Chapter 13 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 27

36K to 39K   out of 80K words

ya zauna yana cemin wai in ban fita harkar ki ba sai ya bani mamaki, ke kin ji wula™anci da cin fuskar da yaron nan yayi min akan ki?." Maryam ranta ya Saci tace, "na rasa abinda yake damun wannan yaron wallahi, ya takura min kamar shine ya haife ni ko kuma shine babban yaya a gidan gabaWaya. Nima fa yanzu cewa yayi wai kar a barni na fito."



Kamal yace, "kar a barki ki fito?."

"Wallahi haka yace."

"Lallai ma yaron nan ya fara wuce gona da iri. Dan ina son ki hakan ba yana nufin zan Wauki wula™anci daga wajan ™anin ki ba Maryam, bazai yu yazo har gida yaci min fuska ba, darajar ki akwai yaci matsayin sa na jinin ki amma wallahi da yanzu ba wannan magana ake ba ke kin san waye ni."



Maryam tace, "ka barni dashi zan yiwa tufkar hanci, bazai sake aikata abinda ya aikata ba in sha Allah." Kamal yayi shiru baice komai ba tace, "kayi ha™uri, bazai sake faruwa ba in sha Allah."  Ya kalle ta yace, "soyayyar da nake miki shine ya saka nake bibiyar ki bayan wannan kin san babu komai, amma yaron nan yazo har cikin gida ya ci min mutunci. Da farko da yaje nayi tunanin wajan su Nabil yaje ashe ba haka bane."



Maryam tace, "kayi ha™uri don Allah."

"Ya zanyi, ai dole nayi ha™urim."

"To kayi dariya mana." Ya kalle ta ya kawar da kai bai yi murmushi ba sai ta tuna lokacin da take gidan sa in yayi irin haka, ta kalle shi suka haWa ido sai tayi murmushi yasan abinda ta tuna shima kuma shi ya tuna a lokacin amma shi baiyi Murmushin ba so yake sai ta aikata abinda ta tuna Win dan yasan zatayi bata jurewa fushin sa ko kaWan.



Hannun ta ya ri™e sai ta kalle shi ya Waga mata gira yace, "ina kewar ki." Murmushi tayi tace, "har nayi farin ciki da ka wuce."

"Na mayar dake gida ko akwai inda zaki je?."

"Eh, Mamy ta aike ni kasuwa akwai atamfar da zan siyo mata."



Bai ce komai ba ya kunna motar har lokacin yana ri™e da hannun ya fara tafiya sannan ya kalle ta yace, "ina tuna yanayin da muke kasancewa dake, yanayi mai daWi da yake gusar mana da hankali ni dake, ha™i™a kin yi matu™at iya sarrafa...." Sai yayi shiru ya kalle ta sai ta kawar da kai tana dar1ya amma bata ce komai ba.



Shima dariyar yayi suka cigaba da tafiya ya kai ta kasuwar ya jira ta shiga ta fito ya dawo da ita gida sannan ya wuce inda zai je.



Tana shiga gida wajan Mamy ta ajjiye ledar tace, "Yanzu Mamy abinda Bebi yake a gidan nan ya kyauta? Ya dinga yin abu kamar shine Yaya komai cikin gadara. Kamal fa yaje ya samu har gida yaci masa mutunci kawai dan yana kawo min yarana ina ganin su, yanzu me ya aikata don Allah?."



Lubna da ke gefe tace, "haka kawai ya hana ni kula Mujahid, ina son shi yana sona yana son rabu mu kawai dan baya son sa, shine nima bazan so shi ba. Wallahi Yaya zanje na samu da maganar nan na gaji, a gida yake so nai ta zama duk wanda yazo yace ya tafi."



Mamy da take jin su tace, "to meye na zuwa wajan Kamal kuma?." Maryam ta zauna tace, "wula™anci mana." Mamy tace, "gaskiya bai kyauta ba, ko babu komai akwai yara tsakanin ku da Kamal dan an gaisa ai ba wani abun bane. Maganar Mujahid nima yana bani mamaki ya hana Lubna kula shi a gidan nan gabaWaya, kuma in kika tambayi dalili babu, akan ra'ayin sa kawai yake son danne mata ha™™i."



Maryam tace, "to kuwa wallahi bai isa ba, sai ta aure shi dan ni ban ga aibun da yake dashi ba." Mamy ta girgiza kai tace, "abin da mamaki." Maryam ta girgiza kai domin kuwa ta Waura Wamarar cigaba da kula Kamal ko dan taga abinda zai yi.





Kamar yadda ya saba bai dawo ba sai dare ya faka motar sa a gidan ya shiga wajan Mama dan da yunwa ya dawo sosai, yana shiga ya tarar da ita a zaune ita da Rumana ne kawai dan su Mimi basa wajan. Zama yayi yace, "Sannu da hutawa, Mummy yunwa nake ji."



Mama ta kalli Rumana tace, "kawo masa abinci." Ta tashi ta wuce kitchen ba jimawa ta kawo abincin ta bashi ya karSa ya fara ci yana zaune kafin yace, "Ina Mimi take?." Mimi da yake fitowa daga daki tace, "Gani Yaya, Sannu da zuwa."



Zama tayi sannan yace, "Yauwa. Wannan saurayin naki" sai yayi shiru yana shan ruwa kafin yace, "mun gama magana dashi zai zo gobe, da yau ne ma zai zo sai da ya kira ni nake sanar dashi na manta ban sanar dake ba amma gobe yana nan zuwa" ya faWa yana kallon ta.



Da to ta amsa Mama ta kalle shi tace, "ka gama yi masa interview Win kenan ko?." Yayi murmushi baice komai Mama tace, "wata™ila a haWa auren naku kai da ita ai, in Allah yayi shine mijin ta shikenan faWuwa tazo daidai da zama sai ayi auren naku a wuce wajan."



Shi dai baice komai ba yana cin abinci Mama tace, "ko ba haka ba Rumana?." Rumana tayi ´ar dariya tace, "Haka ne Mama." Sai da yaci abincin sosai sannan ya tashi yace, "yau ban shiga wajan Mamy ba, zanje mu gaisa daga nan bazan fito ba sai gobe."



Mama tace, "Allah ya tashe mu Lafiya" ya amsa da amin ya juya zai fita Rumana tace, "Gud night Beb." Bai amsa ba bai kuma juyo ba ya fice daga falon haushin ta yake ji sosai a zuciyar sa, ita ko kunyar Mummy bata ji ta dinga abu kamar mara hankali.



Wajan Mamy y shiga da sallama ta amsa a ciki bai ma lura da yanayin ta ba ya zauna yace, "Mamy barka da dare, yau ban shigo mun gaisa ba gabaWaya."

"Barka, ya aikin?." Sai da ya kalle ta jin a yadda ta amsa kamar bata so, amma sai bai nuna ba yace, "Alhamdulillah."



Maryam da take gefe tace, "wai Bebi meye damuwar ka da Kamal ne? Dan rashin kunya da rashin mutunci har cikin gidan sa kije ka ci masa mutunci? Meya tare mata wai? In ma bibiyar tawa yake ina ruwan ka ba rayuwa ta bace ba?." Kafin yayi magana ta sake cewa, "dan tsabar wula™anci da raini shine Wazu kace wai kar a barni na fita da yake ga wacce ka haifa ko?, ko kuma ga gidan da ka gina ubana?."



Bebi yace, "Duk abinda nake yi ina yi ne saboda rayuwar ki, badan son raina ba ko kuma dan ra'ayina ba....." a fusace ta katse shi tace, "Ina ruwan ka da rayuwar tawa? Ka cire hannun ka daga cikin rayuwar tawa mana sai me?."



Ya kalli Mamy tace, "Mamy nasan ke kin fahimci abinda nake nufi, ya kamata ki mata faWa abinda take yi ba daidai bane nan gaba zai jawo mata dana sanin da har ta mutu baza ta daina ba. Meye amfanin kula mijin da ya rabu da kai har da zama dashi a mota ko ina a kulle da sunan gaisawa?. Ko Wazu shine ya ajjiye ta a ™ofar gidan nan, meye amfanin aikata hakan a wajan ta don Allah?."



Mamy tace, "A'a Bebi, Wazu nice na aike ta kasuwa, kuma dan sun gaisa da tsohon mijin ta kamar ba laifi bane ba ai ko?." Jin abinda Mamy tace sai ya kalle ta da mamaki sosai yace, "Mamy kina goyan bayan hakan kenan?."

"Ai babu wanda zai ™i hakan sai kai, ka hana Lubna sauraren Mujahid kawai dan bai maka ba, ko kuma dan ta samu miji su Mimi basu samu ba shine damuwar ka?."



Maryam tace, "ba dole ba, kishin ´an ubancin ne ya tashi shiyasa yake so ya korar mata shi, yadda nasa basu samu ba itama ta zauna haka."



A fusace ya kalle ta yace, "Kul kar ki sake faWar haka in ba haka ba zaki nadama. Mimi, Lubna, Kausar, Maryam da Farida duka Waya ne a wajena basu da wani banbanci sai na halitta. Kuma bara kiji, ko me zai faru sai na tabbatar na raba ala™ar ki da Kamal wallahi, haka itama Lubna indai ina da rai bata isa ta auri Mujahid ba, duk abinda zaku ce kuce wannan kamar umarnina ne babu wanda ya isa ya canja shi koda Abba ne, dan ni kaWai nasan hatsarin da yake cikin abinda kuke son yi. Sam baki San abinda kike yi ba, miji ya sake ki saki uku amma kice kike biye masa har ake zama a mota ana tuna rayuwar da ta wuce ana dariya, hakan a wajan ki daidai ne ko kuma wayewa. Rashin sanin darajar kai ne, da kuma rashin sanin ciwon kan ki da bakya yi, ki gyara rayuwar ki ko dan yaran ki" ya faWa cikin faWa dan tasan daman dole zaiyi haka baya jurewa tension, kuma in ransa ya Sac1 kome yazo bakin sa faWa yake kuma a gaban kowa.



Maryam ta kalli Mamy tace, "Mamy kina jin abinda yake cewa ko?" Ta sake kallon shi tace, "ni kuma wallahi sai Lubna ta auri Mujahid sai dai duk abinda akayi kayi" ta faWa shi lokacin ma yayi  nisa da barin falon. ta sake kalli Mamy tace, "Daman Mamy ke kike goya masa baya, gashi yanzu a gaban ki yake zazzaga min rashin kunya kamar ba gaba nake dashi ba, ko da yake har ke ya yiwa bama ni kaWai ba." Mamy na zaune dai kawai bata ce komai ba amma ya bata mamaki kam sosai.



Rai a Sace Bebi ya shiga Wakin sa ya rasa abinda yake damun Maryam gabaWaya bata da girma sai na jikin ta, in badan haka ba da hankalin ka da tunanin ka ka dinga sauraren tsohon mijin da ya sake ka har ka dinga yi masa dar1ya kuna zama waje daya?. Yayi tsaki ya zauna, dole ya yiwa tufkar hanci kar abinda yake gudu yazo ya faru.







Nana Haleemad'ş>ØBİ



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



©şNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.





*BOOK 1*

*Page 015.*





Washe gari bai fita da wuri ba tunda yaje ya gaida su Mama da asuba, sai da ya tashi ya shiga wajan Mamy  ya gaishe ta ta amsa da™yar bai yi wata magana ba ya wuce wajan Mama ya same ta a zaune ita kaWai babu kowa ya zauna yace, "Mummy basa nan ne?." Mama ta kalle shi tace, "Basa nan, sai ka tashi kaje ka haWa tea Win da kanka tunda kai komai sai an maka, Rumana ta shiga uku da yawan saka aikin ka wallahi."



Baice komai ba shi dai, ya tashi ya haWa tea ya dawo yana cewa, "Wai Mummy baki wannan kunun ba?, ni tea ba damuna yayi ba, shan sa sai dole."

"Ai tunda nayi kace babu daWi bazan sake maka kunu ba Bebi, na hana idona bacci na dama maka amma sai kace wai kamar ba'a dama ba."



Yayi ´ar dariya yace, "Allah Mummy ranar tuntuSen hannu kika yi, ni na Wauka ma fa Mimi ce ta haWa ashe wai kece da kan ki."



Ta harare shi tace, "Yanzu ai sai ka samu mai yi maka."

"Tuba nake Mummy." Kausar ce ta shigo falon da sallama suka amsa ya kalle ta yace, "me ya dawo dake?."

"Test muka yi, kuma daman yau bani da class."

"To Wauko min sugar" ya faWa yana ajjiye tea Win.



Shiga kitchen tayi ta kawo har zata tafi yace, "baki Wauko tea spoon ba." Ta juya ta sake kawo masa sai ya kalle ta  bayan ya karSa yace, "haka zan sha babu madara?."



Kausar kamar ta zubar da hawaye ta sake kawo masa tan ajjiyewa tayi ciki gab da zata shiga Waki yace, "Kausar bani ruwa, ki buWe flaks in akwai wani abun ki kawo min." Ta juyo ta Wauko ta kawo masa tare da doya da kwai a plate ta wuce ciki a guje dan kar ya sake aiken ta.



Mama ta kalle shi tace, "kai dai saka aikin ka yayi maka yawa wallahi, indai kana waje shikenan baza su huta ba? Šauko min wannan Wauko min wancan?. Yamzu ba sai kace mata Wauko min sugar da madara, ki haWo min tea spoon da ruwa, in akwai wani abun a flaks ki kawo min, shikenan zuwa Waya taje ta dawo amma sai da ka mayar da ita sau huWu."



Baice komai ba ya shanye tea Win da yake sha Mama ta kalle shi tace, "Adnan ka cire hannun ka daga batun Maryam da Lubna don girman Allah."



Jin magiyar da Mummy tayi masa sai ya kalle ta yace, "me ya faru?."

"Jiya Maryam tazo har nan bayan ka fita tace nace maka babu ruwan ka da lamarin su, in ma tana kula Kamal Win rayuwar tace ba taka ko ta Farida ba. Sannan ko ™anin far'auna ne Mujahid saboda ba™in halin babu ruwan ka, ka cire lissafin Lubna baza ta aure shi ba a ran ka don Allah. Komai kayi ba gani ake ba, a kullum a Wan kishiya ake kallon ka."



"Ke tazo ta faWawa haka?" Ya faWa  alamun bai ji daWi ba tace, "kaga kwantar da hankalin ka, bada rashin kunya ta faWa ba cikin lallami ta faWa,  domin kasan ita ko yaushe ´an Wakin su sune ´an uwan ta, ku kuma ´an Wakin nan daban ku ke a wajan ta."



Bebi ya ajjiye kofin tea Win Mama tace, "dan haka ka ™yale su babu ruwan ka ko me ya faru kayi iya bakin ™o™arin ka amma basu gani ba, ´an uwan ka basa son abinda kake musu tunda su basa ganin sa matsayin gyara, su suna jin abinda Lubna take faWa a kan ka, suna jin ciwo domin kai nasu ne kamar yadda su suke Wauka ´an W'akin su sune ´an uwan su. Mimi da Kausar ko kara ka ajjiye baza su tsallake maka ba zasu yi maka biyayya domin  sun san baza ka cutar dasu ba, yadda ka ke kishin rayuwar su kake tarairaiyar su ko mahaifin su baya yi. Tunda su basa gani a dakatar da wannan abun haka, ka ™yale su suyi abinda suke so dom Allah."



Bebi ya kalli Mama bayan ya gama jin abinda tavr yace, "Mummy inda zan iya ™yale su dana ™yale su  Win amma bazan iya ba."



Mama tace, "zaka iya Bebi, ka kawar da kan ka daga  duk abinda zasu aikata tunda haka suka zaSa."

"Wallahi Mummy bazan iya ba, zafi nake ji a zuciyata a duk wanda naga suna sauraren waWannan mutane guda biyun. Mummy Allah ya saka min kishin ´an uwana dukkan su ji nake kamar ana tafasa min zuciya lokacin da na gansu da wani namiji wanda na tabbatar ba mutumin kirki bane. Mummy ban sani ba ko kowa haka yake ji akan iyalan gidan su, ni yadda nake jin  iyalan gidan nan zan iya sadaukar da raina saboda farin cikin ku gabaWaya. Da naga wani abun ya cutar da Wayan ku gwara ni ya cuce ni. Aka cigaba da tafiya haka wallahil azim Mummy nan gaba sai sunyi hawaye domin Mujahid ba sonta yake ba, yana amfani da ita ne dan ya Sata min rai, shi kuma Kamal yana amfani da son da take masa ne yana cigaba da bibiyar ta duk da babu aure tsakanin su, in aka zuba musu ido me zai faru?. Taya zan iya barin wannan Wanyen aikin Mummy?."



Mama tace, "Na sani Bebi, nasan kana yi da zuciya Waya amma su basa gani ne."

"Kar su gani mana ai Allah yana gani, babu abinda zai dakatar dani ga daidaita musu zama a gidan nan ko meye zai faru kuwa, don Allah ki cire bakin ki Mummy, ki ™yale ni nayi abinda nake ganin shine daidai."

"Zaka sake yin ba™in jini a wajan su, dmaan suna cewa mahaifin ku yafi son ka."

"Na amince, ba™in jinin na Wan lokaci ne, daga sanda suka fahimci ni ne a kan daidai shikenan zai gushe."



Mama tace, "ai shikenan Allah ya bada lada." Ya amsa da amin ya tashi tsaye tace, "nasan abinci kuma ya fita daga ranka, Sacin rai ya daina saka ka ™in cin abinci kan ka zaka cuta." Yace, "Zanje na shirya zan wuce aiki."

"Allah ya kiyaye."

"Amin" ya faWa yana fita zuciyar sa cike da Sacin rai ya kuma yi alqawarin ki ne zai faru bazai bar Lubna da Mujahid ba, haka bazai bar Kamal da Maryam ba.



Da wannan tunani da Sacin ran ya shirya ya fita zuwa asibiti, yana zuwa kai tsaye office ya buWe ya shiga yayi zaman sa a ciki dan baya cikin yanayin da zai iya zuwa yaga wani mara Lafiya.



A can Wakin su Mama tana zaune sosai ta samu lafiya dan shayi ta gama sha Manal na zaune sai Baba shima da yake zaune a Wakin.



Huzaifa ne a Wakin a tsaye yana kallon Mama yace, "Mama sugar ki ne ya hau sosai ya kamata a gujewa shan abubuwa masu za™i, sannan kuma a dinga yawan shan magani kar a dinga bari sai ya ™are." Mama tace, "likita rai

13 / 27