zainarsa Cike da mamaki take kallonsa tana Tambayansa bai Tafi Gomben bane..?
Ganin Baya Cikin Natsuwarsa ne yasa Haddir ya Bata amsa da bai samu Tafiyar ba Abun ya bata mamaki ganin Firstlove baya ma iya Hada ido Da ita kamar Alhaji Tsoho ya sann Suna Cikin Uzurin son Tafiya ya Hanasu ya Zaunar dasu yana gaya musu Gobe akwai Taron Family Duka iyayan nasu suna Tafe Inna Rukayyah ma Tana Tafe Daga kano Haka ma Baban kaduna da Mom Iklima Da Daddyn Abuja da Mama Safiya Da Hamdiya zasu zauna kan mganar Auran Hamdiyan daya Taso watan Gobe ne,Zain bai kara Jin Sagewar Gwiwa ba sai da yaga Sadiq babba ya shigo nan yake gaishesu tare da Shaida musu Dazu shima ya Shigo garin yazo gida yayi Hutun Sati Biyu ya koma Alhaji Tsoho nata Murna ganin Jikansa Haddir da zain sai dai suka kalli Juna kawai Kowa da Abunda yake sakawa Sai da Alhaji Tsoho ya gama Jawabinsa kana ya barsu suka Fita suna Fita basu koma ko"ina ba sai Cikin asibitin Office din Haddir din suka sake komawa Suna Kulla yadda zasu Bulloma wannan al"amarin Dake Tunkaransu Dirshan zain ya zauna yana kukan Haddir ya Taimakamai kada Asirinsa ya Tuni Ya bashi Tsausayi matuka kuma Har ga Allah baya Fatan wannan mganar ta fasu a kunnuwan iyayensu ko bakomai ya zama Silan Rufama Dan"uwansa asiri.
****
Dina kuwa Da Fara Nadaman Biye ma Shawaran Zakiya Domin Lokacin da Kwamishina ya Dawo Gida yaci karo da wannan Labarin sai da ya Kusa Fadi haka ya Zube gaban gadon Dina yana Jijjigata yana Fadin"Dina..?me kika nema kika Raasa..? Wani irin gata ne ban baki ba..? Wata irin Soyayya Uba ce ban baki ba..? Harda ta uwa na Baki Dina na Hana Dangin mahaifiyarki Daukanki Saboda ina sonki Ina son na baki Dukkan gatan Duniya..? Yanzu da Kanwar mahaifiyarki Maimunatu zata Zo sati mai zuwa Da wani baki zan mata wannan bayanin..? Na baki ilimi Na ingantan Rayuwarki saboda kada kice na zama mai Takura gareki ashe wannan sakewar har yakai ki kwasomin wannan Abun kunyar dina.? Nifa Dan Siyasa ne da wani ido kuke so na kalli mutane in wannan mganar ta Fita waje..?
Ya karishe Fada Cikin zubar Hawaye Ita kanta Dinar kukan take Hajiya Batula ma sai da ta Share kwallah Zakiya ce kadai batayi kuka ba Cikin kuka Take Fadin"Kayi Hakuri Daddy..Plz Forgive me.Ba laifina bane Wlh Yaudarata yayi da Kalmar zai Aure ni ya lalatamin Rayuwa Shine kuma Daga baya yace sai dai azubar da Cikin bazai Aureni ba Shine na Gudo Gida.."
Ta fada Cikin gunjin kuka Gefe Daya na Zuciyarta Tayi Rauni ganin Daddynta nakuka Hajiya Batula tace"Dama wani Namijin arziki ne zai yi Lalata da mace kuma ya aureta..? Ai Shima macen kwarai yake nema kinyi Kuskure Dina.."Kwamishina ya mike Tsaye yana Share Hawayensa ya kalli Zakiya yana Fadin"Wani asibiti kika kaita Kafin kuzo nan..?
Cikin Ladabi Ta saka Hannu Cikin Jakarta Ta Dauko Farar Takarda Ta mikamai Tana Fadin"Asibitin Da take aiki ne Daddy....Gama sakamakon awajena.."Karba yayi ya Duba na wani Lokaci kafin ya Hada da wanda Dr.Bala ya Bada ya Tusa Cikin aljihunsa yana Fadin"Taga yamiki wanda yayi mata wannan Zaluncin..?
Cikin Makirci Zakiya tace"Nayi nayi da ita Taki gayamin Daddy.."Tafada kanta na kasa Cikin Tsawa Kwamishina ya Kalli Dina ya Daka mata tsawa yana Fadin"Kimin Shuru anan wajen ki Fadamin wanda yayi miki wannan Abun kunyar..?
Tsorata Tayi Tafara ja da baya zuwa Wajen zakiya Ita kuma Zakiya Fadi Take"Dina ki Fadama Daddy ko waye..Na Tabbata zai kwato miki yancinki na Zalunci da yaudaranki da yayi da kalmar zai Aureki yayi Miki Ciki kuma yake neman ya sake Jefaki ga Halaka.."Tafada Har tana matso kwallah Jin Haka yasa ta Fara Shesshekan kuka Tana Fadin"Likitan ne asibitin Dana ke aiki..!
Kwamishina yace"Waye sunansa..? Waye kuma Ubansa a kasar nan..? Kan Dina na kasa tace"Sunansa DR ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA...! Tafada tana Rufe bakinta Waro Ido Zakiya tayi Tana Fadin"La Dr.Zain kike nufi..?Kai Dina ta Daga mata sai ta Fara Tafa Hannu Hajiya Batula tace"Kinsan shi ne..? Kodai wannan Saurayin da Dina take matukar so ne..?
Da sauri Zakiya tace"Shine Wlh Anty...Tun suna London suke Soyayyah Tunda makaranta Daya Sukayi nasha cema Dina Ta Rabu Dashi ba Auranta zai yi ba sai tace Yace zai Aureta asibitin ma Datake aiki shi ya bata aikin fa asibitin mallakin Kakansa ne Dr Saulawa dake Garin Bauchi..'
Hajiya Batula tace"Nifa banga laifinsa ba laifinta ne..Don Namiji yayi ma mace alkawarin Aure sai akace ta bashi Jikinta yayi yarda yaga Dama..?kwamishina ya Dago yana kallon Hajiya Batula kafin yace"Batula koma Miye Bai isa yaci Bulus ba...Na yarda Dina nada laifi Shima yana Dashi Saboda Haka Tunda ya Riga ya bari Haka Ta Faru..Wlh Tallahi ko Zan rasa Mikamina sai na kwatan mata yanci..Ke Zakiya kunsan gidan yaron..?
Da Sauri Zakiya tace"Eh Daddy ai gidansu ba Boyayyen Gida bane agarin Bauchi kakansa Dr.Abubakar Saulawa yayi suna sosai.."Kai tsaye ya kada kai yana Fadin"Ku Shirya gobe daSafe zamu tafi Chan Bauchi zan je na gaya musu Abunda D'ansu yayi ma yata in ma basu sani ba gobe zasu sani..Batula kema ki Shirya dake zamu tafi sai Excort dina guda Biyu saboda Sirri yau ma Domin Anjima ina da ganawa da gwamma ne da a Daran nan zamu Tafi garin Bauchin..'
Yana gama Fadar haka ya Fice Daga Dakin Kamar zai Tashi sama Hajiya Batula ta mara mai baya Suna Fita zakiya tatashi ta Rufe Kofar tazo ta Rumgume Dina Tana Fadin"Ina Tayaki Murna kin kusa samun Cikar Burunki..!.
Wata Dariyan Farinciki Da Nishadi Dina tayi kafin tace"Da farko na Karaya..Ammh yanzu naji Kamshin na zami matar Zain..ammh kuma wani Fargaban Zakiya Shegiyar Firstlove din nan nashi zata yardada mganganunmu kuwa balle har ta Rabu Dashi..?
Ta fada Tana kallon zakiya wacce ta Mike tana gyara zaman mayafin Kanta Lokaci Daya Tana Fadin"Karki damu da ita Tuni nagama da ita..Zatazama Comfuse mana Na wanda ka yarda dashi Fiye da kowa aduniya yaci Amanarka..Ammh Zan aika mata da Abunda Dole zata nemi karin bayani ni kuma zan gayyato inda zata ji gaskiyan komai kinga Daga Lokacin Zata ji Zain din yagama Fita Daga kanta Indai ita macece wacce ta amsa Sunanta..."
Dina tace"Bangane Nufinki ba..? Zakiya ta Dauki Jakarta Tana Fadin"Ai Ba zasu zo Taji wannan mganar ba..Zasu yi Kokarin Rufa mganar kada Taji..Ammh ni zan gayyatota har zuwa Gidan kakan nasu da suke ji Dashi nayi Miki alkawarin aagaban Idonta zamu Fallasa Komai...Kin manta kin samo min Lambarta Awayar zain..?Hade kuma da aikin da na sakaki..?
Kai Dina ta Daga mata Cike da mamaki Dariyan Mugunta Zakiya ta saki Tana Fadin"Ai Duka Shirin nata ne..Domin Ba lalle bane in wanchan Bomb din ya Fashe ba"a gabanta ba Mganar Daga bakin wasu Tayi mata Tasiri..Zata yi Tasiri ne Daga bakinki Da kuma Shaidunmu.."hannu kawai Dina ta Bata suka Tafa Tana Fadin"Aikin SS ya dace Dake Zakiya ba aikim kamfanin Sardawa ta Layi ba..".
Dariya kawai Zakiya tayi mata kafin tace"Zan tafi Gida na kwana Dina..Saboda kinsan komai lalacewar gida gidanku ne kuma Tunda Tsoho nada Rai Bari na Leka Duk da wanchan Watan na Lekosu.."Dina ta kada kai Tana Fadin"Da safe kenan zaki Dawo..?
Zakiya tace"Da yardan Allah.."Sallama sukayi Kana Zakiya ta Fice Koda ta sauka Kasa bata ga kowa kawai sai ta Fice Daga Gidan Security suna ganinta suka Bude mata get ta Fice Da Motarta Motar Dina kuma Tana kano Gidan Wata kawarta Teema suka kai Motar Dina Ajiya Tun Jiya Saboda kada Barinta ya bata musu plan dinsu.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
1️⃣6️⃣
"Zakiya iyayenta suna zaune a anguwar gadon kaya ne,Mahaifinta Mallam Nuhu Talaka ne mai Rufin asiri Tunda Sana"ar Dinkin Surfani na Hannu yake Da Saida Zaren Dinkin kala kala Tun yana da Samartkansa.
Shago garesa a kofar gidansa Inda yake gudanar da Sana"arsa,Bayan Rasuwar Mahaifiyar Zakiya Adama Ya kara Auran Wata Samira yar garin Danbatta ne,Bayan ita ma ya kara Auran wata Lubabatu suna Kiranta Luba ita yar nan garin Kano ne, a kofar wambai.
Mahaifiyar Zakiya yar asalin Kauyen Minjibir Dake kano ne,iyayenta ma ba masu Hali bane Kuma Dukkansu yan kauye ne Shiyasa bayan Rasuwarta da Mallam Nuhu ya hanasu Su Dauki Zakiya su maidata chan Minjibir din sai sukayi Fushi suka Fita Batun Zakiyar basu kara waiwayarta ba itama bata Damu ba Tunda ba wani Abun hannu garesu ba Uwa uba kuma Tana ganin ci baya ne ta koma Kauye da Zama.
Sai ta tashi Hannun Kishiyar Uwa Samira irin mugayen Matanan nan ne da basu Dauki Ya"yan Kishiya ya"ya ba Dalilin ta shi yasa Zakiya ta Fara kangarewa,Da kuma Shigarta prine Collage da Haduwarta Da Dina lokacin Mallam Nuhu na Zamaninsa da Dinkin Surfani Shiyasa Zakiya tafi Sauran ya"yansa samun Ingancin Rayuwa mai kyau.
Mtslanta Da Mahaifinta ya samo asali ne da Samarin da Zakiya ta Fara mu"amala dasu na Banza,Wannan Motan tazo ta Dauketa wannan ta Sauke sai manganganu suka Fara yawo kan Yana ganin Zakiya zata lalace bazai Dau mataki ba Da Zugan Samira yayi amfani yace In Zakiya ta gama Babban Sakandiri zai mata Aure ita kuma tace Bata so karatu zatayi,Rigima tayi Tsanani Har ya sako Dangin Mahaifiyarta Adama aciki Har zuwa sukayi suka samu Zakiyan suka mata Fada ammh Tace ita karatu zatayi ba Aure ba Ran Mallam Nuhu ya baci yace Taje duk inda zata ammh bada gwabonsa ba da wannan Dalilin Taje ta samu Dinar da kukanta itakuma ta Share mata Hawayenta ita ta Taimakamata ta Biya Jamb ta zana kuma taci Dayake duk Iskancinsu basu wasa da karatu Barin ma Zakiya Da take ganin Bayan karatu bata da komai Bariki bai sa ta sakar ma karatu ba Taana da Burin ta tsaya ga kafafunta wata Rana
ABU zaria Tana daga Cikin Inda Ta nema kuma ssi gashi ta samu Bata Nemo kowa ba sai Dina Ita Tayi mata komai sai dai ita ta Rigata Tafiya Lagos inda ta Fara karatu kafin ta Wuce lagos,Ita kuma Zakiya sai Daga baya ta wuce Zaria Bayan ta gama Hada Abubuwan da zata Bukata wajen abokan Shashancinta Domin Zakiya Tun tana SS2 ta san Tabama Namiji Jikinta ya Biyata kaso mai Tsoka Gidan ma Datake Zaune azaria Cikin Samarinta wani ya kamata Zuwanta Zaria da Shigarta Jami"a Shiya Kara Sauya Zakiya Idanuwanta suka Bude tayi kawaye na Banza Dana arziki anan ne Takara sanin Rayuwa sanari kuwa ba adadi Tayi na Arxikin kuma Tayi na Banzan Kawayenta na nan Zaria suka Fara koya mata Harka da malamai kuma Tunda ta Fara take jin Dadin Haka zakiya ta kama kudi Sosai Wajen Abokan Shashancinta Shiyasa Har ta gama karatunta Sisin Mallam Nuhu bata Taba nema ba Shi kuma ya kawo ido ya saka mata.
Zakiya Tana da kanne mata Sunfi Shida,kuma dukkansu sun yi Aure Tunda ba karatun suke ba,Bayan Tagama karatu ta Samu aiki a Bauchi Shima da Taimakon Mahaifin Dina kwamishina Gaddafi Sheerif,Ta tattara ta koma chan da zama bayan ta mallaki gidan zama da Motar Hawa In taje gidansu sai dai Tayi awa Daya zuwa Biyu,ta koma Bayan ta kawo musu kayan Abinci da kudi Mallam Nuhu baya karba sai ya kalleta yace"Zakiya ina Fatan wannan kudin bana Shanshancin kibane kika kawomin ba ko..?
Yau ma Data iso Gidan Hakan ce ta Faru Tsskaninsu Bayan Ta Shiga Dakinsa sun gaisa Da zata Tashi Ta ijiye mai kudi a gabansa Tana fadin"Gashi Baba ku kara acefene..!
Sai Tayi Dariya Tana Fadin"Ko Daya Baba..Daga cikin Albashina ne..."Sai kawai ya kada kai yana kallonta yana Fadin"Zakiya yanzu ina amfani ga wannan Rayuwar da kika Daukan ma kanki..? Kinga ma karatunki kin samu aiki me zai Hana ki nemi ko Cikin Abokan Shashancin naki ne kuyi Aure .?
Mirmishi Tayi ta sadda kai Yana Fadin"Haba Baba meyasa kake Damuwa ne..?Aure fa wani Lokacin in baka yi sa"a ba Duk Wahala ce baga su Sahura ba Sunyi Auran ammh Suna Cikin Wahalan Rayuwa ba, yanzu da karatunsu sukayi irin nawa da Suna Tsaye ga kafafunsu Baba...!
Carbinsa kadai ya Cigaba da ja yana Fadin"Ban taba la"antanki ba Zakiya kuma bazan Taba ba..Akullum Tsakanina Dake addu"an Shiriya ne Allah ya Shiryeki Zakiya.."Cikin Mirmishi Tace"Shiyasa nake sonka Babana..Ameen ya Allah..Bari na Koma ciki.."Dakai kawai ya yi mata mgana Har tatashi ta Fice ya bita da kallo yana mata Fatan Shiriya Tun zakiya na zuwa ana Gulmar ta zama karuwa Taje chan wani gari da Sunan aiki Tana iskanci tayi kudi ta sai Mota Har akazo aka Daina Domin Mallam Nuhu ya Toshe kunnansa ne Fatansa Allah ya Shiryeta yasa Ta gane Rayuwar da Takeyi ba Rayuwa bace.
Tana komawa Cikin Gida Dakin Luba ta sauka Daman nan take Sauka Tunda ita take Rawan Jiki da ita Saboda Kwadayi ita kuma Samira Daman basa Shiri da Zakiya Tun baya ballatana yanzu da Girma ya kamata,Samiran ma ya"yanta Biyu an sakosu suna gabanta Zakiya bata Damu ba,Haka ta saki kudi Luba tayi lafiyayen Girki sukaci Ita dai Zakiya bata ci ba, tea ta Hada tasha ta kwanta kan Katifar da Luba ta mata Shinfida.
*******
Haddir da Zain sun gama Tsaida mgana kan sai gobe da Safe zasu Tafi kano,Gidan Abba Suka koma Tunda Zafeera nata Kiran waya tana Korafin Bata gansu ba Duk wanda yaga Zain sai yasan wani Abu na Damunshi baya Cikin Natsuwarsa chan suka kara ganin Zaina dama Ta gayama Zain Zata wuce gidan Umma,Yace mata Toh.
Ita kanta Zareena Ta Fahimci Wani Abu Haddir ta kalla Tana Fadin"Aboki Haddir meya ke Fauwa da Aboki Zain ne..? Naga ya Zama wani Shuru Shuru ne wani Abu ya Faru ne...?Haddir ya Juya yana kallon Zain wanda ya kura ma waje Daya ido kawai Daga ganinsa Baya Cikin Natsuwarsa.
Yake yayi mata Lokaci Daya yana Dafa Zain din yana Fadin"Bakomai...Strees ne na asibiti.."Jin haka yaasa Zain ya Fahinci Abunda ke Faruwa Shima yake yayi wanda bai kai Zucci ba,Zareena dai bawai don ta yarda ba sai don Taga Basu san gayamata,Zain kuwa duk iya Kokarinsa na Kada agane yana Cikin Wani hali sai da aka gane Haka Nene ta Tusashi Cikin Daki Tana Tambayanshi meke Damunsa..! Ammh ya kasa Furta komai ba amsa Dayan ce Bakomai nan suka kai Dare Har Abba ya Dawo Daga Gidan Alhaji Tsoho Shida Baban kaduna Suka Shigo da Mom iklima Da Mama Safiya da suka Biyoshi zasu kwana gidan su Umma.
Nan fa su Umma suka Fara maraba Da baki,Zain fa Hankalinsa ya Tashi Komai ma ya Riga ya kwacemai Haddir ne ke Zugurinsa in gaya yayi Tagumi ya Shiga Dogon Tunani,Sai wajen 10pm na Dare suka Rabu da Haddir Shi kuma Ya Dauki Zaina zuwa Gida,bayan sun yi Dinner agidan Umma wanda Zaina tana Lura da zain abinci ma Tsakura kawai yake yi batare ma Dayaci ba.
Suna Cikin Tafiya Zaina sai kallonsa Take ganin sai Sakin Numfashi yake sama sama Tunda Suka Shiga Mota bai iya cemata komai ba Driving kadai Yake ammh Rabin Hankalinsa Baya Jikinsa Gefe Daya kuma yana ta gwada Kiran Layin Dina da Koda yaushe ake cewa akashe,Mamaki ya Cikata ganin kamar Baya cikin Natsuwarsa ne yasa a sanyaye tace"Firstlove..!
Waigowa yayi yana kallonta Batare da yayi mgana ba gyara zama Tayi Tana Fadin"Firstlove meke faruwa ne... ? U Look so silent.."Maida kansa yayi Ga Tukin Dayake yi kafin ya Sauke Numfashi kawai batare da