Chapter 6 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 27

15K to 18K   out of 80K words

sani ba. Surayya tace,  amma dai tana da ciwon sugar.



Kai ya girgiza ya tashi ya shiga ciki ba jimawa ya dawo ya sake tsugunawa yana auna sugar ta kafin ya ya buWe bakin ta ya saka wani tablet a ™asan harshen ta ya kalli mutumin yace, "ku canja asibiti kawai zai fi." Surayya tace, "bamu san inda zamu je ba, ko kuWin mota babu a hannun mu." Mutumin Ya sauke numfashi ya kalli Manal yace,  kar ki damu zan taimaka miki in sha Allah. Kuka take kamar zai sake magana sai ya fasa ya kalli wani namiji da yake tsaye ya taimaka masa suka fita da Mama su kuma suka bi bayan sa da gudu aka saka mama A mota suma yace su shiga suka tafi.



Sai da suka tafi ya kalli Manal da take baya tana kuka yace, "kar ki damu zata samu sauki in sha Allah. Akwai asibitin da zamu je yanzu za a kula da iya sosai. Duk da yanayin garin a cike yake amma haka yake gudu dan ya isa asibitin, nan da nan suka isa ya faka motar ya budWe ya fito da sauri ya shiga ciki sai gashi an fito da gado aka Wora mana a kai suka shiga su kuka suka bi bayan sa.



Wani Waki aka shiga da Maman tsabar ruWewa zasu shi shiga aka dakatar dasu suka tsaya bai jima sosai ba ya dawo yana nan tsaye wani nurse ya fito ya kalle su yace, "Ya akayi aka bari sugar Win ta ya hau da yawa haka? Magani ta daina sha ko me?." Manal hawaye ya zubo mata tace, "Tunda maganin ya ™are ta daina sha, kuma kwana biyu tana yawan sham shayi da sugar." Ya girgiza kai yace, "sugar tane ya hau sosai, sai kuma zuciyar ta da bata bugawa yadda ya kamata.



Mutumin ya kalli nurse din yace,  yanzu ya ake ciki likita? Ya jikin Maman?. Ya sauke numfashi yace,  yanzu dai mun samu komai ya daidaita, Amma akwai likitan da zai zo anjima zai duba yanayin zuciyar ta ta in sha Allah komai zai zo da sau™i. Tayi wani gwaji ne na zuciya cikin kwanakin nan?. Manal ta daga kai tace,  eh tayi.



Nurse din tace,  yana ina?.

 Wallahi Mun bar shi a gida.

 To a kawo kafin zuwan likitan. Manal ta girgiza kai tana kallon Surayya da wanda ya taimake su.



Ta kalli Surayya tace, "™awata ko zaki je ki Wauko? Wallahi hankalina bazai kwanta na bar Mama a nan bana wajan ba." Surayya tace, "kar ki damu Milky, zanje na Wauko, a ina suke?."

"Suna nan cikin jakata ta islamiyya."

"Shikenan zan je, kinga ko kulle gidan ma bamu yi ba Allah yasa Mama ta kulle. Amma bani da ™udim motar tafiya Manal."



Manal tace, "kuma akwai kuWi a jakar Baba ya bani jiya suna ki Wauko su. Wanda ya taimake su yana jin ta sai yayi murmushi yadda take kuka saboda mahaifiyar ta abin burge shi, da alama duk abinda ya nema saboda babar ta zata yi. yace, "ga dubu biyu kije ki dawo da sauri, kin ga lokacin sallar juma a ya kusa. Surayya ta kalli kuWin da yake mi™a mata ta kalli Manal sai Manal ta girgiza mata kai yayi murmushi yace, "karSi kar ki damu." Hannun a rawa ta karSa tace,  mun gode, Milky sai na dawo ta faWa tana yim gaba.



Manal ta kalli mutumin da bata san shi ba, bata taSa ganin sa ba balle sunan sa tace, "bawan Allah na gode Allah yasa maka da alkhairi ya baka abinda ka ke so. yayi murmushi yace, "bani zaki godewa ba, akwai wanda ya saka nayi miki shi zaki yiwa godiya. Shine yace duk abinda ake bu™ata nayi miki, yana tausayin ki sosai. Manal tace, "yana ina?." Yayi murmushi yace, "anjima zan zo na kai ki wajan sa, yanzu ya tafi saboda sallar juma a, amma zuwa yamma zai dawo sai ki masa godia har gida. Kai ta girgiza tace,  to sai kazo Win. Yayi murmushi ya tafi ta samu waje ta zauna.



Ba jimawa ya dawo da ledar abinci ya bata ta sake yin godiya ya tafi. Sai kuma gaban ta ya faWi sosai tsoro ya mamaye mata zuciya, a zabure ta mi™e ta le™a Wakin da Mama take ta tagar dake wajan ta hango Mama a kwance tana bacci cikin Wakin mai a.c.



"Mai na aikata ne ni Manal? Waye wannan? Meyasa ma na amince dashi har aka kawo ni nan?. Waye shi? In Mama ta tambaye ni nace mata meye?. Ta wara ido waje tace, "in aka cutar dani ko Mama fa?."



"Manal!." A firgoce ta juya jin an kira sunan ta kuma muryar namiji sai hakan ya bata mamaki ta kalli wajan, Dr Huzaifa ta gani a tsaye yana mata murmushi yace,  me kike yi a nan?." Manal ta juya tana kallon sa tace, "ina kwana?."

"Lafiya lau, ohhh! Mana ce aka kawo yanzu ko?. Haba nidai ina ta tunanin nasan fuskar ashe Maman ki ce. Ya akayi kika bari sugar ta ya hau sosai haka?."

"Bata Shan magani kuma kwana biyu har sugar take sha."

"Zata samu sau™i in sha Allah, ki daina kuka."



Ta goge idanun ta yace, "waye ya kawo ku nan asibitin?." Manal ta kalle shi tace, "wani ne ya taimaka mana wallahi, ban san ma nan zai kawo mu ba a can Emergency ance babu gado aka ™i kula Mama" ta faWa tana kuka sosai. Dr Huzaifa yace, "kar ki damu zata samu lafiya in sha Allah. Ki zauna nace aje a kawo gwajin zuciyar zuwa anjima likitan da zai ga sakamakon zai zo."



Kafin tayi magana ya kuma cewa, "Jiya da nace kije wajan sa baku je ba kenan?."

"Naje, tun jiyan Mama babu lafiya sai naje na kai masa dan ya rubuta magani shine ya kore ni." Yayi murmushi yace, "dole ya kore ki ai, kin taSa ganin anje ganin likita babu mai jin ciwon?."



Tayi shiru bata ce komai ya sake cewa, "zata samu lafiya in sha Allah." Yana faWa ya bar wajan ta koma ta zauna, sai a lokacin taji sanyi a ranta ganin likitan da ta sani wanda suke wasa da dariya kamar ba likita ba in suka je wajan sa. Ba jimawa sosai Surayya ta dawo amma tayi wanka ta canja kaya a nan suka yi sallar azahar suna zaune suna jiran tsammani.



Ba jimawa Dr Adnan yazo asibitin kai tsaye office ya wuce yana zama Huzaifa ya shiga yace masa, "daman kai nake jira wallahi, duba min wannan result Win" ya faWa yana bashi takardar, bai musu ba ya karSa yana dubawa ya kalle shi yace, "ina patient Win?."

"Anyi admitting Win ta, tana nan emergency." Adnan yace, "ciwon ya Wan yi ™arfi kaWan gaskiya, tana bu™atar magani masu kyau sosai. Wanne magani take sha?.



Huzaifa yace,  bani dasu a yanzu.

 Okay, tana da bu™atar kula dai sosai, in aka cigaba da haka ciwon wuce yanzu.



Huzaifa yace, "patient Wina ce duk two weeks suke zuwa wajena itace “arta, itama “at ciwon ne da ita amma na uwar yafi yin worst tunda kaga ya taSa mata ido yanzu ko gani bata yi sosai, ga zuciya ma."





"Subahanallahi, haka ciwon naku yake Sarna?."

"Yanzu kazo muje ka ganta don Allah, ni kaina ya kulle wallahi na rasa ma abinda zan mata.."

"To kai da kake endologisy baka iya komai ba ina ga ni cardiologist? Me zan iya?."

"Experience Winka akan zuciya ne kana da abinda zaka iya."

"To kai kuma akan ciwon ne gabaWaya, kamar ka fini sanin aikin ka."



Huzaifa yace, "Nidai kazo muje ka ganta kawai don Allah." Ba musu ya tashi suka fita bai ma kula da Manal ba ya wuce zuwa Wakin ba jimawa suka fito Huzaifa ya tsaya ya kalli Manal tace, "kar ki damu Manal, ga wanda zai kula da lamarin zuciyar Mama nan, kar ki damu." Kallon Adnan tayi suka haWa ido ta glasses Win Idon sa, ita ta gane shi amma shi bai gane ta ba sai ta sauke kai ™asa bata ce komai ba, shi kuma a zuciyar sa yana ayyana ita kuma ko gaisuwa bata iya ba.



Ya wuce ya shiga office ya samu Hamza a zaune a ciki bai kula shi ba ya kalli Huzaifa Adnan yace, "Huzaifa meye ala™ar ka dasu?." Huzaifa da yake bayan sa yace, "babu komai wallahi, patients Wina ne kawai kamar yadda nace maka."

"To yayi, tana bu™atar hutu a ™alla one week to ten days a nan, sannan akwai abinda yake damun ta wanda yake jawo mata ciwon, in aka yi bincike sosai babu lallai diabetes ya kawo shi.



Hamza cikin tsokana yace, "taya ka gane?." Ya Harare shi yace, "iya pulse Win ka zan ri™e zan fahimci yanayin heart beat Win ka, in stress ne ya saka ta bugawar zan gane, in gudu kayi zan gane, in damuwa ce zan gane ka fahimta?. Nan ba office Win kallon matan mutane bane, i am cardiologist.



Hamza yayi dake shi yace, "wallahi zan baka amsa a lokacin da matar ka zata haihu a hannuna." Bebi ya taSe baki yace, "Allah ya kiyaye, ni matata ta haihu a wajan ka& ? ai har abada wallahi." Suka yi dariya a tare banda Bebi da yake sake kallon sakamakon gwajin Maman Manal.



Sai ya ajjiye takardar ya furzar da iska yace, "wa kuka sani a police station? Akwai wanda na ke so a kama min." Huzaifa ya ce, "to me yayi maka kuma?."

"Mijin Maryam nake so a kama, in ba kama shi nayi ba bazai daina bibiyar ta ba."



Hamza yace, "wannan matsalar fa daga Maryam take ba daga shi ba Bebi, da bata bashi dama da fuskar zuwa wajan ta bayan ya sake ta ba wallahi da bazai zo ba." Huzaifa yace, "wannan gaskiya ne abinda kake faWa, itace ta bayar da dama tun farkon rabuwar su da bata bada dama ba da hakan bata kasance ba.



"Shiyasa nake so ayi mana iyaka dashi, tunda babu ragowar igiyar auren sa a kanta a kan me zai dinga bibiyar ta? Tunda dai babu damar mayar da ita wallahi kar ya sake sauraron ta. Jiya da daddare bayan na koma na ganshi da ita mota, me ake a motar? Meye ala™ar su da har zata dinga shiga motar sa?." Hamza yace, "wannan ita zaka tambaya, kuma ira zaka jawa kunne ba wani ba." Ya girgiza kai kawai baice komai ba suma basu sake ce masa komai ba suka fita shima ya fita.



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



©žNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11





https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp



*BOOK 1*

*Page 008*





A Sangaren su Manal yunwa Surayya take ji gashi a zaune basu ci komai ba ta kalli Manal tace, "Milky Yunwa nake ji sosai." Manal tace, "a kuWin da kika Wauko kije ki siyi wani abun Kkici."

"Kefe Milky? Baki karya bafa."

"Bazan iya cin komai ba in Mama bata farka ba." Wayar Surayya tayi ™ara ganin sunan Maman ta sai tace, "bara naje na shigo da Mama." Fita tayi ba jimawa siai gasu da Mama har da abinci ta kawo musu Mama tace, "ya jikin Maman taki Manal?."



Manal tace, "tana nan dai kwance."

"Kin san wanda ya kawo ku nan ne? Surayya ta faWa min komai."

"Wallahi Mama ban san shi ba, ni kaina gabana faWuwa yake yi sosai. A lokacin a ruWe nake sai yanzu na nutsu na fahimci nayi kuskure.

"Hankalin ki baya jikin ki a lokacin ne shiyasa Manal, amma babu komai Allah yana gani dan mahaifiyar ki kika yi bazai bari ki cutu ba." Ta Waga kai alamun haka ne Mama tace, "Mubeena bata zo ba?." Manal ta taSe baki kawai bata ce komai ba dan ita ta manta ma da wata Mubeena.



Ganin haka dai Mama tace, "ga abinci nan ki ci bana son musu dan nasan yunwa kike ji. Akwai salad a ciki sai ki zuba ki ci. Jin abinda tace ya saka dole ta karSi abincin da Surayya ta zuba mata tana ci da™yar. Manal tace,  ni na manta, wanda ya kawo mu ya kawo mana abinci ta faWa tana jawo ledar ta buWe.



Mama na wajan har akayi magriba ta kalli Manal tace, "ki kira Mubeena a waya tazo ta taya ki zama a nan." Da to kawai ta amsa dan ba yi zatayi ba dan Sata lokacin ta zatayi indai Mubeena ce ba zuwa zatayi ba.



Ba jimawa suka tafi Manal tana ta godiya harda kuka suka tafi ta dawo ta zauna tare da yin shiru.

"Sannu Manal." Ta Wago ganin wanda ya taimaka mata sai tayi murmushin tace, "Yauwa."

"Ya jikin Maman?."

"Da sau™i, bacci ma take."

"Haka ake so sosai Allah ya bata Lafiya."

"Amin. Na gode sosai." Yayi murmushi yace, "ki kula da ita zuwa gobe zan zo sai muje wajan wanda ya taimaka miki." Manal ta Waga kai tace, "to Allah ya kaimu, na gode sosai."



Murmushi yayi ya tashi ya bar wajan ya tsaya bayan ya bar wajan tare da Waukar waya ya saka a kunne yace, "Ranka ya daWe tana hannu yanzu, zuwa nan da gobe duk abinda nace tayi zatayi domin akwai target Wina a kan ta, shiyasa na zaSi wannan asibitin saboda yana da tsada sosai."



Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "zuwa gobe zan kawo ta." Shiru ya sake yi kafin yace, "Allah ya taimaki uban g1dana, wannan ai abu ne mai sau™i, Tunda ka ganta kaji tayi maka ai an wuce wajan. Ba da ™arfi zamu yi amfani ba da kanta zata amince saboda bata da mafita, in ta™i ta kwana a hannun yan sanda."



Dariya yayi mai sauti kafin ya kashe wayar ya juya yana hango Manal da ke zaune ya girgiza kai yace, "ba ™arya yarinyar akwai kyau, iya wannna farin nata ko shi kaWai ya Wauki hankalin mai gida balle in tayi magana. Ta haWu ba ™arya wallahi, zata yi abinda ake so. Sorry yarinya kin zo hannu yana gama faWar hakan ya tafi yana dariya mai kama da dariyar mugun ta.



Manal tana nan zaune har akayi i'sha a nan tayi sallah dan wajan yana da tsafta sosai, tana idar da sallah Bebi yazo wajan ya kalle ta yana mamakin yadda bata gajiya da kuka, ta idar da sallah amma sai kuka take yi jikin ta har rawa yake yi sosai, har ya wuce ta sai ya tsaya yana kallon ta yace, "Kina ji? Ki shiga wajan maman ki zauna."



Jin magana a kanta sai ta Wagp suka haWa ido yace, "tashi kije ciki." Jikin ta a sanyaye ta tashi fuskar ta ji™e da hawaye ta shiga ciki yabi bayan ta har lokacin Mmaa bacci take.



Bugun zuciyar ta ya sake dubawa ya rage gudun ruwan da yake shiga jikin ta ya sake yi mata allura sannan yace, "anytime zata iya farkawa, in ta farka zaki iya zuwa reception ki sanar da nurse." Ta Waga kai alamun to har lokacin kuka yake yi ya bita da kallo yana tunanim ita wannan yarinyar kuka baya mata wahala ne ko kuwa me?. Huzaifa ne ya shigo Wakin yana cewa, "kai nake ta nema ashe ka shigo nan" ya kalle ta yace, "Manal kar ki damu zata ki sau™i, ki daina wannan kukan kar ya cutar da ke.



Ta Waga kai alamun to yace, "ina Yayyen ki suke?." Ta kalle shi tace, "Bana da yayye, Yayata guda Waya ce kuma tana makaranta."

"Ke kaWai zaki kwana a nan?."

"Eh" ta faWa a sanyaye tana kallon sa. Yace, "shikenan to zuwa da safe duk zamu dawo, in akwai abinda kika ga Mama nayi in ta farka kije ki sanar a reception."



"To" ta fadWa muryar ta na rawaHuzaifa yana kallon ta Allah ya sani yana jin tausayin Manal sosai har zuciyar sa bai san dalilin hakn ba. Shi kansa Bebi kallon ta yake yi kafin ya kalli Huzaifa ya wuce ya fita shima ya biyo bayan sa.



A wajan ajjiye mota ya samu Bebi yana niyar shiga mota Huzaifa yace, "yarinyar nan tana bani tausayi Bebi, har zuciyata nake jin tausayin ta wallahi ban san meyasa hakan ba." Bebi yace, "Akwai tausayi kam, sai da safe" ya faWa yana shiga mota ya fita daga asibitin. Shima Huzaifa shiga motar yayi ya tafi.



Yana komawa gida ya tarar da Sacin rai a harabar gidan nasu domin kuwa Lubna ce tana zaune da saurayin da ya hana ta kulawa suna hira. Ransa yayi mugun Saci ya rasa ya zaiyi da yarinyar nan duk abinda yace sai ta tsallake, in yace kar tayi sai tayi bata san abinda yake ji a zuciyar ba in hakan ta kasance.



Lubna tana ganin sa ta tashi ta shiga gida da sauri shi kuka saurayin nata sai ya tashi ya nufo inda Bebi yake a lokacin ya fito daga mota ya mi™a masa hannu yace, "Barka da dare Yaya Adnan." Kallon hannun nasa yake yana kallon fuskar sa kafin yace, "Mujahid wannan abinda kake yi bai kamata ba, dani kake faWa banga dalilin da zai saka ka sako ™anwata a ciki ba."



Wanda aka kira da Mujahid yayi dariya yana kallon sa yace, "Neman aure nake fa Yaya Adnan, ba da wani abun nazo gidan nan ba auren ta nake so nayi in an bani dama." Adnan ya gyara tsayawa yace, "zan maka last warning akan Lubna, babu kai babu ita ka fita daga cikin rayuwar ta in ba haka ba.." kafin ya kai ™arshe Mujahid yace, "in ba haka ba zaka saka a Wauki raina?" Sai yayi dariya ya ce, "naga Lubna ina so kuma auren ta zanyi, baka isa ka hana ni neman auren ta ba, domin kuwa ba kaine mai gidan ba kuma ba kaine ri™e da gidan ba. dan haka zan nemi auren Lubna sai kuma na aure ta sai naga iya abinda zaka iya yi."



Juyowa yayi zai tafi sai kuma ya dawo ya saka kallon sa yace, "in ma ban aure ta ba zata faWa cikin soyayya ta wacce zata kasa sarrafa ta, daga nan duk abinda nake so zanyi da ita

6 / 27