Chapter 21 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 27

60K to 63K   out of 80K words

so ya raba shi dashi. Murmushi yayi daga bayan su yace, "Ina da Shawara...." Duk a tare suka juya suna kallon sa cike da mamaki.









Nana Haleema>ΨBέ>Ψφή<Ψϋί



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



                ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



*BOOK 1*

*Page 023*







HaWa idanu suka yi da Mujahid yana tsaye yana aiko musu murmushin da ya saba na yaudara yace, "Ya naga dukkan ku kuna kallona?, Kun manta Mujahid abokin ku ne?." Hamza  ya kalle shi yace, "Yaushe ka shigo nan?."

"Ban wani jima ba, daman wajan Bebi nazo."



Ya tako ya ™araso zuwa inda suke ya kalli Bebi da shima shi yake kallo tace, "Yayan mu barka da dare, nasan da cewa Yayan mu bai san da cewa soyayya ta da Lubna tayi nisa ba ko?." Sai yayi dariya yace, "kai a ganin ka wai zaka iya raba mu da Lubna ne? Ai na riga na shiga zuciyar Lubna mai raba mu a wannan lokacin babu shi, in kaga Lubna ta bar ni tabbas lokacin hakan ne ya yi a wajena."



Huzaifa yace, "Mujahid ka faWi abinda ya kawo ka bama son maganar banza da wofi." Yayi ΄ar dariya yana kallon hotunan Adnan da suke manne a bangon office Win wanda ya samu awards a ™asar india da saudia da sauran wurare, ya kalli hoton su su huWu ranar da aka buWe asibitin yayi murmushi yace, "cardiologist Adnan, ya kamata ka duba zuciyar ™anwar ka tunda aikin ka ne zaka cire mata Mujahid in ka isa. Kana ganin kamar kwana biyu bama haWuwa saboda baka ganina ko?" Ya faWa yana Wauko wayar sa ya nuna masa yace, "to kalli wannan Kaga Yaya."



Kallon fuskar wayar Adnan yayi yaga hoton su ne da kayan da ya ganta ta ta shigo gidan ya kalle shi yayi dariya yace, "Lubna na sona, ko yanzu nace Lubna tazo g1dana ta same ni zata zo zan kuma zan iya yin duk abinda nake so da ita baka isa ka hanani ba, sai naga bayan license Wina me zaka sake a karSa. But I found something important better than this, so maybe I'll get it twice, nayi al™awarin sai na saka ka rasa farin cikin ka kamar yadda ka saka na rasa nawa."



Bebi ya kalle shi yace, "Baka isa kayi nasara a kaina ba Mujahid, na fika ™arfin ikon samun nasara a ko yaushe saboda zuciyata a tsarkake take, baka isa ka yiwa Lubna komai ba in kuma ka iya kayi Win." Ya ™yal™yale da dariya yana kallon su yace, "kun ji abinda yace ko?" Ya kalli Bebi yace, "Wallahil azim sai nayi nasara a kan ka Bebi, ko yanzu ko nan gaba sai na saka maka ™una a zuciyar ka kamar yadda ka saka min."



Bebi ya gyara tsayawa yace, "go ahead." Huzaifa ya kalle shi yace, "babu nasarar da zaka iya yi Mujahid, domin kuwa komai ya faru kaine ka jawowa kanka ba wani ba, kuma ko yaushe gaskiya ce take nasara ba ™arya ba."



Mujahid ya girgiza kai yace, "mu zuba dai mu gani" yana faWa ya juya ya fice suka bishi da kallo har ya Sace. Bebi ya kalle su yace, "Kun gani ko? Yarinyar nan Lubna daman nasan baza ta rabu da Mujahid ba, sun yi min shiru suna ganin kamar bana kula da komai amma nasan suna haWuwa har ita Maryam suna haWuwa da Kamal, so suke su kashe ni su huta kawai."



Hamza ya sauke ajiyar zuciya yace, "Kayi ha™uri Bebi, babu abinda zai faru in sha Allah. Amma laifi na Maryam ne wallahi, ita Lubna ka ture maganar ta yarinya ce dole zai yi galaba akan zuciyar ta, ka sani na sani ko da muna karatu Mujahid ya iya tsara ΄an mata, lokaci Waya yake yake galaba a kansu, amma Maryam fa?. Miji ya sake ki kuna da yara biyu shi bai mayar dake ba kuma ya dinga bibiyar ki kina biye masa?. Ko me ya faru ita ta jawo."



Ya sauke ajiyar zuciya yace, "haka wasu matan suke yanzu ai, miji zai sake ki amma rashin hankali da sanin ciwon kai sai ya saka ya dinga bibiyar ki kuma kina sauraren sa, nida Kamal a office Win hisba yace ko da akwai ragowar igiya bazai mayar da ita ba, amma da yake bata san abinda take yi take zuwa inda yake wai da sunan tattaunawa akan batun yara."



Huzaifa yace, "Abba ne zai maganin lamarin Maryam fa, kai tana ganin ™anin tane baka isa ka hana ta ta hanu ba." Ya kalle shi cikin ™unar rai yace, "Abba! Hmm." Abinda yace kawai kenan.



Knocking ™ofar aka yi aka shigo wata nurse tace, "Dr akwai wanda aka kawo yanzu ™arfe ya soke shi a zuciyar sa, "it's emergency."

"Bebi yace, "They come with police?."

"Yes sir."

"Okay I'm coming" ya faWa ya kalle su yace, "Zamu ™arasa maganar, ina zuwa." Dukkan su fita suka yi ya ™arasa wajan mara lafiyaa, a nan yaga ™arfe ne dogo aka soka masa dan a sume ma yake,  ya kalle shi yana karanta yanayin shigar ™arfen sukayi handling case Win da police ya kalli wanda ya kawo shi yace, "garin ya hakan ta kasance?" ya faWa a lokacin ana Waukar sa aka shiga dashi theatre room.



"Matar sace ta soke shi." Bebi da mamaki yace, "matar shi?."

"Eh wallahi likita." Ya girgiza kai kawai ya wuce zuwa Wakin, nan da nan aka shiga aikin cire masa ™arfin Allah ya taimaka ma a gefen zuciyar ne da a tsakiya ne da yanzu ba labarin ake ba.



Kusan mintina arba'in aka kwashe a ciki kafin ya fito zuwa lokacin ΄an uwan sa sun ™aru a wajan ya kalle su yace, "kar ku damu zai samu Lafiya." Suka amsa a tare ya wuce su ya zauna akan kujera yayi shiru.



Raba dare yayi ranar a babban asibiti yana aiki yaso tafiya g1da ma sai ya fasa kawai ya kwana a ciki, da asuba  ya koma gida a nan ya samu yayi bacci sosai sai azahar ya farka. Da ya shiga wajan Mama bata nan ya fita suka gaisa da Mamy ya koma ya zauna.



Wayar sa ya Wauka yana kallon lambar Manal da ta bashi jiya yana tunanin ya kira ko kuma kar ya kira, "in na kira nace mata meye?." Ya kifa wayar bai san ya kira Win ba yana can yana kallon wani wajan yaji ance, "Hello." Da sauri ya kalli wayar yaga seconds suna tafiya alamun ya kira har an Wauka yace, "Hello."



Manal daga can Sangaren ta gane maganar sa amma sai taso raina masa hankali sai tace, "ina ji, da wa nake magana?." Shiru yayi bai bata amsa ba jin wai da take magana ta raina masa hankali Manal tace, "na kashe kenan?."

"Kina so kice baki gane mai magana ba?."

"Inda na gane bazan tambaya ba." Yayi murmushi domin haka nan yaji a jikin sa ™arya take yi yace, "okay, basai kin san waye ba zaki iya cewa Mama ina gaishe ta."



"Sai nace Mama wani ya kira ban san shi ba yace yana gaishe ki?."

"Yeah you can." Murmushi yaji tayi yasan daman ta gane shi rainin hankali ne kawai sai yace, "Adnan ke magana, duk da na san kin sani." Yayi murmushi tace, "ina yini."

"Lafiya lau, ya jikin?."

"Alhadulillah, na samu lafiya."



Bebi yace, "Allah ya ™ara lafiya." Ta amsa da amin yace, "kina cin cucumber Win?." Manal tace, "eh." "Ki daure zai daidai miki blood sugar Win." Bata amsa ba yace, "meye real name Win ki?."

"Fatima."

"A ina kika tsaya a karatu?."

"Secondary school."

"Baki da burin cigaba da karatun?."

"Ina so, amma nafi son culinary school."



Shiru ya biyo baya daman ya jima da fahimtar tana da magana sosai sai yace, "You're so good in kitchen?." Yaji tayi murmushi tace, "i think so." DaWin waya da ita yake ji sosai komai tana bashi amsa in ya tambaya kamar kar su daina sai yaji waya na zuwa ya kalla ganin daga asibiti ne sai yace mata, "Kashe kiran it's emergency." Datse kiran tayi ya Wauki waccan yayi shiru ana faWa masa kafin ya tashi ya fita.



Cikin kwanaki biyu Manal da Adnan sun saba sosai duk da babu wani kalaman soyayya da yake yi mata in ya kira ta, hira ce akan abinda ya shafe ta sai yanayin jikin ta dana Mama bayan wannan babu wani abun da yake ce mata. Shi a wajan sa kalaman soyayya kamar sai yara, shi kawai sai ya tsaya yana wani tsara kalamai, ai tunda yaje gidan su da niyar aure zancen soyayya ya ™are. Tunda yaje zuwan farko bai sake zuwa ba sai dai suna waya sun saba har tana mamakin dama yana magana kuma yana da kirki haka.



       A ranar litinin yayi nufin zuwa gidan nasu bayan sallar i'sha kamar wancan lokacin yaje ya haWu da Haroun a waje  suka gaisa ya raka shi har inda suka zauna a wancan lokacin.



Bai jima sosai da zama ba ta shigo Wakin da haske wutar solar amma ba sosai ba kasancewar babu wuta ta zauna bayan tayi sallama tace, "ina yini." Khamshin turaren ta yayi masa yawa sosai hakan ya saka shi kulle ido ya buWe, ya dafe kansa da lokaci Waya ya harbawa. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "Manal i forgot to tell you that bana son khamshin turare da yawa, wannan turaren na ki yayi min yawa sosai, yana bani ciwon kai sometimes it cause dizziness."



Manal tace, "Ayya nan sani ba, kuma ni ban saka ma turare ba Wauko hijjabin nayi kawai."

"So please duk lokacin kika san zamu haWu dake ki daina amfani da irin wannan, zaki iya amfani dashi a cikin gida amma in zaki fita ma ki daina please."



Tayi murmushi tace, "in sha Allah." Ya Wan dafe kansa kafin yace, "I don't like it!" Ya faWa a ™asan murya kansa har ya fara ciwo.



Ganin da gaske fa baya son Win sai tace, "I'm sorry, let me change it."

"No, is okay." Ya Wago ya kalle ta suka haWa ido ya sauke ajiyar zuciya, "Manal I'm here to ask you what's on your mind about me. Kina ganin zaki iya aurena?."



Manal tayi ajiyar zuciya ta sauke kai ™asa bata ce komai ba yace, "please kar ki min ™arya, na faWa miki bana son ™arya. Duk son da nake miki ™arya zata iya rage kaso mai yawa a ciki." Ta kalle sho ya Waga kai yace, "eh ina sonki, sonki shine ya kawo ni gidan ku. Bana son Sata lokaci da jan lokaci a soyayar baki, ki sanar dani gaskiya bana son auren wacce bata sona."



Tayi ajiyar zuciya tace, "ina da ciwon sugar, ina da fushi, ina da yawan magana in ji Mama. Ina son Mamana, ina da ΄ar uwa guda Waya."

"I know all this, ina magana a kaina ne Manal."



Ta sauke ajiyar zuciya tace, "zan faWa maka."

"Why now?."

"No, not now, zanyi shawara da Mama."

"Baki da bu™atar shawara, abinda yake ranki shi zaki faWa." Tayi murmushi tace, "akan abinda yake ran nawa ai zamu yi shawara da ita, I'm sorry komai sai Mama ta sani sai kuma tace nayi shiyasa nace haka."



Ya girgiza kai yace, "good! Zuwa nan da yaushe?." Manal tace, "maybe gobe."

"Okay, I'm waiting, saboda bana son Sata lokaci." Bata ce komai ba tayi shiru tana kallon sa yana kallon ta sai yaga tayi murmushi tace, "meyasa kake son kallona?." Yayi murmushin shima baice mata komai ba yace, "ina so mu gaisa da Mama."



Ta mi™e tsaye tace, "to bara na faWa mata." Zata wuce shi ya kalle ta yace, "ji mana." Ta jiyo ta kalle shi yace, "Meyasa ko yaushe kike murmushi?." Sai ta sake yin murmushi mai kyau mai bayyanar da asalin kyan ta tace, "it's my nature" Tana faWar hakan ta fita ya bita d kallo cikin tsananin farin ciki da soyayya.



Ba jimawa ta dawo ta tsaya daga bakin ™ofar tace, "tace kazo." Tashi yayi ya fito yana sako ™afa tsakar gidan aka kawo wuta, haske ya gauraye ko ina fiye da Wazu.  ya kalle ta a hasken ya rasa meyasa hijab yake mata kyau har haka ko dan tana da gaske ne bai sani ba.



Ita ta fara shiga wajan Mama tana zaune akan carpet ta saka hijjaba ya shiga da sallama Mama ta amsa ya zauna yace, "Barka da dare Mama." Tayi murmushi tace, "Barka dai Adnan, ya aiki da mutanen gidan?."

"Alhamdulillah, ya jikin?."

"Jiki da sauki, Wazu kamar almara naga haske a idona daga nan dai ban sake gani ba, amma tabbas Wazu idona ya buWe. Ko manali ban faWawa ba."



Manal ta wara ido tace, "da gaske mama?." Mama tace, "A'a da ™arya." Sai Manal ta haWe fuska tace, "tambaya fa nayi, kuma naga baki faWa min Wazun ba." Mama tace, "nima ai amsa na baki."



Murmushin da Adnan yayi ne ya saka Mama ta tuna waye Adnan a wajan ta yanzu sai taji yace, "in sha Allah a hankali idanun zasu buWe koda ba duka ba tunda anyi sakaci a baya, amma ganin zai dawo in sha Alalh ciwon bai kai ace idanun sun rufe duka ba."



Mama tace, "ai naga alamun hakan kuwa, na gode sosai Allah ya yi albarka."

"Amin Mama" ya faWa yana saka hannu aljihu ya ajjiyewa Mama kuWi sannan yace, "sai anjima."



Mama tace, "a gaida mutanen gidan, na gode." Ya amsa ya fita Mama bata ji motsin Manal ba alamun bata fita ba tace, "baza kije ki raka shi ba?." Manal tace, "Sata zaiyi ne Mama?." Girgiza kai taga Maman ta Waga sai tayi kamar zata ta tashi alamun zata dake ta kenan ta fito tana dariya a lokacin har ya fita.



Wajan Maman ta koma ta ajjiye hijjabin tace, "Mama ga kuWi nan fa ya ajjiye miki." Mama tace, "na ji su yanzu, kuma nawa ne?."

"Dubu Wari ce." Mama tace, "na gode Allah ya saka da alkhairi."

"Amin" ta faWa tare da yin shiru.



Mama tace, "To ya ake ciki yanzu? Kina jin zaki iya auren sa Manal?." Manal tayi dariya tace, "Allah Mama kina bani kunya, ki ta tambayata a kansa." Mama tayi dariya tace, "baki da ™awa sai ni, faWa min abinda yake ranki a kansa na baki shawara." Manal tace, "zan iya Mama, na fahimci yana da mu'amala mai kyau, sai ka mu'amalance shi zaka gane waye shi, a haka zaka masa fassarar bashi da kirki lokaci Waya."



Mama tayi dariya tace, "shiyasa hausawa suke cewa ba'a yankewa littafi hukunci da bangon sa. Naji daWi sosai tunda kika ga haka to Allah yayi shine mijin ki. Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Manal Wina zata yi aure." Manal ta dawo jikin Mama ta kwanta tace, "Mama kunya nake ji." Mama tayi dariya tace, "Zamu fara shirin biki da wuri, zan faWawa Maman ki Balaraba a fara shiri."



Bata ce komai ba sai dariya da tayi Mama na tsokanar ta. Mubeena ta fito da yake ma sun saba bata zama sun mata da ita a gidan. GabaWaya ta rame  ko fitowa bata yi ita lallai an yi mata ba daidai ba, Jim kaWan  ta dawo ta sake wucewa Mama bata ce mata komai ba haka Manal.





*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



   ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 024.*







A daren babyn Mubeena ya faka a ™ofar gidan su Bily yana shirin yiwa mai gadi magana sai ga Bily zata shiga gidan ya sauke glass yace, "Sannun ki." Kallon sa tayi ta matso kusa da motar tace, "Yauwa sannu."

Yace, "ina neman Mubeena ne, Tana ina kwana biyu shiru haka?." Bily tace, "Ayya ai sun bar Kano sun koma garin su." Gaban sa ya faWi sosai ya kalle ta yace, "me kika ce?, dama ba a Kano suke ba?."



"Eh, a Adamawa suke fulanin can ne, daman ai da kaga Mubeena kaga bafulatana. Sun tafi shiyasa da ka aiko da waya ma nace ace bata nan."



Yace, "Adamawa! Ya maimaita cike da mamaki da tsoro kafin ya sake cewa, "kenan nan ba gidan su bane ba?." Bily tace, "eh, gidan mu ne nan, Mubeena ™awata ce mun zama kamar ΄an uwa a nan take zaune kamar gidan nasu yake." Ya girgiza kai yace, "ki bani lambar ta."

"Kasan ai babu waya hannun ta, a haka ta tafi bata yi sabon sim card ba." Yayi shiru alamun damuwa Biky ta Harare shi ta gefen ido tace, "da yake aure ma zasu yi mata shiyasa suka yi tafiyar gaggawa." Da sauri ya kalle ta da faWuwar gaba yace, "aure kuma?." Ya faWa da mamaki zuciyar sa na bugawa sosai domin haka kawai yake ji gaban sa na faWuwa.



"Eh aure, ina jin in ba'a yi bama an kusa. Sai anjima" ta faWa tana wuce ta barshi a bayyane tana cewa, "sai na raba ku ai wallahi, haka kawai zaka lalata yarinyar mutane kai ka bar naka a gida" ta faWa tana shiga gida shi kuma yana motar ya tafi cike da damuwa mai yawan gaske.



Maryam na zaune a motar Kamal tana kallon sa da mamaki tace, "amma kace min ka goge hotunan, meye na dawo dashi kuma?." Yayi dariya yace, "meye na dawo dasu kuma? Gani nake ina tunawa dake." Maryam tayi tsaki kaWan yace, "wannan ba abinda zaka dinga gani kana tunawa bane ba, don Allah ka goge. Tsaraicina ne fa, kuma yanzu ni ba matar ka bace."



Wani

21 / 27