Chapter 1 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 27

1 to 3K   out of 80K words

ÿþ*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025



              ©þ *Nana Haleema.*



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11





_Da sunan Allah mai rahama mai jin ™ai, godiya ta tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bamu aron rai da lafiya har muka kawo wannan lokaci. Ina yiwa kowa barka da shiga sabuwar shekara, ina ro™on Allah ya sada mu da alkhairin da yake cikin ta, ya kiyaye mu daga sharrin da yake cikin ta. Ya zaunar mana da ™asar mu lafiya, ya kare mu daga duk wata fitina Amin. Ina ro™on Allah ya bani lafiya da numfashin ganin ™arshen labarin nan kamar yadda na fara lafiya cikin aminci amin._



_Labarin BAYA DA ˜URA ™ir™irarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba, in yayi kama da labarin wani ko wata ayi ha™uri rashin sani ne._



_Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba!._



https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp





*BOOK 1*

*Page 001.*





Madaidaicin gida ne mai kyau a unguwar tudun maliki dake cikin ™wayar birnin Kano, kai tsaye kana kallon sa baza kace wanda suke ciki takalawa bane irin sosai Win nan, haka baza kace musu suna da kuWi ba sosai. Zasu shiga cikin masu rufin asiri wanda suka fi ™arfin abubuwan yau da kullum. Yana da babban tsakar gida mai tsaho mai Wauke da bishiyar mangwaro wacce ta mamaye ko ina baka ganin hudowar rana ko kaWan sai iska da take kaWawa busassun ganyaye suna faWowa kan tiles Win da yake ™asa. A share gidan yake tasss sai ganye da yake faWowa bayan wannan babu ko tsinke a tsakar gidan komai yana mahallin sa.



Mata ne guda biyu masu matu™ar kama da juna sosai, kana kallon su zaka fahimci uwa da ´a ne duba da yanayin shekarun su. Yarinyar wacce baza ta wuce shekara ashirin da huWu zuwa da biyar fara ce tass irin farin nan mai kamar madara, tana da haske sosai wanda a kallo Waya kawai zai Wauki hankalin mutum. Tana da idanu masu kyau da gashin gira yalwatacce, ga bakin ™arami mai Waukar hankali. Kallon farko zaka fassara ta a kyakkyawa don ta cancanci ta amsa wannan sunan musamman hasken ta da yake da Waukar hankali, suna zaune a kan tabarma ciki inuwar bishiyar suna cin kwaWon zogale a cikin kwano Waya, yadda suke ci suna hira sai ka Wauka yaya da ™anwa ne saboda yadda suka sha™u da junan su.



"Mama!." Yarinyar ta faWa tana kallon ta. Wacce aka kira da Mama ta haWWiye ganyen da yake bakin ta tace, "Na'am." Tace, "Maganin ki ya ™are, ya kamata mu koma asibiti muga likita kar a samu matsala."Mama ta sauke numfashi tace, "Manal nawa ya ™are saboda takura min da kike yi da shan sa amma ke bakya shan naki. Ko yaushe tunanin ki akan nawa yake bakya tunanin kanki, ciwon nan kina dashi ina dashi, amma bakya maganar kan ki sai ni."



Manal tayi shiru ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mama tace, "Manal koda bana gani da idanuna zuciyata tana nuna min duk abinda yake faruwa, nasan bakya shan magani a ko yaushe ni kike siyawa ke kuma ki zauna da ciwo bayan kina kallon illlar da ciwon yayi min, bakya tsoron yayi miki ke?."



Manal tace, "Allah Mama ina mantawa ina da wani ciwon sugar indai ba maganar kika yi ba, in kika samu lafiya kamar na samu ne. Wallahi koda na sha maganin indai baki samu lafiya ba bazan samu tawa lafiyar ba Mama." Mama ta janye hannun ta daga cikin kwanon zogalen ace, "Meyasa haka? Lafiya fa lafiya ce Manal, babu abinda ya kaita mahimmaci a duniya. Ni na girma har na haife ku keda ´ar uwar ki ke kuwa fa? Kwata-kwata shekarun ki nawa a duniyar? Ko aure baki yi ba balle a kai ga batun haihuwa, rayuwar ki tafi tawa mahimmaci Manal."



Manal tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Mama taki rayuwar tafi tawa wallahi, da na samu lafiya gwara ace kece kika samu. Shiyasa bana tambayar Baba kuWin magani na, indai ba shine ya siyo ba bana faWa masa." Mama ta girgiza kai tana murmushi tace, "Manal Win Mama kenan, to ban amince da abinda kika ce ba, da kaina zan sanar da Baban naku bakya shan magani." Manal bata amsa ba Mama ta kuma cewa, "Wannan karon ki tambayi Baban kuWin naki maganim, bana so wani abu ya same ki Manal. Kin san waccan Yayar ta ki ba hankali ne da ita ba, ta Wauki rayuwar da tafi ™arfin ta Wora a zuciyarta, ta raina ni bata jin maganata saboda tana da kyau, ke kaWai ce dani Manal, shiyasa bana so wani abu ya same ki."



Manal zata yi magana kenan suka jiyo muryar Mubeena tana faWin, "Wallahi bazan ci ganye ba, na gaji ai ni ba akuya bace da za'a dinga yanka tsinannen salad Win na naira hamsin ana cewa shi zamu ci safe da rana a gidan nan wallahi bazai yu ba. In ku kuna da ciwo ni ai lafiya nake. Haka kawai a dinga tauye ni? Ina! bazata saSu ba." Mama ta girgiza kai Manal tace, "Kar kici mana, Yay Mubeena cikin ki ai."

"Daman bance zanci ba ai, zan fita na nemo abinda zanci ne yanzu" ta ™arewa gidan kallo tayi tsaki tace, "Wallahi ni ba kalar gidan nan bace gabaWaya, ban cancanci zama a gidan nan ba. Tsausayi ne kawai ya saka aka haifo ni a gidan nan, amma ni kalar babban gida ce wallahi."



Manal ta kalli Mubeena sannan ta kalli Mama taga tana girgiza kanta kawai sai ta mi™e ta ™arasa kusa da Mubeena tace, "Baki da hankali ne wai ke? Yaushe zaki nutsu ki fuskanci rayuwa don Allah?. Ke a ganin ki wannan banzar rayuwar itace wayewa?." Hararar ta tayi tace, "ni kike cewa bani da hankali dan ma kin raina ni?" Ta kalli Mama tace, "Mama yarinyar nan bata san ni Yayar tace ba ko me?" Ta sake kallon Manal tace, "bazan zauna a gidan nan ba, ban cancanci zama a cikin sa ba domin kuwa ni ba kalar wacce za'a ce a nan na rayu bace." Manal tace, "bazan girmama ki ba domin baki cancanci hakan ba, a gaban Mama kike cewa baki cancani zama a gidan na ba?, wallahi baki da kunya."





"ki ™yale ni wallahi bazan zauna a nan ba talauci ya kashe ni, common abinci irin wanda nake so naci ace ya gagare ni wallahi bazai yu ba. Ke da kika ga zaki iya sai ki zauna ni kam bazan iya zama a gidan nan ba, kinga tafiya ta" kafin Manal tace wani abun Mubeena ta fita da sauri kawai ta bita da kallo zuciyar ta babu daWi ko kaWan. Allah ya sani bata son wannan Wabi'ar da Yayar ta take yi, bata son wannan rawar kan da take ji dashi kamar itace tafi kowa kyau a faWin duniya.



"˜yale ta Manal, zo ki cigaba da cin abincin ki, Mubeena Itace ajalina ita zata ga bayana" ta faWa murya na rawa alamun kuka zata yi. Da sauri Manal ta koma kusa da ita ta zauna ta ri™e ta tace, "Don Allah Mama ki daina faWar haka addu'a zaki mata."

"Manal na rasa wacce irin yarinya ce, gabaWaya bata jin magana abinda taga dama shi take yi. Ita a ganin ta raina ni da tayi shine daidai?, a ko yaushe bata ganin ™ima ta saboda na kasance ni ba irin uwar da take so ace itace mahaifiyar ta ba. Hmmm! Taje tayi ai duniya ce ga ishe ta duk abinda take so tayi. Wanda suka fita ma ya duniya ta bi dasu balle ita ™aramar alhaki."



Manal tace, "Ki yi ha™uri Mama, ki mata addu'a zata daina in sha Allah." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Manal tace, "Mama Ina zuwa." Mama tace, "Karfa ki bi bayan ta."

"Šaki zan shiga Mama" ta faWa tana shiga Wakin da sauri.



Babu komai a falon sai carpet amma a share yake tass sai fridge ™arami a gefe a ajjiye, ta shiga wata ™ofar da take falon ta ™arasa wajan akwatin kayan ta tana bincika inda ta ajjiye kuWin taji babu su alamun Mubeena ta kwashe. Zama tayi a wajan dan daman ta san za'a yi haka a bayyane tace, "Innalillahi, na shiga uku Yaya Mubeena ta kashe ni" ta faWa tana dafe kanta tana shirin yin hawaye saboda halin da ta jefa ta. Wayar ta Wauka tecno andriod wacce bata da girma sosai dan ko a hannu ba babba bace, hannun ta har rawa yake ta kira lambar Muneeba tana Wauka tace, "Yaya kin san da yadda Baba ya samu kuWin nan ya bani kuwa?, Mama zan kai asibiti dasu fa, meyasa zaki kwashe?."



Daga can Sangare tace, "Shi Baban zaki komawa ya sake baki, ai kowa ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, tunda har zai iya ri™e mu matsayin ´a´an sa dan yayi asarar wannan kuWin ba komai bane. Kar ki manta kuma ™anin Wan uwan baban mu ne, ko babu aure tsakanin sa da Mama zai sake biya. kije ki tambaye shi in ba haka ba ki nemo kawai ni na kashe su ma" tana faWa ta yanke wayar. Manal ta dafe kanta zuciyar ta na harbawa cike da Sacin rai, dan da ace Mubeena Win tana kusa da ita a wannan lokacin wallahi zasu iya yin dambe dan kowa yasan halin Wan uwan sa. Da ya aka samu kuWin ma bata sani ba kawai burin ta taje tayi ™arya ita a lallai ga mai kuWi.



Numfashi ta sauke ta kalli agogom wayar taga huWu na yamma tayi ta share idon ta ta fito ta tarar har Mama ta tayar da sallar la'asar itama tayi alwala tazo kusa da ita tayi sallar, bayan ta idar ta kalli Mama tace, "Mama zanje wajan Surayya yanzu zan dawo, babu abinda kike so?."

Mama tace, "kin daina zuwa islamiyya dai Manal."

"Ba daina zuwa nayi ba Mama, bana so na tafi na barki ke kaWai ne shiyass kawai. Kuma mun sauke har sau biyu na samu abinda na samu ai."



Mama tace, "to haka zaki zauna kina tauye kan ki saboda ni Manal?, kin ™i cigaba da karatun boko tunda idanuna suka rufe, islamiyyar ma gashi kin ajjiye. Ita waccan da bata da amfani a gidan sai ita take zuwa kuma ta raina mai biya mata ™udin makarantar, ko yaushe a banza take kallon sa saboda bashi da kuWi kuma ba shine ya haife ta ba."

Manal tace, "Wallahi Mama babu inda zan iya zuwa na barki, ko naje bazan yi karatun ba tunanin ki zan dinga yi. Kuma ni culinary school nake so, na zama fitacciya a fannin girki." Mama tace, "to ai ko ita Win kin ™i Manal."



Tayi murmushi tace, "Zan yi Mama amma ba yanzu ba, zan tafi Mama akwai sabon girkin da na gano mana nake so naje mu gwada da Surayya."

Mama tayi dariya tace, "shiyasa kika iya saboda in dai kin gani zaki ce zaki gwada. Jeki babu abinda nake so Manal sai kin dawo, Allah yayi miki albarka ya baki abokin zama na gari, ya haWa ki da masu taimaka miki kamar yadda kike taimakona."

Murmushi tayi tace, "Amin Mamana, sai na dawo" ta faWa tana tashi ta fita zuciyar ta gabaWaya babu daWi akan lamarin Yaya Mubeena.



Da sallama Mubeena ta shiga falon gidan babba mai kyau kai da kaga falon kasan mazaunan falon ma ™ananun masu kuWi bane ba saboda yadda ta tsaru sosai, babar macen da take zaune sanye da glasses a idanun ta tana duba waya ta Wago ta kalle ta tayi murmushi tace, "Mubeena kece." Murmushi tayi ta ™arasa ta zauna kusa da ita tana murmushi tace, "Mummy ina wuni?."



Wacce ta kira da Mummy tace, "how was your day?, Ya Maman ki?."

"She's fine Mummy. Tace tana gaishe ki."

"Ina amsawa" ta faWa tana kallon mai aikin ta tace, "ina so ki dafa min couscous amma baki iya ba." Tayi shiru bata amsa ba Mubeena tace, "mummy ki kawo na dafa miki." Mummy tayi murmushi tace, "noo! Bilkisu tana ciki jeki" da sauri Mubeena ta tashi ta shiga cikin Wakin ta samu Bily a zaune tana waya ta bita da kallo kafin ta tsaya jikin mudubi tana kallon kanta cikin burgewa. Ita kanta tasan tana da kyau ko ba'a faWa ba, tana da kyaun da lokaci Waya zai Wauki hankalin ka in ka kalle ta sai ka sake.



Sake kallon kanta take yi kafin tace, "Allah bai yi za'a haife ni a irin wannan gidan ba, da a wannan gidan nake ai sai nafi haka kyaun gani, da wannan gidan na dace ba waccan ba."



Bily ta katse kiran tace, "ke kullum kika zo gidan nan sai kin maimaita maganar nan, dallah ki shiga kiyi wanka mu wuce bana son Sata lokaci." Bata ce komai ba ta shiga banWakim tayi wanka ta fito ta zauna tana shafa mai Bily ta kalle ta tace, "Gaskiya Mubeena dole ki dinga ba™in cikin haihuwar ki da aka yi a gidan ku, ke kin ganki kuwa?, kina da kyau sosai, kawai farin Manal da yake mai haske ne yafi burge ni, dan kin ga ita babu masu wannan hasken da yawa a cikin nigeria. Ke kuwa haske dai wanda kowa ya sani ki ke dashi, amma kina da kyau."



Mubeena tace, "bari kawai, bayan talauci ma ga uwa makauniya, ga mai ri™on namu ma talaka, ga ™anwa soloSiyo babu abinda ta iya kullum cikin kiyi ha™uri da duniya take faWa min. Shiyasa ko a school ban taSa bari na nuna ta matsayin ™anwa balle kuma na nuna babar ta mu balle kuma gidan namu gabWaya." Dariya Bily tayi tace, "Shege talauci. Amma bai kamata ki cewa Mama haka ba, kuma a ko ina zaki iya nuna Mama saboda ta fi ki kyau. Kawai dai da ace ke ´ar Alhaji ce da an gama magana." Itama dariyar tayi tace, "Ina jin daWin haWuwar mu dake, ke kan ki farkon haWuwar mu kin Wauka irin wata shegiyar nan ce ni baki san ganye na baro su suna ci ba."



A tare suka sake yin dariya Bily tace, "Wallahi baki da kirki, ke baki bar kowa ba har Mama." Mubeena ta tashi ta buWe kayan Bily ta Wauki kayan da take so ta saka ta tsaya tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba kaWan ba. Bily ta bita da kallo tace, "Gab nake da daina baki kayana domin in kika saka sai naga sun fi miki kyau a kaina."

Dariya Mubeena tayi ta shirya tsaf tayi kyau sosai suka dau™i jaka suka fita ko mummy basu yiwa sallama ba dan su ´an boko ne babu ruwan su basa tauyewa Bily ha™™in ta, Bily taja mota suka fita daga gidan.





***** A yadda ya shigo falon zai tabbatar maka da ransa a Sace yake, cikin fuskar sa da bata da alamun walwala a ko yaushe dan kana kallon sa  zaka fassara shi a mutum mara fara'a, kuma baza'a rasa faWa a wajan sa ba.



Kyakykyawa ne mai duhun fata da madaidaicin jikin, yana da ido da dogon hanci siriri, fuskar sa Wauke da zagayayyen gashin da ya kewaya ko ina. Cikin glasess Win da yake idanun sa ya kalle ta tana zaune kafin yayi magana cikin fusata tace, "wai kai waye gaba tsakani na dakai ne? Yayar ka ma Farida gaba nake da ita balle kai da zaka dinga min shishshigi a cikin lamarin rayuwata, ina ruwan ka da abinda na zaSarwa kaina?, har nawa aka ke da zaka dinga nuna min daidai da ba daidai ba?."



Wanda take yiwa maganar yana tsaye yana jin ta ya kalle ta yace, "ba yaya ta ba, ko kece kika haife ni baki isa kina yi abu ba daidai ba na zuba miki idanu ina kallon ki. Yasan yana son ki meyasa ya rabu da ke? Ya san zai dinga bibiyar ki har ki dinga shiga motar sa meyasa ya miki sakin da bazai iya mayar dake na?."

"Ina ruwan ka dani?, haka na zaSa baka isa ka hana ni ba wallahi."

"Ai kuwa zaki ja masa, na rantse da Allah na sake ganin sa ™ofar gidan nan sai na saka n kulle shi ya kwana biyu a cell, in kina musu ki sake gayyato shi kiga nida ke waye zaiyi nasara."



Anty Maryam ta harzu™a matu™a kamar zata kifa masa mari tace, "baka isa ba walalhi, ™arya ka ke Bebi baka isa ka hana ni abinda nayi niya a cikin gidan nan ba. gidan ubana ne kamar yadda yake gida uban ka, ina da iko kana da iko, baka iya ka hana ni abinda nake so ba. In kana hana ™anen ka ni Yayar kace." Ganin Mamy tazo wajan sai baice komai ba ya juya ya fita ransa a Sace sosai.



Yana fita ta kalli Mamy tace, "yaron nan yana neman raina min hankali, Mamy kiyi mana tsakani dashi, ni yayar sace babu ruwan sa da abinda zanyi."



Mamy ta kalle ta tace, "Gaskiya yake faWa miki ai, kishin ki yake matsayin ki na yayar sa shiyasa yake tsaye akan lamarin ki. Ke kuma banza shashasha mara kamun kai miji ya sake ki amma ya dinga bibiyar ki kina masa dariya saboda baki san abinda yake miki ciwo ba. Ya san yana son ki ya miki saki har uku?."

"Mamy su Nabila da Nabil na duba fa."

"Zaki min shiru ko sai na tsinke ki da mari?, babu mota a gidan nan da baza ki hau kije wajan yaran naki ba? Ki aika a Wauko miki su ko lallai sai kinje inda suke?."



Anty maryam ta sauke numfashi tace, "kenan yanzu Mamy shine mai gaskiya ni mara gaskiya?." Mamy ta Harare ta tace, "ki cigaba da abinda kike yi nan gaba zaki dana sani, sai a lokacin zaki fahimci Bebi gaskiya yake faWa miki. Bebi gata yake miki wanda uban ki bai miki shi ba." Tana gama faWa mata haka ta shige ta barta a wajan.





1 / 27