Chapter 3 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 27

6K to 9K   out of 80K words

"Mummy me aka dafa?."

"Tuwo nayi."

"Tuwo! A daren nan?" Ya maimaita yana kallon Mama. Mama tace, "eh shi, ba kai naji kana cewa kana son cin tuwon semovita ba? Shine nayi maka."



Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy gaskiya bazan iya ci ba. Tuwo a daren nan, inaa!." Mama ta harare shi tace, "daman ai ba'a iya maka, sai kaje ka san abinda zaka ci ai." Rumana tayi caraf tace, "Beb ko na dafa maka taliya?."

"Bana so" ya faWa yana fita ba tare da ya kalle ta ba. Sai ta Sata fuska kamar zata yi kuka Mama ta kalle ta tace, "meye na jin haushi bayan kin san halin sa?, dan ya gwale ki ba komai bane a wajan sa, ki yi abu yace bai masa ba duk kin san da wannan, meye na jin fushi to?" Ta faWa tana tashi ta fito falon ta tarar dashi a kitchen Win a tsaye yana zuba kunu a kofi kafin ya fito ya zuba madara a kunun ya zauna a falon.



Mimi da Kausar sun fito ya bisu da kallo ganin kayan jikin su na bacci ne marasa nauyi masu kama jiki, ba kamar Mimi da take da jiki ya kamata kayan sosai yace, "baku da hankali ku ka yi wannan shigar a wannan lokacin?." Mimi bata san yana nan ba da bazata fito ba saboda indai ya gani sai yayi magana, tace, "Yaya dare ne fa."

"Na fiki sani ai, Ku koma ku saka hijjab, ku ka san wanda zai zo yanzu?."



Ran su bai so ba suka saka hijjabi suka dawo suka zauna sai mita suke a zuciyar su dan Allah ya sani yana takura musu, ga shegen saka aiki. Mama tayi murmushi, tana jin daWin yadda yake kula da tarbiyyar ´an uwan sa, ko ya ya yaga sun karkace zai dawo dasu daidai kuma dole su hau layi. Kallon da Rumana take masa ne gabaWaya ya dame shi hakan ya saka ya mi™e ya kalli Mimi  yace, "in an idar da sallar i'sha dake da Kausar da Lubna kuzo ku same ni" yana faWa ya fita daga falon Rumana ta bishi da kallo kamar ta jawo shi ta rungume haka take ji.



Murmushi Mama tayi dan tana ganin irin kallon da take masa, shima tana lura dashi kallon ne ya saka ya gudu amma zata yi maganin sa dan ita kam tana son haWa auren su duk da sai turjewa yake yi bayan a baya yaso Rumana fiye da ko wacce mace. Rumana tace, "Mama nima bara na koma gida gobe na dawo." Mama tace, "to ki gaida Sumayya" ta amsa to ta Wauki key Win motar ta fita.



     Mimi ta kalli Kausar bayan fitar sa tace, "ke me muka yi yake neman mu?." Kausar tace, "me muka yi kuwa? Laifin Lubna ne ya shafe mu. Tsoron wannan faWan nasa nake  yi da in ya fara babu full stop, gashi abokan sa in sun kai dubu a falon sa dan ya miki faWa a gaban su ba komai bane. Shine abinda yake haWa ni dashi, bana son faWa a cikin mutane." Mimi tace, "haka ya yi min ranar juma'a, ke kin ji faWa a gaban Huzaifa wai fita da ™aramin mayafi?,  kuma wai ina magana da maza, Kausar da fa Huzaifa Win kawai na gaisa, ai ya bani haushi wallahi."



"Kema ke kika ja, shifa Yaya yafi so in kika ganshi a waje cikin mutane kar ki nuna kin san kowa ki wuce, wannan magana da mutanen ma laifi ne. Balle yaga kina yiwa wani namiji magana da dariya ki sha harara."

"Matar sa ta shiga uku, Wan mayafin zamanin nan bazai bari ta saka ba. FaWa a cikin mutane wannan bai Wauke shi komai ba." Mama na jin su bata ce komai ba suna zaune har akayi kiran i'sha suka tashi da nufin sallah.



Kamar yadda yace ana idar da sallah suka nufin Sangaren Mamy suka tarar da Mamy da Maryam da kuma Lubna suka shiga da sallama Mamy ta amsa suka zauna tare da kallon Lubna Mimi tace, "to ki tashi boss yana neman mu yace muje." Lubna ta bata fuska tace, "me kuma muka yi?."

"Ke zamu tambaya ai, in ma faWan zai mana ai ke ki ka ja mana,"

"Mtsw! Gaskiya ni Yaya Bebi yana takura min wallahi, haba shi komai bazai barka kayi yadda kake so ba, ni na gaji da wannam rayuwar."



Mimi tace, "in baza ki je ba sai ki faWa mu kama gaban mu, Kausar muje in ya tambaya muce tce ya takura mata." Tare suka fita, Mimi haushin Mamy take ji ganin a gaban take wannan maganar ta amma bata ce komai ba. Basu san ya abin ya faru  ba sai gano Lubna Win sukayi  ta fito.



Suna shiga falon nasa suka same shi a zaune yana sanye da glasses a idanun sa fari wanda yake taimaka masa wajan kallon takarda da wani document a hannun sa yana dubawa. Sallama da suka yi ya saka ya kalle su ya amsa tare da ajjiye littafin yana kallon su suka ™araso suka zauna akan kan carpet Mimi tace, "Yaya gamu." Kai ya girgiza alamun na gan ku kafin ya ce, "tambayar ku nake so nayi, ina so ko wacce ta faWa min asalin abinda yake zuciyar ta. Bana son ™arya ku faWa kai tsaye kar a Soye min."



Basu ce komai ba ya kalli Mimi yace, "me kika shiryawa rayuwar ki a yanzu? Aure ki ke so?." Yadda yayi tambayar ya saka ta kalle shi suka haWa ido dan bata kawo abinda zai ce ba kenan ya Waga mata kai yace, "asalin abinda yake zuciyar ki nake son ki,aure kike so?." Mimi ta sauke kai ™asa tace, "ni Yaya abinda Allah ya tsara min shine daidai."

"Kowa ma haka Mimi, but there's something on your mind that you wish to happen in your life, maybe aure maybe kuma karatun kike so ki gama har ki fara aiki."



Mimi tace, "Yaya ina so, amma nafi so na kammala karatun tunda kaga ina final year."

"Are you sure?." Ta girgiza kai alamun eh. Kallon Kausar yayi yace, "sai ke what's your plan about yourself?." Kausar tce, "ni Yaya ina karatu, in auren yazo zan karSa. Amma kaga yanzu ko saurayi ma bani dashi, karatun shine a kan gaba."





Ya girgiza kai ya kalli Lubna yace, "ke dai daman nasan auren ki ke so ko?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "then what?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "in ba haka bane a ranki meyasa kike tara samari? Yau in na ganki da wannan, gobe da wannan an ganki. Kuma dukkan su babu wanda zai aure ki a cikin su duk ´an Sata lokaci ne, wannan wanda na ganku Wazu nayi miki warning a kan sa amma baki ji ba. Ta™amar ki shima ai abokina ne, na fiki sanin abokina ne, shiyasa nace ki barshi sboda na san shi din amma baka jin magana Lubna."



Lubna tayi shiru bata amsa ba yace, "duk wacce take ji a zuciyar ta she's ready to get married please let me know zan tabbatar ta samu abinda yake so. Abu Waya ne bana so ku dinga hiding abinda ku ke yi ko ku ke so a gare ni, baku san duk wani motsin ku akan idona kuke yin shi ba shiyasa. Ke Kausar ai baki nasan na san kinje Sufi mart ba Jiya. Mimi Wazu kinje biki baki sanar dani ba." Shiru sukayi dukkan su ya kalle su yace, "zan muku duk abinda kike so amma ku tsayar da hankalin ku waje Waya, bana son kula samari barkai musamman ke Lubna" ya faWa yan nuna ta da yatsa.



"Kece Babba a cikin su amma kin fi kowa wannan rawar kan, ki dawo hankalin ki kafin ranki ya Saci,  na sake kama ki da makamancin wannan zan baki mamaki.  duk wanda yace yana son magana dake invite him to come over and talk to me, sai muyi magana akan ki na san waye shi da komai na shi, I'll only let him to talk to you if i trust him, otherwise l'll reject to him. Bama ke kaWai ba dukkan ku, in na samu wata da akasin haka gaskiya ranku zai Saci" ya faWa yana nuna su gabaWayan su.



Mimi tace, "To Yaya in sha Allah zamu yi abinda kace." Ya sauke numfashi yana kallon su yace, "good. Akwai abinda kuke so?." Mimi da Kausar aka kalli juna kafin Mimi tace, "daman Yaya gobe akwai get together na class mate Win mu tun na secondary ina so naje." Ya kalli Mimi yace, "which time?."

"Around 4pm."

"Where?."

"Green pack." Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "okay zan saka a kai ki." Tayi murmushi tace, "na gode."



"Baku da abin cewa?" Ya faWa yana kallon su suka ce babu yace, "okay zamu iya tafi, zan tura muku kuWin kati."Suka yi murmushi dan sun san kyautar sa a gare su akai daWi suka fita ya bisu da kallo.



Allah ya sani baya so wani abun ya samu Waya daga cikin ™annen sa mata, yana tattalin su sosai musamman yanzu da duniyar ta gama lalacewa kowa ba abin yarda bane, baya son yaga wani abun da zai Sata musu rayuwa shiyasa bai basu fuskar sauraren ko wanne namiji ba, sannan bai basu fuskar karSar komai a hannun ko wanne namiji ba. duk da iyayen su suna da halin da zasu basu kuWi amma yana yawan basu kuWi da canja musu waya saboda kar rashin basu yasa su tambayi saurayi. GabaWaya aikin da mahaifin su ya kamata a ce yayi ya dawo kansa bashi, tunda yayyen sa maza guda biyu kowa yana gidan sa shine tamkar uba a wannan lokacin, shiyasa bashi da nutsuwa sai yaji sun kwana lafiya sun tashi lafiya wani abun bai sake su ba. Gashi Allah ya yi shi a mutum mai kishin ´an uwan sa, baya so yaga suna kula ko waye balle saurayi.



Ajiyar zuciya yayi a bayyane yace, "Abba!." Kai ya girgiza kawai yana jin haushin halin mahaifin su amma ya zaiyi ba'a canja uba dolen sa dai shine mahaifi a gare shi. Tashi yayi da niyar shiga Waki sai yaji ana buWe  gate ya ™arasa wajan window yana kallo sai yaga motar mahaifin su ta shigo kawai ya saki labulen dan bai ga amfanin dawowar tasa ba dan da safe zai ce zai koma.



Yana zaune yana cigaba da duba takardun hannun sa yaga wayar sa na haske ganin sunan Abba ya saka shi kulle ido ya buWe ya Wauka da sallama yayi shiru alamun ana amsawa kafin ya tashi ya fita waje. Kai tsaye Sangaren Abba ya nufa ya same shi a zaune a kan kujera ya shiga da sallama ya amsa ya ™arasa ya zauna a kasa yace, "barka da dawowa Abba, ina fatan an dawo Lafiya."

"Lafiya lau Adna, ya aikin naka?."

"Alhamdulillah" ya amsa a ta™aice daga nan bai sake cewa komai ba.



Abba yace, "sai ha™uri aiki ne suke min yawa ga shirye-shiryen zaSe mai xuwa shiyasa abubuwan sai a hankali." Adnan yace, "amma Abba duk mahimmacin abinda ka saka a gaba bai kai mahimmacin iyalan ka ba."

"To iyalai na me suka rasa Adnan? Babu abinda babu a gidan nan koda babu ni na tabbata baza ka bar wani yayi kukan babu ba. Yadda kake kula da iyayen ka da ´an uwan ka ko ni bana kula dasu, indai kana da rai ragamar g1dana tana hannun ka dan na yi shekara bana gida bazan damu ba."



Adnan ya kalle shi Wan daman shi ne kawai mai iya faWa masa gaskiya yace, "Amma Abba ko mu yaran ka  ace babu ha™™in mu a kan ka akwai iyayen mu mata, dukkanin suna bu™atar kulawar ka wacce a wajan ka kawai zasu samu, ni da ka bar min komai a hannuna bazan iya samar musu da kulawar da zasu samu a wajan ka ba. Idan zan iya kula da ´an uwana su kuma fa Abba?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kulle ido ya buWe yace, "Haba Adnan! Iyayen naka bafa yara bane da kake wannan zancen a kansu, dukkan su babu wacce bata aurar da yara a cikin su ba har da jikoki, to me suke nema a wajena kuma?."



"Kulawar ka suke so Abba domin matan ka ne, na tabbatar ka san suna bu™atar hakan." Yayi murmushi yace, "gashi ai na dawo, zan kuma yi sati a nan duk kulawar da suke so zasu iya samu a cikin kwanakin da zanyi." Kallon sa Adnan yake yi zuciyar sa gabaWaya babu daWi yaja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba kafin Abba yayi magana Mamy da Mama suka shigo da sallama ya amsa sai Adnan ya mi™e yace, "Abba sai da safe."



"Allah ya tashe my Lafiya, da safe kafin ka fita kazo nan Ina son ganin ka, koda ina bacci ka jira ni. Maganar da na kira ka muyi bamu samu ba zamu yi daga baya."  Ya amsa da to ya fita. Kallon Mamy da Mama yayi da suke zaune ko wacce fuskar sa babu yabo babu fallasa yace, "ko wacce ta shigo tana shan kunu kamar wanda aka yiwa dole."



Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta mi™e tace, "barka da zuwa muka zo muyi maka daman, da fatan an dawo Lafiya." Yabi Mama da kallo ita kuma ba shi take  kallo ba yace, "Sannu da zuwan ce sai an tashi tsaye?."

Mama tace, "Ina sauri ne zan je na kwanta, sai da safe" ta faWa tana hanyar fita Mamy ma ta mi™e tace, "jira ni mu koma yadda kuka shigo tare" ta faWa tana tashi tsaye itama.



Mama ta kalle ta tace, "baza ki zauna a nan ba?."

"Lissafina ya kwace min bazan iya banbance wacece ma ya kamata ace ta kwana a nan Win ba, ga dai abinci nan Maryam zata kawo yanzu" ta faWa tana fita ta bar Mama a tsaye dan har ta riga taficewa. Mama na shirin fita tace, "kar ki fita Hauwa, dawo ki zauna muyi magana." Ta juyo ta kalle shi tace, "ko meye ma tattauna da safe in Allah ya nuna mana, ka kwana lafiya" ta faWa tana fita ya bita da kallo yana murmushi.



Shi kam mamaki matan nan masa suke bashi ko wacce ta girma a cikin su amma basu daina mararin neman wani abuna wajan sa ba, shi Wauka yake gabaWaya ma an Wauke musu wata sha'awar sa tunda ko wacce har jikoki tana dasu. Har gwara ma Mama tafi Mamy ™arancin shekaru amma Mamy tafi Maman nunawa. Shafa fuskar sa yayi dan shi kam yana da Wanye jini a waje bai ga abinda zai nema a wajan wannan tsofaffin matan nasa ba, shiyasa ko a jikin sa in suna wannan abubuwan, duk wacce ta kawo kanta ita ta sani, shi ban damu ba.



Nana Haleemad'ş>ØBİ



*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



    ©ş *Nana Haleema.*



https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp



*BOOK 1*

*Page 004*





A daren Manal suna zaune da Mama a falo cikin hasken fitilar da ya haske falon nasu Manal tace, "Mama gobe da safe zamu koma

Asibiti." Mama tace, "Manal ni ba sai mun je ba lafiya lau nake jina, in mun je goben wani maganin zasu sake bayarwa kuma ba wani kuWi ne a hannun Baban naku ba yanzu."



Manal tayi dariya tace, "za'a samu Mama, Allah dai ya nuna mana goben. Kuma kin ga wajan Dr Huzaifa ne."

"Eh gaskiya, yana da kirki ya Wauke ki kamar ™anwa, sai a Wauka ma ya jima da sanin mu."

"Auu na manta fa wajan likitan zuciya yace muje a kai masa wannan result Win, Allah ya kaimu goben da wuri zan fita dan ance ba wani kirki ne da likitan goben ba."



Mama tayi murmushi tace, "to Allah ya nuna mana. Yadda kike kula dani Allah ya baki mai kula dake Manal Win Mama." Tayi murmushi ta amsa da amin Mama tace, "Ya sayyadi bai yi waya ba?." Manal tayi dariya tace, "Mama kina bani kunya, ni nace miki Ya Sayyadi ba sauryina bane kawai muna gaisawa ne."

"Nima ai baki ji nace saurayin ki bane ba ai, Yayan ki ne." Tayi dariya kamar yadda Maman take yi Manal ta kalle ta tace, "Wallahi Mamana kina da kyau sosai."



Mama tayi murmushi sosai tace, "duk kyauna bai kai na Manalin Mama ba." Manal tayi dariya kawai Mama tace, "Allah ya kawo miki miji na gari wanda zai kula min dake ya inganta rayuwar ki ya cika miki burin ki na zama shararriyar mai dafa abinci ta duniya ma gabaWaya." Manal tayi dake ya tace, "Mama ta duniya fa kika ce?."

"Ko baza ki iya bane?."

"Zan iya mana, amma ta duniya yayi girma."

"Kina wasa da ikon Allah?."

"A'a Mama."

"To kice amin kawai."

"Amin Mamana. Amma ni bazan yi aure ba."



Mama tayi dariya tace, "wannan kalma ta baza ki yi aure ba na faWa miki bana  son ji." Cikin sha'agwaSa tace, "ni dake zan rayu Mamana, indai kuma zanyi aura sai dai mijin yazo nan mu zauna ko mu tafi dake." Mama tayi dariya sosai tace, "Allah ko Manal?."

"Allah Mama. In na tafi waye zai kula min dake?" Ta faWa jikin ta nayi  tunawa fa da gaske wata rana zata yi auren ta bar Maman ta. Jin yadda Manal Win tayi magana sai Mama tace, "ki cigaba da addu'a kawai, duk inda alkhairi yake Allah ya kawo miki shi." Ta amsa da amin bata ce komai ba.



"Ashe yau da arzu™in nepa a unguwar" aka faWa ana shigowa cikin falon. ko ba'a ce sun san wacce ta shigo. Manal ta kalle ta tace, "Yaya ko sallama baki yi ba fa." Hararar ta tayi tace, "bazan yi sallamar ba, bana son iyayi."



Ta kalli Mama da take zaune daga gefe tace, "Mama ki shiga tsakanin a da yarinyar nan ta daina shiga harkata." Mama bata ce komai ba Mubeena ta wuce Waki sai gata ta fito tace, "ke Manal wai babu abinda aka dafa a gidannan ne?."

"Inda kika je basu baki abincin ba?" Mama ta faWa tana daga inda take zaune. Mubeena tace, "in baza'a bani ba ai sai a faWa min kawai, daman nima karanbani na ne ya saka na tambaya, ina za'a samu irin abincin da nake so a cikin gidan nan?."



"Wallahi Yaya baki da hankali." Wara ido tayi tana kallon Manal tace, "ni ki ke

3 / 27