Chapter 8 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 27

21K to 24K   out of 80K words

dan ta san ba daidai take aikatawa ba. Babu nisa da asibitin sosai ya tsaya aka buWe masa gate suka shiga ya faka motar yace, "kinga masu neman taimakon ko?." Ya faWa yana nuna mata wasu mata da suke tsaye da hijjabai su biyu.

Kai ta Waga tana kallon su jikin sanyi jiki, murmushi yayi yana aiyana ai kin zo hannu yarinya ya buWe motar ya fito yace,  muje ko?.



Manal jikin ta har yayi Wumi saboda tashin hankali ta fito tana kallon gidan, yana da girma sosai ga haske ko ina kamar rana, gaba yayi ganin hakan sai ta sauke numfashi suka nufi ciki kai tsaye.



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



©žNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



*BOOK 1*

*Page 010*



Suna daga cikin falon a tsaye a bakin window suna hango masu shigowa da masu fita, ganin Manal ta fito daga mota sun doso ciki sai Alhaji Magaji yace, "to kaga yarinyar nan an kawo maka ita, Wanya sharaf ga shegen kyau, yadda kaga fuskar ta na tabbatar ka san daga ciki ma zata yi kyau ai ka gane, ni na tabbatar ko ita wacce kake zance bata kai wannan ba. Kalle ta fa, komai yaji da gani zata yi sau™in kai, kayi abinda ka ke so kai kaWai babu mai takura maka.



Alhaji Mu'azzam yayi murmushi yace, "akwai haske kam kamar yar india, kasan ko a can ba a samun masu wannan hasken kamar madara. Hasken ta akwai Waukar hankali tun daga nesa na tabbatar. Amma ni wallahi hankalina yana ga Mubeena. Ina son yarinyar, ina kuma ™aunar ganin ta ko yaushe, saboda Mubeena ta haWu daidai gwargwado. Ganin zasu shigo sai suka koma suka zauna a lokacin suka shigo da sallama.



Suka amsa yana binta da kallo duk da kanta yana ™asa, ta tsuguna kamar yadda wanda ya rako ta ya tsuguna yace, "Alhaji gata itace mai mara lafiyar, tazo tayi maka godiya ne." Jin haka sai tace, "ina wuni." Alhaji Mu'azzam ya amsa fuska a sake yana so yaga fuskar ta sosai amma ta™i bada damar hakan, taee, "Na gode Alhaji, Allah ya saka da alkhairi ya biya bu™ata."

"Haba ai yiwa kai ne “an mata. Kamar ku bai kamata ace kuna neman abu ku rasa ba, mu kuma in muka ga haka dole sai mun taimaka.



Wanda ya rako ta yace, "gashi takardar allura ce za'a siya, na tambayi kuWin allurar ance duba Wari ce shine nace tazo in tayi maka godiya sai ka bada kuWin."



Murmushi yayi masa alamun ya tashi ya tafi, ya kalli Alhaji Magaji sai ya mi™e yace, "Nidai zan wuce sai gobe." Ya Waga masa kai kawai, falon ya rage daga ita sai shi sai ihun a.c. Ya fito da kuWi daga aljihu sa ya ajjiye yace, "zo ki karSa aje a siyo. ya faWa yana mika mata kuWin, ta taso ta ™arasa zata karSa sai ya haWa da hannun ta ya ri™e, da ssuri ta kalle shi gaban ta ya faWi suka haWa ido sai yayi murmushi yace, "kar ki damu ba komai bane wannan."



Hannun ta ta zame ba ta karSi kuWin ba ta matsa baya yana kallon ta yace, "bakya son kuWin?."

"Bana so indai sai ka ri™e hannuna." Yayi murmushi yace, "kin amince kar a yiwa Maman ki allurar kenan?." Tayi shiru bata amsa amma tsoro ya gama mamaye ta, dana sanin zuwa kuwa kamar ta cakawa kanta wu™a saboda takaici yace, "kar ki manta ba'a biya kuWin asibitin ba sai za'a sallama ku, kinga kenan ke zaki biya duka abinda aka kashe in ba haka ba su kama ki. Wannan ai ba komai bane ki amince na baki kuWin ki tafi. Kamar baki waye ba “an mata? Wannan ai ya zama normal ba wani abin damuwa bane.



Gaban Manal faWuwa yake sosai ta kalle shi suka haWa ido, haka kawai gaban sa ua faWi dan tayi yanayi kaWan da wata da ya sani a baya tace, "na gode ka ri™e kayan ka, bana so na amince a kama ni Win indai sai ka ri™e ni ne. Kuma Allah sai ya saka min abinda kayi min, Allah bazai barka ba, indai haka ne taimakon Allah ya wadaran sa wallahi. kuma abinda ka yiwa Wan wani sai an yiwa naka Wan ko yanzu ko nan gaba ta faWa tayi tsaki ta fita a guje tana hawaye da dana sani, tashin hankali, rawar jikin duk sun tarar mata. Lokacin da taje fita an buWe gate mota zata shigo sai ta sake kwasa da gudu ta fice tana kuka sosai.



Babu nisa sosai daga gidan zuwa asibitin tana kuka sosai ta isa asibitin, a ™asa lokacin har duhu yayi tana shiga ta zauna inda take zama ta dafe kai tana kuka sosai, jikin ta har lokacin rawa yake saboda gani take kamar zai biyo ta. Sai kalle-kalle take yi saboda tsoro da tashin hankali, hakan bai taSa faruwa da ita ba sai yanzu, hakan ya saka ta firgita sosai bata Wauka ita wannan halin bazayen mazan zai zo kan ta ba.



Babban tashin hankalin ta bai wuce yanzu abinda ya kamata tayi ba akan kuWin asibitin da kuma kuWin allurar da akace ana so da gagawa, gaban ta ya tsananta faWuwa kana kallon ta zaka hango tashin hankali ™arara akan fuskar ta. _yanzu ya zakayi Manal? Da wanne kuWin zaki biya kuWin asibitin nan da a ™alla ya kai dubu dari biyu? Ga kuWin allurar da akace za'a yiwa Mama, ya zanyi ni Manal me zanyi na samu wannan kuWin?._



Hawaye take yi sosai cikin zullumi da tsoro, ™irjin ta sai bugawa yake yi sosai hankalin ta ya tashi saboda tsoro da tashin hankali. "Ashe daman amfani aka yi da rashin lafiyar Mama dan a keta min haddi? Innalillahi wa inna ilaihir raji un! yanzu ba a taimakon mace sai dai ayi amfani da ita?. Babban ba™in cikin ma babbba dashi, ya kusa jika dani amma ba kunya ba tsoron Allah. Duk laifina ne, nice na jawowa kaina ta faWa tana kuka sosai.





"Manal! Huzaifa ya faWa yana zuwa inda take ganin tana kuka sosai sai ya tsorata yace, "jikin Maman ne ya tashi?" Ya fadWa le™a Maman yaga bacci take ya dawo yana kallon ta yace, "Meya faru kike wannan kukan? Me ya faru? Wani ne ya rasu a gida?.



Manal kukan take yi sosai muryar ta har sar™ewa take, so take tayi magaar amma ta kasa. Ganin hakan sai yace,  nutsu, nutsu ki faWa min abinda yake faruwa..



Manal tace, "Bani da kuWin da zan biya kuWin asibitin nan, ni zan Wauke Mama mu tafi gida kawai. Tsoro nake ji, tafiya zamu yi.

"Me kike cewa haka? Ina shi Yayan naki da kika ce ya kawo ki nan?."



Ta girgiza kai tana hawaye wani yana bin wani tace, "Ba Yayana bane, wallahi ban sa shi ba, kawai yayi amfani da ciwon Mama da ruWewar da nayi ne a can babban asibiti ya kawo mu nan. Nidai tafiya zamu yi, baza mu zauna ba. Daidai a lokacin Bebi yazo wajan yana kallon su Huzaifa yace, "to yanzu yana ina? Ina allurar da likita ya baki yace a kawo kafin dare?."



"Tana hannun sa" sai ta sake fashewa da kuka mai cin rai tana rufe fuska da hannun ta duka biyun. Ya kalli Bebi da yake tsaye ya sake kallon Manal yace, "yana ina shi? Ki yi bayani lokacin allurar yana yi.



Sai da ta tsagaita kukan yace, "ban sani ba, nidai na bashi sai yace sai mun je na yiwa wanda ya saka aka kawo ni nan godiya& ..! Sai muryar ta tsay tana kuka kafin tace,  Nidai a can na barsu na gudo nan bazan iya abinda suke so ba, wallahi tsoro nake ji sunce za'a kama ni tunda bani da kuWin biyan asibitin nan, Nidai ka taimaka min Mama ta samu lafiya koda za'a kama ni Win, na yarda naje prison indai har Mama zata warke na tabbata zata dinga min addu'a. Amma bazan iya abinda suke so ba, wallahi bazan iya ba ta faWa tana kuka sosai.



Huzaifa ya kalli Bebi da suka fahimci maganar ta, yadda take maganar ya nuna musu kenan dai sai ta bayar da kanta za a taimaka mata shine abinda take cewa baza ta iya ba. Huzaifa ya sauke Ajiyar zuciya yace, ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai kama ki, kuma kuWin asibiti dana magani duk kar ki damu za'a yi Mama komai in sha Allah. Kin amince bazan cuce ki ba?.



Ta Waga kai alamun eh yace,  to ki daina kuka, za a yiwa Mama komai har sai ta samu lafiya in sha Allah Ya kalli Bebi yace, "don Allah ka sake bani allurar sai naje a samo ayi mata, lokaci na tafiya kace kafin dare.

TaSe baki Bebi yayi yace,  Done! yana faWa ya bar wajan shima yabi bayan sa.



Office ya koma yana tattara kayan sa zai tafi gida Huzaifa yace, "ka duba rashin imani irin na mutanen mu, baza'a taimake ta ba kenan sai ta bada kanta?. Anyi amfani da rashin wayo da kuma ruWewar da tayi ana neman lalata mata rayuwa. Na tsani irin wannan mutanen wallahi. Yarinyar nan yadda take son Maman ta abin a taimaka mata ce, amma mutanen mu an lalace ba a taimako tsakani da Allah.







Bebi baice komai ba amma har zuciyar sa ta bashi tausayi ya sauke numfashi ya Wauki wayar sa yana kallon huzaifa kana yace, "haka duniyar ta koma, itama kuma bata da hankali ne. Tun farko ma bai kamata a barta a wajan nan ba, ina Baban ta? Ina “an uwanta?, duk baza su zo ba sai a barta ita kaWai yau kwana biyu?. Tun farko meyasa ma ta amince dashi har aka kawo ya nan? da ace komai ma ya faru da ita tace ta jawowa kanta."



"Bebi yarinya ce fa, kuma tana cikin ruWewa in ka duba. A yadda na san yarinyar nan akan Maman ta wallahi zata iya yin komai, in akace yau diabeties Win Maman ta yyai high yadda hankalin ta yake tashi ko Maman nata baya tashi, tsaf za a cuce ta akan Maman ta.



Bebi ya taSe baki yace,  wa™ila ma ™arya take, daman bata da abin biya tazo na, wannan duk cikin plan ne.

 Na faWa maka na san ta, baza ta yi haka ba wallahi.



"Shikenan shugaban masu sanin mutane, Allah yayi tana daga cikin wanda za'a yiwa komai for free, ta huta. Ni gida zan wuce" yana faWa ya wuce shi shima ya fita ya samu ta koma ciki wajan Mama amma har lokacin kuka take. Da™yar ya lallaSa ta ta daina kuka ta kuma amince baza'a kamata ba sannan ya tafi shima.



Sai a sannan Manal ta Wauki wayar ta wacce Surayya ta kawo mata ta kunna ta kira lambar Baba amma a kashe ake cewa ta ajjiye wayar kawai tayi tagumi tana kallon Mama har lokacin zuciyar ta rawa yake saboda tsoro.





"Da yake baki da mutunci ki ko ki kira ni ki faWa min Mama babu lafiya" Mubeena ta faWa tana shigowa cikin Wakin. Ganin ta sai Manal taji daWi sosai ta tashi da sauri ta rungume ta sai kuwa ta janye ta tace, "ke bana son sabon salon iskanci, da yake kina so a dinga yi dani a baki a unguwa ana cewa ban damu da uwata ba sai kika ™i faWa min kina nan, Sai Surayya muka haWu da ita takr cemin ai kuna wanna asibitin. A ta™aice ma ubanwa ya baki kuWin asibitin nan?."



Manal kallon ta kawai take yi ta kasa magans, ita kuma ta isa wajan Mama da take bacci ta sake kallon Manal tace, "ni zan koma bacci nake ji sosai gaskiya, waye ya kawo ku nan?." Manal kallon ta kawai take yi bata ce komai ba ta Wauki apple guda Waya a wacce take ajjiye tace, "ashe daWi ma kike ci, ni na wuce" ta faWa tana hanyar fita Manal tace, "Yaya tun jiya Mama take tambayar ki, ki dakata ta farka ta ganki don Allah."



"Manal na faWa miki bacci nake ji, ina so na huta sosai zan dawo da safe."

"Hutun yafi zama a wajan Maman ne?."

"Ke bana son iyayi, baga ki nan ba ai dani dake duka Waya ne ko?." Wayar tace tayi ™ara sai bata sake magana ba kawai ta fita Manal ta bita da kallo.



Tafiya take tana waya har ta Wan yi tafiya mai nisa kafin taga motar wanda take nema ya sauke ba™in glass Win sa, ganin hakan sai ta shiga tace, "meyasa baka je bakin gate Win ba ka barni Ina takawa a ™asa?."

"Sorry Baby, akwai wanda bana son haWuwa dasu ne shiyasa." Cikin shagwaSa tace, "to ba sai ka turo a Wauko ni ba, ni duk ™afana ya gaji."



Murmushi yayi yace, "sorry na tuba, in kina so zan iya miki tausa." Ya faWa yana jan motar suka tafi. Tayi dariya bata ce komai ba yace, "Tunanin ki kawai nake yi sai naga kina waya, in ba ke ba babu wanda zai saka ni na fito daga gida yanzu, sai ke Win kawai."



Tayi farrr da ido cikin jin daWi kafin tayi magana yace, "amma wa kika zo dubawa a nan?."

"Wata course mate Wina ce."

"Kin taSa zuwa asibitin ne?."

"Ban taSa zuwa ba sai yau. Yana da kyau a ido gaskiya. Yayi murmushi yace, "akwai kyau a ido amma ba wani aiki suka iya ba, kar ki sake zuwa ma saboda kar ki Wauko ciwo."



Tayi dariyar jin daWi tace, "an gama Baby." Yayi murmushi sai ya kai hannun sa cinyar ta inda hannun ta yake ajjiye ya ri™e bai kalle ta ba yaga dai ta kalle shi reaction Win ta ya canja amma bata nuna ba yace, "ina sonki Baby, in muna tare Ina kasa ri™e kaina sai na rasa nutsuwa ta gabaWaya Baby."



Murmushi tayi har lokacin hannun sa yana kan nata ya ri™e yana matsawa a hankali yace, "Baki ce komai ba Baby."

"Me zance?."

"Komai ma kice." Tayi murmushi kawai bata sake magana ba har akazo ™ofar gidan su Bily.



Ta kalle shi tace, "zan shiga gida kar Daddy yayi min faWa. ˜are mata kallo yake irin kallon “an bariki yake mata har ta tsargu da irin kallon da yake mata ta gyara zama kaWan ganin haka sai yace,  kike so?." Jin abinda yace sai tace, "waya nake so a canja min."



"Iphone ko android?."

"Iphone." Kai ya girgiza yace, "gobe zaki ga sabuwar waya Baby, in kina so muje yanzu ki zaSi wacce kike so." Mubeena tace, "A'a, Allah ya kaimu gobe Win."

"Amin Baby. Sai sauri kike ki gudu ki barni ko? Bayan ni kewar ki nake ji kamar na jawo ki jikina haka nake ji."



Ganin babba dashi yana wani abu kamar yaro sai ya bata dariya tayi murmushi shima sai yayi y shafa fuskar ta yace, "kina da kyau Baby" ya faWa yana matsowa kusa da fuskar ta.



Ta saka hannun ta akan masa ta cire hannun sa a fuskar ta yace, "ya kike haka Baby? Wannan fa ba komai bane soyayya ce, kar ki zama wanda basu waye ba mana, ina kallon ki wayayyiya meyasa zaki bayar da kan ki baya?."



"Ina sauri ne kawai."

"Okay, hug me before you leave." Ta kalle shi zata yi magana ya riga ta yace, "please baby" kafin tayi magana ma ya rungume ta, sai taji wani iri domin duk rawar kanta wannan shine karo na farko da aka rungume ta, har gwara dai ri™e hannu amma ruguma bata taSa yi ba.



Kam ya ri™e ta sosai ga turaren da ta saka mai ™arfi da sanyi yana sake tasiri wajan sake ri™e ta sai lumshe ido yake da™yar ta iya janye jikin ta tace, "sai da safe." Muryar a sar™r yace, "okay Baby." Tana faWa ta fita ta shiga gidan jikin ta yayi sanyi shima ya ja motar ya tafi.



Bebi yana tsaye daga baya yana kallon mace ta shiga motar Abban nasa amma bai ga wacece ba, yaga dai an shiga dan lokacin ya karya kwana yaje ya siyawa Mama wani zabo gashashe da take so shigar macen ya gani da kuma wucewar motar dan yasan lambar motar mahaifin sa. Zuciyar sa sai bugawa take yi ji yake kamar yabi bayan sa amma zuciyar sa na hana shi hakan dole yaja motar ya tafi yana hana zuciyar sa tunanin da yake kai kawo a zuciyar sa akan Abba.



A haka ya shiga gida ya shiga wajan Mama ya same ta zaune ta ajjiye abinda ya kawo mata ya kalli Kausar da take zaune ya bata leda Waya yace, "kaiwa Mamy wannan. ba musu ta karSa ta fita ya zauna yayi shiru zuciyar sa dai harbawa take.



Mama tace, "Zabon ne? Allah yayi albarka. Amma lafiya kake?."

"Babu komai Mummy, na gaji ne."

"Ga abinci nan in zaka ci."

"Me aka dafa?."

"Fried rice ce" Mimi ta bashi amsa tana zaune. Ya sauke numfashi yace, "bani kaWan naci." Mimi ta tashi ta zubo masa ya karSa yana ci amma hankalin sa baya tare dasu gabaWaya.



Mama tace, "Sumayya tazo, tana ta zancen ka sai jiran ka take baka dawo ba. Ban Wauka ma a gida zaka kwana ba yau. Yace, "zan je na gaishe ta in sha Allah."

"Da ka kyauta, daman ina so kaje gidsan kodan ku tsayar da lokacin auren ku da Rumana."



Ya kalli Mama ta san kallon na meye sai tace, "haka za'ayi da Bebi, kana sonta tana sonka meyasa kake son zillewa ne?." Ajjiye bowl Win abincin yayi ya tashi yace, "na ™oshi, sai da safe" ya faWa zai fita Mama tace,  don nayi maka maganar Rumana shine ka bar abincin? Da yake ga wacce ka tsana ko?.



Bebi yace,  A a ba haka bane, na tuna ina da aiki anjima ne shiyasa zan je na kwanta ya faWa yana fita. Yana fita

8 / 27