Chapter 10 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 27

27K to 30K   out of 80K words

nazo" ta faWa da shagwaSa wacce ta shige shi lokaci Waya ya kwance ya kasa gane kansa. Da™yar ya danne abinda yake ji yace, "Yanzu zan fita ke kawai na tsaya na gani."



Bata ce komai ba y sake cewa, "Dama zaki raka ni da nayi farin ciki." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta mi™e tace, "zan koma gida Baby, sai ka dawo a kawo min tsarabar lagos." Ya mi™e tsaye yace, "kar ki damu, in ma lagos Win kike so a Wauko miki zan kawo miki" ya faWa yana matsowa kusa da ita kafin yace, "in na tafi zanyi kwana biyu ban ganki ba, baby please ki bani hug guda Waya wanda zan tuna dashi in bana nan." Jin abinda yace sai ta kalle shi kamar wani yaro har marairaicewa yake sai tayi murmushi dan wallahi dariya yake bata tace, "A'a ni dai."



"Yanzu bazan samu ba kenan? Ni ki bani dama to." ˜afa take bugawa cikin son sake burge shi tace, "A'a nidai." Hakan da tayi bai san lokacin da ya jawo ta jikin sa ya rungume ba yana furta, "ina sonki Baby." Sacanni bai wuce goma ba ta janye jikin ta tana turo masa baki gaba wanda yake jin wani abun na fizagar sa akan bakin tace, "to zan tafi." Cikin taushin murya yace, "bana so ki tafi, ki tsaya a nan kin ji baby" ya faWa yana ri™e hannun ta.



Bata ™wace hannun ba tace, "A'a ni dai tafiya zanyi." Ya sauke numfashi yace, "shikenan Baby tunda bakya son kasancewa dani." Bata ce komai ba bai saki hannun ta ba ya Wauki wayar sa yana dannawa da hannu Waya kafin ya kalle ta yace, "na tura miki kuWin shan ice cream." Murmushi tayi tace, "thanks you Baby."

"I love you Baby."

"I love you so much" ta faWa da wata murya mai Waukar hankali.



Šakyar yake iya ri™e kansa, amma ji yake kamar ya fizgo ta ya kama bakin ta ya tsotse shi ya haWe kirjin sa da mata  yana jin buguwar zuciyar shine abinda yake bu™ata a wannan lokacin, amma baya son yi mata shigar sauri dan sabuwa ce shiyasa yake bin ta a hankali, ya san lagon mata irin ta sababbi. Har ™ofar falon ya tako ta kafin ya koma ciki ta shiga mota su Wauki hanyar gidan su Bily.



Shima gidan ya shirya ya bari ya tafi gidan sa ya ajjiye motar sa ya shiga Sangaren sa kai tsaye. Mama daman jiran zuwan sa take tunda ta san yana garin, tana ganin ya dawo ta nufi Sangaren nasa ta same shi a tsaye a falon yana amsa waya yana murmushi a lokacin da yake cewa, "zanyi kewar ki sosai Baby, kamar na fasa tafiyar nan." Taji abinda yake cewa sai bata nuna ta ji ba ta shiga da sallama ya amsa yana yanke wayar bai kalle ta ba tace, "sannu d zuwa." Sai da ya kalle ta sannan ya cigaba da abinda yake yi yace, "Yauwa."



Mama tace, "ina so zanje na gaida Hajiya an jima." Fuskar sa a Waure matu™a yace, "sai kin dawo." Ta juya zata tafi yace, "zanyi tafiya zuwa lagos yau, ki faWawa  “ar uwar ki." Mama ta kalle shi tace, "ai mu ko yaushe a baka nan muke Waukar ka a gidan nan, ko baka faWa mana ba, hakan ba sabon abu bane a wajan mu Alhaji."



Kallon ta yayi kamar zai magana sai ya fasa tayi dariyar takaici tace, "Su baby sune suke ganin ka ko yaushe, amma matan gidan ka sune basa ganin ka sai lokacin da ka so, sai lokacin da su Baby suka sallame ka ka ke zuwar mana." Ya kalle ta yace, "me kike nufi?." Kai tsaye tace, "“an matan ka nake nufi, sune suke ganin ka ko yaushe available amma matan ka na gida ko yaushe baka nan a wajan su, Allah ya kiyaye hanya. Sannan ina yawan faWa maka ka dinga sara kana duban bakin gatari, kar ka bar baya da ™ura" tana faWa ta fice ya bita da kallo sai ya share dan kar maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Abinda yazo Wauka kawai ya Wauka ya fito y sake gida mota driver ya ja suka fita.





Zuwa yamma Manal taji faWin jikin ta sosai, wanka take so tayi ya canja kaya gashi Surayya ta tafi. Tashi tayi ta fita zuwa Wakin da Mama take tana kallo duk da bata ganin ta a wajan ta kallon Wakin ma kawai hankalin ta kwanciya yake yi. Tana zaune tayi tagumi tana hawaye Bebi ya fito daga Wakin ya kalle ta dan bata ji fitowar sa ba.



Wucewa sa ta gani ta gaban ta ta kalle shi taga dai shine sai taji tsoron tambayar sa halin da Mama take ciki dan babu wannan fuskar a tare dashi. Mi™ewa tayi kawai tabi bayan sa duk da bata jin dadi amma haka ta tashi ta bishi zuwa office Win da ya shiga, ™wan™wasawa tayi ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ta same shi a tsaye shan ruwa, ya kalle ta ta kalle shi ya sauke jarkar ruwan daga bakin sa ya amsa sallamar sannan tace, "Likita don Allah ya jikin Mamana?."



Kallon ya yayi yaga kamar jiri take a tsayen sai yace, "zauna" ya faWa yana nuna mata wajan zama ta zauna ya ajjiye ruwan ya ™arasa inda take ya zauna akan kujerar da yake zama ko yaushe yace, "jikin ta da sau™i zata samu lafiya." Ta goge idanun ta tace, "yaushe zata tashi?."

"Nan kusa!" Ya bata amsa a ta™aice.



Kafin tayi magana yace, "meye sunan ki?." Murya na rawa tace, "Manal."

Ya maimaita sunan a zuciyar sa kafin yace, "Ina Baban ku?."

"Baya nan yayi tafiya ina ta kiran wayar sa a kashe take."

"Baki da Yaya namiji?." Ta girgiza kai tace, "bani dashi, sai dai Wan Baban mu kuma baya ™asar nan yna Qatar."



Yayi shiru kafin yace, "yaushe Mama ku ta samu ciwon rashin gani?." Manal tace, "ba'a fi shekara uku ba, kuma da tana gani da rana da daddare ne ganin yake raguwa sosai."



Ya girgiza kai kafin yace, "zuciyar fa?."

"Ta riga samun zuciya akan idanun, ciwon baiyi yawa bane sai yanzu." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "zata samu lafiya in sha Allah. Kar ki damu, kwantar da hankalin ki."



"Allah yasa" ta faWa a raunane hawaye na zubo mata. Sosai yaji ta burge shi da alama tana son Mama ta sosai, shi kuma duk wanda yasan darajar iyayen sa yana samun matsayi babba a wajan sa yace, "zaki din shan wannan magani kema shine  zai dinga daidaita sugar jikin ki, but na iya lokaci kawai ba ko yaushe ba" ya faWa yana tura mata maganin gaban ta yace, "ki buWe yanzu ki sha kafin ki tashi."



Da to ta amsa ta buWe  maganin ta ri™e a hannu tana kallon inda taga yasha ruwa, tana niyar tashi ya dakatar da ita ya Wauko mata ya ajjiye tayi murmushi tace, "Na gode." Maganin ta sha ya kalle ta yace, "zaki iya tafiya."



Manal tace, "don Allah zan iya zuwa gida na dawo? Har na dawo Mama bata farka ba?." Ya Waga  mata kai ta tashi ta fita ya sauke numfashi yayi shiru cikin tunani. ganin macen da yayi a motar mahaifin sa yana sake dawo masa cikin zuciyar sa da idanun sa.



Manal daga nan Wakin da take kwance ya koma ta saka takalmi ta fito zuwa bakin titi. Titin kamar anyi shara babu abin hawa ko kaWan  shiru, kasancewar asibitin a cikin gra ne ba'a samun mota sosai a hanyar sai kayi sa'a. Tana nan tsaye sai taji tsayuwar baza ta yu ba sai ya zauna akan wani ™aramin dutse da yake gefen wajan.



Wanda ya kai ta wajan Alhaji Mu'azzam ta gani gaban ta yayi mugun faWuwa ta tashi tsaye tana kallon sa, ganin kamar ita yake nufowa tana ja da baya bata san ta shiga kan titi ba ga mota ta tawo sai jin ta tayi a ™asa tayi ™ara.



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



©žNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



*BOOK 1*

Page 012





Da sauri ya fito daga motar yana kallon ta da take zaune a ™asa a da alama ya taSa ta da motar, kallon ta yake maimaita sunan ta yaga sai waige-waige take yi a ransa yana mamakin har lokacin bata tafi ba kenan, "kina lafiya?." Ya faWa yana kallon ta.  Da sauri ta kalle shi tace, "shi na gani yana kallona, tsoro nake ji dom Allah ka taimake ni."



Kallon inda take kallo yayi yaga babu kowa yace, "waye?."  Ganin a ruWe take sai yace, "tashi." Yun™urin tashi take amma ta kasa dan ta Wan bugu a ™afar ta ya ri™e hannun ta ta tashi tsaye tana Wingishi ta shiga motar shima ya shiga motar har lokacin a tsorace take. 



 Nidai na shiga uku da wannan mutum, wallahi shi na gani yana zuwa inda nake" ta faWa tana kuka. Kallon ta yayi yace, "waye?."

"Wani ne wanda ya taimaka min ya kawo ni nan shine daga baya ya kaini wani gida na gudu, yanzu ma shi na sake gani yana zuwa inda nake."



Tunawa yayi da abinda ya faru a wancan lokacin yayi tsaki dan shi tun a lokacin laifin ta ya gani sam-sam bai san meyasa matan yanzu basa kishin kan su ba. ˜afar yaga ya ri™e tana cize baki yace, "Kina Jin ciwo?." Kai ta girgiza kafin tace, "kaWan ne."

"Kin tabbatar?." Ta daga kai alamun eh.

"Ina zaki je?."

"Gidan mu zanje." Unguwar ta faWa masa ya kaita har bakin layin tace ya isa ya tsaya ta kalle shi taga titi yake kallo tace, "na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."



Da Amin ya amsa ya kalle ta yace, "a gidan zaki kwana?." Ta girgiza kai tace, "A'a yanzu zan koma, bazan iya kwana Mama na asibiti ba."

"Okay" ya faWa a ta™aice ta fita daga motar shi kuma ya juya motar ya tafi.



˜afar na mata ciwo amma haka ta taka zuwa g1da ta shiga gidan su Surayya ta karSi makulli suka fito da Surayya suka shiga gidan. Yana nan yadda ta barshi wanka ta shiga tayi ta fito Surayya na zaune taga tana tafiya da™yar tace, "Meya same ki?." Manal ta zauna tace, "™afata ciwo talemin, bige ni akayi da mota."

"Yaushe? Ta faWa da tashin hamkali.

"Yanzun nan, wannan likitan mai haWe fuskar nan ne ya buge ni tsoron sa nake ji shiyasa ma bance masa ina jin ciwo ba kuma shine ya kawo ni." Surayya tayi dariya ta ce, "ke nima tsoro yake bani, da kina kwance nan fa da nayi abu sai yayi tsaki, ai wannan sam bai kamata ya zama likita ba.



Manal tayi dariya tace, "Dr Huzaifa ya fishi kirki, bara na shirya na koma. Baba bai dawo ba ko Surayya?."



"Bai dawo ba gashi naji ana zancen ba'a samun sa waya." Manal tace, "Allah yasa lafiya" ta faWa tana shiga Waki ta jiyo Surayya na cewa, "Wazu Mubeena tazo gidan nan ai." Manal bata ce komai b dan lamarin Mubeena yanzu tsoro yake bata ba iya mamaki ba. Shiryawa tayi cikin doguwar riga kusan ko yaushe kayan ta kenan, doguwar riga musamman abaya ta Wauki wasu a leda harda sabulun wanka ta Wauka da humrar da turare duk ta saka a leda ta fito tace, "Surayya zan koma."



Suka fito tare da Surayya tana cewa, "Milky dare yayi baza ki bari sai gobe ba?." Manal tace, "bazan iya ba wallahi, gwara na koma hankalina zai fi kwanciya, in ina na bazan iya bacci Mama na can ba, to in ta farka ma fa?" ta faWa tana kulle gidan ta bawa Surayya makullin kafin tace, "tafi dashi ina shiga Mama han ni tafiya zata yi, bara na shiga na gaida su Umma." Surayya tace, "to nima bara na kawo miki abinci kafin ki fito." Ta amsa da to ta shiga gidan Baba da sallama jin muryar ta aka amsa a daqile tace, "Umma ina wunin ku?."



Wacce ta kira da Umma tace, "da ban wuni ba ai baza ki ganni ba, ana can ana yawon banza an fake da uwa babu lafiya, a haka dai za'a ™are uwa yawon banza ya haka ™anwa ma haka. To haka ne mana tunda a hanya aka tsinto uwar, waye ya sani ma ko duk a yawon banzan aka samar daku?.



Ajiyar zuciya Manal tayi bata ce komai ba saboda darajar Baba, amma badan Baba ba wallahi sai tayi mata tas nan gaba ta kiyaye bakin ta, to ko babu komai Baba uba ne a wajan ta.



T fito ta shiga gidan su Surayya dan bata fito ba Maman su take cewa ta zauna taci abincin sai ta tafi haka kuwa akayi taci ta ™oshi, a nan take faWawa Mama wanda ya kawo ta Mama tace,  An gode masa, Amma Manal kar fa ganin Mama na kwance ya saka ki dinga yin abinda ba halin ki ba, wancan lokacin na san ruWewa ce ta saka ki shiga motar wanda ya kai ku asibitin wannan lokacin fa?.



Manal tayi shiru Mama tace,  ba halin ki bane kar ki fara yanzu, duniyar babu yarda a ciki masu zuciyar taimako kaWan ne Manal. Manal tace,  zan kiyaye in sha Allah Mama.

 Allah ya tsare, sharrin mutum da aljan yasa ku fi ™arfin su. Suka amsa da amin sannan ta fita zuwa kan titi ita da Surayya zuwa lokaci har anyi sallar i'sha.



Bebi kuwa koda yayi gaba ja yayi ya tsaya haka nan yaji bazai iya tafiya ya bar Manal Win ba bayan tace masa asibiti zata koma ba, in Kausar ce ko Mimi ko Lubna bazai tafi ba, kuma shi duk wata mace a duniya indai ta ri™e mutuncin ta yana matu™ar kishin ta, baya so yaga ta wula™anta haka nan Allah ya halicce shi shiyasa in ba Allah ne ya kiyaye ba mace zatayi saurin cutar sa saboda raunin da yae dashi a kanta.



Tunawa yayi da abinda ya faru da wanda tace ta gani a bayyane yace,  in wani abun ya same ta kamar ina da alhakin hakan.



Yana hango su madubi akan titin sai taSa ™afar ta take yi ya ™araso da motar ya tsaya ya sauke glass ya kalle ta itama ta kalle shi tana son yin magana amma babu wannan fuskar hakan a tare dashi, ganin tayi shiru bata ce komai yace, "shiga na mayar dake.



Ta kalli Surayya itama ta kalle ta, da ido Surayya tayi mata alama da ta shiga hakan ya saka tace, "Sury sai kin zo, na gode."

"To Milky Allah ya ™ara lafiya" ta faWa tana juyawa ita kuma ta shiga motar haka nan take jin gaban ta na faWuwa. Bata taSa shiga motar wani ba tunda take, ita adaidaita sahu ta saba hawa shiyasa take a takure ga faWan da Mama tayi mata sai yawo yake mata. Gata ga namiji dai a mota bata taSa yi ba sai yanzu, gabaWaya a takure take sai addu a take dan Wazu a ruWe take.



Tana shiga khamshin turare ne ta ya kai masa ziyara, ya kulle ido ya buWe a duniya baya son khamshi mai ™arfi yanzu sai ya Sata masa rai ko ya saka shi ciwon kai, hakan ya saka baice komai ba ya kunna a.c sosai a motar yaja suka tafi.



Baice komai ba bata ce komai ba sai wayar sa da aka kira ya Wauka yace, "Na am Mummy." Shiru yayi alamun ana magana kafin yace, "Yanzu zan dawo, bazan wuce mintina goma ba in sha Allah. Yanke wayar yayi ya cigaba da tafiya har bakin asibitin ya kai ta ya faka daga gefe ta kalle shi kamar Wazu ba ita yake kallo ba tace, "na gode, Allah ya saka maka da alkhairi."



Da amin ya amsa kawai ta fita ta shiga shi kuma ya wuce gida yana tsaki bai san meyasa mata suke son saka turare ba bayan sun san haramcin da yake cikin hakan. Inda Mimi ce ko wata cikin ™annen sa ta isa ta shigar masa mota tana wannan khamshin? Itama kawai saboda taimako ne.



Yana gab da gidan yaga an sauke Maryam a mota ya girgiza kai zuciyar sa na zafi a bayyane tace, "zanyi maganin abun" ya faWa yana shiga da motar gida ya shiga wajan Mama.



Mama na tsaye da hijjabin tace, "au ka dawo?, shirin tafiya nake ai daman gidan Hajiya zani na jira ka shiru shine zamu tafi da Mimi."

"A daren na Mimi zata ja mota Mummy? Muje na kai ki."

"Daga dawowar ka baka ci abinci ba, baka huta ba kace zaka kaini?.

"Bana jin yunwa naci abinci da yamma" ya faWa yana fita Mama ta fito ita da Mimi ya buWewa Mama baya ta shiga ya shiga shima Mimi ta shiga.



Tsaki taji yayi gaban Mimi ya faWi dan tasan da ita yake yace, "Mummy meyasa basa jin magana ne? Meya amfanin saka wannan banzan turaren da daddaren nan?. In ma turaren yana da daWi da sau™i, amma wannan turare kamar na aljanu?.



Mama tayi dariya tace, "ikon Allah, ni na jima banga mutumin da baya son turare ba sai kai, kamar mai aljanu? Baza a yi na haya™i kana nan ba, baza a saka a jiki ba. Ke Mimi koma ki canja rigar kizo mu tafi in ba haka ba kafin muje aljanun sa zasu iya tashi."



Mimi ta fice tana ™un™uni haka kawai ya hana su saka turaren da suke so dan kawai shi baya son yaji khamshi na tashi sosai, shi wai daga dry spary sai body mint kawai zakayi amfani dashi, ko yaya ka saka mai ™arfi in kazo inda yake yaji yayi ta bala'i kamar a jikin sa aka saka. Kuma Mummy ce take goya masa baya shiyasa ya samu damar ham turaren wuta a falo ko su saka turare. Mimi na mita ta canja kaya ta dawo ta shiga motar suka tafi dan tasan badan Mama ba bazai jira ta ba.



       A can gidan Hajiya

10 / 27