Chapter 5 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 27

12K to 15K   out of 80K words

ba ni, ganin wannan abun haram kake gani ka goge dan Allah."



Yayi murmushi ya sake kallon screen Win wayar ya kalle ta ya ajjiye wayar yace, "in na goge me zan dinga gani yana tuna min ke?."

"Zaka iya kira na ko yaushe, amma kallon wannan ai tsaraice ne bai kamata ba."

"To meye baona?."

"Na san babu, amma yana dakyau ace ka goge yanzu ni ba matar ka bace ba. Wallahi tunda muka rabu na goge naka a wayata saboda ba abu ne mai kyau ba. Yayi murmushi ya kalli wayar ya goge ya nuna mata yace, "shikenan na goge." Tayi murmushi zatayi magana ta kallo kan titin nan ta hango motar Bebi na shiga gida.



Sai da ta gama shiga ta kalle shi tace, "kaini ofar gida." Ba musu ya kai ta bata ce komai ba ta buWe ta fita ta shiga gidan a lokacin Bebi na tsaye jikin motar sa ya bita da kallo yace,  ki faWa masa in na sake ganin afar sa a ofar gidan nan wallahi sai na saka an kama shi, Tunda baki da hankalin da zaki hana tsohon mijin ki zuwa gare ki ni zan koya masa hankali, har ke zan koya miki tunda naga hankalin ki ya gushe.



A fusace ta jiyo tace, "ni kake cewa bani da hankali Bebi?." Baice mata komai ya juya ya fita daga gidan zuciyar sa nayi masa zafi sosai baya son wannan banzar Wabi'ar ta yayar sa. Miji ya sake ka har saki uku ammaya dawo ki dinga kula shi, Bebi ya shiga Sangaren Mama ya tarar da Mimi a zaune kawai a falon gani sa sai tace, "Yaya Sannu da zuwa."



Har ya wuce sai ya tsaya ya kalle ta yace, "Yawwa."

"Naje na dawo daga get together na gode sosai." Kai ya girgiza alamun amsawa yayi shiru akwai abinda yake so yaji ta faWa ganin tayi shiru sai ya Waga afa zai tafi tace, "Yaya!." Sai kuma tayi shiru ganin hakan sai ya kalle ta yace, "ina Jin ki."

"Daman wani ne ya biyo ni wai yana sona, tun a can ban kula shi ba ka tambayi Saminu kaji, har ofar gidan nan yazo da ya takura min sai nace Saminu ya bashi number wayar ka kawai, ya bashi yanzu.



Kallon ta yake yi daman abinda yake so yaji kenan bata san yasan komai ba ya mata shiru ne ko zata faWa masa, ya kawar da kai gefe tace, "shikenan abinda zaki ce?." Ta Waga kai tace, "eh Yaya, daman kar ya kira ka ne kayi min faWa." Ya kalle ta yace, "ba shine wannan ba?" Ya faWa yana nuna mata fuskar sa, sai kuwa taga lokacin da Saminu yake bashi lambar, ta kalli fuskar Bebi tana nan kamar kullum babu fara'a amma sai taga ya saki fuskar yayi murmushi ya dafa kafaWar ta yace, "na san komai, ina so naji kin faWa ne shiyasa ban miki magan ba. Kar ki damu indai ya kai yadda nake so ya kai zan bashi number ki da kaina ya faWa yana yin gaba kafin taji yace, "in bai kai ba zaki ji shiru" ya faWa yana shiga Wakin mummy.



Ita mamaki ya daskarar da ita a wajan, kenan dai Yaya Bebi duk wani motsin su yana gani, ya riga ya saka musu matakan tsaron da su kansu basu san dashi ba, duk wani motsin su ya sani shiyasa da zarar kin saSa lamba zaki ji waya. Girgiza kai take yi sai kuma tayi murmushi a bayyans tace, "wani lokacin naga kamar takura ce, wani lokacin in na nutsu dai naga mutunci ne." Tana nan tsaye yazo ya wuce ta tayi murmushi ta zauna sosai take alfahari dashi a wannan lokacin.





"Nayi sabuwar baby ina faWa maka, da ganin ta kuma kai kasan sabuwa ce dal yadda na dama haka zan sha" Alhaji Mu'azzam yake faWawa wani abokin da da yake zaune a kusa dashi yana kallon sa.



Sukayi dariya a tare suka tafa yace, "shegen, kace ka samo ar shawalwala." Alhaji Mu'azzam ya cire hular kansa yace, "Tayi ta ko ina mutumina, kyau kamar ita tayi kanta, da farko har fargabar yi mata magana nayi saboda kyau. In tana magana kamar mage saboda sirantar muryar ta, dayar na iya rie kaina walalhi." Alhaji Magaji yayi dariya yace, "wato Alhaji Mu'azzam kana abinda kgaa dama wallahi, ka bar mata a guda biyu a gida kana nan mana shee ayar ka."

"To sun tsufa ai, har wani fushi suka yi dani basu san ni hakan nake so ba, ta haka zan yi abinda nake so da hujja."



Alhaji Magaji yayi dariya yace, "yanzu su kuma yaran naka fa? Baka Tunanin wani mai irin halin ka ya lallaSa musu?." Alhaji Mu'azzam yayi dariya yace, "Bebi fa yana da rai, ai Bebi shine katangar da take kare gidana. Ko tafiya zanyi naje nayi shekara goma bana nan Bebi zai kula da komai bazai bar wata yarinya ta wulaanta ba. Kai shi wani irin mutum ne da Allah ya masa kishin iyaye da an uwan sa, yadda yake son family sa ko kansa baya so, kana iyalan gidan nan zai iya yin komai ganin ya basu kariya. Haka Allah yayi zuciyar sa, in kaji yadda yake kishin annen sa mata sai ka Wauka matan sane, ko kusa baya so yaga wani ya raSe su musamman wanda suka kasance na banza."



Alhaji Magaji yace, "irin ka kenan." Alhaji Mu'azzam yayi tsaki yace, "ya ishe ka malam, ni ai na banza bane saboda biya nake ba kyauta ake bani ba. Yayi dariya yace, "Wato shiyasa hankalin ka kwance saboda kasan Adnan yana kular maka da iyalan ka."





"Babu abinda zai dame ni, na san kuma Adnan zai yi iyakar yin sa dan killace annen sa dama iyaye nasa, dan haka bani da wata fargaba akan wannan." Alhaji Magaji ya bashi hannu suka tafa yace, "Gaskiya ne mutumina, kana basu wuta wallahi." Suka sake yin dariya a tare Abba yace, "sai ma kaga Mubeena, a nan zaka tabbatar da ni din bana wasa bane ba, ni Win mai sa a ne. A hankalin zan jawo ta jikina daga nan kuma" ya fad'a yana masa alama da hannu suka sake yin dariya mai sauti suka sake tafawa.



Alhaji Magaji yace,  da yake naga kana son mai kyau har na hango wata yarinya, fara ce al wannan iya kallon fatar ta ma ya isa a ci kuWin ka wallahi.

 Allah mutumin?.

 Wallahi, da gani sabuwa ce dal kuma. Daman kai nake so a Waukowa ita ni kasan sababbin na basa gabana, nafi son ar hannu wacce zata kawo kanta.



Alhaji Mu azzam yace,  yanzu ya za a yi?.

 Ka jira ni kawai, zan saka a kawo maka ita daga nan sai ka san abinda zaka yi. Abba yayi dariya yace,  ayi da gaggawa, kasan in naji labarin mace tsigar jikina tashi take wallahi. Alhaji Magaji yace,  saboda tsabar jaraba ko?. Sukayi dariya a tare.



"Hello Yaya Mubeena bakya kina ne?, koma ina dare yayi baki dawo ba?." Manal ta faWa a waya na kunnen ta." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sauke wayar ta kalli Mama da Baba tace, "wai tace a gidan su Bily zata kwana."



Mama tayi tsaki tace, "kuma waye yace ki bibiyi wannam yarinyar? Yau ta saba kwana a waje ne?." Baba ya Wauki waya ya kira Mubeena amma ta kashe wayar ya kalli Manal yace, "daman akwai lokacin da bata kwana a gidan nan?."

"Eh Baba."

"Amma Meyasa baki taSa faWa min ba?." Mama tace, "Meya amfanin faWar? Mubeena ai ta riga ta zama abinda ta zama, babban bain cikina da na saka mata sunan mahaifiyata, da Manali na sakawa duk da nafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali.."



Manal yace, "don Allah Mama kiyi hauri kinga baki da lafiya." Baba ya kalle su yace, "amma dai gobe zata dawo ko?." Manal tace, "eh zata dawo zuwa gobe." Baba yayi shiru gabaWaya baya jin daWin abinda yake faruwa yace, "kin san gidan su wacce tace tana can Win?.

 Ban sani ba Baba. Baba yayi shiru kafin yace,  tafiya zanyi gobe da safe shiyasa na shigo yanzu, amma n fasa sai naga dawowar Mubeena gobe."

"Kayi tafiyar ka kar ka jira dawowar ta domin kuwa babu abinda zaka tsinka a ciki sai bain ciki da takaici, indai Mubeena ce sai ta saka maka ciwo kamar yadda nake fama dashi nima."



"A'a ba haka ya kamata ko dinga faWa ba, addu'a itace abinda ya kamata y dinga fitowa daga bakin ki a kanta." Mama bata ce komai ba ta kawar da kai Baba ya saka hannu aljihu ya Wauko kuWi ya bawa Manal yace, "duk abinda kike da buata a siya koda na tafi. Manal tace, "to Baba, Allah ya kiyaye." Ya amsa da amin Mama ma tayi addu'a ya amsa ya fita.



Manal dan ta kawar da maganar Mubeena sai tace, "Baba kamar shine ya haife mu, ba dan na san mahaifin mu ya rasu ba da nace Baba shine ya haife mu. Mama bata cekomai ba ta kawar da kanta gefe abubuwa na dawo mata cikin kanta tayi murmushi tace, "albasa bata yi halin ruwa ba, koda yake barewa baza tayi gudu Wanta yayi rarrafe ba." Manal tace, "Mama me kike nufi?." Shiru bata amsa ba dole Manal din tayi shiru itama, amma tana mamakin wannan karin maganar da Mama take yawan ji ta faWa akan Mubeena, me hakan yake nufi kenan?.......



*BAYA DA URA.*

Fitattubiyar2025



 *Nana Haleema.*



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp



*BOOK 1*

*Page 007*





Tun asuba Manal ta lura da yanayin Mama babu daWi, bata mata magana ba amma idanun ta na kanta sai da taga yanayin ta ya canja gabaWaya ta birkice hankalin Manal ya tashi tayi kanta a guje tana faWinn, "Mama! Mama! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Mama ki tashi don Allah." Sai ta fita a guje zuwa gidan Baba, ta samu matan sa guda biyu a tsakar gida Waya tana dama kunu Waya tana aikin wanke waken osai tace, "Umma, Inna, Mama na bata numfashi, ku taimaka min don Allah na kaita asibiti.



Wacce take amsa sunan Umma ta galla mata harara tace, "bazan taimaka ba, kaji min yarinya da sakarci, ni zan taimaki uwar taki dan bata da lafiya?. To ni ce na Wora mata ciwon da zan taimake ta?. Wacce take wanke waken tace, "ke kika saurare ta ma ai, wanda yake goya mata bayan baya nan sai a canja wani sarkin." Manal tana kuka tace, "don girman Allah ku taimaka min, Mama bata numfashi ban san ya zanyi ba."



Ganin sun ma i sauraren sai ta mie ta fita a guje ta sake komawa wajan Mama ta tarar da ita yadda ta barta dayar take numfashi, ta saka fita a guje ta shiga gidan su awar ta Surayya a guje. Maman su Surayya tana zaune ita da Surayya Win suna ta shirin haWa abin karyawa Manal ta faWo tana kuka Maman su Surayya tace, "Subahanallahi Manal Lafiya?." Manal tana kuka tace, "Mama ce bata numfashi sosai, ki taimaka min don Allah, na rasa ya zanyo.



A firgice tace, "Subahanallahi, Surayya tashi kuje maza bara na faWawa baban ku sai na biyo bayan ku" ta faWa tana shiga wani Waki, suka fita ita da Surayya suka shiga gidan. Surayya ta tsorata da ganin yanayin Mam tace, "kina ji Manal, asibiti zamu je bara na nemo mai napep mu tafi" ta faWa tana fita a guje ba jimawa sai ga Maman tasu ta shigo Manal na zaune kusa da Mama tana ta kuka. A guje Surayya ta dawo tace, "ga mai adaidaita sahun na samu."



Maman su Surayya tace, "to yanzu ai Waukar ta wahala zai mana" ta kalli Manal da take kika tace, "a gidan Baban ki babu wanda zai taimaka mana mu fita da ita?." Manal girgiza kai kawai take kafin tace, "Zamu iya Mama, mu gwada kar Mamana ta mutu." Haka suka Wauki Mama suka fita aka saka ta a daidaita sahu Manal da Surayya suka shiga suka tafi asibitin Murtala.





A safiyar Adnan da kasala ya tashi kamar bazai je wajan aikin ba, tunawa da akwai masu jiran sa ya saka shi ya tashi dole yayi wanka ya shirya ya fito zuwa Sangaren Mamy.





A falon Mamy ya tarar da ita da Maryam da kuma Lubna a zaune ya shiga da sallama Mamy ta amsa tana faWin, "Har an fito Bebi?." Ya arasa ciki yace, "eh wallahi Mamy, zan shiga babban asibiti ne shiyasa. Barka da safiya" ya faWa yana kallon ta amsa fuska a sake tare da faWin, "Allah ya taimaka ya kiyaye hanya."

"Amin ya Allah" ya kalli Maryam da take zaune fuska a haWe ya kalli Lubna da take kallon sa sai tace, "Ina kwana Yaya."



"Lafiya lau, baki tafi school ba?."

"Bani da lecture yau." Ya kalli Maryam yace, "ina kwana." Kallon sa tayi tace,  Lafiya lau." Daga haka bai bata sake cewa komai ya tashi yace, "Mamy sai na dawo" ta masa fatan alkhairi shi kuma ya fita.



Wajan Mama ya shiga ya same ta a tsaye kitchen tana yankan albasayace, "ina Mimi da Kausar suke da zasu barki kina aiki?" Ya faWa yana niyar juyawa zai je ya kira su Mama tace, "yale su, ba wani abun bane nice nace su huta."

"Amma Mummy kina aiki su suna kwance suna bacci meye amfanin su?."

"yale su kawai. Baka fita ba kenan?."

"Yanzu zan tafi. Ina kwana" ya faWa yana durusawa har asa ya gaishe ta amsa tare da faWin, "Lafiya lau. Yau me ya hana ka fitowa da wuri?."



Ya tashi tsaye yace, "gabaWaya da bazan ma fita ba bana son jin daWi ne" ya faWa yana shiga kitchen Wim ka karSi albasar hannun ta wacce ta gama yankawa yaga kwai guda uku a ajjiye da alama shi zata soya, ya Waulp bowl amari ya fasa kwan ya zuba albasar ya kunna gas cooker Win dan ta Wota fan a kai, da kallo take bishi tana murmushi kafin tayi magana yace, "Abba bai kwana a gida ba kenan?."



"Hmmm kai ka damu wannnan ai an saba, iris nake jira da mahaifin ku wallahi." Jin abinda tace sai yayi shiru baice komai ba kafin ta kawar da maganar tace, "yaushe zaka yi aure ne Bebi?."



Baice komai ba ya zuba mai a kaskon ya juye wan a kai tayi dariya tace, "haka zanci ba gishiri ba maggi?." Ya dan dafe kai yace, "na manta" ya faWa yan Waukar abinda yasan tana ajjiye gishiri ya zuba mata ta sake cewa, "yaushe zaka yi aure ina tambayar ka."

"Mummy sai ranar da Allah yayi."

"Komai akwai niya ai Bebi, ya kamata zuwa yanzu kana da iyali kaima."

"To Mummy zan fara neman matar aure in sha Allah" ya faWa a lokacin yana juya wan sama ya dawo asa.



Mummy tace, "Rumana ai a shirye take ko yau kace zaka aure ta zata shirya." Ya Wan sauke numfashi ya kashe gas Win baice komai ba tace, "kayi shiru." Ya kalli Mummy yace, "Wallahi Mummy babu Ruman a raina a ya kamata ku fahimci hakan, Tunda daga lokacin da tace na barta shikenan na barta har raina, bana tunanin zan sake dawo da ita yanzu ko nan gaba."



Mummy ta ta kalle shi shi kuma ya Wauke wan daga cikin fan Win ya saka a plate ya fito mata dashi ta zauna tace, "ya kamata ace ka mayar da ita kam Adnan, tana sonka kaima kana sonta, kawai abinda tayi maka ne ya saka ka kasa mantawa, amma da ka kawar da komai shikenan. Ai soyayya bata fita duka, tana nan a zuciyar ka na tabbatar da hakan.



Shiru yayi baice komai ba kafin ya kalli agogo yace, "zan tafi."

"Allah ya kiyaye in ka dawo zamu tattauna akan maganar dan baka da matar da ta wuce ta indai ina da rai, Rumana itace matar ka in sha Allah. Baice komai ba ya fita hau mota ya fita daga gidan gabaWaya baya jin daWin maganar Rumana da ake masa ko kusa, dan shi kam ko meye zai faru bazai aure ta ba, yadda ta barshi tayi aure shima haka zai barta yayi auren sa.



angaren Manal suna yashe a ofar shiga A&E an hana shiga da Mama ance babu gado, hankalin Manal ya tashi ta fita daga hankalin ta saboda gigicewa musamman in taga idanun Mama suna yin harrrr kamar zasu kulle sai hankalin ta ya saka tashi matua. Babu irin magiyar da bata yi musu ba amma sun i sun ce babu gadon da za'a Wora Mama, sai kuka take tana zaune kusa da Mama Bata da tsuntsu bata da tarko.





Wani mutum ta gani ya fito daga cikin A&E din ta tashi a guje taje wajan sa tace,  Don Allah ka taimaka min Mamana bata da lafiya, don Allah ka taimaka min sunce babu gado ban san ha zanyi ba. Mamana zata mutu anki karbar ta ance Wai babu gado. Na rasa abinda zanyi dan Allah ka taimaka min." Kallon ta yayi ya murmusa a zuciyar sa dan ya tabbatar itace yace,  Subahanallahi! Maman ce babu lafiya tana ina?." Da sauri ta nuna masa inda Mama take ya wuce ta zuwa wajan ya kalli Mama ganin da gaske fa Mama babu lafiya ya bar wajan zuwa wajan mai gadin shiga ciki ya tabbatar masa da babu gado a ciki ko ina ya cika, ya kalli ciki yaga mata da maza nan a ajjiye a kasa..



Da baya ya dawo ya kalli su Manal da Surayya da dukkan su kuka suke ya kalli Manal yace, "tana buatar taimakon gaggawa ina zuwa" ya faWa yana shiga ciki bai jima ba ya dawo tare da wani nurse ya tsuguna kusa da Mama, ya kalli Manal yace,  me yake damun ta?. Manal tana kuka sosai tace,  ban

5 / 27