Chapter 22 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 27

63K to 66K   out of 80K words

kallo yake mata na bama ki da hankali kafin yace, "zan goge, yanzu gida zan kai ki ko muje nawa gidan?." Kallon sa tayi suka haWa ido tace, "muje gida, amma nafi son don Allah ka goge hoton nan."

"Wai meye abin damuwar ne? Naga lokacin da aurena a kan ki akayi hoton nan ko? Kuma kema kina da nawa meye na damuwar?."

"Ni bani da naka, auren mu na mutuwa na goge dukkan hotunan dan basu da amfani tunda ba kai ba mijina bane ba."

"Saboda bakya kewata ne, ni da nake kewar ki ai ban goge ba."



Maryam tace, "Gaskiya zamu yi yin faWa akan hoton nan." Ya sake yin dariya yace, "zan goge kar ki damu my love" ya faWa yana jan motar sai fushi take yana dariyasuna tafiya.



A bakin bakin su ya sauke ta ta fita yace, "gwara mu tsaya a nan kafin yayan ki ya gani mu." Bata ce komai ba yaja motar yana dariya yace, "da wannan hotunan tsaraicin naki zanyi amfani na samu abinda nake so a wajan ki, sai na saka Bebi kuka domin sai na tabbatar da kin yi ciki Maryam" ya faWa yana ™wafa.



      Tana shiga gidan yana ajjiye mota shima bata kalle shi ba ta wuce shima bai mata magana ba ya fito ya shiga wajan Mama tana zaune kamar ko yaushe a inda ta saba zama tana cin abinci. Ya shiga ciki da sallama ya zauna ta kalle shi tace, "ina kake zuwa ne ka ke kwalliya haka?." Kafin yayi magana Mama tace, "baka je ka samu Daddy akan maganar Rumana Win ba ko?."

"Aiki ne yayi min yawa shiyasa, amma zanje."



"In baka je bama ni zanje na same shi na sanar dashi." Mimi ya kalla yace, "Mimi bani abinci naci." Ba musu ta tashi ta kawo masa bata dawo ba sai da ta haWo da ruwa da lemo gudun kar ya mayar da ita amma ta ajjiyewa yace, "baki Wauko kofin ruwan ba, koma ki Wauko ki haWo min da ketchup kin san bana son cin doya sai dashi ai." Juya tayi ta koma ta kawo masa ta ajjiye ya fara jin doyar bai sake magana ba haka Mama ma.



Sai daga baya yace, "Mummy Tahir mai son Mimi, su Daddy sun gama bincike a kansa har sun bada dama ya turo tunda tana son sa." Mummy tace, "Abban ku ya faWa min Wazu, shiyasa ai nake so kayi abinda ya kamata a haWa bikin naku."



"Ni Mummy ai ban shirya ba, ko gini ba'a ba ina ni ina aure yanzu?."

"In an saka ranar auren zaka mayar da hankali ka gama ai, kana da kuWin yi ai, in babu baban ka na dasu. Balle ai ba kai ka ke yi ba, Abban ku ne yake maka." Shiru yayi bai kuma magana ba ya gama ci.



Yana shirin tashi yaji tace, "Adnan ka jini da kyau, wallahi babu wata mace da zaka aura in ba Rumana ba kaji nace wallahi, wannan kwaliyyar da kake kwana biyu na lura zance ka ke zuwa to ka fita daga idona na rufe, ko wacece ita ka dakatar na faWa maka domin kana da mata a ™asa tun baka kai haka ba." Jikin sa ne yayi sanyi jin Mama har da rantsewa, bata taSa rantsuwa haka ba sai yau shiyasa jikin sa yayi sanyi sosai. baice komai ba ya tashi ya fita shi ya rasa wannan wanne irin abu ne da Mama take masa akan Rumana.



Šaki ya shiga ya rasa ma tunanin da zaiyi kawai sai ya kira Farida, tana Wauka tace, "Bebi ya akayi ne?."

"Ya zanyi da Mummy ne?."

"Me ya faru?."

"Mummy yanzun nan ta rantse akan bazan auri kowa ba sai Rumana." Farida tace, "Mummy na son Rumana ita dai kam, kana ji gobe kazo mu tatttauna nasan abinda za'ayi in sha Allah." Bai ce komai ba ya yanke wayar ya sauke numfashi ya shiga banWaki bai jima ba ya fito ya saka kayan bacci riga da wando masu kyau ya kwanta.



Da safe da wuri ya shirya da ya shiga wajan su Mama ma bacci suke ya fita kai tsaye gidan Farida ya wuce a lokacin ™arfe bakwai na safe. Mai gadin gidan ta ya buWe masa ya shiga yana zaune a motar ya kira ta amma bata Wauka ba kawai ya fito ya shiga cikin gidan.



A babban falon ta yara ne guda biyu suna ta shirin makaranta sai mijin ta da yake zaune yana breakfast ya shiga da sallama.



Mijin nata ya amsa yana kallon sa yace, "Adnan yau kai ne a gidan namu?." Ya ™arasa inda yake suka yi musabaha Bebi yana yamutsa fuska saboda khamshin falon da alama bata jima da gama turaren wuta ba ya zauna yace, "na shigo da sassafe kamar gidan rasuwa, in ba yanzu ba bani da lokaci."

"Haka ne kam, ai kuma ™o™ari ma sosai Allah ya taimaka." Bebi ya amsa ya kalli babar ´ar ta yace, "ina Mama naki?."

"Tana sama" ya dafe kansa jijiyoyin kansa har sun fara harbawa yace, "kice mata nazo, jeki da sauri" ya faWa yana tashi mijin mata ya kalle shi yace, " ka hau saman mana."



Bebi yace, "zan jira ta ba sai na hau ba" ya faWa yana Waukar waya sa ya fita daga falon. Bai jima da fita ba ta sauko tace, "A'a ina bebin?."

"Ya fita waje."

"Ohh shifa baya son turare, wannan khamshin ne ya dame shi shiyasa ya fita. Kasan yanzu sai ya saka shi ciwon ko ya fara jiri." Yayi dariya yace, "kowa dai da yadda Allah yayi shi, mu muna so shi baya so."



Tayi dariya ta fita ta hango shi a kan kujerar ™arfen da take ajjiye a harabar gidan ta ™arasa ta zauna kusa dashi tace, "Kai dai ka saba zuwa gidan mutane da farar safiya, badan yara zasu makaranta ba ka sanai ban tashi ba." Ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Lokacin da nake dashi kenan. Duk kin lalata gidan ki da wannan khamshin mai sakawa mutane ciwo." Tayi dariya tace, "mijina yana so nima ina so."



Ya taSe yace, "ina jin ki, ya zamuyi da Mummy?." Tace, "kai da gaske akwai wacce ka ke so Win?." Kallon ta yayi kafin ya girgiza kai yace, "da gaske, lokaci nake jira aje ayi magana a gidan su." Yaya Farida tace, "kasan meye mafita a lamarin nan?." Ya girgiza kai alamun a'a tace, "Hajiya kawai zaka je ka samu kayi mata bayanin abinda yake faruwa, itace gaba da Mama ita kaWai ce zata ne a bar maganar nan kuma dai an barta."



"Nayi tunanin hakan, amma bakya ganin in na samu Hajiya da maganar ran Mummy bazai Saci ba? Zata yi fushi dani sosai." Farida tace, "da wannan gaskiya, Tunda dole zata san kai ne kaje ka faWa mata zata ga ka tsallake abinda take so ne." Bebi yace, "kin fahimta. Abinda ya kamata ayi ke kije wajan Hajiyar, ki yi mata bayanin komai don wallahi in na aure Rumana na cutar da ita na cuci kanta, bazan iya kallon ta matsayin mata a wajena ba saboda ta riga ta fita daga raina gabaWaya. Zuwan ki zai fi nawa sau™i a wajan Mummy, in ni naje sai tafi fusata."



Farida tace, "Anjima in na dawo daga aiki zan biya wajan Hajiyar. Nima bana goyan bayan auren ka da ita wallahi, da farko ai kowa yana so, da taga Wan hamsha™in mai kuWi ai guduwa tayi ta aure shi ko shekara auren bai ba ya sako ta. Amma ban san meyasa Maman ta dage a kai ba, bata ganin itace ta guje ka da farko."



Ya sauke numfashi yace, "Yanzu dai kije kiyi magana da Hajiya yadda ku ka yi ki sanar dani" ya faWa yana tashi tsaye itama ta tashi tace, "ji mana, baka faWa min a ina aka samo matar ba." Ya kalle ta yace, "mu gama da wannan case Win tukunna, sai mun yi waya" yana faWa ya wuce ya shiga mota tayi dariya ta koma ciki.







Nana Haleemad'ş>ØBİ



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



     ©şNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 025*





Koda ya fita kai tsaye unguwar su Manal ya huce, yana zuwa daf da layin su yayi murmushi shi kaWai ya tsaya daga nesa yana hangen layin ya sake yin murmushi kamar mai kallon wani abun. Kamar a mafarki ya hango ta da leda a hannun ta ita da Haroun suna tafiya suna hira shima hannun sa da leda sun shiga cikin layin. 



Ransa yaji ya Saci sosai, ya rasa meyasa take son yawo da wannan saurayin, sau biyu kenan yana ganin su, da sassafiyar nan me ya fito ma da ita har da zai ganta da wani?. Dana sanin zuwa wajan ta dabaibaiye masa zuciya ya ja motar ya tafi ba tare da ya sake kallon inda suke ba amma zuciyar shi zafi take masa sosai.



Haka yayi wunin ranar bai kira ta ba itama bata kira shi ba, sai bayan sallar azahar ta kira shi sai bai Wauka ba ta sake kira yana kallo ya sake yin banza daga nan bata kuma kira ba. Tsaki yayi ya Wauki wayar ya kira ta kafin yayi magana yaji maganar ta hankali tashe tace, "Dr Mama ™irjin ta ciwo yake, wanne magani zan bata tasha bata da lafiya sosai?." A ruWe take masa magana hakan ya saka shi ya nutsu yana sauraron ta yace, "nutsu ki saurare ni." Ina ta kasa nutsuwa tace, "sosai yake ciwon, ko magana sosai bata yi ka taimaka min kar wani abun ya samu Mama."



"Ki nutsu nace, ki saurara da wannan kukan ki tsaya kiji abinda zance miki." Ta kasa magana kuka kawai take da alama bata nutsuwar ta, sai ya yanke wayar ya tashi yana tunanin abinda ya kamata yayi, fita yayi da sauri zai shiga mota kenan nurse ta fito a guje tace, "Dr patient Win da aka yiwa theater jiya yana bleeding,kazo muje zubar jinin yayi yawa."



Rasa abinda ya kamata yayi a wannan lokacin dole ya bi bayan ta da sauri amma hankalin sa baya wajan ya shiga kusan mintina talatin kafin ya fito. Turus yayi ganin Baba da kuma ita Manal Win a reception tana ta kuka fuskar ta tayi ja sosai.



Ganin sa sai Baba ya mi™e tsaye Bebi ya ™araso yace, "Baba ya jikin nata? Ina aka kai ta?." Baba yace, "Dr Huzaifa ne ya karSe ta." Da sauri ya juya suka haWu da Huzaifa ya nuna masa Wakin ya shiga don ganim abinda ya kamata ayi.



Nan da nan ta samu bacci ciwon ya lafa, ya fito daga Wakin ya koma reception ya tarar dasu har lokacin suna zaune sai dai ta daina kukan sai jan numfashi da take yi. Ya kalli yace, "Baba muje ciki."



Ba musu Baba ya taso suka tafi cikin har Manal Win ya zaunar dasu a wani personal room. Sai a sannan yace, "Baba bamu gaisa ba." Baba yayi dariya yace, "Manal ta ruWa ni, ta ruWa kowa taya zamu iya gaisawa?."

"Barka da rana."

"Barka dai Adnan, ya aikin?."

"Alhamdulillah. Jikin nata da sau™i, akwai damuwa ko Sacin ran da ya haifar da ciwon, amma yanzu zai daina mata ciwon in sha Allah."



Baba ya girgiza kai yace, "Ban san me yake damun Fatima haka ba da zata dinga saka damuwa a ranta bayan tasan ba lafiyar kirki ce da ita ba." Baba ya sake cewa yace, "zamu iya zuwa mu ganta?." Adnan yace, "sosai, muje na raka ka" tare suka fita aka bar Manal a zaune bata dawo daidai ba har lokacin tayi shiru kawai.



Sai bayan sun fita tabi bayan su zuwa Wakin Mama na kwance tana bacci Manal ta tsaya kusa da ita Baba yace, "Hankalin ki ya kwanta ko Manal? Ga Mama nan ta samu lafiya, to sai ki nutsu don Allah." Bata iya cewa komai ba sai daga baya murya a sar™e tace, "Baba kaje ka baro kasuwar babu kowa zan zauna da ita a nan."



Baba yace, "A'a bazan barki a nan babu kowa ba, mu zauna duka ai yamma ta kusa daman."

"Yaya Haroun zai zo, kaje kawai Baba."

"To bara yazo Win na tafi." Adnan yace, "babu damuwa Baba zaka iya tafiya duk muna nan tare." Jin haka sai Baba ya amsa gudun kar ya gwale shi yaji babu daWi ya fita bayan sun yi sallama.



Kallon ta yayi amma ita Mama take kallo yace, "ki barta ta huta a nan, muje ko?." Gaba tayi tana tafiya a hankali kamar bata so suka fita. "Manal jikin nata yayi sau™i ko?." Kai ta Wagawa Huzaifa da yake tsaye a bakin ™ofar. Yayi dariya yace, "Tunda naga kin daina kuka nasan jiki Alhamdulillah, ki shiga wannan W'akin ki zauna ki huta kema." Šakin da ya nuna mata da hannun ta kalla taga wanda suka zauna da Baba ne, ta nufi Wakin shi kuma ya kalli Huzaifa yace, "Ya akayi suka zo nan?."



"Kirana tayi hankali a tashe, da yake ina kusa da gidan na su sai naje kawai muka taho nan." Gaban Adnan yayi mugun faWuwa cikin fargaba da kishi mai tsanani yace, "kana da number ta kenan, kuma har ka san gidan su ma?." Yayi dariya yace, "eh mana, kasan da yake yanzu da ita za'ayi na fasa da waccan" ya faWa cikin wasa ba tare da yasan ala™ar su da Adnan ba ya tafi ya barshi a wajan kamar an dasa shi a tsaye shi kuma bai lura da yanayin sa ba.



Gaban sa ne yake faWuwa sosai tashin hankali ya dabaibaye shi, zuciyar sa na bugawa da ™arfin gaske saboda kishi. kallon inda Huzaifa ya shiga yayi ya kalli inda Manal ta shiga nan da nan ransa ya kai ™arshe wajan Saci, yayi ™o™arin sarrafa kishin sa da Sacin ran ya huce zuwa office bai ma sake waiwayar ta ba.



"Amma na faWa mata bana son ™arya meyasa bata sanar dani wannan ba?, Meyasa bata ce min Huzaifa yana son ta ba?" Ya faWa shi kaWai yana dukan kujera yana jin zuciyar sa har wuya ya tsaya gabaWaya ya rasa ma abinda ya kamata yayi.



Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zagaye yake daga nan yaje nan, da™yar dai ya samu ya zauna yayi shiru baice komai ba ya zubawa waje Waya idanu zuciyar sa na bugawa a guje. Kishi ne yake addabar sa, baya so a Soye masa komai shiyasa ya faWa mata tun farko, meyasa bata faWa masa Huzaifa ya san ta har haka ba?.



Huzaifan ne ya shigo da sallama yace, "Bebi ya ka yiwa Abba maganar machine Win nan?." Lumshe ido yayi ya haWWiye yawu ya buWe idanun nasa ya kalli Huzaifa da shima shi yake kallo tace, "lafiya kake idon ka yayi ja haka?, Meyasa cikin kwanakin nan baka zama daidai ne?. Idanun ka sunyi ja, akwai wani abu ne?" Ya faWa dan shi ya manta da katoSarar da ya aikata.



"Huzaifa kasan bana son Soye-Soye, bana son ™arya kuma, meyasa baka faWa min kuma soyayya da Manal ba?." Huzaifa mamaki ya dabaibaiye zuciyar sa yace, "ikon Allah, meya kawo wannan maganar kuma?. Ban da abin ka in ma ina soyayya da ita ai kamar ba sai na faWa maka ba ko?, kai ma baka faWa mana da wa ka ke soyayya ba, dan na Soye maka ai ban yi laifi ba."



Baice komai ba amma ya zuba masa idanu yana kallon sa Huzaifa yace, "wannan shine silar Sacin ran naka?, To meye na Sacin ran? Akwai aibu a ciki in ma son nata nake?. Kai ko Lubna ce nake soyayya da ita ai bana tunanin ranka zai Saci haka balle ita da baka da ala™a da ita. Ba kai ka ke cewa daman sonta nake ba?, meye na damuwa kuma?."



"Ya isa! Ya isa Huzaifa!. Don girman Allah bani waje bana son magana ma dakai gabaWaya." Mamakin sa Huzaifa yake yi yayi shiru ya tafi tunani na wani lokaci kafin ya sake kallon sa baice komai ba sai ya fice.



Wajan Hamza yaje ya jawo hannun sa suka fito daga Wakin da yake cewa, "Meya faru?." Huzaifa yace, "Adnan ya faWa maka akwai ala™a tsananin sa da Manal ne?."

"Wace ma Manal?."

"Wata yarinya kwanaki da suka kwanta a nan da Maman ta?. Duk suna da ciwon sugar ka gane ta?."

"Ohh na gane, bai faWa min ba meye ya faru?." Huzaifa yace, "Wasa nayi masa nace yanzu da ita za'ayi na fasa auren waccan kaga yadda ya canja?, da naje na same shi a office ya tsare ni da ido yana cemin baya son Soye-Soye na faWa masa yaushe na fara son ta."



Hamza yayi dariya yana kama baki da mamaki yace, "kar dai itace yarinyar da yake faWa mana?." Huzaifa yace, "nima nayi wannan tunanin, kai kaga yadda ya tashin hankalin sa sosai? Fuskar sa ta kaza Soye abinda yake zuciyar sa, kai da ka gani kasan akwai kishi a lamarin." Hamza yayi dariya harda tafa hannu yace, "Shege Bebi yana son mata masu kyau. yanzu dai naga kuna mutunci sosai da ita, muje ka tambayar mana, ka san gulma akwai daWi." Huzaifa yayi dariya shima yace, "jira ni ina zuwa" ya faWa yana wucewa ya bar Hamza yana dariya kafin ya cigaba da abinda yake yi.



Wajan Manal Win yayi niyar zuwa amma sai ya fasa tunawa da aikin da

22 / 27