Chapter 26 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   26 / 27

75K to 78K   out of 80K words

Waga kai yace, "eh na sani Yaya, Huzaifa ne likitan da take gani."



Yaya ce, "ma sha Allah, sai mu jira lokaci."



Bebi yace, "haka ne, Allah ya kai mu lokacin." Yayan sa ya amsa da amin Bebi ya tashi ya fita zuciyar sa cike da tunanin meyasa Manal bata faWa masa abinda yaji yanzu ba?.



Mota ya shiga zai ja kenan sai aka masa waya sai ya tsaya ya Wauki wayar daga can Sangaren aka ce, "Bebi kamar yadda ka ce na nemo maka na nemo, Yayar Manal Mubeena an jima da korar ta daga makaranta, yarinyar bata jin magana zan iya ce maka ma tana Wan taSa yawon banza. Sannan Haruna Wan wanda yake ri™on su son Manal Win yake."



Ajiyar zuciya yayi yace, "na gode." Yana faWa ya sauke wayar zuciyar da masa zafi akan ™aryar da Manal tayi masa, meye in ta faWa masa gaskiya ai ba wani abun bane tunda ba itace take yawon ba. A haka yaja motar zuwa asibiti ransa a Sace sosai auren ma yana fitar masa daga rai.



          Mama tana zaune da glasses Win ta a ido tana gani amma ba sosai ba Baba yana zaune ya ajjiye mata kuWin da aka kawo na aure da kuma na saka rana a haWe yace, "Baki ce komai ba, ga kuWi an kawo har naira dubu Wari biyar na aure da na saka rana, kuma su suna so ayi auren ne nan da wata huWu masu zuwa in Allah ya nuna mana."



Mama tace, "to ai shine ya saka na kasa magana, wata huWu ai yayi kusa Baban Manal, ina laifin ma shekara Waya?."

"Ban da abin ki Fatima ko shekarar aka saka zai zo fa."

"Eh haka ne, amma wata huWu me muka shirya?. Akwai aiki sosai fa, ko da kayan kitchen aka bar mu aiki ne mai yawa balle gasu gado da manyan abubuwa." Baba yace, "iya abinda za'a iya shi za'a yi ai, kuma kin manta akwai kuWin ki a hannuna wanda ake juyawa?, sannan nima akwai nawa matsayina na mahaifi?."



Mama tace, "ban manta ba, amma duka kuWin zamu kashe muyi amfani dasu?." Baba yace, "A'a da wasu za'a yi amfani, kar ki damu wallahi Allah zai rufa asiri ayi komai a gama. Bikin ´ar gata za'a yi in sha Allah, ke kan ki sai bayan komai ya lafa zaki dinga tunanin a ina aka samu kuWin da aka yi wannan aka yi wancan, ki mi™a lamarin ki ga Allah kawai." Mama tace, "haka ne wallahi, Allah ya nuna mana lokacin. Gwara a bar shi a hakan ma ayi a gama."



"Amin. Ina Mubeena take?." A lokacin Mubeena ta shigo tace, "gani." Baba ya kalle ta sai da zauna yace, "kin mayar da kan ki wata shiru-shiru saboda kawai an miki faWa gaskiya Mubeena? So kike mu bark1 kina abinda kike so da sunan wayewa?." Tayi shiru baba yace, "tunda haka kika zaSarwa kan ki daidai ne, Tunda kin zaSi ki janye jikin ki daga cikin mu saboda akwai an miki faWa akan abinda kike yi ke kika sani. Kina gani an kawo kuWin auren ™anwar ki har an saka rana, ki yi ™o™ari kawo naki mijin a haWa ku duka biyun a aurar a huta."



Mubeena tace, "to." Baba yace, "tashi ki shiga ciki." Ba musu ta tashi ta shiga Mama ta kalle ta dan tana iya ganin ta bayan ta wuce tace, "Ni tunda idona ma ya buWe nake mata wani kallo, wallahi gani nake kamar an canja ta, wayewa ta tayi yawa idanun ta cikin na mutane take magana bata jin kunya. Kaii!" Ta faWa tana dafe kai akwai abinda ta tuna.



Baba yace, "ki cigaba da yi mata addu'a." Mama tace, "Allah ya shirya. KuWin fa, ka barsu a nan?."

"Ki bar su a hannun ki, ki fara siyan kayan kitchen



Mama tace, "to bara a na tura ta wajan Balaraba su yi lissafin abubuwan da zasu siyo." Baba ya amsa ya fita Mama tace, "Manal." Ta amsa tana fitowa ta zauna kusa da ita Mama tace, "ga kuWin auren ki da na saka rana, abinda za'a yi kije ki samu Balaraba ku rubuta abubuwan da zaku siyo in yaso sai ku shiga kasuwa keda Surayya ku siyo a ajjiye a gidan su."



Manal kallon kuWin take yi abin mamaki yake bata wai kuWin auren ta, har yaushe suka haWu da shi gashi ana maganar aure har an kawo kuWi, lallai in akace lokaci to tabbas in yazo baya jira.



Mama da take ganin ta dishi-dishi ta kalli ta tace, "ya naga kin yi shiru?."

"Mama da gaske wata huWun za'a bari?."

"Eh mana Manal, ko shekara huWu aka saka ai zata zo, gwara ayi a gama kawai a huta."



Idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Mama wata huWu yayi kaWan, kwata-kwata yaushe muka haWu dashi da za'a ce za'a yi biki nan da wata huWu?."



Mama tayi murmushi tace, "™arya kike, ki faWi asalin abinda yake zuciyar ki Manal. Kina son Adnan, dan haka kina son kasancewa matar sa nan kusa, abinda yake ran ki na san bai huce zaki yi aure ki bar gidan nan ba." Sai kuwa ta fashe da kuka ta kwanta a cinyar Mama tana kuka kamar wacce akace gobe ne auren, Mama tana shafa bayan ta tace, "Manal aure ai ba mutuwa bane, zaki dinga zuwa kina gani na indai ina da rai, kuma bakya ganin yanzu na samu lafiyar idanu? Har girki zan iya yi da kaina ai ba abin damuwa bane wannan Manal."



"Nidai Mama a'a, a bar shi nan da shekara don Allah."

"Baza'a Waga bafa Manal, aure ne sai anyi shi in sha Allah. Da kike wannan koke-koken wata rana mutuwa zanyi na bar ki." Manal tace, "ai sai na riga ki mutuwa Mama." Mama tayi dariya tace, "ni dai bana son wannan kukan naki Manali, aure fa zaki bautar Allah zaki je ki yi to meye na kuka?." Zatayi magana ta hana ta tace, "Kiyi addu'a kice Allah yasa hakan shine alkhairi a rayuwar ki."



Shiru tayi Mama ta Wago ta ta share mata hawaye tace, "amarya! amarya!." Dariya ta bata ta Wora kanta a kafaWar Maman tana dariya Maman ma tayi dariya tace, "Ko kefa fa Manali na, yanzu kije wajan Maman su Surayya ki faWa mata sai ku zauna ku rubuta duk abinda kike so, ko me kike so ki siya indai ya burge ki, daman ke mai son harkar kitchen. in kun gama rubutawa gobe sai ku shiga kasuwar ke da Surayya ku siyo duk abinda kika rubuta."



Manal tace, "har da Yaya Mubeena ko?." Mama ta kalli Mubeena da take zaune daga cikin Waki tana kallo su tace, "baza taje ba, ki ™yale ta gaba take yi da mutanen gidan gabaWaya." Mubeena da take gefe tace, "zan je."



Mama tace, "babu ruwana sai kin tambayi baban ku, in ya barki to." Ta kalli Manal tace, "tashi kije ki same ta, baki da wata uwa kamar ta bayan ni." Ta amsa da to ta tashi zata fita Mama tace, "zo ki kai mata kuWin ta ajjiye a wajan ta." Manal ta turo baki tace, "to kawai sai na kai mata kuWi nace na kuWin aurena na ne?."



Mama ta kalle ta tace, "kunyar ta ki ke ji?." Manal tace, "eh." Mama tayi dariya tace, "™arya kike, yadda bakya jin kunya ta itama bakya kunyar ta." Manal tana dariya tace, "To Mama ai ke aminiya ta ce, ita kuma Maman su Surayya ce fa." Mama tana dariya tace, "zo ki Wauka ki wuce, ina wata kunya a wajan ´an matan yanzu?. Sai dai gulma da munafurci." Manal ta Wauka ta fita tana dariya tana son dramar su da mahaifiyar ta sosai.



          ** Suna zaune a cikin mota ita dashi, gabaWaya ya gama kashe mata jiki yadda yake faWa mata yana sonta abin yana sake jefa zuciyar ta cikin kogon soyayyar sa. Ya iya kalmai, ya san ta kan iya tsara ´an mata, yanzu zai miki murmushin da zai rikita zuciyar ki. Ya kalle ta ya ce, "yanzu Lubna haka zamu zauna kenan? Meye aibu na? Na taSa ™o™arin koda taSa jikin ki?." Ta girgiza kai alamun a'a kamar zaiyi kuka yace, "to meyasa baya so na Lubna?, meyasa yake so lallai sai ya raba mu dake?."



Kamar zata yi kuka saboda rauni tace, "ban sani ba, ni na rasa me na yiwa Yaya baya sona ma gabaWaya." ya sauke numfashi yace, "ga Mimi an kawo kuWin ta ko?."

"Har an saka rana ma, shima an kai kuWi sa har an saka rana amma ni ya hana." Da sauri ya kalle ta kamar bai sani ba yace, "an saka rana?."



"Eh an saka ranar sa, kuma wata huWu aka saka." Girgiza kai yake yi lallai Manal ta shammace shi, shi a tunanin sa tunda bata da wani ilimi mai zurfi ba wani wayo ne da ita ba, kasancewar ba wata babba bace zata yi sauri yarda da abinda zai ce sai gashi tayi watsi da abinda yace mata. Nan da nan ransa ya Saci, Bebi bai isa ya cigaba da yin nasara yana barin sa ba, ya zama dole yayi nasara a kansa ya cusa masa ba™in ciki da takaici kamar yadda yake ji a zuciyar sa.



"Tunanin me kake yi?." Kallon Lubna Win yayi yace, "ina tunanin yadda baya qauna ta ne, ina so na samo mana mafitar da zai amince dani." Tayi shiru cikin damuwa ya kuma yace, "Ko Abba na samu da maganar bazai kawo mana mafita ba?." Tace, "Abba sai ya kira Bebi ya faWa masa kuma bazai amince ba tunda baya son ka."



Ya kalle ta sosai cikin taushin murya yace, "Sweetheart!." Ta kalle shi itama yace, "Kina sona?."

Ta kalle shi tace, "Wannan wacce irin tambaya ce?."

"Ki amsa min kawai." Ta girgiza kai tace, "ina son ka." Yayi ajiyar zuciya yace, "kin amince bazan cutar dake ba?."



Tana kallon sa cikin soyayya da shau™in da yake gani a idanun ta tace, "na amince baza ka cuce ni ba." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "Alhamdulillah! Sweetheart bazan cutar dake ba saboda ina son ki, mafita nake nemar mana da zamu kasance a inuwa Waya matsayin ma'aurata."



Ya gyara sosai yana kallon ta yace, "shawara zan kawo ko nace mafita, ban sani ba ko zaki amince ko baza ki amimce ba, sannan ban san da wacce fuska zaki kalle ta ba." Ta kalle shi a raunane tace, "na amince ka faWi ko meye zan amince da kai, na tabbatar baza ka cutar dani ba."



Ya sauke numfashi yayi shiru yana kallon ta kamar ba zai magana ba kafin yace, "ban san ta ya zaki Wauki abun ba, amma dai ina so na taimaki junan mu ne dan na tabbatar in muka rasa junan mu zamu faWa wani hali."



Lubna tace, "ka faWa kawai, ni na amince da kai nasan baza ka taSa cutar dani ba." Ya girgiza kai cikin gamsuwa a zuciyar sa kuwa tausayin ta yake ji amma ya zaiyi bazai bari tausayi ya rinjaye shi akan fansar sa ba, saboda fansar sa yake komai har soyayyar da yake nuna mata duk ta ™arya ce. yace, "ina so ki bani dama ki amince dani har zuciyar ki, ki yarda bazan cuce ki ba, ina so mu kusanci junan mu...." Kafin ya kai ™arshe ta kalle shi da sauri, sai ya tari numfashin ta yace, "ki jira na gama faWar abinda yake bakina kafin ki yanke min hukunci please."



Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "so nake hakan ya faru,in ya faru babu wanda zai hana ni auren ki. Wallahi Lubna zamu yi hakan ne saboda a bani ke na aura ba dan wani abun ba Allah ya sani kema kin sani. Amma in kina ganin hakan bai dace ba shikenan sai mu ha™ura da junan mu tunda Bebi bazai bari mu auri juna ba."



Shiru tayi alamun tunani, shi kuma yana sake karyar da murya yana yi mata bayanin yadda abin zai kasance har yaga ta fara aminta da maganar sa ta kalle shi tace, "in na amince baza ka guje ni ba? Baza ka manta dani ba in hakan ta kasance?. Kaga ni ba ´ar iska bace ba, wallahi ko hugging wani namiji ban taSa yi ba har yanzu, zan amince da abinda kace ne saboda ina sonka, na amince da kai baza ka cutar dani ba domin kana sona kuma kamar ™anwar ka nake. Kayi min alqawarin baza ka guje ni ba?."



Kalaman ta sun saka yaji wani iri a zuciyar sa ya sauke numfashi yace, "bazan guje ki ba Lubna, ina son ki bazan taSa abinda zai cutar da ke ko rayuwar ki ba." Ta sauke numfashi tace, "Allah yana kallon ka in ka cutar dani, Allah bazai bar ka ba domin kaci amanar ™aunar da nake maka."



"Lubna ina wannan abun ne dan neman mafita ba dan ina so na kasance dake ba, inda ni mutumin banza ne da yanzu kin fi kowa fahimtar hakan Lubna." Ta girgiza kai cikin amincewa da maganar sa tace, "nima ban ce kai na banza bane, kawai ina so ka ri™e min al™awari ne kar ka guje ni bayan ka raba ni da abinda nake dashi." Mujahid yace, "indai al™awari ne nayi miki."

"Shikenan, na amince da abinda kace" tana faWa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa daga idon ta. sai jikin sa yayi bala'in sanyi ya kalle ta murya a raunane yace, "meye na kukan?."



Murya na rawa tace, "Daga zuciyata yake zuwa, ban san dalilin zuwan sa ba." Yayi murmushi yace, "kar ki damu, zan nema mana wata mafitar in bamu samu ba sai muyi amfani da wannan Win. Hakan yafi miki ko?."



Ta sauke Ajiyar zuciya ta Waga kai tace, "to." Ya kalle ta yace, "to ki yi murmushi mana, haba Sweetheart." Murmushi tayi shima yayi yana kallon ta kafin yaja motar su tafi zuciyar sa nayi masa sa™a da warwara akan lamarin Lubna, Anya yayi mata adalci? Anya in yayi hakan bai cuce ta ba?. Amma Itace hanyar da yake da ita wacce zai sakawa Bebi ba™in ciki a zuciyar sa, babu yadda zaiyi dole yaci amanar qaunar da take masa.





Nana Haleema.>ĜBŬd'ŝ



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



     İŝNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



*BOOK 1*

*Page 30*





Abban su Bebi lokacin da ya shiga gida Mama ya kira a waya yace tazo da yake yamma tayi sai ta tafi da abinci ta kai masa ta ajjiye ta zauna kamar yadda yake a zaune shi da Mamy tace, "sannu da zuwa."

"Yauwa sannu, ya gida?."

"Lafiya lau."

"Ayyuka sun mana yawa shiyasa kwana biyu komai ya sake lalacewa, ku yi ha™uri komai zai wuce da zarar komai ya dawo daidai."



Mamy tace, "Allah Sarki."  Abba yace, "nasan bana kyautawa amma ayi ha™uri, cikin kwanakin nan zan jima a gidan nan in sha Allah." Mamy tace, "hakan yayi kyau, Allah ya daWa gyara komai."



Ya amsa da amin Mamy ta mi™e tace, "ina da ba™i zan je na sallame su, in kuma ban dawo ba sai da safe" ta faWa tana fita. Mama ya kalla ganin wani wajan take kallo yace, "ran ku nasan a Sace yake dani, ayi ha™uri kawai."



Mama tayi murmushi tace, "Sai yanzu zaka ce ayi ha™uri?. Kudin ´ar ka ta cikin ka aka kawo aka saka rana baka san anyi ba, aka kai kuWin Bebi aka saka rana shima baka sani ba. Wanne irin uba ne kai?, Hakan yana nufin kana sauke ha™™in da yake kan ka wanda Allah ya rayata ya maka kenan?. Yanzu da babu ´an uwan naka haka yaran zasu zauna basu da wanda zai shige musu gaba a lamuran su?."



Ya sauke ajiyar zuciya yace, "duk na Wauki laifin, kuma za a gyara in sha Allah." Tayi murmushi na takaici tace, "sai da lokaci ya ™ure za'a gyara kenan?. To ina so ka tunda duk abinda ka ke yi mana sai an yiwa yaran ka wallahi, mu ma ´a´an ne kamar yadda naka suke ´a´a mu ma haifar mu akayi. Ko me ka ke aikatawa a waje wallahi sai an yiwa yaran ka a suke cikin gida koda kuwa ka saka ™arafuna kayi musu katanga ne, wallahi sai an samu wani ya Salle wannan katangar ko da kuwa mai gadin gidan nan ne."



Kallon ta yayi hakan ya saka ta sake yin murmushi tace, "´an matan ka na waje, in soyayya ka ke dasu ba don ka aure su ba kana da ´an mata a gidan nan ai, in ma lalata su ka ke dasu kaima kana da ´an...."

"Hauwa wacce irin magana ki ke yi haka? Kina cikin hankalin ki kuwa?" Ya faWa yana kallon ta a fusace.



Mama tayi Murmushin takaici tace, "Da hankalina nake maganar kamar yadda ka fahimci abinda nake nufi. Mu matan ka mun zama banza saboda kana da wasu a waje shiyasa ka raina mu kana ganin kamar mu Win ba komai bane face wanda suka tsufa, kana da sabon jini a waje wacce tsiyar zamu yi maka?. Kar Ka ga dai ina da jikoki a gidan nan ko?, to hakan bazai hana na bar gidan nan ba walalhi, tura ta fara kaiwa bango ™iris nake jira, lokaci kaWan kawai" tana gama faWar hakan ta mi™e ta fita ya bita da kallo hankalin sa ya tashi sosai. Kenan duk sun fahimci yana da ´an mata a waje ko me? Kenan da gaske maganar ta zata tabbata na wani zai nemi ya lalata masa yara?.  Ya firgita sosai da abinda tace hakan ya saka shi saurin kawar da tunanin amma zuciyar sa bugawa take matu™a.





          **** Maryam kuwa tun bayan abinda ya faru tsakanin ta da Kamal ta shiga damuwa sosai ko wayar sa bata Wauka, babban tashin hankalin ta bai wuce abinda ya wakana tsakanin su ba in ta tuna hankalin ta tashi yake yi sosai. Yana kiran ta bata Wauka, yayi message bata reply domin kuwa bata ga amfanin cigaba da kula shi ba, tayi nadamar abinda tayi sosai haushin kanta take ji.



A ranar yayi mata message sama da goma tayi banza bata bada amsa ba,

26 / 27