Chapter 7 Reading BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt Arewa Novels

BAYA DA KURA BOOK COMPLETE BY NANA HALEEMA.txt

Author :  Nana Haleema Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 27

18K to 21K   out of 80K words

baka isa ka hana ni ba, sai dai kaji ance likitan zuciya Dr Adnan Mu'azzam yana kwance yana jinyar zuciya saboda saurayin ™anwar sa. Wannan fagen nawa ne Adnan, ba wajan ™wace leinses bane ya faWa yana murmushi tare da barin wajan ya fita daga gate Win gidan dan motar sa ma a waje ya barta.



Ransa ya Sace sosai ya nufi cikin gidan ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga Waki ya zauna a kan kujera yana tunani. Shi yasan da biyu Mujahid yake zuwa wajan Lubna, yasan saboda wani nufin da yake zuciyar sa ne yake zuwa ba don Allah da annabi ba. Waya ya Wauka hannu na rawa ya kira Lubna tana Wauka yace ta zo ta same shi ya yanke wayar ya ajjiye.



Ba jimawa ta shigo jiki a sanyaye ta zauna tace, "gani."

"Ban miki warning akan kula Mujahid ba?, bance kar n saka ganin ki dashi bane yasa kike haka ne Lubna?." Tayi shiru bata ce komai ba amma a zuciyar ta mamaki yake bata, to wai shi ina ruwan sa da samarin tane?. Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa, "magana nake miki fa, in baki amsa ba sai na taso na fasa miki baki." Jin yadda yayi magana sai tace, "To ni ina son sa."



Wani iri yaji a zuciyar sa ya kulle ido ya buWe cikin takaicin abinda tace ya fuzar da iska yayi shiru baice komai ba. "Allah Yaua ina son sa, kuma daman kace na zaSa aure ko karatu ko?, to ni aure nake son yi kuma shi zan aura." A fusace yace, "ba sonki yake ba shi, yana amfani dake ne saboda wani nufi masa amma ba dan yana son ki ba. Ki dawo hankalin ki malama, wannan tunanin da kike bashi da amfani domin kuwa baza ki aure shi ba. Tayi shiru ganin yana zare mata idanu, ido ya cika da hawaye sai ya dafe kai yace, "look Lubna! Mujahid ba irin mazan da zaki saurara bane a matsayin wanda zaki aure kin gane?."



Magana take so tayi amma ta kasa yace, "faWi abinda yake bakin ki ina jin ki." Tace, "Yaya naga abokin kane fa, meyasa baka so yake zuwa wajena? kuma ni nace auren sa zanyi ina son ..."'yadda ya taso kamar zai mare ta shine ya hana ta k'arasa maganar yace, "shut up your mouth, stupid girl ina miki magana kina sake maimaita min kina son sa? Ni zaki faWawa kina son sa don kin raina min hankali..? Ina magaa kina maganq? baza ki aure shi ba ki rubuta wannan ki ajjiye. Indai Adnan yana da rai baza ki auri Mujahid ba, ya kamata ki san da wannan. Kuma na sake ganin ki dashi sai nayi miki dukan da ba'a taSa yi miki irin sa ba tunda kika zo duniya, sai na miki dukan da shi Mujahid Win bazai gane ki ba, daga ranar zaki shaida waye Adnan.



Cikin tsawa yake magana hakan ya saka ta shiga hankalin ta sosai, ya sake cewa,  Tashi ki bani waje." Da sauri ta zabura ta mi™e ta fita da sauri ya daki kujera cikin takaici da ba™in ciki.



Mujahid yayi nasara a kansa tunda har Lubna ta fara son sa shikenan ya gama karya masa lagon Lubna, amma yasan abinda zai masa bazai sake waiwayon Lubna ba itama dole ta ha™ura dashi domin bai dace da ita ba, ba irin sane ake kira da mijin aure ba.



Mujahid da murmushi ya bar gidan ya shiga mota ya zauna ya samu abokin sa a zaune yana jiran sa yace, "tunda naga kana murmushi nasan akwai abinda ka shirya wanda kake gab da samun nasara." Yayi dariya kaWan yace, "burina na ba™antawa Adnan kamar yadda ya ba™anta min, badai ™annen nasa yake tattali kamar ™wai ba? To ni kuma sai na saka ™afa na take wannan riritawar da yake musu dan wallahi sai na saka masa ba™im ciki a zuciyar sa."



Wanda yake sanarwa ya shigo a kai yace, "kar ka manta Adnan abokin nake fa Mujahid, da sunan ka aka buWe asibitin getting better kana daga cikin ma'aikatan sa kafin ka daina aiki."



"Kafin yayi silar daina aiki na dai, har abada bazan manta da abinda Adnan yayi min ba, kuma wallahi sai na rama akan ™anwar sa Lubna. Bashi da weakness point a duniya kamar familyn sa, musamman ™annen sa mata guda uku, tabbas zan yi amfani da Lubna na saka masa ba™in cikin da na WanWana a zuciyata nima."



"Kenan baka son Lubna?." Yayi tsaki yace, "bana ce ba" ya faWa yana jan motar suka bar wajan yana aiyana irin abinda zai yiwa Lubna, dan walalhi sai ya saka Adnan kuka in ba haka ba bazai daina jin da daWin abinda yayi masa a zuciyar sa ba.



*BAYA DA ˜URA.*

Fitattubiyar2025



©žNana Haleema.



Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11



*BOOK 1*

Page 009



Washe gari Bebi ya jima yana bacci bai tashi ba sai zuwa ™arfe goma na safe sannan ya fito bayan ya shirya, motar Abba ya gani a ajjiye alamun ya dawo kenan sai ya nufi Sangaren sa da niyar gaishe shi.  A nan ya tarar da yayyen sa maza a zaune da alama sun shigo gaishe shi, suka gaisa ya samu waje ya zauna baice komai ba shima saboda sun ce ya zauna ne.



A lokacin Abba yace, "kuna gani dai gashi tun Wazu na kira iyayen ku gashi sun ™i zuwa, ni ban san me suka Wauke ni a cikin gidan nan ba, basa jin maganata a ko yaushe so suke suga raina ya kai ma™ura wajan Saci." Bebi ya kalli Abba yace, "kayi ha™uri Abba, ban san me ku ka tatttauna a farko ba kafin shigowa ta nan, amma Abba gaskiya matsalar gidan nan daga Sangaren ka take. Dan iyayen mu sunyi fushi ba laifi bane duba da kwanakin da ka Wauka baka gidan nan, da ka dawo kwanan ka Waya ka sake fita sai yau da safe ka dawo."



Abba ya kalle shi yace, "Daman ai Adnan na jima da sanin kai kake son maye gurbin ubana Alhassan da ya mutu, kama kunne na ka faWa min kamar zan fi ganewa sosai." Bebi yace, "Allah ya wuce zuciyar ka, ba haka nake nufi ba." Sai kuwa abba ya fusata yace, "me kake nufi to? Haihuwar ka nayi ko haihuwata kayi da zaka zo gabana kana faWa min wai dole su yi fushi da ni?. Akwai abinda na rage su dashi a cikin gidan nan ne? Akwai abinda ban ajjiye kafin na bar gidan ba?, Meya damuwar su dan naje nayi kwanaki a wata ™asar ko wani garin? Meye abinda zai shafe su?."



Dukkan su sunyi shiru ganin ya fusata sosai babu wanda ya sake magana. A lokacin Mama ta shigo jin yana faWa sai taja ta tsaya bata zauna ba ya kalle ta yace, "ita babar taka abinda take yi daidai ne?, Dana dawo gidan akwai wacce ta nuna taji daWin zuwa na? Akwai wacce ta bani abinci?. Dukkan su bana gaban su shiyasa nima na ajjiye su a gefe tunda basu damu da tawa rayuwar ba nima ban damu da tasu rayuwar ba." Mamy ma na tsaye a baya tana jin duk abinda yake cewa.



Ya sake kallon yaran nasa yace, "indai iyayen ku basu gyara ba kar wanda ya sake zuwar min da maganar abinda nake ba daidai bane, in kuma ba haka ba wallahi ransa ya Saci dan sai na saSa masa fiye da tunanin ku. Kai Adnan kaine daman mai bakin magana, ko magana aka kasa faWa min kaine mai iya faWa to ahir, ka jawa iyayen ka kunne in ba haka ba kuma ranka ne zai Saco matu™a." Ya girgiza kai yace,  kayi ha™uri Abba. Abba bai kuma magana ba ya tashi ya shige Waki ya barsu a zaune a  wajan.



Mamy da Mama basu ce komai ba ko wacce ta fi daman basu zauna ba. Adnan ya kalli babban yayan su yace, "yanzu tsakani da Allah a haka za'a tayi a gidan nan?." Yaya Bilal yayi masa alama da su tashi su fita. Dukkan su tare suka fito suka tsaya a rumfar ajjiye motocin gidan Bebi yace, "na rasa abinda zai mu yiwa abba, yanzu tsakani da Allah ina amfanin maganar nan da yake yi a gaban idanun mu?, a ganina wannan saSani ne da ya shafi zaman auren sa da matan sa meyasa baya jin kunyar faWawa iyayen mu magana a gaban mu ne? Meyasa Abba bai san lokacin wannan ya wuce ba?."



Yaya Bilal yace, "Bebi su kansu iyayen mu suna kuka da wannan halin, in suka masa laifi a gaban yaran su zai faWa musu maganar da zata saka su hawaye bai damu ba." Yaya isma'il yace, "ni ban san abinda zance bama wallahi, amma iyayen mu suna cikin damuwa sosai."

"Ni na gama yanke hukuncin zan samu wani babban malamin da nasan Abba yana da alaqa dashi na kai masa maganar yayi masa nasiha" Bebi ya faWa cikin yanayin damuwa.



"Hakan ma mafita ce" Yaya Bilal ya faWa yana kallon sa. Bebi ya furzar da iska daga bakin sa yace, "zamu san abinda za'a yi, duk da baza mu canja shi ba ya riga ya saba zama ba'a gida ba, amma zamu yi addu'a ba dan mu ba, ko dan ™annen mu da suke gidan." Yaya Ismail yace, "kana ™o™ari akan kowa a gidan nan Adnan, Allah ya cigaba da baka ikon sauke ha™™in da ya hau kanka tunda kaine kamar mahaifi a gidan namu." Ya amsa da amin kafin ya wuce zuwa wajan Mama.



A zaune ya same ta kamar komai bai faru ba ita dasu Mimi suka gaishe shi ya amsa ya zauna yana kallon Mmaan kafin yace, "Mummy barka da safiya." Ta kalle shi tace, "Barka dai Bebi, yau ma kasha bacci."  Kafin yayi magana tace, "yaushe zaka je ka gaida Hajiya ne? Yanzu da muka yi waya muka gaisa sai da tace ina Adnanu basarake, shi baya zuwa inda mutane suke, tace a gaishe da sarkin sarakuna. nace yana nan." Ya Wan saki fuska kaWan yace, "zanje ko anjima ne ko gobe in sha Allah.

"Nima anjima nake so na le™a na kwana biyu bamu gaisa ba, gashi Sumayya tace min zata zo in tazo muje tare ko kuma naje zuwa dare ko gobe."



Jin tace Sumayya yasan Maman su Rumana take nufi ™anwar ta kenan sai ya girgiza kai yace, "Allah ya nuna mana." Ya amsa da amin ya kalli Mimi yace, "kawo min abinci naci."

"Akwai ragowar shinkafar nan ta jiya na ajjiye maka ayi warming sai a kawo maka naga kana son ta." Ya kalli Mummy da mamaki jin tace wai warming yace,  ta jiya dai Mummy?.

 Eh, naji kace ta maka daWi ne ai.

 Ai Mummy a barta kawai, ina ni ina cin abincin jiya?. Na sha tea, Mimi kawo min.



Sai kuwa Mimi tayi dariya ita da Kausar Mama ta kalle su tace, "daman sai da suka ce kar na ajjiye ba ci zakayi ba amma na ™i ji, gashi yanzu maganar tasu ta tabbata shine suke dar1ya." Mimi ta tashi ta kawo masa tea da kuma soyayyen dankalin hausa dana turawa a haWe sai ketchup a gefe dan tasan ko bata saka ba sai ta koma.



KarSa yayi yana ci dan shi tea bai dame shi ba sam, ya rasa me zai cewa Mama akan maganar Abba shiyasa yayi shiru bai ce komai ba. Har ya gama ci baice komai ba ya cinye dankalin amma bai shanye tea Win ba dan tea ba wani abokin sa bane. Sai Mama tace, "Yauwa bebi Kausar tace min tana son zuwa asibitin ku wajan Hamza, Wai marar ta ke ciwo haka kawai kuma gefe Waya ya ri™e sosai."



Ya kalli Kausar Win sai yaga ta sunkuyar da kai ya kalli Mama yace, "Hamza yana asibiti ina jin yanzu ma."

"To tazo sai ku tafi gwara taje ta san matsalar ta kar azo abin yafi haka."

"In na tafi da ita waye zai dawo da ita?."

"Sai ta dawo ita kaWai, kai wai kallon su kake kamar yara ™ananu, daga asibitin naku zuwa nan wani nisa ne dashi?.



Yace, "ba haka bane Mummy, Yawon su kaWai ne bana so" ya kalli Kausar yace, "muje." Ya mi™e tsaye ya kalli inda Mimi take ya kalli Mama yace, "mun gama magana da wanda yace yana son Mimi, ban bashi damar zuwa ba banyi binciken da nake so nayi ba, zuwa nan da jibi dai haka." Mama tayi murmushi tace, "To Baban Yaya, Allah ya taimaka." Ya amsa da amin ya wuce ya fita Kausar tabi bayan sa.



Sai da yaje wajan mota ya lura da ita a bayan sa ya bita da kallo up and down yace, "wannan wanne irin mayafi ne? Koma malama ki canja." Da sauri ta juya shi kuma ya shiga motar ba jima ta dawo ta saka abaya akan kayan ta shiga gaba ya fita daga gidan. 



A hanya ya kalle ta yace, "bakwa yiwa yayar ku Lubna faWa ko?." Tace, "Wallahi Yaya muna yi bata jin magana ne, sai tace wai takura mata ake ita da Yaya Maryam." Ya girgiza kai yace, "bata jin magana." Bata ce komai ba ya cigaba da tafiya kafin yace, "tun yaushe kike ciwon?."



"Kusan sati kenan."

"Kuma kin tabbatar ba period bane?." Ta Waga kai ta amsa da eh baice komai ba ya cigaba da tafiya har suka je asibitin ya faka motar ya fito itama ta fito suka shiga ciki.  Office Win sa suka shiga da ita akwai patient guda biyar da suke jiran sa tana zaune duk suka shigo ba jimawa suke fita har ya gama dasu sai ga Hamza da Huzaifa Win sun shigo.



Huzaifa ya kalli Kausar yace, "Kausar yau ke kika yiwa Yayan naki rakiya?." Tayi dariya ta gaishe su suka amsa ya kalli Hamza yace, "wajan ka tazo." Hamza yace, "to Allah yasa Lafiya." Huzaifa yace, "Kuje office ai kowa yana son sirri." Ba musu ya fita ita kuma bata tashi ba tana jira Bebi ya bata umarnin tafiya.



Lura da hakan sai Huzaifa yayi dariya yace, "Kausar tashi kije na baki umarni a madadin sa." Sai a sannan ya Wago dan shi ya Wauka ma ta fita a lokacin ta fita ya cigaba da abinda yake yi.



Ba jimawa ta dawo da sallama suka amsa tace, "Yaya an gama." Ya Wago ya kalle ta yace, "to yanzu ya za'ayi? Tafiya zaiyi ko zaki jira na gama?."

"A'a zan tafi dai."

"Allah ya kiyaye" ya faWa yana cigaba da rubutun sa. Sai tace, "babu kuWi a hannuna ai."



Huzaifa ne ya bata dubu biyu ta karSa tace,  An gode, Yaya na tafi.

 Allah ya kiyaye, ki kula. Ta amsa da to ta fita, Huzaifa yace, "wani lokacin kana burge ni akan yaran nan, wani lokacin kana bani haushi." Baice komai ba ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa yace, "Yauwa, wanne magani kake ganin za'a bawa matar nan ta jiya?."

"Wacce mata?."

"Mahaifiyar yarinyar nan mana da suka kwana a nan."

"Ohh! Sai naje naji yanayin bugawar zuciyar sannan nasan abinda za'ayi." Bai jima ba ya tashi zuwa Wakin ya samu Maman a zaune Manal Win na gefen ta tana bata apple da ta yanka mata ™ananu.



˜arasawayayi yace, "Sannu Mama." Mama duk da ba gani take ba sosai tace, "Yauwa sannu likita."

"Ya jiki?."

"Da sau™i" ta faWa a wahala kana ganin ta kasan tana jin ciwo har lokacin. Hannun ta ya ri™e yana sauraren bugun zuciyar ta kafin ya saki yace, "Mama saka damuwa a zuciya ba komai yake kawowa ba sai ciwo, ki kawar da abinda yake damun ki kodan Lafiyar ki."



Mama tayi murmushi kawai tana girgiza kai bata ce komai ba ya kalli Manal kamar zai magana sai ya fasa ya fita. Ba jimawa ya dawo ya bawa Manal takarda yace, "babu wannan allurar a nan sai gobe za'a kawo, zuwa dare ki bawa yayan ki a siyo ta. KarSa tayi ya fita ita kuma ta ajjiye takardar a kusa da ita.



Mama tace, "Manal wanne Yaya yake nufi?." Manal tace, "Mma ki yi shiru kina wahala in kina magana."

"Mubeena bata zo ba ko?." Manal tace, "eh bata zo ba." Mama ta girgiza kai kawai bata sake cewa komai ba.



Sai da Mama tayi bacci Manal ta fito neman wannan mutumi bata ganshi ba haka ta koma a lokacin Surayya da Maman ta sun sauke zuwa suka Wauke mata kewa har magariba sannan suka tafi. Suna tafiya yazo bai shiga inda Mama take ba ya tsaya a inda ya ganta Manal tace, "sannu da zuwa."

"Yauwa Sannun ki. Ya jikin Maman?."

"Da sau™i sosai. Tun Wazu nake neman ka an bani wata takardar magani ance a siyo allurar, da kuWi a a hannuna amma ban saninda za'a siyo ba ko zaka taimaka min."



Yayi murmushi yace, "siyan allura da magani duk aikin wanda ya Wauki nauyin Mama ne, abinda zai faru yanzu tunda tana bacci Mama kizo muje ki masa godiya daga nan sai a baki allurar. Kin San godiya tana daWi, sai yafi jin daWin sake miki wani alkhairi musamman in akace kin taka kin je har inda yake.



Manal cikin faWuwar gaba tace, "amma bi kaWai ce a wajan Mama, in na tafi waye zai zauna?."

"Ai ba jimawa zaki ba, amma in kina ganin basai kin gode masa ba shikenan." Manal murya a sanyaye tace, "ina ne inda zamu je?."

"Nan ne gidan sa babu nisa, da mu je zaki ga mata ma wanda ya taimakawa kamar ki."

"Da zamu bari sai da safe maje ko?."

"To ya za'ayi da allurar?." Manal tace, "zan siya da kuWina." Yayi murmushi yace, "kuWim ki baza su iya ba, wannan allurar da kike gani a ™alla zatayi dubu hamsin, kizo muje a siyo a yi mata dare yana yi."



Manal tayi shiru tana tunani yace,  ko kina da dubu hamsin Win?. Ta girgiza kai alamun a a yace,  muje.



Gaban Manal dai faWuwa yake sosai ta Waga kai alamun to ta biyo bayan sa. Mota ya shiga itama ta shiga suka fita daga asibitin, sai salati take a zuciyar ta

7 / 27