Chapter 15 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 27

42K to 45K   out of 80K words

ko?, bata isa na aure ta Win ba ko kuma ni ban kai matsayin auren ba?."

Kallon sa yake yi kafin ya taSe baki yace, "Ba laifi kam" ya faWa yana sake juya masa baya.



"Kai kasan ina da wacce zan aura bikina bai wuce kwanaki kaWan ba, ina mata kallon ™anwata ne har a jikina haka nake ji saboda yarinyar ta san abinda take yi, ina son naga wanda ya san mahimmacin mahaifiyar sa." Bebi ya sauke numfashi baice komai ba ya juyo ya kalli Huzaifa yace, "to naji mai tausayi, zaka iya bani waje?." Nan da nan ya hasala Huzaifa yace, "bazan fita ba ka fitar dani."



Murmushi yayi ganin ya fusata baice komai ba ya zauna, lokaci ya tafi har magriba ta kusa sanin babu abinda zaiyi kawai ya tashi ya ya kalli Huzaifa yace, "in ka gama ka bada key Win a ajjiye min" ya faWa ya fita ya barshi a tsaye cike da jin haushin sa.



Mota ya hau ya fita abin mamaki sai ya hango su Manal a tsaye Maman su kuma tana zaune da alama babu abin hawa, har zai canja hanya sai ya fasa, ya ™arasowa inda suke  ya tsayar da motar ya sauke glass daidai inda Baba yake yace, "Baba ku shigo na kai ku gida, wajan nan ba'a samun motar haya sosai daman."



Baba ganin sa sai yayi murmushi yace, "ai kam ka kyauta likita, mun gode Allah yyi albarka. Manal ri™e Maman ki mu shiga?." Manal ta buWe baya Mama ta shiga itama ta shiga Baba ya shiga gaba suka tafi.



Jan motar yayi suka tafi Bebi yace, "hanyar babu jama'a sosai." Mama da take baya tace, "Likita Allah ya saka da alkhairi, Mun gode da taimakon da ku ka yi mana Allah ya biya ku." Ya amsa da amin Manal dai tayi shiru bata ce komai ba kafin Bebi yace, "Ku dinga zuwa asibiti duk bayan sati biyu ana gwada jinin ku sannan ana duba ki saboda matsalar zuciyar ki, sannan Mama sai kin daina ajjiye damuwa in ba haka ba ciwon ki bazai yi sau™i ba." Mama tayi murmushi tace, "to likita na gode. Manali kina ji a dinga shan magani, likita itace bata son magani ko kaWan, dana matsa mata sai ta fara min kuka dole na ™yale ta."



Baba yace, "da yake bakya son kukan ta ba." Mama ta sake murmusawa ta ri™e hannun Manal tace, "To nima ai bata son nawa kukan ne shiyasa bana son nata."



Šago ido Bebi yayi ya kalle ta ta mirror sai yaga tana sake goge ido alamun kukan sannan gashi face Winta yayi ja alamun tayi kuka. Šago ido itama tayi sai suka haWa ido ya janye idanun sa daga kanta dan yaga alama ta cika sangarta da yawa.



Da yake Manal ta basu labarin har g1da ya kai ta basu yi mamakin ganin ya tsaya a bakin layin ba sai kuma ya kalli layin yace, "mota tana shiga?."

"˜yale mu nan ma, Mun gode sosai" Baba ya faWa yana kallon sa.



"A'a muje ciki" ya faWa yana shiga da motar daidai gidan Baba yace, "nan ma yayi likita, Allah ya saka da alkhairi yayi albarka ya raya zur'ia." Bebi yace, "Amin. Babu komai."

Mama tace, "Gashi zamu fita ban san sunan ka ba, muryar ka kawai na sani." Bebi yayi murmushi yace, "Adnan."



Mama tace, "mun gode sosai Allah biya" ya sake amsawa da Amin har lokacin Manal bata ce komai ba domin tsawar da yayi mata tana cikin kanta sosai, bata son sake masa magana ya wula™anta ta dan ba jurewa zata yi ba.



Suka fita daga motar bayan juya motar yaga Manal ta shiga wani gida su kuma sun isa ™ofar gidan da yake a kulle da alama nan ne gidan, gama juya motar yayi amma ya kasa tafiya kawai so yake ta fito ya sake ganin ta dan yaga kukan take yi. Sai gata kuwa ta fito tana murmushi tana kuma magana ta isa ™ofar gidan ta buWe suka shiga, ita kuma ta kwashe kayan ta shiga dasu. Kallon ta yake a bayyane yace, "shegen surutun tsiya ne da ita, ga shagwaSa kamar wata auta." sai yaji babu daWi akan abinda ya mata Wazu, duk da ba laifin sa bane laifin tane, yayi ™aramin tsaki yaja motar ya tafi.



Nana Haleema>Ψφή<Ψϋί>ΨBέ



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



  ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



Masu nema daga farko ku shiga wannan link din

https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 017.*





        Kai tsaye gidan Yayan sa ya wuce kamar yadda yace yana neman sa, kafin ya shiga sai da yayi sallar magriba sannan ya shiga cikin gidan ya samu matar sa da suke kira Anty Khadija tana zaune a falo, ya shiga da sallama sai ga yara guda uku sun tawo a guje ana masa oyoyo. Shi fuska babu fara'a sannan ga Sacin rai hakan ya saka Wan yayi murmushin da babu wanda ya lura ya ri™e  hannayen su yace, "baku zo gida ba ba ko?." Zama yayi sai ya kalli matar Yayan nasa suka gaisa tace, "wato dai Bebi ba'a ganin ka a gidan nan ko da ziyara sai da dalili."



Yace, "kin san aikin namu, ko yaushe tasowa yake babu excuse."

"Haka ne kam, Allah ya taimaka ya bada nasara. Ai tunda yaran nan suka ji zaka zo shikenan ake murnar ganin ka." Yayi dariya yana kallon su yace, "gashi yau ban zo da chocolate ba ko?." Babbar ciki tace, "zamu je a siyo ko?." Ya Wan saka sakin fuska yace, "to sai a siyo." Matar Yayan nawa ya sake kallo yace, "Ina Ummi?."

"Tana ciki tana aikin karatu wai debate zasu yi Monday a school tun yau take ta practice."

"Ta kyauta."

"Khalifa kira Yaya" ta faWa tana kallon Waya daga cikim yaran, ai kuwa ya shiga a guje sai gasu tare da matashiyar budurwa wacce zatayi shekara sha huWu zuwa sha biyar sun fito tace, "Lah Yaya Adnan."



Kallon ta yayi tace, "ina wuni."

"Lafiya lau, ya school?."

"Lafiya lau yaya."

"Yayi kyau" ya amsa kawai tana tsaye a wajan mahaifin nasu ya shigo. Ganin Bebi sai yace, "A'a Alhaji Adnan ko nace Bebin Mummy, ashe kazo?." Anty Maimuna tace, "ya kamata ku ajjiye Bebim nan don Allah, haka zai aure kuna ce masa Bebi kamar wata ΄ar tsana?" Ta faWa tana dariya. Bebi yace, "sun kasa ajjiye suna, tun ina jin haushi har na gaji da magana."



Yaya yayi dariya yace, "zo muje mu tattauna. A kawo mana abinci." Tare suka fita zuwa nasa falon suka zauna ya kalli Bebi yace, "yarinyar nan ce tazo min da maganar wani yaro Mujahid Wazu, sai nace ai kai zata samu da maganar sai take cemin wai kace baza ta aure shi ba bayan ita kuma tana son sa. Nasan kana da hujja shiyasa nace bara na kira ka naji meye dalilin ka."



Bebi yace, "Yaya in wanda muka haWa kai dashi aka buWe asibitin nan namu dashi?." Yaya yace, "wanda ku ka raba hanya daga baya kenan."

"Yauwa, shine to yake sonta. Ba kuma dan komai ba sai dan ya Sata min rai kamar yadda yake ganin nayi masa." Yaya yace, "Wai wannan wanda yaso Sata muku sunan asibitin?."

"Shifa Yaya, inda da gaske yana son tane sai a bashi auren ta amma wallahi ba sonta yake ba, ya nemi Mimi ta™i sauraron sa shine ya dawo kan Lubna kawai dan ya samu damar da zai rama abinda na saka aka yi masa."



Yaya yace, "Ai ko yana sonta ai ba mijin aure bane, wanda aka kama yana neman marasa lafiya ta hanyar banza meye amfanin bashi aure?." Bebi baice komai ba Yaya yace, "ai an soke wannan maganar gaskiya, abinda akayi kayi daidai in ka sake ganin su tare kayi mata dukan tsiya."



A lokacin Ummi ta kawo musu abinci ta ajjiye ta fita Bebi yace, "ni na kai Kamal ™ara hisba fa Yaya, ya™i rabuwa da Maryam ko yaushe yana zuwa wajan ta da rashin dalili, ta™i fahimta, ya™i fahimta. Na kai shi hisba anyi mana iyaka dashi, abin mamakin a gabana yake cewa shi babu niyar mayar da ita auren ta koda an samu damar hakan."



Yaya ya girgiza kai yace, "Wannan fa laifin maryam ne Adnan itace ta bashi dama wallahi, da bata bashi dama ba da bazai yi ba itace take biye masa har yake zuwa wajan ta. Da yazo ta kore shi, ya sake zuwa bata je ba, bazai sake zuwa ba saboda ta ri™e mutuncin ta, amma da yake bata da hankali wai har shiga motar sa take yi.  Hakan da kayi shima daidai ne Adnan Allah ya cigaba da baka ikon yin abinda kake yi."



Ya amsa da amin yace, "Daman Sacin rai bai barni naci abinci ba" ya yana buWe abincin yaga dambun shinkafa ne sai farfesun nama a gefe. Rufe naman yayi ya zuba dambun ya fara ci Yaya ya kalle shi yace, "ashe fa kai baka cin nama, gaskiya ka bar daWi." Murmushi yayi kaWan yaci dambun sosai, dan  ya masa daWi suna hira da Yayan nasa kafin ya gama ya fita yaje mota ya tafi gida dan ya gaji sosai.





       ****** Su Manal bayan sun shiga gidan ana ta kiran sallah hakan ya saka Mama zama a tsakar gidan tace, "bani ruwa nayi alwala Manal." Manal tace, "Mama tsakar gidan yayi dauWa kika zauna."

"Ke bani ni, abinda a cikin ™asar za'a saka mu wata rana." Manal ta Wauko buta zuba ruwan ta kaiwa Mama ta fara alwala Baba yace, "nima zanje sallah na dawo" ya faWa yana fita Manal ma ta fara alwala duk da tana jin ciwon kai.



Bayan Mama ta kammala tace, "Wauko min sallaya nayi a nan kawai, babu wuta ciki zafi zaiyi." Da to ta amsa ta Wauko ta shimfiWa mata ta itama ta saka tata ta yayar da sallar. Bayan ta idar Maman ma ta idar Manal tace, "Mama me za'a dafa miki?." Mama tace, "basai muna da abincin ba, duba ki gani in akwai Win dan yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba Wazu." Tana niyar tashi Baba ya shigo bai ™arasa shigowa ba sai ga Maman Surayya a bayan sa da Surayyan ri™e da babban kula suka shigo.



Maman Surayya tace, "Maman Manal Sannu, kin sha jiki." Mama jin muryar ta sai tace, "bari kawai, sai dai muce alhamdulillah." Manal tace, "Mama, Baba, kullum Mama ce take bawa Surayya abinci kai mun mai yawa. Wani lokacin in Surayya ta tafi makaranta aika min take dashi, abincin na dinga ci har kawo yanzu." Baba sai yaji wani iri cikin takaicin halin mata sa yana da abinci ba babu ba amma matar sa na kwance asibiti babu wanda ya je inda take balle yayi tunanin basu abinci yace, "Allah ya saka da alkhairi." Mama tace, "Haba dai, babu komai wallahi da Manal da Surayya duk Waya ne a wajena."



Mama da take zaune tace, "Godiya ta zama dole ai, Allah ya saka da alkhairi. Ni daman na san ko babu raina Manal tana uwa." Maman Surayya tace, "haba don Allah ki bari, Kamar yadda kika ce ni uwa ce a wajan Manal, babu godiya a tsakanin mu ya kamata ace mun wuce wajan nan tun ba yau ba." Surayya ta ajjiye abincin tace, "Milky ga abinci nan kin huta girki." Manal zatayi magana Maman Surayya tace, "ke bana son ki ce min komai. Surayya tashi muje Allah ya ™ara lafiya yasa kaffara ce." Mama ta amsa da amin tana mata godiya sosai sanma suka fita.



Manal ta tashi ta Wauko plate ta buWe abincin sai kuwa taga tuwon alkama ne da miyar ganye ta zubawa Maana tace, "Mama kinga tuwon alkama suka kawo mana, kuma kin san Mama daman ko za'a kai min abincin a can har salad sai an saka saboda lalura ta." Mama tace, "Ai Balaraba mutum ce wallahi, tun kuna yara muke tare har yanzu bata ΄ar dani ba. Kaf unguwar nan bani da kamar ta, jin ta nake kamar Yayata komai abu ya taso min ita nake faWawa." Manal ta fara cin na Maman tace, "kuma Mama akwai wani ma, Baba ma zai iya ci har mu ajjiye da safe mu ci."



Mama tace, "Allah Sarki, da yawa haka suka kawo?."

"Wallahi" ta faWa tana cin tuwon itama Maman tana ci. Ganin duhu yayi sai Manal ta tashi ta Wauko  fitili ta kunna a tsakar gidan ta dawo suka cigaba da ci har suka gama suka wanke hannu suna nan zaune har akayi i'sha.



Bayan i'sha ne sauro ya dame su a tsakar gidan dole suka koma cikin falon a lokaci. matan Baba suka shigo da sallanma,  a ciki Mama da Manal suka amsa suka zauna Umma tace, "Ya jikin?." Mama tace, "da sau™i."

"Allah ya ™ara Lafiya" Inna ta faWa Manal ta amsa da amin daga haka suka tashi suka fita.



Mama tayi murmushi bayan ta fita bata ce komai ba Manal da take kallon ta tace, "Umma da Inna basa son mu Mama. Ranar da baki da lafiya da naje wajan su na faWa baki ga abinda suka min ba, ni wallahi duk na tsane su." Mama bata ce komai ba Baba ya shigo da sallama Manal ta amsa bayan ya zauna tace, "Mama akwai tuwo da aka kawo na Wauko maka?." Baba yace, "A'a kuci, su Umman ki sun shigo?." Manal tace, "eh sun zo."

"Su suka kawo tuwon?."

"A'a maman Surayya ce." Yayi tsaki zai tashi Mama tace, "Alhaji ka ™yale su don Allah, mu mun ™oshi ma munci  tuwon alkama da aka kawo mana ka barsu kar rai ya Sac1."



Kafin ya bada amsa Mama ta ace, "Mubeena a ina take kwana ne?." Baba yace, "dana dawo nayi mata waya bana samun ta, Manal ke kina samun ta?." Manal ta girgiza kai alamun a'a Mama tace, "me yarinyar nan take son zama ne? Ko asibiti bata je bafa inda nake, me take so ta zama? kashe ni take so tayi?." Baba yace, "kiyi ha™uri, ™uruciya ce amma ki cigaba da mata addu'a."

"Yayar Manal ce fa, meyasa ita bata yi abinda take yi?. Wallahi na mutu a yanzu na tabbatar da ba™in cikin ta na tafi lahira. Yarinya kamar mai kunnen ™ashi? Tsakani da Allah a ina take kwana? Tana da inda ya wuce gidan ka ko gidan su Surayya ne?."



Baba yace, "Haba Zahra! Wannan maganar bata kamace ki ba, addu'ar  da kike mata ko yaushe ita zaki sake dagewa a kai, wannan kalaman da kike babu abinda zasu gyara sai dai su Sata, don Allah ki kwantar da hankalin ki kina jin abinda likita yace akan saka damuwa a zuciyar ki. In dai kina yi mata addu'a nan da lokaci kaWan zaki ga canji a rayuwar ta."

"Damuwa da ita zan mutu ai indai akan Mubeena ne, yanzu tana ina? A ina take kwana don girman Allah?."



Baba ya kalli Manal da ta fara hawaye yace, "kira wayar ta." Manal hannu na rawa ya Wauki wayar ta sai kuma tace, "bani da kati" ta faWa murya na rawa. Baba ya Wauko naira Wari biyu ya bata yace, "siyo a kanti Bala kizo ki saka, in baya nan kar kije ko ina ki dawo wayata na bayar chaji." KarSa tayi ta Wauki Hijjabai ta fita.



Ba jimawa ta dawo ta shiga da sallama tace, "Baba na saka katin."

"To maza ki kira ta." Ba Musu ta kira ta amma bata Wauka ba ta sake kira ba'a Wauka ba sai tace, "bata Wauka, gashi bani da number Bily ™awar ta na tabbatar da™yar in basa tare."



Mama ta girgiza kai tace, "kace kuma kar na damu?, in ban damu ba me zanyi?. Sati Waya bana gida ban san a inda yarinya take kwana ba ba dole na damu ba. Mubeena! Mubeena!! Hmmmm" ta faWa kawa bata ce komai ba ganin hakan sao Manal tace, "Baba bara naje gidan su Surayya na dawo" ya amsa mata ta fita dan tana so ta basu waje ne ya rarrashi Mama.



Tana fita Baba yace, "Kiyi ha™uri  mana, ki cigaa dayi mata addu'a zata yi hankali in sha Allah."

"Halin uban ta tayi ne kawai, bazata taSa gyaruwa ba kamar yadda nasan bai gyara ba har kawo gobe in dai yana da rai. Ya cuce ni, ya saka ΄ata tayi gadon halin sa tsiya."

"Wai ba magana nake miki ba? ina miki magana kina sake karkacewa, Meyasa baza ki ha™uri kiyi abinda nace ba?, yanzu wannan maganar itace zata gyara Mubeena ko ita zata saka ta dawo? Meyasa baza kice Allah ya shirye ta bane?."



Mama tace, "Allah ya shirye ta." Ta faWa tana Jan numfashi Baba ya dinga rarrashin ya har ya samu ta Wan sauka amma shi Kansa zuciyar sa cike yake da son sanin inda Mubeena take.



       Manal a gidan su Surayya ta zauna suna hira sai da tara na dare tayi sannan ta dawo gida ta tarar Mama har tayi bacci Baba ma yana falon sa na tsakar gida.



Zama tayi bayan ta cire kaya ta Wauki wayar ta tana sake kiran number Mubeena amma bata Wauka. Katin da Baba ya saka mata ta siyi datar naira Wari ta shiga WhatsApp rabon ta dashi har ta manta kasancewar babu wani abu a kai babu messages Win kirki duk yawanci groups Win makaranta ne, duba lambar Mubeena ta ganta

15 / 27