Chapter 27 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 27

78K to 80K   out of 80K words

kawai taga an turo mata hoto a ™asan hoton an rubuta, _Ko dan saboda wannan ki amsa wayata Maryam._ gaban ta yayi mugun haWuwa ganin hoton ta babu suttura irin wanda take tura masa a lokacin da take gidan sa matsayin soyayya.



Jikin ta rawa yake sosai, hankalin ta ya kai ™arshe wajan tashi kallon hotun take yi cikin kiWima da nadama mara amfani. yana kiran wayar hannu na rawa ta Wauka daga can Sangaren yace, "har ni ina miki waya ki daina Wauka? Na baki ha™uri meyasa baza ki ha™ura ba Maryam?." Maryam tace, "Kamal kace min ka goge hotunan nan."



"Akan me za'a goge bayan gashi yayi min amfani yanzu?."

"Kamal ya kamata ace ka goge shi saboda ni ba matar ka bace ba. Barin tsairicina a wayar ka haram ne."

"Zan goge, amma Ina so ki fito anjima ina so mu yi magana."

"Bazan sake zuwa inda kake ba, na daina zuwa inda ka ke, baza ka kuma ganina ba ko me zai faru." Yayi dariya yace, "Maryam kenan, kina so kice kin daina ganina?."

"Na daina ganin ka, na kuma daina zuwa inda ka ke, kuma ka fita daga rayuwata."



"Ni kuma wallahi yanzu na fara jin daWin rayuwa dake, a baya ji nake kamar ma ban taSa wata mu'amala dake ba kamar yadda ya faru yanzu. Maryam ki fito mu haWu yanzu in ba haka ba wallahil azim zan Wora hoton nan na ki a Facebook da tiktok." Gaban ta ya faWi matu™a, ta wara idanu hannun ta yana kan ™irjin ta saboda rashin hankali. Murya a sar™e tace, "me ka ce?." Yayi dariya yace, "ai kin ji abinda nace, ko ban saka hoton fuskar ki ba zan saka na jikin ki, ke kina gani kin san jikin ki ne. Kuma zai zaga ko Ina babu inda bazai je ba ke kin san yadda hoton tsaraici yake zaga ko ina, Balle ma da fuskar ki zan Wora dan babu amfanin kullewa."



Kasa magana tayi shiru hankalin ta ya tashi sosai ta rasa ma abinda zata ce, gaban ta faWuwa yake yi nadama ta mamaye ta lokaci Waya har zazzaSi take ji. Kamal ya katse mata tunani yace, "in kin shirya ganin hoton ki a social media kar ki fito Maryam, in kuma baki shirya ba zan miki text na inda zamu haWu ki tabbatar kin je wajan. in ba haka ba wallahi!, wallahi!!, wallahi!!, kin ji uku ko?, sai na watsa hoton nan media, ke kin san ba iya hoto nake dasu ba har videos ina dasu. Videos Win ma sun fi komai kyaun gani, saboda....." sai kuma yayi dariya yace, "Na san ma kin sani, Sai na jiki" yana faWa ya katse wayar. FaWuwa tayi a wajan jagwab hankalin ta ya kai maatu™a wajan tashi, me hakan yake nufi...? kenan blackmailing Win ta Kamal yake da hotunan tsaraicin ta wanda take tura masa a zaman auren su ko kuma me? Yanzu ya zata yi? Dama zata Wauka ko haggu?.



Zina zata je ta aikata dashi saboda kar ya watsa hotunan ta?, in kuma bata je ba ya watsa hotunan ta da wanne ido zata kalli yaran ta guda biyu?, da wanne ido zata kalli duniya ma gabaWaya. Ta daki katifar gado ta dafe kai a bayyane tace, "ya zan yi ni Maryam, ya zanyi?. Aikata zina ko kuma yaWa hotunan tsaraicina?."





          Bebi ya fito daga cikin asibiti yana shiga mota Huzaifa ya buWe gaba ya shiga, Bebi ya kalle shi Huzaifa yace, "ka ajjiye ni a gida please, motata na kai ta gyara sai gobe zan Wauko." Kana kallon fuskar Bebi kansa ransa a Sace yake sosai yace, "sai akace maka kuma hanyar da zaka yi zan yi ni?."

"Ko ba nan zaka yi ba kaje duk inda zaka je ka sauke ni." ˜aramin tsaki yayi ya ja motar ya bar asibitin zuciyar da zafi take akan ™aryar da Manal tayi masa.



Suna zuwa bakin layin gidan su Manal ya tsaya ya Wauki waya yana kiran ta, Huzaifa yayi dariya yace, "sai kace min zance kazo ai, daman kana zuwa da ™ananun kaya ne?." Bai kula shi ba ya kira ta a lokacin tana kwance ciwon marar da take fama dashi duk wata ya dame ta sai kuka take, gashi ita in bata da lafiya dole sai ta ji ta a jikin Mama take samun sau™i-sau™i, amma bata son damu Mama saboda bata da lafiya sai ta fito tsakar g1da ta zauna.



Tana wannan kukan kiran sa ya shigo ta duba kamar baza ta Wauka ba sai kuma ta Wauka ta saka a kunnen yace, "Kizo Ina bakin layin ki sa™o zan baki." Yana gama faWa ya kashe wayar bai jira yaji abinda zata ce masa ba. Manaltabi wayar da kallo tana mamaki, bai taSa cewa tazo bakin layin su ba sai yau, hakan ya saka ta daure ta tashi tunda ciwon bai yi zafi ba ta shiga wajan Mama tace, "Mama wai Dr Adnan ne ya kira ni nazo bakin layin nan zai bani sa™o."

"Sa™o kuma Manal? Meyasa bazai shigo ba?."

"Ban sani ba wallahi."

"To jeki, amma kar ki jima dai kinga dare yayi sallar i'sha za'a yi" ta amsa da to ta saka Hijjabai ta fita zuwa bakin layin.



Hango ta Huzaifa yayi sai ya kalle shi yace, "Wai daman a mota ku ke zance ne Bebi?, gaskiya hakan ba daidai bane tunda kai ma baka so a yi haka da ™annen ka. Ban taSa ganin ka bar su suna zance a mota ba, kaima bai kamata ka yi ba." Bebi ya gaji da maganar Huzaifa a ™ufule yace, "ya ishe ka Malam, in baza ka zauna ba ka fita ban nemi zaman ka ba ko?."



Kallon sa Huzaifa yayi ganin da gaske ransa a Sace yake sai yace, "bazan fita ba sai mun gaisa da ™anwata. Kuma haka zata ™araso ka wani ci magani kamar wani boss?." Banza yayi masa ta ™araso gaban motar ta gane motar sa ce amma bata ganshi a tsaye a bakin motar ba. Sai da ta ™araso sannan ya sauke glass ya kalle yace, "zaki iya shigowa?." Ta girgiza kai alamun A'a ya buWe motar ya fito yana kallon wajan da babu jama'a sosai daman layin nasu bashi da mutane.



A jikin motar ya tsaya yana kallon ta itama haka yadda fuskar sa take haka ta ta fuskar take dan ciwon da yake damun ta ba kaWan bane, jira take taji me zai ce ko mai zai bata amma yayi shiru. Ya kalle ta sosai yace, "abinda kika yi kin kyauta kenan Manal?." Ta kalle shi alamun me tayi yace, "na faWa miki tun farko bana son ™arya meyasa kika min ™arya?."



"Wacce ™arya nayi maka?" Ta faWa tana kallon sa da mamaki.

"Meyasa baki faWa min Baba ba ™anin mahaifin ki bane?, meyasa baki faWa min mahaifin ki bai rasu ba?, meyasa baki faWa min aura ne kawai tsakanin Mama da Baba amma babu ala™a ta jini a tsakanin ku?." Gaban Manal ya faWi sosai ya kalle shi tace, "me kake nufi?."

"Kin san me nake nufi, meye amfanin Soyewar?."

"Dakata mana, ni ban fahimci akan abinda kake magana ba" ta faWa dan taga da faWa yake mata magana kamar wanda ya haife ta.



"Kin san dukkan abinda yake faruwa, na faWa miki ™arya tana sakawa mutum ya fita daga raina lokaci Waya amma baki ji ba. Sannan meyasa baki faWa min yayar ki ba makaranta take zuwa yawo take tafiya?." Da sauri Manal ta kalle shi dan ta gane me yake nufi da kalmar yawo Win da ya ce, Ya wara ido aka fuskar ta yace, "eh!. Shi kuma wanda kika ce min yayan ki ne ashe saurayin ki ne, ke a ganin ki wannan daidai ne?, a ganin ki kin kyauta?."



Ran Manal itama ya Saci sosai musamman kiran Mubeena da yayi wai tana yawo, kalmar tafi komai ™ina mata rai hakan ya saka a fusace tace, "duk wannan maganar da ka ke akan ban faWa maka abinda ban sani ba shine ka ke yi?."

"Amma na faWa miki ai bana son ™arya,™arya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina na faWa miki wannan tun farko ba yanzu ba" ya faWa cikin fusata sosai yana kallon ta kamar zai dake ta.



A wuya itama take jin ta, daman ga ciwo ga kuwa Sacin ran da yake faWa mata ya sake tunzura zuciyar ta, katse ta yace, "I'm higly disappointed, banyi wannan tunanin daga wajan ki ba."



"Duk wannan maganar da kake yi kana so kace ka fasa aurena kenan?, gashi kana maimaita min ™arya tana sakawa abu ya fita daga raina kenan na fita. To ka fasa mana Adnan sai meye in ka fasa?, fasawar ka bazai hana wani yazo yace zai aure ni ba. sannan kar ka sake kuskuren cewa Yayata tana yawo, Yayata bata yawo duk wanda ya faWa maka ™arya yake yi. Dan kawai kana son ka ce ka fasa aurena ka faWa kan ka tsaye ba sai kazo kana min maganganun da babu su a cikin rayuwata ba. Ka fasa auren sai me? Waye ya ragu ni ko kai?." katse ta yayi ta hanyar cewa,



"Ai bazan tsaya a gaban ki ina miki ™aya ba dan na burge ki ko dan wani dalili nawa, ya kamata ki san waye ni." Ganin mutane suna wucewa ana tafiya masallaci ya saka Manal danne ciwon da take ji tace, "ka furta ka fasa aurena sai me waii? Daman ai an gargaWe ni na™i ji nace ba haka ka ke ba, ka fasa auren nawa wannan ba komai bane. Wallahi ban da kai Win ne ina ganin girman ka saboda abinda ka yiwa mahaifiyata wallahi da yanzu ka fara dana sanin sanin wacece Manal a duniya, ka turo a karSar maka kuWin auren ka da ka kawo, ko kai baka fasa ba ni Fatima bazan aure ka ba!. Adnan ka je ka ssmu shugabar masu gaskiya ka aura, ka bar ma™aryaciya mai Soye maka abubuwan da ya kamata ace ka sani. Ko baka furta ba na fahimce ka, to na hutar da kai furtawar, ni Fatima Manal na fasa auren ka, ba shikenan ba?" tana faWar hakan ta juya ta bar shi a wajen dan ciwon marar ya dame ta sosai.



Da kallo ya bita zuciyar sa na bugawa sosai, Sacin ransa ya ninka na baya sau babu adadi. kamar shi tayi masa laifi yazo yana faWa ta dinga yi masa wannan faWan har da tafiya ta bar shi kamar wani sa'an ta?. Tsaki yayi yana ji a zuciyar sa dole ma ya fasa auren nata!.



End of book 1.



_Tofa ana dara ga dare yayi, ya ku ke ganin salon zai kasance nan gaba?. Shin mahaifin Adnan zai samu galaba akan Mubeena?, to in hakan ya faru wanne irin abun kunya za'a tafka?. Hmm da gaske auren Manal da Adnan babu shi ko kuwa zasu shirya nan gaba?, ya matsayin Maryam da Kamal?, zata amince ta sake aikata zina daahi saboda hotunan tsaraicin ta ko kuwa zata ™i amince shi kuma yayi posting?. Ya batun Lubna, shin Mujahid zai aure ta  bayan ya raba ta da budurcin ta?, anya lubna bata yi gangancin amincewa da Mujahid ba?. To wai wacece Maman Manal ne?, ina mahaifin su Manal yake?, Waye shi?, yana da rai ko ya mutu?. Ya batun Rumana da Adnan? Auren nasu zai yu ko kuwa zai sake bijirewa Mama?. Hmmm kwamachala Win kenan._=ĜƒÜ<Ĝüß=ĜŜ



_Duka amsoshin wannan tambayoyi suna cikin book 2&3, akwai soyayya, akwai taSa zuciya, akwwi nadama, akwai dan sani, akwai zallan kishi a cikin littafin BAYA DA ˜URA BOOK 2&3. Zai fara zuwa 20/1/2025 in sha Allah. promo is over za'a biya asalin kuWin littafin. an fara yin payment tuni na book 2&3 regular akan naira 500 kacal. Akwai vip group shi kuma naira 1000 ne. Ga masu bu™ata zasu yi min magana a kan wannan number 09030398006 but only on whatsapp. KuWi kawai zamu karSa banda katin waya!._



Nana Haleema>ĜBŬd'ŝ

27 / 27