Chapter 19 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 27

54K to 57K   out of 80K words

yace, "Wan gidan tsohon minister noma ne Alhaji Mu'azzam Alhassan, baban sa babban mai kuWi ne sosai kuma ya shiga siyasa a yanzu."  Sai Mama tayi shiru tace, "to, sai kuma jikina yayi sanyi, anya kuma bai fi ™arfin Manal ba Baban Manal? Minister fa?." Sai Baba yayi murmushi yace, "in Manal bata fi ™arfin sa ba bana tunanin zai fi ™arfin ta, kin manta wacece mahaifiyar Manal ne? Kin manta wacece ke ne?."



Mama ta sauke numfashi tace, "wannan duk ya wuce ai, babu wanda yasan da shi in ba kai ba, ka manta da waccan da aka sani ta yanzu ake magana a ka." Baba yayi murmushi yace, "ai ba'a canjawa tuwo suna."



"In aka yayyanka shi aka saka mai da yaji ya zama kwaWo." Yayi dariya yace, "bai fi ™arfin Manal ba Fatima shine daidai ita, kuma har zuciyata na amince dashi ina so ta amince dashi itama domin ya shiga raina sosai."



Mama tace, "nima zan so hakan, amma Allah kaWai yasan abinda ya shirya mana baki Waya."

"Haka ne, yanzu na bashi dama yazo gobe su gaisa da ita, kafin nan ni kuma da safe zan saka ayi min ™aramin bincike akan sa da kuma halayen sa." Mama tace, "hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya amsa da amin kafin ya Waga murya yace, "Manal!." Daga tsakar gida ta jiyo kiran ta amsa ta shigo tace, "Gani Baba."



Baba yace, "Wannan likitan da yazo yanzu yazo ne akan ki." Manal ta kalli Baba tana jira ya cigaba taji akan me yazo kuma sai Bab yace, "Yazo ne akan yana sonki yana kuma son a bashi dama ku yi magana dake dashi a matsayin mai neman auren ki."



Gaban Manal ya yanke ya faWi,ta zauna daga tsugunen da take ta kalli Mama taga sai murmushi take yi da alama abin ya mata daWi shima Baban murmushin yake yi ya cewa, "na bashi dama gobe yazo ya ganki ku tattauna abubuwa a tsakanin ku. Sai ki shirya zuwa goben nasan bazai wuce da yamma ko da daddare zai zo ba."



Manal dai ta kasa magana kallon Baba take yi abin mamaki yake bata, yaushe hakan ta faru bayan ita wula™anci ne ya raba su?, Yaushe ya fara son ta har ya samu ™arfin guiwar zuwa gidan su?, Har yaushe ma ya santa suka yi sabon da soyayya zata shigo tsakani?. Ashe daman zai iya sonta? Daman kallon da yake mata Wazu na so ne?. Katse mata tunani Baba yayi yace, "tashi kije" ta mi™e jiki a sanyaye ta fita tana tunanin lamarin kamar a mafarki, wai Dr Adnan ne yake sonta.



Nana Haleema>ĜBŬd'ŝ



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



  İŝNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



Masu tambaya daga farko zaku samu a wannan link din https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 021.*





Mubeena kuwa a daren suna zaune a falon gidan su Bily su Mummyn sun je wata dubiya su dawo Mubeena sai ™unci take yi Bily tace, "wai duk akan an ™wace miki waya shine kike wannan ™uncin? Ni Baba yayi min daidai domin kuwa wannan shegen mutumin iskanta ki zaiyi wallahi."



Mubeena bata ce komai ba mai gadi ya shigo da sallama Bily ta amsa yace, "akwai wanda yazo yace ayi masa magana da Mubeena shine nazo na sanar da ku." Mubeena ta kalle shi tace, "waye?." Mai gadin yace, "ban san shi ba, amma babban mutum ne."  Kafin yace wani abun Mubeena ta mi™e ta yafa mayafi ta fita Bily ta bita da kallo tana girgiza kai cike da jin haushin ta.



Waje ta fita taga motar tasa ta buWe gaban motar ta shiga ya kalle ta yace, "kin wahalar dani Baby, yau kwana biyu wayar ki a kashe baki neme ki ba, wallahi ko abinci bana iya ci. Duk akan abinda ya faru ne kike min wanna horon? To kiyi ha™uri bazan sake ba." Mubeena itama kewar sa take yi sosai a zuciyar ta sai ta fara kuka ta gigita shi lokaciyace, "Haba Baby, me kuma don Allah? Kina so nima nayi kukan ne?."



Bata amsa ba yace, "Don Allah ki faWa min abinda ya faru, in akan abinda nayi ne nace ayi min afuwa ko?." Mubeena ta goge idanun ta tace, "wayata ce ta faWi kuma bani da lafiya."

"Me ya same ki Baby? Wani abun yana damun ki?."

"Ciwon kai ne, amma naji sau™i sosai."

"Yaushe wayar taki ta faWi?."

"Tun washe garin da muka rabu."



"Amma da sai ki saka Gmail Win ki a wata wayar ki Wauki number ta ki kira ki sanar dani, na damu sosai baby." Ta share idanun ta tace, "ban yi wannan tunanin ba." Yayi murmushi yace, "to shikenan, indai waya ce za'a sake siya miki wata dan ma dare yayi ne da yanzu za'a kawo miki amma gobe da safe ki shirya karSar waya. Sim card Win fa?." Mubeena tace, "zan canja wani kawai, daman bana son wancan damuna ake da waya." Yayi murmushi yace, "an gama ranki ya daWe, zan aiko ayi miki register har gida ba sai kinje kin bi layi ba."



Tayi murmushi tana turo baki ya bita da kallo kurilla yace, "Ina kewar ko baby." Ta kalle shi itama tace, "Nima haka" ta faWa tana kallon sa tana tuna abinda yayi mata sai tsigar jikin ta ta tashi. Hannun ta ya ri™e yace, "yaushe zaki raka ni Abuja? Ina so naje na gana da president kinga sai muje ko?." Mubeena Jin ance president sai ta kalle shi tace, "Mummy baza ta barni ba, faWa zata yi min." Yayi murmushi yace, "to yanzu ya za'ayi? Ina so kiyi min rakiya muje mu dawo a ranar."



Mubeena tayi shiru tace, "a ranar muje Abuja mu dawo?." Yayi dariya yace, "sosai, jirgi zamu hau kuma private get ne sai lokacin da naso muje mu dawo." Jin haka sai ta sake jin daWi tayi dariya tace, "to zan duba na gani in zanje."

"Zaki je ma kawai Baby." Tayi murmushi shima yayi tare da yiwa hannun ta kiss yace, "hankalina ya tashi akan rashin magana dake, yanzu dana ganki sai na samu nutsuwa."



Tayi dariya bata ce komai ba yace, "in badan ke ba bana driving da kaina, amma bazan iya zuwa da wani wajan ki ba Baby" ya faWa yana Wauko leda a bayan motar ya ajjiye akan cinyar ta.



BuWe ledar tayi taga kayan ciye-ciye ne kawai a ciki, tayi murmushi tana kallon ledar sai ji tayi ya mata kiss a kumatu ta kalle shi ya Waga mata gira sai suka yi dariya a tare.  A haka suka rabu ta koma ciki shi kuma ya ja motar domin baya so Maubeena ta guje masa bai samu abinda yake so ba, in hakan ta faru yayi babbar asara.



Mubeena bata dawo ba sai goma na dare Baba yana zaune a ™ofar gida yana jiran yaga ta inda zata Sullo dan lamarin ta ya lura sai ana mata yi jan ido,  ai kuwa ya hango ta shigo layin, baiyi magana ba har ta shiga cikin gidan sannan yabi bayan ta ya kulle gidan dan a wajan Mama yake ya shiga ciki.



"Daga gidan uban wa kike?." Jin abinda Baba yace sai da gaban ta ya faWi ta juyo tana kame-kame,  ya Wauke ta da mari mai zafi kafin ta dawo hankalin ta ya sake marin ta sai ta zube a wajan tana gani biyu-biyu dan rabon da a mare ta har ta manta yace, "ni zaki mayar Wan iska? Dan kinga ina bin ki a hankali sai ki mayar sa'an wasan ki? Daga ina kike a cikin daren nan?." Baya yayi ya Wauki  igiyar shanya yace, "Wallahi ko ki faWa min ko yau na zane miki jikin ki, daga gidan uwan ban wa ki ke a daren nan?."



Mubeena ta tsorata sosai karo na farko da Baba yayi mata haka,jiki na rawa ta rasa abinda zata ce kawai taji ya fara dukan ta dan ta gama Sata masa rai.



A guje Manal ta fito jin maganar Baba da ™arfi ganin ana dukan ta sai jikin ta yayi sanyi ta fara kuka tana daga tsaye Baba yace, "baza ki faWa min ina kike zuwa ba?."

"Makaranta naje, sune suka tura mu wani aiki sai yanzu na dawo."

"˜arya kike, har makarantar taku na saka an duba bakya nan, ko faWa min inda kikaje ko yau sai na lahira ya fiki jin daWi, ko ki faWa min uban da yake goya miki baya yake zuga ki ko yau na karya ki." Ganin Baba dukan nata zai sake yi da sauri tace, "Wallahi Ina can, ina can babu inda naje" ta faWa tan kuka sosai dan ta daku.



Baba yace, "duk abinda kike ganin daidai ne a wajan ki Mubeena ki yi, ki cigaba da Wurawa babar ki ba™in ciki, ki cigaba da bari tana zubar da hawaye a kan ki. Daga lokacin da kika yi sake tayi miki baki daga wannan lokacin zaki gane kuskauren da kika tafka a rayuwar ki wanda baza ki gyara ba. Ina so ki sani, daga yau babu ke babu zuwa makarantar na soke, sannan daga yau kar na sake gani kin fita ko da gidan su Surayya ne. wallahil azim kika sa ke aikata wani abun sai nayi miki illa, sai na karya ki gida biyu" ya faWa yana cillar da igiyar ya shiga Wakin sa cikin Sacin rai sosai.



Manal da take kallon ta tana kuka tace, "Ko yaushe burin ki ran Mama ya Saci, bakya damuwa da wanne hali zata shiga saboda son zuciya da son kuWi ya riga ya rufe miki ido. Ki yi abinda kike ganin ya dace, abinda baki sani ba nasan ba makaranta kike zuwa ba Yaya akwai inda kike zuwa in kika fita, bana zargin ki a baya, amma yanzu ina zargin kin fara wata Wabi'ar da baki da ita. Kije ki yi ke zaki dana sani, ke zaki nadama a lokacin da bata da amfani, ke abin zai bibiya har mutuwar ki" tana faWa ta shige ciki ta barta a wajan tan kuka sosai. Mama duk tana jin abinda yake faruwa tayi kamar tayi bacci nan kuwa idon ta biyu babu wanda ya kai ta jin ba™in ciki a zuciyar ta.



Tana jin wucewar Mubeena Win tana kuka bata ma Waga kai ta kalle ta ba balle tayi mata magana. A haka suka kwana kowa rai a Sace. Da ciwon ™irji Mama ta tashi sai da Manal ta bata magani sannan ta Wan ji daWi. Mubeena na Waki ta™i fitowa ko cin abinci balle wanka babu wanda ya neme ta duk suka share ta.



Gab da sallar azahar Bily tazo gidan Baba yana nan dan bai fita ba saboda case Win Mubeena, Bily ta gaishe da Mama suka gaisa da Manal kafin tace, "Manal Baba yana nan?." Manal tace, "eh yana nan, amma yana wancan gidan." Bily tace, "muje ki raka ni wajan sa na zo" Ta amsa da to ta tashi ta saka mayafi suka fita.



A lokacin zai fito daga gidan suka  haWu a soron gidan, Bily ta gaishe shi ya amsa kafin Manal tace, "™awar Yaya ce Baba, tace tana son ganin ka." Baba yace, "Allah yasa Lafiya."

"Ba Lafiya ba Baba, magana ce akan Mubeena."

Baba ya nutsu yana kallon ta yace, "Ina jin ki."



"Baba tun shekarar mu ta farko aka kori Mubeena daga makaranta saboda bata maida hankali akn karatun, duk wata ™arya da take yi akan makaranta ™arya take wallahi bata da register babu sunan ta a jerin ´an makaranta, tana dai taya ni zama mu dawo. To yanzu ta daina zuwan ma saboda akwai wani Alhaji da yake wure mata kunne da sunan zai aure ta, baban mai kuWi ne sosai a garin nan, har waya ya siya mata mai tsadar gaske. Nayi shiru da ban faWa ba, amma yanzu rawar kan nata yafi na baya, shiyasa naga in nayi shiru naci amanar ku dalilin da ya saka nazo na faWa a saka mata ido domin a kansa babu abinda baza tayi ba."



Baba ya girgiza kai cikin mamakin Mubeena yace, "Ya sunan ki?."

"Bilkisu."

Baba yace, "Na gode Bilkisu, Allah yayi miki albarka, Allah ya saka miki albarka a rayuwar ki."



Bily tace, "Amin Baba. Nayi anyi da ita akan ta bari ta™i shiyasa na yanke hukunci nazo na same ka, kuma daman gidan mu shine mafakar ta, a nan take wuni har dare sannan ta tawo." Baba yace, "kin kyauta da kika faWa Sin, na gode sosai Allah yayi miki albarka" ta amsa da amin tayi musu sallama ta wuce. Manal ta koma ciki jikin ta duk babu daWi jin abinda akace Mubeena Win nayi.







Manal da ta shiga gida kai tsaye inda Mubeena take ta wuce ta shiga ta zauna kusa da ita tace, "ni kaWai ce ´ar uwar kuma wacce zan faWa miki gaskiya Yaya, ni kaWai kike da ita ko kina so ko bakya so. Rayuwar da kika Wauka ba komai bace face watsewa da kuma lalacewa, in kina ganin hakan da kike yi shine daidai kuma shine wayewa wallahi rashin hankali ne da kuma rashin wayo da lalacewa. Zai jawo miki dana sanin da har ki mutu baza ki daina ba a lokacin da bazai miki amfanin komai ba, ita wannan duniyar kayi daidai ma ya ka cika balle baki yi daidai ba?. Kabi iyayen ka ya ka zauna balle ka raina iyayen ka?."



"A ko yaushe burin ki Satawa Mama rai, bakya ganin girman ta bakya darajata dan ta kasance a wannan gidan da kika raina kuma bata gani, ke a ganin ki Allah bai miki daidai ba da ya yo ki a gidan nan. Ba ™arya kowa yasan kina da kyau amma meye amfanin kyau babu kyaun zuciya? Meye amfanin kyaun da zai kai ki wuta da ™afar ki?. Ke a tunani ki wannan Sacin rai da kike saka Mama bazai iya kai wuta ba? Ko hawayen da kike saka ta a kulluS ruwa ne yake zubewa daga idanun ta Yaya?."



Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Manal tace, "duk abinda kike aikatawa in ya kamata kin sani wallahi, kome kike yi ki na sane domin kuwa da hankalin da kuma ilimin ki, ki sauke tunanin da ya shiga kan ki, ki yi rayuwa mai kyau in ba haka ba dana sani zata riske ki a lokacin da hakan bazai miki amfani ba. Na faWa miki haka ne a matsayin ki na ´ar uwata ta jini, bani da kamar ki shiyasa na faWa miki gaskiya, in kin ga zaki gyara kanki, in baza ki gyara ba kan ki" tana gama faWa mata haka ta tashi ta fita dan in tana zaune kusa da ita ji take kamar ta mare ta.



angaren Bebi haka ya kwana ya yini cikin karsashi  da farin ciki da annushuwa, koda yaje asibiti sun lura da yadda yake komai da kazar-kazar kai da ka ganshi kasan akwai wani abu mai daWi da ya same shi.



Lokacin da yake asibitin su na getting better babu wani conjunction na marasa lafiya in ma akwai ba Sangaren da bane da yawa Sangaren su Hamza ne da ´an team Win sa, hakan ya saka shi zama kawai yana tunanin Manal da abinda zaice mata in yaje wajan ta a ranar.



Bai jima sosai ba ya tashi zai tafi sai a sannan suka haWu da mutanen nasa Hamza ya kalle shi yace, "Ahha Bebi wannan yanayin da na ganka a ciki duk soyayyar ce?." Šaure fuska yayi gudun kar su jawo masa raini ganin basu kaWai bane a wajan, hararar su yayi yace, "ku kuka sani" yana faWa  yayi gaba suka yi dariya suka cigaba da abinda suke yi shi kuma yayi gida.



Yana shiga gidan Maryam tana shigowa itama ya bita da kallo, gabaWaya baya amincewa da yawan fitar da yake gani suna yi ita da Lubna su kaWai,  amma da yake idanun sa basa ganin abinda baya so a tare dasu bai wani damu ba.



Ciki ya wuce ya shiga wajan Mama ya samu Yayar sa Farida a zaune ita kaWai tana danna waya. Ya zauna yace, "saukar yaushe?."

"Na jima a nan, ya aikin?."

"Alhamdulillah. Ina Mummy?."



"Tana ciki. Ya batun Rumana ne?, Mama ta matsa a kai fa, yanzu ma kafin ta tashi maganar take yi min, maganar ta taso da gaske ne?." Ya kalli hanyar da Mama zata Sillo yaga bata nan yace, "zan zo gida mu tattauna a kai."

"Ya dai kamata, ni sam-sam bana so yanzu wallahi, da dai naso ka aure ta amma yanzu abin ya fita a kaina haka kawai."

"Hmm! Kema dai kya faWa."



Mama ce ta fito tana cewa, "A'a Bebi an dawo?." Yayi murmushi yace, "eh Mummy, na dawo" ta ™araso ta zauna tana kallon sa tace, "to Sannun ka."

"Ina su Mimi?."

"Sun je gidan Yayan ku."

"Me ake yi?."

Mama ta kalle shi da mamaki tace, "Sai ana wani abun zasu je gidan Yayan su? Meyasa ka ke haka ne wai?."



Baice komai ba yayi shiru ya tashi ya shiga kitchen sai gashi da abinci yana yamutsa fuska san baya son macaroni amma gashi an dafa kuma jellop duk tayi sanyi ba yadda yake so ba.



Mama ta kalle shi yana ci yana taSa baki yace, "Bana son wannan abar Mummy."

"Sai ka ajjiye ai." Baice da yawa ba kuwa ya ajjiye ya kalli Farida yace, "dama zaki min girki da naji daWi." Hararar sa tayi

19 / 27