Chapter 2 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 27

3K to 6K   out of 80K words

Kai tsaye Bebi Sangaren mahaifiyar sa Mama ya shiga wacce shi kaWai yake kiran ta da Mummy kowa Mama yake cewa, amma shi tun yana yaro yake cewa Mummy har girman sa. Yana shiga  ya same ta a zaune ita ™anwar sa Mimi ya ce, "yanzu Mummy abinda yarinyar nan Maryam take yi daidai ne? Miji ya rabu da ita ya sake ta amma ya dinga bibiyar ta har yana Waukafr ta a mota? Akan wanne dalili?."



Mama tace, "to Bebi ni me zance? Ina ruwana tasan daidai ai sannan tasan ba daidai ba." Ya kulle idanun sa bala'i kishi yake ji yana addabar zuciyar sa ya kalli Mama yace, "shikenan sai a zuba mata ido kenan?."

"To maganar taka me ta canja? Su mazan yayyen ta akwai wanda ya damu da yayi maganar ne?, kai kaWai ka ke tayar da jijiyar wuya akan lamarin Maryam da Lubna."

Bebi ya girgiza kai kawai yace, "bazan bari ba kin san da hakan Mummy." Mama tayi dariya tace, "shikenan Bebi, zaka dinga asarar maganar ka kuwa dan ba ji zatayi ba ita da kanwar ta." Kallon Mimi yayi kamar zai yi magana sai ya fasa ya fita ya shiga mota kai tsaye ya bar gidan.



Nana Haleema.



*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025



    ©ş *Nana Haleema.*



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp





*BOOK 1*

*Page 002.*







Getting better specialist hospital ya nufa, babban private hospital da ya samu lambar yabo a fannin abubuwa da yawa, asibitin shine private hospital na farko da aka fara dashen zuciya a cikin sa arewancin nigeria, asibitin ya haWa manyan likitoci masu ™warewa a kan aikin su. Asibitin gabaWaya sa an gina shi ne zuciya, da abinda ya shafi cututtukan jini, da abinda ya shafi Sangaren mata, sauran abinda bai shafi wannan ba ana yi ne kawai amma ba dan saboda haka aka gina shi ba sa. Asibitin mutane huWu ne suka cure waje guda suka samar dashi, kuma suna matu™ar kula dashi sosai, shiyasa ya zama asibiti mafi ™olowar masu zuwa da kuma tsada, a duk shekara suna yin aikin kyauta ga masu bu™ata ta musamman, wannan dalilin ya saka sunan asibitin Getting Better ya zaga ko ina.



Bebi ya faka motar a babar harabar asibitin ya shiga cikin asibitin da babu mutane sosai ya hau sama ya buWe wata ™ofa ya shiga office Win da ya kasance mallakin sa. Kafin ya zauna maza guda wanda baza su wuce sa'anin sa ba suka shigo Waya ya ce, "Haba Bebi kasan kai ake jira tun Wazu kace min gaka nan sai yanzu?." Bai kalle shi ba ya nemi waje ya zauna suka kalli juna Huzaifa yace, "yau kuma waye ya taSo ka haka?." Hamza yace, "naga sai tiriri yake yi shi kaWai. Kasan da yake shi Sacin ran sa baya Suya." Baice komai ba ya buWe laptop sai kuma ya rufe ya dafe kansa baice komai ba har lokacin.



Huzaifa yace, "ko zancen Rumana ne?." Daman ™iris yake jira ayi masa magana ya Wago a fusace yace, "wacece ita? Me take dashi da zancen ta zai dame ni har ya Sata min rai?." Huzaifa yayi dariya yace, "masoyiyar kace wacce kaso kamar ka mutu, dan kayi tunanin ta har ya saka ka wannan damuwar ai ba wani abun bane."

"Mtswwww!" Ya ja tsaki yana mi™ewa tsaye. Hamza yace, "Bebi ni banga abin Sacin rai akan batun Rumana ba, yarinyar nan tun asali ita ka ke so tayi aure ta barka yanzu kuma  ta fito tana bibiyar ka meyasa baza ka amince ba?. Ka sani na sani kana son ta meye na damuwar."



Juyowa yayi ya kalle shi ransa na sake Saci  yace, "nayi maka kama da wanda zai auri bazawara? Nayi maka kama da wanda zai auri ragowar wani?. Look Hamza!  Kasan bana son wannan maganar, ka bar maganar kawai, kai ka san ba ko wanne Sacin rai nake iya jurewa ba." Huzaifa yayi dariya yace, "to waye ya Sata maka rai haka?."

"Waccan yarinyar Maryam mana, mijin ya ya sake ta amma a dinga bibiyar ta har tana bashi fuska suna fita, ina suke zuwa? Meye ala™ar su? Meye rage a tsakanin su yanzu?."



Huzaifa yace, "wai Yayarka Maryam ka ke cewa waccan yarinyar?." Bai samu damar bashi amsa bama Hamza yace, "wannan Sacin ran ai ba shine mafita ba, samun sa zaka yi ki yi magana ya daina zuwa wajan ta in ba haka ba ka Wau mataki."

"˜yale shi, wallahi in yayi wasa dani I'll take him to court over this matter. Bai san waye ni bane shiyasa." Hamza yayi dariya yace, "a nutse zaka same shi kunyi magana,in bai fahimta ba sai ka Wauki matakin da ka ke ganin ya dace. Amma ita Maryam Win itace mai laifi, da ita zaka fara dan da bata bashi fuska na da hakan bai kasance ba." Ajiyar zuciya Bebi yayi Huzaifa yace, "A rayuwata kaf ban taSa ganin namiji mai kishin ´an uwan sa kamar ka ba, shiyasa nake so nayi ko yi da kai amma Allah ba haka ya halicce ni ba, ina son ´an uwana ina kishin su amma ba kamar kai ba."



Dawowa yayi a zauna ya lumshe idanun sa kafin ya buWe ya kalle su kamar zaiyi magana sai ya fasa a saka buWe laptop yana aikin dannawa. Hamza yace, "ni na wuce gida naga kai kana da ba™i anjima ni kam na tashi."

"Nima haka, Bebi sai mun yi magana" yana faWa suka fita duk barshi yana aikin sauke Ajiyar zuciya.

Bai jima sosai ba shima dan mutane biyu kawai ya gani a kulle ya fita ya hau mota ya nufi gida a lokacin magriba tana daf da yi.



Babban falo ne mai kyau da tsari tana zaune a ciki da budurwa guda Waya a gefen ta tana turaren wuta yana tashi a hankali, kallon yarinyar tayi tace, "Mimi ki dakata da yin wannan turaren wutar na, kin san Yayan ku yana hanya ko?." Wacce aka kira da Mimi ta Sata rai tace, "Wai shikenan Mama saboda shi sai mu daina turaren wuta saboda Allah?." Mama tace, "to ai ke kin san baya so ko?."

"To Mama dan baya so ai ba gidan sa bane." Kafin Mama tayi magana wata ta fito daga Waki ta kalle ta tace, "Yaya Farida kin kina jin abinda Mama take faWa, yanzu don Allah saboda Yaya Bebi shikenan sai mu daina turaren wuta a falon nan? Komai in baya so Mama baza'a yi ba kuma yana da nasa Wakin fa."



Anty Farida ta zauna tana dariya tace, "gaskiya dai Mama maganar Kausar da Mimi gaskiya ce, akan sa sai a daina turaren wuta don Allah?." Mama tace, "sanin kan ki ne baya son turare, da ya shigo zai sar™e shi yayi ta tari akan me za'a yi abinda za'a cutar dashi?." Mimi ta taSe baki Yaya Farida tace, "ya kusa ma ai yayi aure ya tarkata ya bar magana gidan kowa ma ya huta. Ban taSa jin mutumin da baya son turare kamar sa ba, shi ko kusa dashi zaki je to kar ki saka turare mai ™arfi. Matar sa ta shiga uku." Mama tayi murmushi tace, "shida Rumana ba, in sha Allah hakan ya kusa tabbata. Rumana ai ta san halin sa tun ba yau ba." Mimi da Farida suka haWa ido basu ce komai ba.



Fita Kausar tayi karSowa Mama sa™o wajan masu kawowa lokacin da ta shigo take cewa, "Mimi kin san ga motar Yaya Bebi tana nufo gidan nan ga kuma Lubna can a zaune tana zance ko mayafi babu, kin san babu abinda zai hana shi magana wallahi." Da sauri Mimi ta tashi ta le™a taga ta hango Lubna a zaune tana hira da saurayin ko mayafi babu a jikin ta, gashi fitted gown ta saka dakyar ta iya zama a akan kujerar saboda ta matse ta.



Sakin labulen tayi tace, "ni da Yaya Adnan zai ji wallahi ya daina shiga harkar Lubna da Anti Maryam, Wazu akan ya yi magana akan tsohon mijin Anti Maryam ke baki ji yadda suka dinga magana a gidan nan ba." Anty Farida tace, "akan me zai daina shiga harkar su?, dan Maryam ta kasance Yayar sa Lubna ai ™anwar sa ce, kuma shine ido a gidan nan tunda sauran mazan duk sun yi aure sai shi kawai namiji babba a gidan nan. Duk abinda kuka yi hukunci ya hau kan ku abinda ya kamata ya dinga yi kenan." Jin an buWe gate ya aka Mimi da Kausar saurin buWe taga suna kallon Bebi ya shigo ya faka motar ya fito ya tsaya cak yana kallon ´ar rumfar da take harabar gidan su wacce Lubna take zaune ya hango suka haWa ido da ita Lubna Win.



Da sauri suka ga ta tashi a guje tayi cikin gida Sangaren Mamy Mimi tayi dariya tace, "ashe rashin kunyar ta ™arya ce." Kausar tace, "Yaya da jawowa kai magana yake, kalli ya nufi wajan saurayin nata ko me zaice masa oho." Anti Farida tace, "maza yazo ya same ku kuna le™e ya haWa har ku." Ganin ya juyo falon sai suka bar wajan a guje suka dawo suka zauna Anti Farida tayi dariya Mama ma tayi tsaki kawai bata ce komai ba.



     Da sallama ya shigo sai yayi turus yana yamutsa fuska, sam sam baya son ™hamshin turaren wutar nan ko kusa, baya son turare mai ™arfi yafi son turare mai sanyin khamshi baya son turaren da zai ji shi ya dabaibaiye shi lokaci Waya. Kansa sarawa yake a duk lokacin da ya ji hakan, lokaci Waya jiri sai ya fara ™o™arin kayar dashi. Mama ta kalle shi tace, "Adnan ™araso mana ka tsaya." Ya tako ya ™araso bayan ya cire takalmin sa yace, "™hamshin falon ya canja." Yaya Farida tace, "kai ka cika iyayi wallahi, yanzu ina khamshin yake da zaka fara Satawa mutane fuska?. Kai haka za'a kai matar ka baza ka bari tana turaren wuta ba?."



Ya kalle ta fuskar sa kamar ko yaushe ba yabo babu fallasa yace, "bana so, sai aka ce sai an yi min dole?."

"Kar kaso" ta faWa tana hararar sa. Sai taga yayi murmushi wanda ba ko yaushe ake ganin sa a kan fuskar sa ba sai mai sa'ar gaske ne yake ganin Murmushin sa tace, "lallai akwai abinda ya saka ka farin ciki, Tunda har Bebi yayi murmushi akwai abinda zai faru."



Mama tayi dariya tace, "kamar wasa kin saka masa suna Bebi ya bishi tun kuna yara. Adnan ne baki iya cewa ba sai Abban ku yace kawai ki ce masa Baby ke kuma sai ki ke cewa Bebi. Gashi yanzu Adnan ya Sace a gidan na sai Bebi, da gaskiyar sa da yace sai yaci tarar ki."  Anti Farida tayi dariya tace, "Bebi kuwa har jikokin sa, a katin Waurin auren sa ma sai an rubuta Bebi.



Baice komai ba ya kalli Mama yace, "Mummy barka da yamma." Tayi murmushi tace, "barka dai Adnan. Ya aikin naka?."

"Alhamdulillah" ya kalli su Mimi yace, "ina islamiyyar?." Kafin su yi magana Mama tace, "sun ce sun daina zuwa ai, wai tunda sunyi sauka an basu allo zuwan ne zasu cigaba da yi sun gaji."



Kallon su yayi baice komai ba sai girgiza kai akwai da yayi dukkan su sun tsure ba kamar Kausar da tafi Mimi tsoro sun san me shirun yake nufi ko bai furta ba. "Mummy haka za'a bar yarinyar nan tana abinda take so a gidan nan?, yau ta kawo wannan namijin gobe ta kawo wancan?. Da ita da Yayar ta me yake damun su?." Mama tace, "to ka isa kace wani abun Adnan? Sai muyi shiru mu zubawa sarauta Allah ido." Anty Farida tace, "Adnan hukunci zaka yi mata tsauri dan wallahi kanta rawa yake yi, daga ita har maryam Win sai kana musu jan ido, kaine ido yanzu dukkan mazan gidan basa nan sai kai kaina Abba."



Jin ta ambaci Abba sai ya kalli Mummy yaga tayi murmushi kawai ya Wauke kai zuciyar sa nayi masa mugun ciwo, halin mahaifin sa yafi damun sa akan komai, sam iyalan sa basa gaban harkar neman kuWi ta fiye masa zama a gidan, ya girgiza kai ya rasa ya zaiyi da Abba in ka Sullo masa ta nan sai ya sauke karkacewa.

"Salam" aka faWa daga bakin ™ofa ana shigowa duk suka kalli wacce ta shigo Yaya Farida tace, "Rumana meye kuma salam? Sallama kenan?."



Tayi dariyar ta ™arasa tace, "ai saboda ta™aitawa, babar Yaya ashe kina nan" ta faWa tana ™arasawa ta zauna a kusa da ita tace, "ina nan, ya Ammi tana Lafiya?."

"Lafiya lau. Mama ina wuni" Mama ta amsa tana murmushi tana kallon ta. Rumana ta kalli Adnan tace, "Beb ina wuni."

"Lafiya" ya amsa a ta™aice ba tare da ya kalle ta ba ya mi™e tsaye yace, "Mummy zan je Waki, duk da ma an kusa sallah" ya faWa yana kallon agogon hannun sa.



Mama tace, "to Wan Mummy, Rumana sai ta kawo maka abinci." Ya girgiza kai yace, "zan shigo naci a nan" yana faWa ya fita daga falon, sam baya son zama a inda turare ya yi yawa ga Rumana dab'iar ta kenan bulbula turare kamar ba mace ba shi kuma hakan yana Sata masa rai.



Wajan Mamy yaso shiga sai kuma ya fasa dan yasan ransa ne zai Saci wani lokacin ita take goyan bayan duk abinda suke yi, ya wuce Wakim sa. Babban falo ne mai Wauke da Wakuna wanda ya kasance na su kafin yayen sa suyi aure su bar masa wajan gabaWaya. Zama yayi akan kujera ya rufe ido ya buWe sai kuma ya tashi ya shiga Waki ya shiga banWaki yayi alwala yana fitowa Rumana na shigowa.



Kallon ta yayi yace, "amma nayi miki warning akan shigo min Waki without notice ko?." Murmushi tayi tace, "Banda abinda ka Beb meye laifi dan na shigo Wakin ka? Auren ka fa zanyi. Kuma ai ba yau aka sqbq ba."

"Mtsww!" Yayi tsaki kawai baice komai ba tayi murmushi tace, "Beb ya kamata ka manta da baya don Allah, na karSi laifina na tuba ina so rayuwar mu ta koma kamar baya dan Allah. Kar ka manta nice Rumanan ka wacce kaso a baya kuma kayi niyar auren ta, nasan har yanzu kana sona meyasa kake min irin wannan abun?."



Fita yayi daga Wakin ya barta ta biyo bayan sa ta sha gaban sa tace, "nasan kana sona har yanzu, dan Allah ka tsaya mu fahimci juna mu yafewa juna abin daya wuce dan Allah."

"Ruman!" Ya faWa yana kallon ta ta lumshe ido cike da jin daWi, shine kawai yake cire harafin A Win gaban sunan ta, in yace Ruman Win na daWi take ji sosai yace, "you should stop thinking that I still have feellings for you, what happened is already in the past as you said, everythings between us is truly over" ya faWa yana kallon ta tana kallon sa.



Ta marairaice tace, "My love!, I know I hurt you, but my heart still beat for you Beb. I see the love we shared hidden beneath the pain. Please, don't deny it, I know me just as much as I love you." Kallon ta yayi yace, "absolutely not!."

"Don't do that Beb." Wani kallo ya yi mata Baice komai ba ya wuce ta zuwa masallaci dan ya gaji da saurare ta. Da kallo ta bishi ta sauke numfashi tana kallon sa tace, "Wallahi Bebi sai na aure ka, ko kana so ko baka so sai na aure ka. ina son ka a yanzu dole ka manta da abinda ya wuce ka aure ni ko da baka so. Baka ka tuna da baya ba, haka zaka ha™ura ko baka so" ta faWa tana fita zuwa falon Mama  ranta a Sace sosai dan Mama ce kawai maganin sa.





Nana Haleemad'ş>ØBİ



*BAYA DA ˜URA*

FitattuBiyar2025



    ©ş *Nana Haleema.*



https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp



*BOOK 1*

*Page 003*





Rumana na fita daga Sangaren Bebi wajan Mama ta wuce tana matsar kwalla ta same ta tana sallah ta zauna kusa da ita har ta idar ta kalle ta tace, "Ruma Lafiya?." Rumana hawaye ya zubo daga idanun ta ta kalli Mama tace, "Mama ina son Adnan amma shi yanzu baya sona, ya™i manta baya, na amince da abinda ya faru a baya laifina ne meyasa bazai amince ya yafe min ba?."



Mama ganin tana kuka ya saka tace, "Ruma yanzu akan Adnan kike kuka haka?."

"Mama I love him so much, bana son sake rasa shi a wannan lokacin, gabaWaya ya canja kamar ba wanda na sani a baya ba, ki yi wani abun Mama....!" Ta faWa tana sake zubar da hawaye. Mama  ta girgiza kai tana murmushi domin kuwa ita hakan daidai ya yi mata, ta tashi daga kan sallaya ta zauna kusa da ita tace, "Haba Rumana, ai indai ina da rai ina numfashi Adnan bashi da mata sai ke kawai. Ki daina asarar hawayen ki kece matar sa in sha Allah."



Ta sake komawa kalar tausayi muryar ta tayi rauni tace, "Amma Mama yanzu baya sona, gabaWaya ya canja ko hira dani baya yi kwata-kwata. Kinga a baya ba haka yake min ba, sai na wuni muna hira dashi amma yanzu ya daina." Mama tayi murmushi tace, "ki kwantar da hankalin ki wannan ba abinda zaki hawaye a kai bane. Ke kin san Adnan bashi da magana sai kun saba sosai, kuma bashi da fara'a ko kusa shima sai kun saba zaki ga murmushin sa, kin san hali ba komai ake yi a burge shi ba hatta ni ba gwanin ta nake masa ba wani lokacin. Ki yi ha™uri yana son ki har gobe, kawai sabon da ku ka yi da ne ya ja baya amma zai aure ki."  Murmushi ya suSuce mata ciki farin ciki da gamsuwa da maganar Mama tace, "Haka ne Mama, yanzu baya sakewa dani, sha™uwar mu duk ta gushe. Amma tunda kina tsakani naji daWi bana son rasa shi."



Mama tayi dariya cikin jin daWi tace, "baza ki rasa ba in sha Allah. Adnan naki ne ke kaWai, duk wannan zille-zillen da yake yi zai daina." Tayi dariya zatayi magana kenan suka ji anyi sallama.



"Assalamu alaikum" ya faWa yana shigowa Wakin Mama ta amsa tana kallon sa yace,

2 / 27