Chapter 18 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 27

51K to 54K   out of 80K words

sa.



Bayan sallar magriba Huzaifa da Hamza suka zo gidan wajan Bebi, har wajan Mummy suka je suka gaishe ta take cewa, "mutumin naku ma da ya dawo bai shigo min ba, na lura tun Wazu kamar bashi da lafiya." Hamza yace, "Mun ga hakan, yau ko damu bai haWu ba ya dawo gida." Huzaifa yace, "bara muje wajan sa Mama." Ta amsa suka fita suka shiga wajan Bebi suka same shi a kan kujera ya harWe hannayen sa waje Waya yana kallon ™asa.



Hamza ya zauna kusa dashi yace, "Me yake faruwa ne ka koma haka Bebi?." Šago kai yayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "ni kaina ban sani ba, wani iri nake ji a zuciyata kamar nayi kuka. Zuciyata tayi min nauyi sosai, na rasa gane kaina nima."

Huzaifa yace, "me ya kawo hakan?."

Tsaki yayi a bayyane kafin yace, "Wata yarinya ce, haka nan na kasa daina tunanin ta." Hamza yayi dariyar sha™iyanci yace, "shine ka shiga wannan damuwar Bebi?, Kamata yayi kayi murna ai ka samu wacce kake so ko babu komai ka samu mafita akan lamarin Rumana."



Huzaifa yace, "Yanzu akan wannan ne duk ka tayar mana da hankali?, wallahi na Wauka wani babban abu ne yake shirin faruwa ko ya faru."



Bebi yace, "ni ba Waga hankalina nayi ba, na tabbatar ina sonta na amince tun ban amince ba na yarda yanzu, amma abin ne yayi min yawa a zuciyata, kwata-kwata magana sau biyar bana tunanin ta shiga tsakanina da ita, amma yadda nake ji zuciyata na bugawa soyyayar ta tayi yawa." Hamza yace, "tsakanin so Win kenan Bebi. Kuma shi so ina ruwan sa da baku yi doguwar magana ba? Daga kallo Waya ana faWawa soyayya."



Bebi a raunane yace, "tun yanzu?, Tun kafin mu saba ina jin haka a kanta ina ga nan gaba?. Wallahi bana son soyayyar da zata wahalar dani Allah ya sani, bana son soyayyar da zata hanani sukuni. Can you imagine Wazu kafin na tafi office sai da naje bakin layin su kawai ko zan ganta?. Na kuwa ganta Win, amma ita da wani namiji da ban san ala™ar su ba. Yanzu wannan soyayyar da na sakawa zuciyata in an yi mata miji fa ya zan yi?."



Huzaifa ya girgiza kai yana murmushi, Allah ne ya kama shi ko yaushe gani yake shi zai saka soyayya a zuciyar sa dan haka sai yadda yaso, Gashi Allah ya nuna masa iyakar sa, ya nuna masa shi ke saka soyayya a zuciyar bayin sa. Huzaifa yace, "Wannan ba abin damuwa bane, kayi addu'a akan lamarin ta?."



"Nayi, tunda na fara tunanin ta na fara addu'a, sai bayan nayi addu'ar nake ji tana sake shiga raina sosai." Hamza yace, "magana ta ™are kawai, kaje ka nemi izinin ganin ta wajan iyayen ta, kaga in kaje in ma da maganar auren a kan ta zaka ji."



Ya girgiza kai yana kallom su da manyan idanun sa yace, "ina niyar hakan, amma zuciyata baza ta jure ace na yi mata miji ba Hamza, a yadda nake ji in akace an yi mata miji zan...." Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai.



Hamza yayi dariya yace, "kar ka damu khairan in sha Allah, mallakin ka ce  wannan yarinyar da izinin Allah." Huzaifa dariya yake yi sosai yana kallon Bebi kafin yace, "Bebin Mummy manya, Wai wacece yarinyar ma?." Hararar sa yayi dan kuwa bazai faWa musu ba sai ya tabbatar komai ya tabbata sannan zasu san wacece.



Hamza ma dariyar yake yi yace, "ka share batun Huzaifa, kaje gobe ka samu iyayen ta akan maganar." Bebi ya wara ido yace, "har sai gobe? Meye amfanin yau?." Hamza da mamakin gaggawar Bebi yace, "kana da theater amma kace yau ko?."



"Eh amma sai goma na dare ai, in banje ba bazan samu nutsuwar yin aikin yadda ya kamata ba, so nake naji an tabbatar min babu maganar aure a kanta."



Hamza yace, "to maza ka shirya kaje yanzu mutumina, Allah ya bada sa'a." Kamar mai jiran umarni sai kuwa ya mi™e ya shiga Waki. Hamza da Huzaifa suka ™yal™yale da dariya har suna tafawa. Sun ji daWin yadda Allah ya kama shi tun ba a je ko ina ba, cika baki akan soyayya ya ™are tunda ya samu wacce yake yiwa son da bai yi zato ba.





Nana Haleema>ΨBέ>Ψφή<Ψϋί



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



                 ©ώNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu. https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36





_Kina neman inda zaki siyi abinci mai daWi? Kina ™iyar yin girki gashi zaki yi ba™i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daWi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daWi akwai a lallaSa. Kina son ki siyi abincin da zaki Wauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daWi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan Sangare, tazo muku da nau in abinci kala-kala na gargajiya da na ™asar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ™asan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr



Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuWi gida.



*BOOK 1*

*Page 020*





Adnan dariyar su ya jiyo daga Waki sai ya fasa abinda yayi niya ya fito yana kallon su Huzaifa ya kalle shi yace, "ka fasa tafiyar ne Wan soyayya?." Sai shima ya samu kansa da yin murmushi ya kama ™ugu yace, "abin mamaki ko? Wai ni Adnan da son wata mace bayan soyayyyar yarinta." Hamza yace, "ba abin amma ki bane ba, ka kai kayi Win ne. Ka koma ka shirya ka ™yale wannan yana da wacce zai aura a hannun sa."



Huzaifa ya tashi yace, "tafiya zanyi ma ni." Hamza yace, "jira ni" ya kalli Bebi bayan ya tashi tsaye yace, "kar kayi wasa mutumina, kaje da zafi-zafi ake dukan ™arfe, Allah ya daidai ku. Na san baza ka zaSo ta banza, duk yadda aka yu tarbiyya da kyau ka gano, dan na san ka akwai son abu mai kyau."



Bayan su ya biyo zuwa harabar gidan suna hira, lokacin sallah yayi Adnan yace, "amin, in ma da biyu ka yi addu'ar in sha Allah zamu daidaita." Suna dariya su biyun shi kuma yana tsakiyar su.



Suna nan tsaye Mimi ta fito cikin riga da siket ΄an kanti sun kama ta musamman rigar, ita da ™awar ta suka fito suna hira sai da suka zo kusa dasu Bebi suka gaisa suka wuce, ta raka ta har bakin gate ta fita sannan ta juya ta koma ciki.



A lokacin su Huzaifa suka hau mota suka tafi shi kuma ya wuce ciki rai a Sace saboda abinda Mimi tayi. Yana shiga yace, "Ke Kausar ina Mimi?." Mimi ta fito da plate a hannu tace, "Gani."

"Wanne irin rashin hankali ne zaki dinga fita waje a haka? Kalli kayan jikin ki, don baki da hankali a haka kike yawo daman?." Ta kalli kanta ta kalle shi tace, "Yaya a cikin gida nake fa."



"Zan tsinke ki da mari in kika sake min magana, kin fini sanin a cikin gidan ki ke?. Wannan wanne irin hauka da shirme ne da kuma rashin hankali?. Kin fito ko mayafi babu kina ganina da Saki maimakon ki dawo ki saka mayafi sai kika wuce ke ga ΄ar gayu ko?." Tayi shiru tana kallon wani wajan Mama ta fito daga Waki taji duk abinda yake faWa tace, "Mimi jeki ki sauke min naman can a kan gas." Hakan ya saka ta wuce Kausar ta tashi ta bita dan wallahi Bebi haushi yake basu wani lokacin dan babu yadda zasu yi dashi ne.



Mama ta kalle sji tace, "Bebi yanzu dan ta fita harabar nan a haka meye laifi don Allah da zaka zo kana mata wannan faWan?, Ka dinga sassautawa yaran nan wani lokacin takurar tana yawa sosai."



Bebi yace, "Mummy tana ganina da ba™i fa, ai sai ta dawo ta saka mayafi sannan taje su gaisa. Sun kasa gane bana son abinda suke yi ne kwata-kwata."

"Sai kayi ha™uri, aure zasu yi su bar maka gidan." Ya juya ya fita bai ce komai.



       Sallah yaje yayi ya dawo yana tunanin abinda zai yi saboda da ya keSe kansa tunanin Manal ke zuwa zuciyar sa. Kamar an bashi umarni sai ya tashi shiga Waki ya shirya cikin manyan kaya da suka yi kyau sosai harda hula, kallon kansa yake a madubi yana jin ™arfin guiwar zuwan, zuciyar sa na sake bashi shawarar Tafiya gidan su Manal. Ya sauke numfashi ya fita ya hau mota ya tafi gidan su Manal kai tsaye.



Sai da ya tsaya a ™ofar gidan sai kuma ya rasa abinda zai yi, yana zaune a mota yana kallon gidan kasancewar akwai haske a layin dan da wutar nepa ko ina da haske har ™ofar gidan su. Baba ne zai shiga gidan suna tsaye da Haroun suna magana a ™ofar gidan, ganin hakan sai Bebi ya fito daga motar ya ™aarasa inda suke yana zuwa yayi sallama Baba ya amsa masa sai ya saki murmushi yace, "A'a dr Adnan, barka da zuwa."



Adnan yayi murmushi yace, "barka da dare Baba."

"Barka dai likita, ya aiki?."

"Alhamdulillah, ya masu jiki?."

"Da sau™i sosai duk sun samu lafiya. Haruna wannan shine likitan da suka taimaka lokacin da su Manal basu da lafiya, shine wanda na baka labari ko naira biyar basu ™arba ba." Suka gaisa da Haroun yace, "Allah ya saka da alkhairi, Wazu ma Manal tayi min wannann zancen, taji daWi sosai, Allah ya biya."  Ya amsa da amin. Baba yace, "ya kamata ka shiga ku gaisa in da damar hakan."



Bebi yace, "babu damuwa Baba, daman wajan ka nazo Baba." Baba yace, "wajena kuma? To mu shiga ciki" ya faWa yana shiga cikin gidan Adnan ya biyo bayan sa yana mamakin kansa wai shine yazo tambayar izinin neman wata yarinya.



Tun daga soron gidan yake jiyo muryar ta tana bada labari tana dariya da alamun tana cikin nishaWi, sai daga baya yaji muryar Mama tana cewa, "Manali Allah ya shirye ki, kice kin yi samari duk babu labari sai yanzu da Allah ya matsa bakin ki." Sai tayi dariya tace, "Amin Mama. Sosai ma kuwa, kawai bana faWa miki ne, amma yanzu zaki sani." Sallamar Baba ya saka suka yi shiru suka kalli Baban sai Baba ya juya yaga Adnan bai shigo ba yace, "Dr shigo mana."



Dr Adnan ya shigo da sallama yana kallon tsakar gidan, kai tsaye suka haWa ido da Manal da take zaune da doguwar riga a jikin ta ta saka huta a kanta wacce ta ja ta baya gashin ta ya Wan fito ta gaba.



Suna haWa ido abinda yazo mata kawai wula™ancin da yayi mata amma sai bata nuna ba dan ya taimaki Mama hakan ya saka tace, "Dr! Sannu da zuwa." Ta kalli Mama tace, "Mama Dr da ya kula dake ne fa."



Mama tayi murmushi tace, "ai daga jin sallamar na gane Wauki murya, kuma naji kin ce Dr. Sannu da zuwa." Sai yayi murmushi ya kalli Manal sai yaga ta wara idanu waje tana kallon sa dan ita mamaki take daman yana sakin fuskar har a ga ha™orin sa?.



Har kan tabarmar da suke kai ya ™arasa ya gaida Mama ta amsa da fara'a tace, "Ya aiki?."

"Alhamdulillah, ya jikin?."

"Jiki da sau™i, Wazu nake cewa Manal kinga ina jin sau™in Idon nan da alama dai abinda ka faWa zai tabbata." Yace, "indai za'a dinga shan maganin ana ganin likita babu abinda zai faru sai alkhairi."

"Allah yasa, sai dai ga Manal nan bata shan nata maganin da aka bata wallahi." Manal da take gefe ta turo baki tace, Allah Mama ina sha, maganin ne daWi fa."



Kallon ta yayi yana jin wata irin kewa a zuciyar sa kamar baya tare da ita, Allah ya saka masa son ta farar Waya a lokacin da bai shiryawa hakan ba. Wani abu yake ji yana jan sa zuwa gare ta musamman yanzu da take magana, hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallo har sai da yaji Mama tace, "™arya kike Manal, bakya sha ni nasan halin ki fa, kuma magani ai ba dan daWi ake sha ba." Manal ta kalle shi suka haWa ido sai ya janye idon sa tace, "ina sha, kawai Mama ce take cewa bana sha."



Baba yace, "kun barshi a dur™ushe sai magana kuke yi, Dr taso mu shiga ciki." Adnan baiyi musu ba ya tashi suka shiga falon Baban yana jiyo maganar Manal cikin shagwaSa Maman na sake gwale ta kamar dai kawaye baza kace uwa da ΄a bane ba.



Baba ya zauna Adnan ya zauna a ™asa Baba yace, "Haba Dr, tashi ka dawo sama don Allah." Adnan yace, "Babu komai Baba, nan ma yayi." Baba yace, "Allah yasa Lafiya."

"Lafiya lau Baba."

"To ina jin ka." Bebi yayi shiru yana tunanin ta ina zai fara kafin ya aro jarumta yace, "Baba nazo ne akan maganar Manal."



Baba yace, "To wani abun ne ya faru? Ko a kan ciwon nata ne?." Bebi ya girgiza kai yace, "Ba akan ciwon ta bane Baba."

"To ina jin ka."

"Baba nazo ne daman akan in ba'a yi mata miji ba ina so a bani dama da izinin magana da ita."



Nan da nan Baba ya saki fara'a yace, "Ikon Allah, Manal dai tawa?." Adnan ya Waga kai Baba yace, "Ba'a yi mata miji ba Adnan, dan kullum cikin rigima ake da ita akan ita baza tayi aure ta bar Mama ba, ka ganta nan kamar yarinya ™'arama haka take. Adnan naji daWi sosai wallahi, ace Manal ta samu kamar ka ya furta yana neman izinin zuwa wajan ta babban abin farin ciki ne, dan mutum nagari ba ya neman wacce bata gari ba, naji daWi sosai musamman yadda baka je gare ta kai tsaye ba kazo ka same ni."



Baba ya sake cewa, "naji daWi sosai Adnan, nayi farin ciki wallahi. Amma sunan ka kawai na sani ko sunan mahaifin ka ba ban sani." Bebi yace, "Adnan Mu'azzam Alhassan, mahaifina shine tshon minister na harkar noma. Kamar yadda ka sani Baba ni likitan zuciya ne, asibitin da muke aiki dashi na mu ne wanda muka wallafa shi da kan mu."



Baba ya girgiza kai yace, "ma sha Allah, ™warai nasan sunan mahaifin ka a kafafan sada labarai, Allah ya bada nasara. Shikenan Adnan, Gobe in Allah ya kaimu sai kazo ku tattauna da ita Manal Win, abinda ya sa bazan ce yanzu ba ina so na sanar da mahaifiyar ta in muna da rai gobe sai a baka damar magana da ita."



Adnan ya girgiza kai yace, "Na gode Baba, Allah ya ™ara lafiya." Ya amsa da amin yana murmushi kafin yace, "ai ni naji daWi sosai, iya zuwan nan da kayi neman izini wajena baka fara tunkarar ta kai tsaye ba ya tabbatar min da nagartar ka da kuma tarbiyyar da ka damu a wajan magabatan ka, Allah ya tabbatar da alkhairi yasa kai ne rabon ta." Sosai yaji daWin wannan addu'ar yayi murmushi ya amsa da amin kafin ya saka hannu a aljihu ya Wauko kuWi ya ajjiyewa baba yace, "Baba a rabawa yara."



Baba yace, "harda hidima?."

"Babu komai."

"To Allah yayi albarka." Ya amsa da amin yayi masa sallama ya taso ya fito tsakar gidan da son sake ganin ta amma bata nan sai maganar ta da yake ji tana dariya, yayi murmushi ya fita zuciyar sa kamar an wanke masa haka yake ji saboda farin ciki.



Falon Baba ya shiga ya kalli Manal yace, "Mubeena bata nan ne?." Manal tace, "Tunda ta fita tace taje makaranta har yanzu bata dawo ba." Baba ya girgiza kai ya zauna ganin hakan sai Manal ta tashi ta koma tsakar gida bayan ta Wauki sabuwar wayar ta daman kallon wani American series da take kalla, dan tana a son su tana ™aruwa a fannin ingilishi sosai.



Baba ya kalli Mama yace, "Kin san abinda ya kawo Adnan gidan nan?." Ta girgiza kai tace, "ban sani ba, amma nasan bazai wuce zance akan ciwo na ba ko?."



Ya girgiza kai alamun a'a yayi murmushi yace, "addu'ar da kike yiwa Manal a ko yaushe itace take bibiyar ta, shiyasa nake faWa miki ki dinga haWawa da Mubeena saboda bakin ki akwai kaifi kasancewar ki mahaifiya. Addu'ar ki bata da hijjabi a wajan Allah, da kin yi addu'a a kan yaran ki da Allah ya amsa, ko yaushe zaki ce Manal Allah yayi miki albarka amma sai ita Mubeena bakya faWar hakan a kanta. Inda kina faWa kina fatan Allah ya shirya miki ita da yanzu wata™ila ta shiryu, ki dinga haWawa da ita domin ta samu itama alkhairin bibiye ta."



Mama tace, "ka lasa min zuma a baki, ka sanar dani abinda yake faruwa don Allah."

"Yazo ne akan yana so a bashi izinin zuwa wajan Manal a matsayin wanda yake neman auren ta." Mama da mamaki tace, "auren Manal kuma? Shine yake son auren ta?." Baba yace, "shine abinda ya kawo shi, naji daWi kuma da ya fara tambayar izini bai fara magana da ita ba hakan ya nuna yasan abinda yake yi yana kuma da tarbiyya da sanin ya kamata."



Mama sai tayi murmushi da farin ciki tace, "ikon Allah! Yanzu shi likitan da kansa ne yake son Manali ta? Kai alhamdulillah Allah na gode maka, ko yanzu Allah ya karSi raina nasan addu'ata na bibiyar Manal."



Baba yayi murmushi ganin tana farin ciki sai tace, "to a ina ya santa? Ko kuma zaman asibitin ne ya saka har ya fara sonta?."

"Shi so a lokaci Waya ma ai shiga zuciya yake balle kuma anyi kwanaki."

"Kaji ikon Allah, Allah Alhakim, daman silar haWuwar sa da ita ne ta kaimu wannan asibitin. Naji daWi sosai wallahi, Baban Manal tun daga kan taimakon da ya yi mata ya kawo ta gida bai barta a titi ba, ganin dare yayi ya jira ta ya mayar da ita asibitin, tunda ta bani labarin nan na tabbatar yasan darajar Wan adam yana kuma girmama mace."



Baba

18 / 27