Chapter 14 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 27

39K to 42K   out of 80K words

ne da buri, kuma yau da gobe sai Allah."

"Haka ne Mama, amma lafiya tafi komai, yanzu gashi shan da kika yi na kwanaki shine ya jawo miki wannan ciwon gashi yau satin ki Waya a kwance." Mama tace, "za'a kiyaye in sha Allah. Manal fa?."



"Ita kuma nata ™onewa yayi alamun tana gushewa cin abubuwa sosai, duk da na bata magani zuwan ta na ™arshe amma da alama bata sha yadda ya kamata ba." Mama ta kalli inda take jin motsin Manal tace, "bata sha kam wallahi, nayi mata faWa sai tace in na sha kamar ya sha ne."



Huzaifa yayi murmushi yace, "zata dinga sha yanzu in sha Allah duk da bana son Wora ta a magani, amma za'a san yadda za'a yi. so nake likitan da yake kula da yazo in yaga kin samu Lafiya za'a iya sallamar ki." Mama tace, "Allah ya saka da alkhairi yayi albrarka."

"Amin. Sannan yace akwai maganin da za'a baki cikin ikon Allah in ana sha ganin ki zai dawo duk da ba duka ba amma za'a dinga ganin ko yaya ne, sannan za'a haWa da glasses shima don ya taimakawa ganin naki." Mama tayi murmushi tace, "Allah ya sa hakan." Huzaifa ya amsa da amin ya fita dan ya duba office Win Bebi dan ya ji shi shiru.



Yana tura ™ofar ta buWe alamun yazo kenan Bebi ya Wago ya kalle shi suka haWa ido sai Bebi ya cire glasses Win sa ya ajjiye Huzaifa ya shigo yace, "yau lafiya har azahar?." Ya faWa yana zama yana kallon sa.



Bebi yayi ™aramin tsaki yace, "raina ne a Sace wallahi, zan iya Satawa kowa rai shiyasa ban fito ba."

"Akan Rumana ne?."

"Nata mai sau™i ne akan wannan. Kasan Mujahid yana can yana neman Lubna wai auren ta yake so yayi." Huzaifa da mamaki ya kalle shi yace, "Mujahid Win?." ˜aramin tsaki Bebi yayi yace, "ban sani ba, ina faWa maka kana sake tambaya ta, bashi ba."



Huzaifa yace, "abin ne ya bani mamaki, da wacce manufa kenan yake son Lubna?."

"Da wacce manufa kuwa wacce ta wuce saboda ya Sata min? Kai ka manta abinda yace min a cikin office Win nan?."

"Ban manta ba Bebi, shine abin ya bani tsoro tabbas ba son Lubna yake ba da wani abun a zuciyar sa. Abinda ya kamata ka raba su ta Sangaren Lubna Win tunda ita kana da iko da ita."



Bebi ya kulle ido kawai bai ce komai ba dan Huzaifa bazai gane abinda yake ji a zuciyar sa ba Huzaifa yace, "Bebi ka bi komai a sannu babu abinda zai faru in sha Allah." Numfashi ya sauke ya mayar da glasses Win sa kafin Huzaifa yace, "kana ganin za'a iya discharging Win su Maman su Manal yau?." Ya Wan wara hannun sa kafin yace, "taya zan sani bayan kai ne suke ™ar™arshin ka? Duk abinda nake musu karanbani ne aikin ka ne" ya faWa a fusace.



Huzaifa yayi dariya dan daman yasan bazai amsa masa ba tunda ransa a Sace yake, kuma shi bai iya sarrafa Sacin rai kowa ma yasan hakan. Kuma in ran sa ya Saci na kowa ma sai ya Saci, kana yi masa abinda bai masa ba zai aikata maka abinda kai ma sai ranka ya Saci.



Dukan table Win yayi Huzaifa ya kalle shi sai kawai yaga ya tashi ya Wauki key Win mota ya fita. Yana fita ya fara tafiya bai ma kula da bayan sa ba yaji ance, "Dr." juyowa yayi sai suka haWa ido da Manal da take tsaye a bayan sa, yau kuma jan Hijjabai ne a jikin ta jalbab har ™asa tana murmushi tana kallon sa fuskar nan a haWe sosai fiye da kullum."



"What?." Ya faWa yana kallon ta. Sai jikin ta yayi sanyi godiya take son yi masa amma sai taga babu fuskar hakan. ˜aramin tsaki yayi yace, "me ya sa kika tsayar dani? What do you want?" a fusace yake maganar kai da ka ganshi kasan ransa a Sace yake sosai. Huzaifa ne ya fito yana jin abinda yake faWa mata kafin ma tayi magana ya bar wajan har ya Sace.



Kawai sai Manal ta fara hawaye Huzaifa ya kalle ya yace, "lafiya me ya faru?." Manal tace, "magana nayi masa kawai ina so mu gaisa na masa godiya akan abinda yayi mana, kuma Mama ce ta turo ni amma ina magana ya fara faWa yayi tafiyar sa." Yayi murmushi a ransa yana girmama shagwaSar yarinyar yace, "shine abin kuka?."

"Bana son faWa, kuma ya wula™anta ni."

"Kiyi ha™uri ran sane a Sace shiyasa kika ga haka."

"Daman shi ai kullum haka yake, na gode" ta faWa tana juyawa ta koma. Huzaifa yana dariya dan halin Bebi sai shi, bai san wani abu sarrafa Sacin rai ba, ko ba kai ka Sata masa rai ba to zai shafe ka.





Kai tsaye Bebi babban ofishin Hisba ya wuce, bai taSa zuwa ba hakan ya saka koda ya faka motar sai da yayi tambaya aka raka shi har ciki yace shi da babban su yake son magana, akace malam baya nan amma mataimakin sa yana nan aka raka shi har wajan sa yana zaune a office ya shiga.



Bayan sun gaisa da girmamawa Bebi yake cewa, "Suna na Adnan Mu'azzam na kawo ™orafi akan wani Kamal tsohon mijin Yayata da suka rabu da yara biyu, babu aure a tsakanin su saboda saki uku ya yi mata amma kuma yana bibiyar ta. Ina so a kira shi ayi tsakani a tsakanin su." Wanda yake faWawa yace, "meye dalilin da ya saka yake bibiyar ta?." Bebi ya masa bayan1n komai nan take yace a bada number Kamal aka kira shi aka bada umarnin yazo ofishin in yana da dama.



Nana Haleema>ΨBέ>Ψφή<Ψϋί



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



   ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 016*



A nan yayi sallar la'asar yana idawar Kamal yana zuwa, tare suka koma ciki dashi da shugaban da kuma Kamal dWin. Kamal sai kallon Bebi yake domin ya tabbatar shine ya kawo ™arar sa baice masa ba shima baice ba a haka suka shiga ciki suka zauna, aka gaisa da Kamal da Malam kafin yace, "Kaine Kamal?." Kamal yace, "™warai ni ne."

"Kasan wannan?" Ya faWa yana nuna masa Bebi ya kalli Bebi yace, "na san shi, ™anin tsohuwar matata ne."



Yace, "kaima kace tsohuwar matar ka amma yace kana bibiyar ta, kana so ka mayar da ita ne?." Kamal ya sauke numfashi cikin takaici yace, "A'a babu wannan a zuciyata. Saboda saki uku ne a tsakanina da ita."



Malam yace, "to meyasa ka ke bibiyar ta?." Kamal yace, "in dai naje wajan ta saboda yaran ta ne, wani lokacin maganar makarantar su ce, wani lokacin maganar rashin lafiya ko abinda yayi kama da haka. bayan wannan babu komai."

"Yara zaka iya haWa su da ita koda a waya ne, sannan zaka iya kai mata su ba lallai sai kun haWu ba. HaWuwar ma inda ba ko yaushe bace dan an haWu an gaisa ba komai tunda akwai zuri'a a tsakani, amma ko yaushe ba daidai bane, shaiWan zai iya shiga tsakanin ku a aikata abinda za'a yi dana sani." Kamal yayi shiru Malam yace, "Gashi da kan ka kace baka da ra'ayin mayar da ita, to meyasa kuma ka kasa rabuwa da ita?."



Kamal yace, "kamar yadda na faWa da farko maganar yara ce take kaini wajan ta."

"In maganar yara ce kaje har cikin gidan su a gaban kowa kayi mata maganar yaran ta wannan ba wani abun bane, ko ka kira ta a waya ko ka kira wani nata kamar shi Adnan Win. KeSewar ku ku biyu illa ce a gare ku, zaku dinga tuna rayuwar ku ya baya ne daga wannan lokaci kuma shaiWan zai ratso ta tsakiya sai wani abun kuma ya afku, ga saSon Allah ga dana sani."



Kamal yace, "za'a gyara in sha Allah." Adnan ya tari numfashi Malam  da yake niyar magana yace, "Malam ayi musu tsakani da ita, tunda babu aure a tsakani to ya jira in akwai rabon zata dawo wajan sa zata koma, ya daina bibiyar ta." Malam yayi murmushi tace, "kar ka damu, duk da itama naso ace tana wajan nan dan itace babbar mai laifi, da bata bada fuskar hakan ba da bai faru ba."

"In bai je inda take ba bazata saurare shi ba" Bebi ya faWa yana kallon Manal.



Malam yace, "A kiyaye Kamal, kodan saboda gujewa aikin dana sani." Kamal yace, "Gaskiya ne, na gode zan iya tafiya?." Ya amsa masa ya tashi ya fita shi kam Adnan godiya yayi masa sannan ya tashi ya fito.



Yana zuwa gaban motar sa yana niyar shiga yaji Kamal yace, "Wai kai me ka Wauki kan ka ne? Mahaifin Maryam?." Bebi ya juyo yana kallon sa yace, "zaka iya kira na da hakan ba laifi bane."

"Kana ganin wai hakan da ka yi  shikenan ka raba ni da Maryam?."

"Ai hukuma gaba take da kowa, in kana ganin kai kana gaba da ita ne ka sake maimaita abinda kayi. Wallahi nan gaba sojoji zan saka su yi maka dukan da zaka kasa tashi."



Kamal yayi murmushi yace, "ni ka wula™anta Bebi har ka kawo ™arata wajan nan. Ka jira abinda zai faru sai na tartarsa maka zuciya wallahi, badan kai mai kishin ΄an uwan ka ba? Na tabbatar Maryam zata baka kunya wacce baka yi tunanin jin ta nan kusa ba. Kuma ina so ka sani bazan nemi wata hanyar da zan gyara auren mu da ita ba, kuma bazan rabu da ita ba kayi abinda zaka yi."



Adnan yace, "zaka ga abinda zan yi kuwa, domin ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, abinda nake so shi nake aikatawa kuma shi nake aiwatarwa akan kowa koda shi baya so. Nafi ™arfin ka tarwatsa min zuciya Kamal, sai dai ni na tsarwata taka. Rashin ilimin addini ne yake sakawa namiji ya bibiyi wacce ba matar  sa ba, ina baka shawara ka koma islamiyya domin ya™i da jahilci domin yana damun ka sosai. Shine ya ke saka ka aikata hakan kan ganin hakan daidai ne, baka san tsabar jahilici da rashin sanin addini ne ya saka ka ke aikata hakan ba" ya faWa yana nuna shi da key na mota kafin ya juya ya buWe motar ya shiga yana ya fita daga cikin wajan.



Da kallo Kamal ya bishi zuciyar sa na zafin kiran sa jahili da yayi, yayi ™wafa shima ya shiga mota lokaci yayi da zai tabbatarwa da Bebi shi zai tarwatsa masa zuciya, zai ga aikin jahilai kuwa, zai yi dana sanin kiran sa jahili da ya yi.



Mubeena ce ta fito daga banWaki Bily ta kalle ta taga ta zauna tana cigaba da danna waya tans murmushi  Bily tace, "Wai da wa kike chart da kika kasa tashi kiyi sallah?." Ta kalle ta tace, "my future husband mana." Ta faWa tana Waga wayar ta yiwa kanta hoto ta kalli hoton tayi murmushi ta cigaba da danna wayar.



Bily tace, "yanzu kuma kin fara jin daWin zancen banzan da yake miki kema kenan?."

"Na fahimci soyayya ce hakan, yanzu ma hoton sa ya tura min babu riga amma view once ne" ta faWa  tana dariya alamun abin bai dame ta ba. Bily tayi dariya tace, "Mubeena ki kiyayi wannan tashon fa, wallahi zai iya saka ki dana sani."



Mubeena  ta kalle ta da mamaki tace, "na rasa yaushe kika canja Bily, Wai duk meye wannan Win? Bafa wani abun yake min ba kawai chart ne, kuma kin san wayewa ce ba wani abun ba."

"Sexy chart din ne wayewa?."

"Ya akayi kika san sexy chart ne?."

"Saboda naga abinda ya rubuto miki a notifications yanzu, shi ko kunya baya ji da ΄a΄an sa da jikokin sa ya tsaya yana wannan shirmen dom Allah?."



Mubeena tace, "kinga Bily don Allah ya isa haka." Bily tace, "bai isa ba Mubeena, sai na faWa miki gaskiya. Dan ina biye miki ina cewa baki dace da haihuwar gidan ku ba hakan yana nufin na biye miki ki fara iskanci ba." Da sauri ta kalle ta tace, "ni kike ceawa ΄ar iska Bily?."

"Ita kike ™o™arin komawa ai Mubeena." Mubeena tunawa a gidan su Bily take sai tayi sanyi tace, "kinga ki ™yale ni kawai ni yunwa ma nake ji" ta faWa tana fita ta bar mata Wakin, Bily ta bita da kallo tana tunanin lokaci yayi da zata raba garo da Mubeena domin tafi ™'arfin ta a yanzu.





Bebi yana komawa asibiti baban Yayan su yayi masa yace in ya tashi daga aiki yazo gida ya same shi ya amsa ya kashe wayar ya ajjiye ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa ne ya masa waya ya Wauka ya saka a speaker yace, "ina ji."

"Nayi discharging Maman Manal suna so su ganka su yi maka godiya abubuwan da suka faru, ka dawo ne?."

"Godiyar me za'a yi min? Me nayi kuma?."

"Kaga Bebi don Allah ka nutsu, Wai kai Sacin ranka kowa sai ya shafa? Meye haka ne wai?."



"Mtsww! To me nayi musu ne? Naga aikina ne ko? Dan na yi aikina sai an yi min godiya?. Bana son takura suj je kawai ai nasan sun gode." Huzaifa yace, "sun ce baza su tafi ba sai sun ganka, sannan akwai maganin da kace min zaka rubuta musu, meyasa kake haka ne wai?." Ya sake jin takaici a fusace yace, "indai magani ne zan turo maka yanzu kaje ka siya musu. Bana son magana ka sani in raina yana a Sace,

domin duk abinda yazo baki na zan faWa musu ne, don Allah ka ™yale ni kawai bana son haWuwa da kowa."



Knocking ake yi hakan ya saka shi datse kiran yace, "yes." Aka buWe ™ofar aka shiga ya hango Manal ta shigo ya dauke kai daga kallon dan ji yayi kan sa ya sara haka kawai bai san dalili ba, ta kalle shi a nutse tace, "Dr zamu tafi, Allah ya saka da alkhairi Mun gode."

"Amin" ya amsa a ta™aice ya cigaba da abinda yake yi. A tsorace take itama tace, "Dr Huzaifa yace zaka bani takardar magani...." A fusace ya katse ta yace, "kije ki same shi zai naki, bana son magana bana son takura kije kawai!" Ya faWa yana nuna mata hanyar fita.



Sai da ta tsorata jin irin tsawar da yayi mata tayi baya tana kallon sa tace, "Allah ya baka ha™uri, baza mu iya tafiya bane ban maka godiya ba ka ceci ran mahaifiyarta wacce bani da kamar ta, koda dukana zaka yi bazan tafi ba sai na tabbatar na gode maka."



Shiru yayi baice mata komai ba, amma ji yake kamar ya tashi ya tsinke ta da marin da zata daina gani, ya lura shegiyar maganar ta inda waje Waya suke zai iya sakawa ya mata dukan tsiya, ta juya tana tafiya ido ya ciko da hawaye. Da wata likita mace suka haWu  tana fitowa tana shiga ita kuma ta wuce wajan Dr Huzaifa ta shiga da sallama ya amsa yana murmushi domin nutsuwar ta na burge shi sosai yace, "Manal zaku tafi ko?." Ta goge idon ta  zata yi magana yace, "ya dai? Ko jikin Maman ne?."

"A'a babu komai."

"FaWa min mana, me ya faru kike goge hawaye?."



"naje wajan Dr nan abokin ka mai glasses na yi masa godiya shine yake ya faWa kamar zai dake ni." Yayi murmushi yace, "Kar ki damu ransa ne a Sace na faWa miki,  haka yake in ransa ya Saci baya son magana. Ga maganin ya bani duk zan baki in har tana sha komai bata zai dawo daidai hatta idanun ta zasu iya gani wani lokacin. Kema kuma zan baki naki ki tabbatar kina sha saboda ya daidai miki sugar jikin ki."



Ido ta goge ta amsa yayi murmushi sai ya kalli maganin ya kalle ta yace, "ki jira ni a inda kuke zama zan je na kawo miki kafin ku tafi." Kafin tayi magana aka shigo taga likitan da suka haWu  da ita a wancan office Win tace, "Huzaifa meyake damun Adnan yau?."



"Kema ya koro ki Win ko?" Ya faWa yana dariya.

"Inda kaga zai min duka ma kuwa" ta faWa  tana dariya  itama yace, "ran sane a Sace kawai shiyasa." Ta girgiza kai tace, "lallai kam naga alama" ta faWa tana fita shi kuma yacewa Manal su je suka fito ta koma Wakin su shi kuma ya fita.



Da maganin ya dawo ya shiga har ciki ya basu suka dinga masa godiya har Baba yace babu komai ai yiwa kaine. Bayan ya fita suma suka fita Manal na ri™e da hannun Mama Baba ya ri™e kayan suka fita harabar asibitin. Bebi yana tsaye yana kallon su ta window sai a lokacin ya tuna abinda ma yayi mata. Yayi tsaki yana kallon su har suka fita daga harabar asibitin daga nan ya daina ganin su.



Yana nan tsaye Huzaifa ya shigo ganin ya juya baya yana kallon taga yace, "abinda kake yi ba daidai bane ba Bebi, bai kamata Sacin ranka ya dinga shafar wanda bashi ne ya maka ba. Meye laifin yarinyar nan da tazo maka godiya? Don Allah?."



Bebi ya juyo yana kallon sa da mamaki yace, "wai na tambaye ka, Yarinyar nan aure ta zakayi ne?."

"In ma auren nata zanyi ai ba laifi bane ba

14 / 27