Chapter 17 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 27

48K to 51K   out of 80K words

yana shafa fuskar sa a bayyane yace, "Yarinyar nan tayi, laushi jikin ta kamar mage, ga wani daddaWan khamshi da take yi, za™in bakin ta kuwa kamar alawa. Wow komai yaji akwai halitta kam a tare da ita, Ta ya zan bari wannan ta kubce min?" Ya faWa yana murmushi tuna yanayin da ya shiga ina kuma ga anyi mai gabaWaya.



Yana zaune ta fito kamar ma bata yi komai ba dan ta mayar da kayan ta tun a banWakin ya kalle ta yayi dariya yace, "muje a sauke ki."



Ya ™aaraso kusa da ita ya ri™e kafaWunta yace, "bana son wannan damuwar da nake gani a fuskar ki, Haba mana Baby ba fa wani abin muka aikata ba na faWa miki, da nayi miki wani abun da yanzu kin ji a jikin ki kema. Ki kwantar da hankalin ki wannan ma soyayya ce ba laifi bane dan kin nuna min yadda kike shau™in sona. Kefa wayayyiya ce Baby ban Wauka wannan zai dame ki ba, ina ganin ki big girl ya kike so ki mayar da kan ki baya?."



Mubeena tace, "Nidai bana so kawai, kar a sake maimaitawa."

"An gama ranki ya daWe" ya faWa yana mata jinjina suka fito tare ya saka a kaita har gida shi kuma yana jin farin ciki sosai a zuciyar sa. Sai bayan ta tafi sannan ya hau mota shima ya nufi gidan iyalan sa, yana fakawa kai tsaye Sangaren sa ya wuce bai nemi ko wacce a cikin su ba har garin Allah ya  waye.



Bebi da wuri ya tashi ya yi wanka ya fito zuwa Sangaren Mama bai ma san Abba ya dawo ba sai a lokacin yaga motar sa ya shiga wajan Mama yana cewa, "Mummy yaushe Abba ya dawo?." Mama da take zaune ta kalle shi tace, "au ya dawo?."

"Yanzu naga motar sa a ajjiye."

"Ban ma sani ba" ta faWa ban tare da ta kalle shi ba.



Ya zauna ta kalle shi tace, "Ka tashi ka Wauko abinda zaka ci babu mai yi maka jeka ka dawo bacci suke yau." Yayi dariya kaWan baice komai ba Mama tace, "Murmushi yana yi maka kyau Adnan amma gaba kake yi dashi, kai kullum fuska a haWe kamar mala'ikan mutuwa. Shiyasa ake fassara ka a mutum mara kirki, dariyar ma sai ka saba da mutum ka ke yi."



Yayi dariya yace, "to Mummy kawai sai na dinga dariya kamar wani mara hankali?."

"Lallai, mu da mu ke yi duk bamu da hankalin kenan ko?." Ya wara ido yacec "Ni na isa?."

"Sak Alhajin mu kayi, shima bashi da fara'a sai kun saba zaka ga dariyar sa, amma in baku saba ba kallo Waya zaka ce bashi da kiri. Allah ya ji™an sa." Ya amsa da amin.



Tashi yayi ya shiga kitchen Win sai gashi ya fito da kofi a hannun sa yace, "Mummy ashe anyi min kunu."

"Eh gashi nan nayi karanbani nayi maka, Allah yasa kar a sake bani kunya ace babu daWi." Ya zauna yana dariya yace, "ai yayi daWi matu™a." Tayi dariya bata ce komai ba shi kam kallon ta yake gabaWaya tausayi suke bashi saboda halin da mijin su ya saka su a ciki.



Mama ta katse masa tunani tace, "Da alama Mimi saurayin nan mata dai yayi mata Bebi." Yace, "na tura shi wajan Yaya ni maganar ya bar hannun kuma ai." Mama tayi shiru kafin tace, "ya zancen Lubna Win?." Yace, "na sanar da Yaya komai akan waye wanda take so Win ya tabbatar da bazai bari ta aure shi ba."



Mama tace, "Bebi kana da saurin fushi amma na rasa meyasa ka kasa fushi akan lamarin su Lubna." Yace, "Mummy ai ba dan su nake yi bane shiyasa" ya faWa yan ajjiye kofin ya tashi yace, "zan tafi Mummy."

"Shikenan har ka ™oshi?."

"Eh, in naje zanci abinci."

"To sai ka dawo, kofin an barni a Wauke ko?." Šaukar kofin yayi yace, "Tuba nake." Ta Harare shi tace, "yau ka saba?, a Wauko maka kuma a Wauke maka, dan gata. Shiyasa in na tura Wakin ka plate Win da na manta dashi ma zan ganshi." yana ji murmushi yayi kawai ya fita daga falon. Wajan Abba ya shiga amma bai ji motsin sa falon ba hakan ya saka shi fitowa ya hau mota ya tafi.





Nana Haleema>Ψφή<Ψϋί



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



  ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 019*





Mubeena haka ta kwana a gida gabaWaya babu walwala, Manal na lura da ita ta share ta kawai dan haushin ta take ji sosai. Sai da safe Baba ya shigo sun gaisa ya kalle ta tana zaune da wayar a hannun ta yace, "Mubeena zo Wakina ki same ni yanzun nan." Haushi taji a zuciyar ta tana tunanin yanzu to me kuma tayi, haka ta tashi rai Sace ta shiga inda ya shiga, ba tsammani taji ya karSi wayar hannun ta gaban ta ya faWi sosai yace, "a ina kika samu kuWin wannan wayar? Waye ya siya miki ita?."



Mubeena ta fara kame-kame cikin rashin gaskiya tace, "ba tawa bace, ta ™awata Bily ce ta ara min." Yadda take maganar kana ji kasan ™arya take yi ya girgiza ki ya saka ta a aljihu tace, "to shikenan kice mata tazo ta karSa a wajena tunda ba taki bace ba, sannan daga yau Win nan kar ki sake fita baki tambaye ni ba, duk inda zaki koda bana nan ki faWawa Manal ta baki waya ki kira ni. Ko makarantar ce kar ki sake zuwa sai na sani."



Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Bab yace, "kin Sata wayon ki indai wannan hanyar da kika Wauka kike ganin itace daidai da rayuwar ki Mubeena, zaki yi dan sani a lokacin da baza tayi miki amfanin komai ba." Mubeena tace, "wallahi ni babu abinda nayi Baba."

"Waye ya sauke ki jiya da magariba a mota?." Gaban ta ya faWi sosai tayi shiru, ya sakar mata tsawar da sai da ta firgita ta kusa faWuwa daga zaune yace, "tambayar ki nake waye ya sauke ki a mota jiya?" Ya faWa da tsawar da bai taSa yi mata irin ta ba.



Tace, "Drivern gidan su ™awata ne." Baba yace, "™arya kike wallahi, ki cigaba da abinda ki ke yi, ke a ganin ki hakan shine wayewa ko? Hmmm Mubeena zaki dana sani indai wannan banzar rayuwar kika zaSarwa kan ki, kin ga ina bin ki ta lallami shine kike abinda kike so kina ganin babu mai hana ki ko?, daga yau mun saka ™afar wando Waya dake, zamu ga waye mai nasara ni ko ke." ya faWa yana tashi ya fita ta bishi da kallo babban tashin hankalin ta itace wayar ta.



Yana fitowa tsakar gidan yaga Mama a zaune da alama taji komai tace, "Wayar mai tsada ce a hannun ta ko Baban Manal? Sannan jiya waye sauke ta a mota?. Ai shikenan Mubeena sai ta kashe ni zata huta."



Baba bai so taji ba yace, "Kar ki saka wannan a zuciyar ki, ta tabbatar min da motar gidan su ™awar tace na kuma amince da haka, wayar ma ba ta ta bace ta ™awar tace." Mama tayi murmushi tace, "Ko Manal baza ta amince da abinda kace ba balle ni Baban Manal, ni fa na haife ta. Shikenan ai duk wanda yayi daidai ya sani, wanda bai yi daidai bama ya sani."



Baba yace, "bance ki saka wannan abin a zuciyar ki ba, addu'a zaki mata itace maganin komai." Mama bata ce komai ba Baba ya kalli Manal yace, "ki kula da ita kin ji."



Ta Waha kai alamun to har ta fara kuka ya fita. Mubeena ta wuce zuwa Wakin jiki a sanyaye Manal ta tashi tabi bayan ta tana shiga tace, "in wani abun ya samu Mama ta dalilin ki Allah ya isa ban yafe miki ba Yaya, sannan har abada kar ki tuna ni matsayin ΄ar uwar ki daga ranar bazan sake kallon ki matsayin jinina ba, daga ranar bazan sake miki kallon ΄ar uwata ba wallahi. Babu ni babu ke kamar yadda kika Wauki hakan a yanzu.  ke bakya son mahaifiyar mu ni ina sonta, in ke kin raina ta ni ina girmama ta, in ke kunya kike ji ace itace ta haife ki ni alfahari nake na nuna ta matsayin wacce ta haife ni."



Mubeena da take kallon ta tace, "ni kike faWawa wannan maganar?."

"An faWa miki, in kinga dama ki dake ni kuma wallahi sai na rama. Meye a duniyar in baka girmama mahaifiyar ka ba? Me zaka tsinka a cikin ta in baka yi biyayya ga iyayen ka ba?, Ke a ganin ki wannan wayewa ce ai ko? To kije ki tayi Allah ya bada nasara. Amma ki tuna daga lokacin da kika saka wani abun ya same ta babu ni babu ke" tana faWa mata ta fita ta barta a tsaye. Taji kunya sossi amma wayar ta kawai take ji domin ko wanne lokaci za'a iya yi mata waya.

Haka Manal ta wuni kusa da Mama, duk da Maman tayi shiru bata cewa komai kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa sosai amma bata nunawa.



Kwanan Mubeena biyu bata fita ba saboda babu fuska wajan Mama gashi Baba ya saka mata ido ko ya ta motsa yana kallon ta ko kuma ya saka ana kallon ta gabaWaya ta damu zaman gidan ya ishe ta sosai.



Ranar laraba a safiyar Mama na zaune suna hira da Manal kamar yadda suka saba tace, "Manal kin ji yadda nake jin idona ya Waure ya daina wallahi, a hankali nake ji yana saki, da alama dai abinda likitan nan ya faWa zai tabbata." Manal cikin farin ciki tace, "Da gaske Mama?."

"Da gaske mana."

"Allah ya tabbatar Mama." Mubeena tazo ta zauna a kan tabarmar da suke tace, "Mama zanje makaranta na dawo."



Mama tayi mata banza kamar bata ji me take cewa ba tace, "kiyi ha™uri ni duk abinda ake zargina a kai ba haka bane ba wallahi." Mama tace, "in ma haka ne Mubeena rayuwar ki ce ba tawa ba, Dana sani ke zata bibiya ai bani ba domin kowa yayi daidai ya sani. Tashi ki bani waje ai ba tambaya ta kike ba in zaki fita." Mubeena tayi shiru ta kalli Manal da ba ita take kallo ba sai ta tashi ta fita.



Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena hmmm!." Abinda tace kenan bata sake magana ba Manal ma bata dawo da zancen ba ta Waukewa Mam hankali da hira dan ta kawar da batun Mubeena.



        A cikin kwana biyun Bebi ya tabbatar da son Manal yake so na gaske ba na wasa ba, duk yadda yaso ™aryata zuciyar sa ta dage akan hakan domin duk wata alama ta soyayya ta gama shiga zuciyar sa ta kuma bayyana a ganganar jikin sa.



Kewar ta yake ji sosai, burin sa ya ganta amma ya rasa ta wacce hanya zai bi hakan ta kasance. Ranar bai ma fita ba yana gida tunani yayi masa yawa akan Manal, da ya kulle ido ita yake gani zuciyar sa na harbawa sosai alamun soyayyar da yake mata mai ™arfin gaske ce. Duk ya damu, tunanin kar yaje an mata miji gashi soyayya ta gama kama shi, hakan ya hana shi nutsuwa gabaWaya shine dalilin da ya hana shi fita.



Yana zaune yana wannan tunani Huzaifa ya kira shi ya Wauka Huzaifa yace, "Bebi baza ka fito bane har rana tayi?." Bebi ya sauke numfashi yace, "gaskiya ba zan shigo ba sai zuwa yamma."

"Amma akwai mutanen da suke jiran ka, akwai wanda aka kawo ma yanzu kuma matsalar zuciya ne. Da zaka daure da kazo Win ka san David da Yasir  suna off." Ajiyar zuciya yayi yace, "gani nan" ya faWa yana yanke wayar ya tashi daga inda yake ya saka kaya ya fito.



Ganin motar Abba tana nan sai ya shiga wajan sa ya same shi a zaune da alama bai san ya shigo ba duk da yayi sallama, Abban yana zaune yana magana shi kaWai yana cewa, "Wai me yake damun wayar yarinyar nan ne? Kwana biyu a kashe Allah yasa ba fushi tayi ba."



Girgiza kai yayi domin kuwa ya fara tabbatar da Abban su yana harka da ΄an mata a waje, duk da bai san ala™ar su ba amma a yadda ya damu hakan ya nuna ya damu da yarinyar sosai.



"Asslaamu alaikum". Bebi ya sake faWa yana kallon sa, sai a sannan ya juya ya ajjiye wayar yace, "Wa'alaika salam, Bebi yau ba'a fita ba?."



Ya ™arasa ya zauna a ™asa yace, "barka da rana."

"Barka dai, ya aiki?."

"Alhamdulillah. Yanzu zan fita sai naga motar ka na shigo mu gaisa."

"Ka kyauta sosai, Allah ya taimaka." Ya sauke numfashi sannan yace, "Amin" ya mi™e yace, "a tashi lafiya" ya faWa yana fita.



Yana fitowa compound na gidan Lubna na shigowa, haka nan bai amince da ita ba duk da hankalin sa ya kwanta kwana biyu baya ganin Kamal baya ganin Mujahid amma yanayin yadda take murmushi ita kaWai kamar bata da gaskiya.



Ganin yana kallon ta sai ta tsargu ta ™araso inda yake tace, "ina wuni."

"Daga ina kike?."

"Mamy ce ta aike ni?."

"Shine sai ki fita ke kaWai?." Lubna tace, "ita tace naje." Baice komai ba ya wuce ta bishi da harara ta wuce Sangaren su itama.



Yana shiga wajan Mama bata falo ya wuce Waki ta ya samu tana Waura Wankwali ya zauna tace, "kace min yau babu inda zaka je gashi naga ka shirya." Bebi yace, "ana nema na ne a asibiti shiyasa zan tafi." Ya sake kallon ta yace, "Mummy Abba ya dawo." Mama tace, "na sani, sai me?."



"Mummy gaskiya a rashin zaman da Abba baya yi a gida nan wallahi da saka hannun ku ciki." Mama ta kalle shi tace, "Bebi akwai abinda baza ka gane bane shiyasa, mahaifi ne a wajan ka shiyasa bana son buWe bakina a gaban ka, amma in kana yi min irin haka wata ran zan faWi  kalmar da zaka kwana baka manta ba."



Bebi yace, "shikenan yanzu haka za'a zauna kenan? Kamar ba mijin ku ba don Allah?." Mama bata ce komai ba sai ta canja maganar tace, "da alama dai wannan yaron saurayin Mimi shine mijin ta, dan Yayan ku yace yaje ya samu Daddyn ku a kan maganar da." Bebi ya gigita kai yace, "Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta amsa da amin ya mi™e yace, "sauri nake Mummy sai na dawo."

"Allah ya kiyaye, dole ka gudu ai saboda kar nayi zancen Rumana, daWin ta a nan zan kwana ai." Baice komai ba ya wuce dan kuwa haka Win ne, yanzu zata masa zancen yaje ya samu Yayan mahaifin sa da suke kira Daddy da maganar Rumana shi kuma baya so.



Bebi koda ya fita sai ya samu kansa da bin unguwar su Manal, umarnin zuciyar sa kawai yake  bi a lokacin ban da son ganin ta babu abinda yake so.  a daidai layin ya faka motar yana kallon layin zuciyar sa na wani irin bugawa tana tura shi akan yaje gidan nasu amma ya kasa.



Kamar ance ya juya ya ganta ri™e da leda a hannun ta ita da Haroun tana murmushi shima haka sun jera sun shiga layin gidan.



Gaban sa ya faWi sosai saboda abubuwa biyu da suka haWar masa a lokacin wanda yake gudun faruwar sa, na farko ganin da yayi mata ya saka gaban sa ya faWi haka kawai, na biyu kuma ganin ta da Haroun ya saka zuciyar sa a ruWani, domin bai san ala™ar su da shi ba duba da murmushin da yaga tana yi masa.



Numfashi ya sauke ya kwantar da kansa a kan sitiyarin motar yace, "kaiii! Meyasa zan faWa soyayya cikin ™aramin lokaci haka? Meyasa?!." Ya jima a haka kafin ya mi™e zaune ya kunna motar ya ja ya tafi jiki a sanyaye gabaWaya bashi da kuzari. Bai je office ba sai da ya fara ganin wanda aka kawo Win tun a ™asa kafin ya wuce office yaga mutanen da suke gaban sa.



Tashi yayi ya fito suka haWu  da Dr Hadiza tace, "Dr akwai meeting yanzu." Ya kalle ta yace, "kuje ku yi bazan iya attending."

"But why?."

"Please!" Ya faWa kawai yana barin wajan a lokacin Huzaifa yazo ta kalle shi tace, "yace bazai attending meeting Win ba." Huzaifa yace, "share shi muje muyi abinda yake gaban mu kawai."



Cikin mota kawai ya koma ya zauna ya rasa abinda yake damun zuciyar sa a wannan lokacin, ji yake kamar ya fashe da kuka saboda abinda yake ji yayi masa nauyi a cikin zuciyar sa.  Ya rasa yadda zai sarrafa kansa, nauyi yake ji a ™irjin sa ya rasa inda zai saka kansa yaji daWi.



Har suka fito daga meeting Win yana cikin mota a zaune sai waya ake masa amma ya kasa kallon wayar ma balle ya Wauka dan baya cikin nutsuwar sa. Kulle motar yayi kawai ya kunna ya ja motar ya fita daga gidan. Babban asibiti ya wuce bai jima ba ya sake wucewa gida ko wajan Mummy bai shiga ba ya shiga Wakin sa yana ji kamar ya zubar da hawaye saboda kaifin soyayyar da take sukar zuciyar

17 / 27