Chapter 4 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 27

9K to 12K   out of 80K words

cewa bani da hankali Manal?." Manal tace, "na faWa akwai abinda zaki min ne?." Kafin Mubeena tayi magann Manal tace, "Mai hankali bazai aikata irin abinda kike aikatawa ba, ke a ganin ki wayewa ce raina iyaye, baki san hauka ne da rashin sanin ciwon kai ba. Sai girmama iyayen wasu saboda neman suna bakya girmama naki, tirrr! Kin ji kunya wallahi."



"Salamu alaikum wai Nusaiba tazo!." Wani yaro ya faWa yana shigowa, abinda ya dakatar da Mubeena ga yiwa Manal masifa ta juya kan yaron tace, "sai naci kaza kazan wanda ya sake kira na da Nusaiba, sai na zage shi duk girman sa na rantse da Allah. Kar a kuma kira na da Nusaiba ba sunana bane, in baza'a ce Mubeena na ba a kira ni da baiwar Allah. Meye wani Nusaiba ana zaune Lafiya? Ni an cuce ni ma da aka samin Nusaiba wallahi."



Yaron da take yiwa masifa tace, "Baba ne yace kizo in baza ki zo ba sai naje na faWa masa" ya faWa yana fita daman dan ya tunzura ta yace Nusaiba. Mubeena tace, "ko ne zan masa da zai aiko nazo oho, ni bana son takura da saka ido wallahi. Tunda ba shi ya haife ni ba meye nasa na takura min?" ta faWa tan figaat mayafi ta fita daga gidan.



Manal ta kalli Mama dan tasan bata so taji Mubeena tana ambatar sunan mahaifiyar ta tana cewa bata so, ranta yana Saci sosai har hakan sai ya nuna a fuskar ta. Manal tace, "Kiyi ha™uri Mama, ki cigaba da yiwa Yaya addu'a wata ran zata daina duk abinda yake yi." Mama bata ce komai ba tayi shiru kawai Manal sai ta tashi ta Wauke kwanon da suka gama cin abinci ta fita dashi ta dawo ta Wauko kayan shimfiWa Mama ta shimfiWa musu tace, "Mama nayi shimfiWa in zaki kwanta."



Kafin Mama tayi magana Mubeena ta shigo tana cewa, "ni wallahi babu wanda zai takura min, sai nayi abinda nake so bazan kuma auri talaka ba wallahi. Ni Mubeena nafi ™arfin Wan mai kuWi,  sai dai mai kuWin kan sa ba Wan sa ba. Bazai yu ace sai uban miji ya bawa mijina sannan shima ya bani ba, na fi so daga hannun mijina sai wajena. Babu wanda zan aure gwara ma Baban ya sani, dan yana ™anin mahaifin mu kuma yana auren Mama ai mahaifin mu bane. Bana son takura a bar ni na sake" ta faWa tana shigewa Waki Manal zata bita Mama tace, "kar ki bita Manali, zo ki bani ruwa na sha." Manal ta canja hanya ta kawowa Mama ruwa ta sha tace, "kashe min hasken falon ki kwanta, in kuma kin kashe shikenan."



Kamar yadda tace haka tayi ta kashe hasken Mama ta kwanta ita kuma ta Wauki alqur'ani ta koma tsakar gida ta zauna tana karantawa zuciyar ta babu daWi.  Bata son halin da Mubeena take nunawa Maman su ko kusa ko alama, tana jin haushin hakan domin yana daga cikin dalilin da ya saka ciwon zuciyar Mama ya™i sau™i saboda damuwar Mubeena.



Da sassafe Manal ta tashi tayi abubuwan da ta saba dan zasu je asibiti da Mama kuma bata so su makara, dan sau biyu suna son ganin likitan makara take hana su ganin sa. Šorawa Mama ruwan wanka bayan ta fito ta juye mata a bokiti ta kai mata banWaki sannan taje ta tarar da maman a zaune ta dafe kanta tace, "Sannu Mama, har yanzu ciwon kan ne?." Mama tace, "kece da sannu Manal, har yanzu bai sake ni ba ciwon nan kaina yayi nauyi sosai."



Manal tace, "har na juye miki ruwa saboda zuwa asibitin, Anya zaki iya zuwa ma kuwa?." Mana tace, "gaskiya bana tunanin zan iya fita, kaina ciwo yake min sosai ba kaWan ba Manal." Manal tayi shiru ta kalli ™aramin agogo falon su tace, "gashi har bakwai ta kusa, ance likitan tun shida yake zuwa. Bara na shirya naje kawai na kai result Win zuciyar sai ya bani maganin na ki." Mana tace, "Anya zai saurare ki?."





"Zan gwada Mama, tun yaushe ake saka mana ran zamu ganshi bamu ganshi ba, ga dama mun samu baza mu yi wasa da ita ba. Bara na saka kayana nayi sauri naje na dawo" ta faWa tana shiga Waki a lokacin Mubeena bacci take sosai ko alamun tashi bata yi ba, ta shirya ta saka hijjabi ta Wauki katin Mama da kuWin mota ta fito ta samu Maman ta koma ta kwanta tace, "Mama zan tafi babu abinda kike so?."



Mana tace, "babu komai Manal, sai kin dawo Allah ya kiyaye yayi miki albarka." Ta amsa da amin ta fita daga cikin gidan. Napep ta hau zuwa asibitin murtala ta sauka ta shiga ciki inda aka yi mata kwancen likitan yana zuwa nan ta hango dandazon mutane mata da maza a zaune a cikin wata rumfa da alama duk likitan zasu gani.



˜arasowa tayi wajen wanda yake tsaye da katina a hannun sa tace, "sannu da aiki." Ya kalle ta yace, "Yauwa."

"Dan Allah nan ne wajan likitan zuciya?."

"Eh nan ne, kawo katin naki." Mi™a masa katin tayi ta koma ta zauna akan abinda ake zama tana jiran azo kanta.



Ta jima sosai sama da awa Waya tana zaune kafin a kira sunan Mama jin hakan ya saka ta tashi da sauri ta karSi katin ta shiga office Win. Bebi yana zaune a kan kujera cikin manyan kaya ya sunkuyar da kai yana rubutu ta zauna ya mi™a mata hannu yace, "bani katin." Ba musu ta bashi katin ya karSa tace, "ga sakamakon gwajin zuciyar da akayi." KarSa shima yayi ya buWe takardar yana kallon ta sai ya Wago suka haWa ido da Manal ya sake kallon age din jikin katin ya sake kallon ta yace, "Zahra'u Muhammad, are you?."



Manal tana kallon sa tace, "Mamana ce, bata da lafiya baza ta iya zuwa ba shine nazo na kawo da kaina. Bana son rasa damar ganin ka ne, sau uku ana saka ran zamu ganka bamu ganka ba shiyasa na karSo nazo a madadin ta." Kallon fuskar ta yake yi jin yadda take magana da sanyi ya jingina da kujera yace, "Maman kice babu lafiya kuma kece kika zo ganin Dr?." Manal ido ya ciko da ™walla tana kallon sa tace, "eh." Wani irin kallo na ta raina masa hankali ma yake mata, yanzu banda ma raini shi zata zo ta cewa wai katin babar ta ne amma itace tazo ganin likitan?.



Tsaki yaja ya ajjiye mata katin zaiyi magana tace, "don girman Allah ka bani maganin kwana biyu har bacci kasawa take saboda ciwon ™irji, yanzu haka bata da lafiya na fito na barta dan Allah ka taimaka ka rubuta maganin dan Allah." Sai hawaye ya sakko daga idanun ta yayi shiru yana kallon ta, yana girmama mace a rayuwar sa duk ™arancin shekarun ta amma baya so azo masa da rainin hankali, in ba rainin hankali ba tazo tace ya bada magani bayan bai ga mata lafiya ba sannan ba'a faWa masa ya ake jin ciwon ba kawai sai ya Wauka ya bayar, wani abun na faruwa kuma sai dai yaji sunan sa a gidan radio ana cewa bai san aikin sa ba. Ta saka shi a gaba tana masa kuka kamar wacce ya daka, baya son shagwaSa ta banza da wofi, in zaka yi ma kayi akan hujja.



"Zaki iya fita daga nan?. Ta Wago idanun ta da suka koma ja tace, "ka taimaka dan Allah."

"ki je, duk sanda Maman naki ta samu lafiya sai kuzo." Ta girgiza kai tace, "wahala ake sha kafin a sake samun ka, dan Allah ka amince ka bani maganin." Shiru yayi yana kallon ta ya lura baza ta fahimta ba.





"Out!" Ya faWa yana nuna mata ™ofa. Jikin ta a sanyaye ta tashi ta Wauki katin da takardar ta fita bata sake cewa komai ba a lokacin wata mara lafiyar ta shigo. Tsaki yayi bai sani ba ya kalli sabuwar da ta shigo ya karSi katin ta ya fara rubutu a kai.



Manal tana tafe tana kuka, wannan shine taga samu taga rashi, ga likitan da suke son gani kwana da kwanaki amma ta ganshi ganin nasa babu amfanin da yayi mata. A haka ta shiga gida tun daga soro take jin muryar Mubeena tana mita kamar yadda ta saba. Kai ta girgiza kawai ta shiga a lokacin Mubeena yake cewa, "Yauwa gwara da kika dawo, sai ki Wauki hanya ki fita bayan kin kulle kitchen da kika bar mu uban me zamu ci?." Manal da fuskar ta tayi ja sosai tace, "kin san inda nake ajjiyewa" tana faWar hakan ta ™arasa falon ta tarar da Mama a zaune har tayi wanka amma kayan shimfiWat suna nan ba'a kwashe ba.



Ajjiye katin tayi tace, "Mama na dawo" ta faWa tana kwashe kayan ta kai Waki ta dawo Mama tace, "sannu, ya bada maganin?."

"Bai bayar ba Mama, wani fusatacce ne ba irin ro™on da ban masa ba amma mutumin nan da yake bashi da mutunci ko ya kalle ni ma, wai tunda babu ke babu amfanin bada magani ba. Amma a haka Dr Huzaifa yake cewa yana da kirki."

"Sai bayan kin tafi nayi tunanin hakan Manal, zuwan babu ni a kamar gwara ba'a je bane dan kin San likitoci basa son ka saka musu baki ko tambaya suka yi balle kuma ace kinje babu ni. Kin ga ai bai san ya nake jin ciwon ba balle ya bani magani."



"Amma Mama tunda na faWa masa uzurin rashin lafiya ne ai yaci ya saurare ni." Mama tayi dariya tace, "shine ki ka sha kuka kenan?." Manal tace, "Mama ya akayi kika san nayi kuka?."

"Manali kenan, ni nasan abun kuka baya miki wahala, sannan ga muryar ki nan ta canja."



"Wallahi Mama ina tafiya ina kuka." Mana tace, "Kiyi ha™uri, Allah ya kaimu wani lokacin sai mu koma nida ke din."

"Amma Mama ciwon nan yana damun ki sosai, bana so abin yazo yayi miki yawa ne."

"Babu abinda zai yi yawa, kar ki damu."



Manal ta tashi tace, "ya bani haushi sosai wallahi, daman fuskar sa a tamke kamar mala'ikan mutuwa ko annuri babu, da gani bazai yi kirki ba." Mama tayi dariya tace, "ke kin taSa ganin mala'ikan mutuwan ne?." Manal tayi dariya tace, "bara na kawo miki kunun ki" ta faWa tana fita a nan ta tarar da Mubeena ta fito daga wanka bata tanka mata ba ita ma haka ta wuce zuwa Waki.



Da kofin kunun ta dawo a hannun ta tace, "Mama gashi." Mama ta karSa tace, "gaskiya yau ma sai na saka sikari Manali." Manal tace, "kai Mama! Jiya ma kin sha sugar shekaran jiya ma fa haka."

"Zuciyata tana so Manal, mutuwa dai ake gudu kuma dole mu mutu. Bani sikarin na zuba."

"Dan Allah Mama kar ki sha."

"Allah sai na sha Manal, Haba kai kenan cikin hana ni abinda zuciyar ka take so, bani ki gani."



Manal ta kwance ledar ta zuba mata kaWan jin tace Allah tace, "gashi nan na zuba miki." Mama ta juya tace, "bai ji ba, ™ara min."

"Haba Mama dan Allah, ki daina sha sugar kwana biyu kina sha sosai kar yayi miki illa."

"Ke ™ara min daga yau bazan sake ba." Manal ta ™ara mata kaWan Mama ta juya tace, "shiyasa naso bakya nan zan sha sikari son raina, da bakya nan ai gashi har biredin da Baban ku ya rage jiya na cinye ba wanda ya sani,"



Manal kamar zatayi kuka tace, "amma Mama kin san hakan zai cutar dake sosai ko?." Mama bata ce komai ba ta shanye kunun ta tsaf Manal na zaune a gefen ta tana kallon kafin Mubeena ta fito cikin hijjabi mai kyau ba™i dogo wanda ya amshi fuskar ta tace, "ke Manal zan tafi makaranta, ina kud'in mota?."

"Bani dasu kuma Baba bai bani ba, in zaki je ki tambayi Baba kije, in baza ki ba sai ki tafi a ™afa." Mubeena tace, "nice zan tafi a ™afa?." Mama tace, "kin wuce kije da ™afar ne?."



Jin mama tayi magana sai tayi shiru kawai ta wuce ta fita Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena na da rai ba dole zuciya ta dinga min ciwo ba." Manal bata ce komai ba ta tashi ta fita ta sha mata kunun babu sikari ta fara gyara gidan kamar yadda ta saba.



Nana Haleema>ĜBŬd'ŝ



*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



             İŝ *Nana Haleema.*





https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp





*BOOK 1*

*Page 006*







Adnan suna zaune shida su Huzaifa bayan sun idar da sallar magriba wayar sa ta fara ™ara, ya duba ganin mai kiran sai ya Wauka ya saka a kunne a bayyane yace, "kun koma gida?."  Yayi jim alamun ana bashi amsa kafin yace, "okay, thanks you." Daga haka ya yanke wayar ya kalli Huzaifa da yake kallon sa yayi murmushi yace, "Bebi kana takurawa ™annen ka da yawa, wannan takura musu Win da ke yi bazai haifar da Wa mai ido ba."



Adnan ya zauna sosai yace, "kai a wajan ka takura ce, ni a wajena kariya ce." Hamza yace, "Gaskiya ne, amma yawan saka musu Idon da kake kamar yayi yawa, duk inda suke je sai ka sani hatta hoto sai an Wauka an turo maka. Ko irin saurayin nan na sirri basu isa su yi ba, ga wayar su kullum a binciken ta kake."

"Ban taSa karSar wayar wata ta duba ba, saboda nasan waya kamar sirri ce, wannan baya gabana abinda na sani duk inda ™annena zasu je ha™™ina ne a kaina na san da fitar su da dawowar su. Bama su ba har iyayena."



Huzaifa yace, "Gaskiya ne, masu irin wannan zuciyar a cikin mutane baku da yawa gaskiya." Hamza yace, "™anne ma fa kenan, wannan ina ga matar ka Bebi?." Bebi ya kalli wani wajan daban yace, "iyayena sai dai ace iyayen mu, yayyena sai dai nace yayyen mu, ™annena sai dai ace ™annen mu" ya kalli Huzaifa yace, "Matata fa? Za'a ce matar mu?." Jin abinda yace suka yi dariya shida Hamza banda Bebin da dar1ya ba dabi'ar bace ba Hamza yace, "kace Rumana zata sha tsaro."



Bebi ya sauke numfashi yace, "wai waye ya faWa muku wannan yarinyar zan aura ne?."

"Babu wanda ya faWa mana, mu muka ga hakan saboda ka so Rumana sosai kai ka sani." Bebi ya taSe baki yace, "Na so ta a da amma banda yanzu.

 First love Win kace fa, har yanzu akwai sauran son ta a zuciyar ka Hamza ya faWa yana dariya.



Bebi yace,  ba dai a zuciyar Adnan ba, ni ba irin wannan soyayyar nake ba, in nace bana son abu to bana so Win ne. Yeah I know a baya naso Ruman sosai, but by now babu wannan soyayyar a zuciyata. Shiyasa bana saka soyayyar da zan cutu a zuciya ta, in na samu fine in ban samu bana zan rayu babu tashin hankali."



Hamza yayi dariya sosai yace, "Dr Adnan kenan, kawai kayi addu'a Allah kar ya Wora maka wacce tafi ™arfin ka, domin kuwa soyayya ita take yin kanta a zuciya a lokacin da baka shirya ba. Kar kaga ka daina son Rumana lokaci Waya ta fita a ranka, akwai wacce zaka iya so nan gaba in ka rabu da ita sai dai kaji ana likitan zuciya yana ganin likitan zuciya."



Bebi ya kalle shi yace, "har abada wallahi, Tunda ban samu ciwon zuciya akan soyayyar family na ba babu wata yarinya da zata saka min ciwon kai. Kai ni fa ba Wan wahalar soyayya bane ba, in na samu fine in ban samu ba kowa ya kama gaban sa." Huzaifa yayi dariya yace, "Shikenan dai Bebi, zamu gani." Ya tashi tsaye ya kalli agogo yace, "ni kam zan wuce."

"Gobe zaka shiga asibitin ne?."

"Naje yau, bana tunanin zan koma. Ta ™arfin tsiya aiki da asibitin gwamnati ya fita a raina saboda rashin gani nayi shiru.

"Ka koma don Allah." Ya kalli Huzaifa da yake maganar yace, "sai nayi niya, kasan ba'a sani ba'a hana ni" yana faWa yayi gaba abin sa ya barsu a zaune kafin suma su tashi sunyi gaba.



          Anty Maryam tana zaune a motar tsohon mijin ta suna daga waje a bayan wani gini ba sosai ake hango su ba ta kalle shi tace, "ka faWi abinda kace zaka faWa min kasan yanzu Bebi yana hanyar dawowa, yanzu in yazo sai ran mu ya Saci. Tsohon mijin ta ya bita da kallo har ta tsargu tace, "wai wannan kallon da kake yi min na meye? Bana son iri wannan kallon."



Ya sauke numfashi yace, "wani abu nake tunawa ne matata, kin manta lokacin da muke gidan mu in nayi miki wannan kallon abinda nake nufi?." Anty Maryam tayi murmushi kafin tayi magana ya ri™e hannun ta yace, "ni nasan baza ki manta da irin yanayin da muke kasancewa ba, musamman in kika bani abinda nafi so a jikin ki, Wato nan" ya faWa yana kai hannun sa ™irjin ta, bata hana shi ba amma ta dan doke hannun tace, "Kamal ya kamata ka tuna yanzu fa ni ba matar ka bace, kace kin zakayi magana dani akan su Nabil shiyasa na fito."



"Abban Nabil Win ne yake son magana dake ba akan su Nabil ba."

"To ka faWi abinda zaka ce min bana so Bebi ya dawo."

"Wai bebin nan ba kece gaba dashi ba?."

"Nice gaba dashi amma magana ce bana so." Yayi tsaki yace, "Ko mu bar wajan na?." Maryam tace, "A'a, ka faWi abinda yake tafe da kai kawai."

"Ai ban gaji da kallon ki bane." Ta furzar da iska tace, "Meyasa baza mu nemi hanyar gyara auren mu ba?, bisa kuskure muka rabu ba son ran mu ba.



Ya Wan sosa kai kafin ya basar yace, "Matata ™addarar da ta raba mu ita zata mayar damu, a baya nasan ban kyauta miki ba amma zan gyara kuskure na." Bata ce komai ba ta sauke numfashi ganin hakan sai ya Wauko wayar sa yace, "kin ga wani abu" ya faWa yana nuna mata fuskar wayar. Gaban ta ya faWi matu™a ganin abinda ta manta ta tura masa a zaman auren su, ta runtse idanu cikin kunya da sanyin jiki tace, "Haba Kamal, wannan ba abinda zai zauna a wayar ka bane, kar ka manta bafa matar ka bace

4 / 27