Chapter 10 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 26

27K to 30K   out of 76.5K words

Allah beta6a mata kyau irin na yau ba.

Usman nata zuba labari yaji ba reply kallonta yayi yaga wurga kafa kawai takeyi, kallon ido cikin ido suke ita da Abdul daga nesa.

"Keeeee" Usman yafada da'dan karfi.

Firgit kamar me mafarki tace "Na'am kai lafiyarka kuwa"

Yace "kedai zan tambaya"

Kafin tabashi am??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sa sun iso gurin.

Usman yace "umma, Anty Zee Yaaya, Anty Raly this is my best friend, wato bestie na kenan Sofiyya Adam Muhammad"

Sannan yajuya ya kalleta yace "bestie these are my family"

Ummace tace "sannu Sofiyya"

A kunyace tace "ina yini umma? "

Kafin umma ta amsa Raliya tace "sister kin tunani kuwa? "

Da murmushi Sofiyya tace "off course natunoki"

Anty Zee tace "bestyn Usman angaisheki, don nasan kinashan surutu"

Kafin kowa yayi magana Abdul yayi subul da baka yace "ai haline yazo daya Anty, don tama fishi surutu"

Ke6e fuska Sofiyya tayi tace "kaiki yaaya nidin"

Harararta yayi yace "kedin fa, kullum da headache din surutunki nake kwana"

Duk zuba musu idanu akayi, Umma kam murmushi tayi don base anfada ba tasan itace budurwar Abdul.

Usman da mamaki yacikashi cewa yayi "wait a Ina kuka san juna wai? "

Raliya tace "so she is Cutie right Yaaya? "

Anty zainab tace "Kodai da ita za'ayi ne Abdul? "

Umma dai batace komai ba se murmushi take, don hakanan taji yarinyar ta kwanta mata arai.


Sofiyya kam kunyace takamata, don haka tajuya tabar gun dasauri.

Shima Abdul dukyaji kunya, yarasa tayaya yayi sakacin sakin zance haka, gakuma tarin tambayoyin da suke masa, a kunyace shima yamike yabar gurin.


Usman da Raliya suka hada suka tafa suka kwashe da dariya.

Anty Zee tace "ja'irai kawai".

Zuly kam tacika tayi fam, tayi data sanin zuwanta gurin yafi cikin carbi.

Munnir duk abinda ake akan idonsa akayi, duk da bayajin abinda suke fada, amma dai sarai yagane Abdul don haka ranshi ya matukar 6aci.

Zuly ce ta hango munnir, mikewa tayi tacewa Anty zainab "ina zuwa Anty"

Anty Zee tace "to ammafa karki dade don munkusa tafiya, "

To tace sannan tanufi gurinsu Munnir.

Neman Sofiyya yayi yarasa hakan yasa shi rarraba idanu yana tafiya, tuntu6e yaji yayi da mutum, ya dago kai kawai yayi kaci6us da fuskar Zuly.

"Keee me kikeyi anan"

Ya furta a mamakance.

Cikin rashin kunya tace "kai me kakeyi anan din if I may ask"

Hannunta yaja sukayi wajen gurin inda babu hayaniya.


...... Abdul kam mota yakoma yazauna se sosakai yake yana murmushi.

Sofiyya takoma gunsu mommy cike da kunya, tazauna kusada Siddika sewani 6uya takeyi, don gani take kamar duk inda tayi kallonta suke.

Ringing wayarta tafarayi, dubawa tayi taga HS (handsome) kin dauka tayi saboda wata sabuwar kunyarsa takeji.

Sake kira akayi, tamikawa Siddika wayar tace "please ki dauka kice yafada miki koma menene"

Harararta Siddika tayi tace "saboda ke bakida bakin magana kome? "

Allah da annabi tadinga hadata dashi tana lalla6ata dakyar tayrda tadauka.

Shiko jin andauka bejira jin me magana ba yace "kizo gunda akayi parking kisameni please "


Bejira amsanta ba ya kashe wayar.

Bayan Siddika ta sanar da ita, tasake lalla6ata sukaje taraka ta.

Suna gurin motocin but basusan wannene motar da Abdul yake cikiba.

Waige-waige sukeyi neman ta inda zasu ganshi.

Shikuma yana cikin mota yana kallonsu, daukar Waya yayi ze kirata.

Motaci tashigo gurin, kuma seda tazo dai-dai kusa dasu tayi parking, mutumin cikin motar ne yafito, ya nufo inda suke.


Abdul na kallonshi yace "Bashir"

Bashiri yabude motar shima ya fito yanufo gurin.

Bashir nazuwa yace "beautiful ashe darabon zan ganki yau"

Kafin tabashi amsa Abdul yakaraso fuskar nan a hade kamar hadari, tsayawa yayi a gurin yarasa wacce kalma zeyi anfani da ita.

Bashir ne ya kalleshi da mamaki yace "kaiii mutumina ashe kananan"

Munnir da Zuly sun fito gurin domin suyi magana idon munnir yasauka akan su Sofiyya
"What!? " Yafurta da karfi

Bejira komai ba yanufi gurin gadan-gadan...................
'?




Me kuke tunanin zefaru>??

Amsoshinku abin sone>??
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah don Allah =?O?

Episode 23-24
Asibiti
Se bayan sallar azahar da Baban Siddika yadawo daga masallaci sannan yasamu ganin likita.

"Alhamdulillah Allah yasauki matarka lafiya" cewar likita

Ajiyar zuciya mustapha (baban Siddika yasauke yana furta "Alhmdulillah "

Likita yadaura dacewa "kunyi gangancin barinta tayi doguwar nakuda a gida batareda kun kawota asibiti ba, badon anan take awo ba tabbas da bazamu kar6eta ba"

Hmmmm mustapha yace batareda yayi magana ba

Likita yadaura dacewa "sakamakon doguwar nakudar datayi, jaririn yasha bakar wahalar daseda ya mutu, yaron bezo darai ba"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'iuun "
Mustapha ya furta

"Amma ya itadin take likita"

"Itakam Alhamdulillah hutu dai take bukata sosai, don haka anyi mata allurar barchi domin ta samu isashshen hutu"

Mikewa Mustapha yayi yana mikawa likita hannu "nagode likita bari inje inganta"

Musabaha sukayi sannan yawuce yafita,
Cike da mamakin rashin ganin 'yan gidan ko mutum daya yakarasa yashiga dakin da aka kai aunty hafsat.

A gidan kam babu wanda yadamu da sanin halin da hafsat din ke ciki, don ko takansu ma babu wadda yabi, kowa harkokin gabanshi yake daga Innar har Baraka.

Hakanne yasa koda mustapha yadaga Waya da nufin kira yarasa wanda ze kira.
Cike da tausayin halin maraicin da hafsat ke ciki wanda shine sila yasauke wayar ya kurawa hafsat din ido
"Allah sarki, tarasa kowa saboda ni, gashi tazo gidan da ba'a sonta"

Jiki a sanyaye yadafa wayar ya lalubo numbern yayanshi Shu'aibh yayi dialing

Bugu biyu aka daga Kiran, bayan sungama gaisawa yake sanar dashi haihuwar hafsat din.

Cikeda farinciki yace "Masha Allah aina tabbatar yanzu kam komai yazo karshe don dama jiran lokacin haihuwar nakeyi, bari inkira Lamido insanar dashi yanzu kuwa"


Shidai mustapha bece komai ba yakatse Kiran, a ransa kam fadi yake "Allahumma kakawo karshen matsalolin hafsat"

..........

Da hanzari yanufi inda suke Zuly na mara masa baya.

"Mutumin kaga zuwan sa'a ko? Bansan zan hadu da beautiful ba abokina ne yace insameshi anan gurin wlh da Kamar bazan zo ba amma dayake inada rabo segashi nazo" yakarasa yana Dariya


Isowa gurin munnir yayi yana huci Kamar wani zaki.

"Sofiyya zo inason magana dake"
Yafada a gadarance

Ko kallon inda yakema batayiba, kai kace ma bataji me yace ba.

Me Siddika zatayi inba Dariya ba, harseda tabawa Bashir dariyar dabeyi niyya ba.

Zuly kam abin yakara dagule mata, tayaya za'ace duk namijin data so shikuma wannan yarinyar yakeso?

Ganin abin na neman yayi masa yawa yasa bazato ba tsammani Abdul ya kamo hannun Sofiyya yajuya, itakuma cikin mamaki babu musu tabishi.

Bude gaban mota yayi yasaka ta ya rufe, yazaga yashiga driver side yazauna yatada motar yabar gurin.


takaici da bakin ciki sune suka ziyarci zuciyar Munnir a lokaci guda, wani ihu yayi yana naushin iska.


Tuntsirewa da dariya Siddika tasakeyi tana "Me Abu yadauke abinsa, kowa yayi takansa kuma"
Wata dariyar takumayi.

Bashir kam mamaki ne ya dabaibayeshi tarin tambayoyi suka darsu a zuciyarshi, meya hada Abdul da beautiful.

Wani naushi munnir yanufi Siddika dashi, dan dama shikam yatsani yarinyar nan tunba yau ba.

Dagudu tayi bayan Bashir ta 6uya

"Dakin tsaya ai shegiya kawai"
Yafurta rai a 6ace

Bashir kam dramar dariya tabashi yace "haba malam yanzu kai in anbarka seka saka wannan gatarin hannun naka a jikin wannan Cute girl din"

Dariya Siddika da zuly sukayi

Munnir dake neman inda ze huce haushinsa, naushi yasake kaiwa Bashir.


Ja baya Bashir yayi yana cewa Siddika "Cutie mubar nan kafin a illatamu, danni ban iya fada ba"

Wucewa sukayi suna Dariya aka bar munnir da zulynshi.

Zuly tace "dazaka bi shawarata daka hakura da yarinyar...... "


Katseta yayi da "dalla malama ki ware kiban guri"


Sum sum zuly tabar gurin, dan a haukar dataga munnir ze iya cewa itama ze doketa.

Abdul tuki kawai yake besan inda ze kaisu ba.

Sofiyya data zuba mishi idanu tayi karfin hali tace "Yaaya ina zaka kaimu haka Kamar zamubar gari"


Tsaida motar yayi ya kife kanshi jikin stiaryn motar.

Shiru duk su biyun sukayi.

Can dai Sofiyya tace "Yaaya lafiya kuwa? "

Shiru yasakeyi bece komai ba

Itama shirun tayi ta cigaba da zuba mishi idanu.

.........

Bashir kam jan Siddika da hira yayi, nan da nan suka saba, abinka da maganannu.

Cikin hirar tasu Basher kecewa "wai nikam har yaushe kawarki tasan Abdul haka"

Murmushi Siddika tayi tace "kawata kuma yayata ba don cousin muke da ita"

"No wonder Kamar taku tayi yawa wlh" inji Bashir


Siddika tace "aikuwa babu ta inda muke kama da Sofy wlh tab"

Bashir yace "todai inaga duk familynku kyawawa ne"


Wata Uwar Dariya tasakeyi sannan tace "kai bakasan inna ba ko hhhhhh, ai wlh Kamar biri haka take, mamanmu kuwa hmmmm bazan dai ce komai ba"


Duk Dariya sukayi yace "bakida M wlh, baki fadamin yadda cousin dinki tasan Abdul ba"

Siddika tace "au wai handsome injita da fada, saurayinta nefa"


Da mamakin gske Bashir yace "saurayinta dai"


Nan tafara Bashi labarin tundaga haduwarsu yadda Sofiyya tabata labari.

.....


Wasa wasa seda suka shafe kusan minti goma babu wanda yayi magana acikinsu.


Kokarin bude motar yaji Sofiyya nayi, hakan yasa yadago kanshi yana kallonta, ganin dagaske fita zatayi yasa bashiri ya riko hannunta.

Fizgewa tayi tana harararsa tace "kayi na farko bance komai ba shine yabaka damar sake maimaitawa, saboda kadaukeni marar mutunci ko"


Kallon yadda tazage take zuba mishi masifa yake, tabbas tabashi mamaki don wlh beta6a zaton ta iya masifa hakaba.


Bude motar tayi tafita, da hanzari yabi bayanta yana "Cutie Naa don Allah kitsaya kiji"

Wani iri taji sunan har tsakar kwakwalwarta, dan murmushi tayi don sunan ya matukar yimata dadi, amma bata tsaya ba taci gaba da tafiya sedai tarage saurin da takeyi.


Taku kadan yayi ya cimmata, a gaban ta ya tsaya ya zuba mata ido.

Itama tsayawa tayi ta sunkuyar dakai, murmushin datake ta kokarin 6oyewa yaki 6oyuwa har seda Abdul yagani, hakan shima yasashi murmusawa.


Nuna mata wani dan dakali a kofar wani shago yayi, ba musu tawuce sukaje suka zauna.


Unguwar tafara karewa kallo, babu yawan gidaje a gurin, Shiru take kamar dai tasu unguwar.

Gyaran murya yayi, ta kalleshi ta sunkuyar dakai.


Magana yafara cikin sanyin murya
"Cutie I know zakiyi mamaki idan nace miki nadan dau lokaci ina karyata zuciyata aka sonki, sedai yanzu yakai limit din dabaxan iya cigaba da karyatata ba. I LOVE YOU cutie don Allah kema kisoni kinji? "

Wani irin yanayin da baze faduba kuma baze fassaru ba ta tsinci kanta, zataso ace wannan yanayin ya dawwama a rayuwarta, takasa dago kai balle tayi magana.


Hakan yasa yacigaba dacewa "i may not propose properly but wlh dagaske nakeyi Cutie kawai dai banson irin kalmomin dazanyi anfani dashi bane gurin bayyanar da hakan"

Itadai murmushi takeyi don batajin zata iya furta komai a yanzu, kuma anan gurin.

"Cutie bakice komai ba please kiyarda dani"

Mikewa tayi tanufi gun motar batare da tace komai ba.


Cike da damuwa shima yamike yabi bayanta yana sosa kai,.

Bayan sun shiga mota ya kalleta yace "Cutie "


A hankali tace "mutafi please "

Ba musu yatada motar yajuya yanufi komawa school dinsu.

A ransa kuma yanata fadin "meyasa nayi saurin proposing batare da nasan kalmomin da ake fads ba? Oh god"


.........


A school kam bayan munnir yagama haukarsa direct gunsu mommy ya wuce, kai tsaye yanufi Hajjaju


"Hajjaju ki kira daddy kisanar dashi wlh sofiyya tafara bin maza"



"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'iuun, laailaha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam, Nashiga uku ni Amina'

Hajjaju ta furta tana mikeyi, tadaura hannuwa akai.


Baramin 6aci ran mommy yayiba, don da biyu munnir yafsdawa Hajjaju hakan yasan yanzu zata tara musu jama'a.

Shiko wani dadi yaji, at least itama taji zafi a ranta.

Kai tsaye gaban mommy Hajjaju tazo tana "nikam kin haihomin jaraba, wlh Allah ya Isa tsakanina dake inbaki kirawo ta yanzu tazo ba"

Mommy iya 6aci ranta yayi, don haka tace "haba Hajiya, yanzunnan fa Sofiyya tabar nan gurin ina ko awa daya ba'ayiba yaje ya shiryo karyarsa kekuma zaki yarda"

Dike ha6a Hajjaju tayi kafin tayi magana Munnir yayi tsalle yace

"Wlh Hajjaju agabana saurayin a kama mata hannu yasata a mota, babu irin maganar da banwa yarinyar nan ba amma taki saurarata tabishi suka tafi"


Hajjaju da tun kafin munnir yakarasa magana hawaye ya wanke mata fuska, taja majina tace

"Kinji ko kindaiji ai Mardiyya, nidai wlh DaDa ta cuceni data hada Dana dake, ai tasan bata baki isashshiyar tarbiyya ba gashi kin gur6atamin iyalai"

"Duk ba wannan ba Hajjaju, yanzu wani hotel zamuje nemanta shine abinda takamata mu maida hankali akai"

Share hawayenta tayi da mayafinta tace "ni kaga ban Isa da mardiyya ba don haka kai in na Isa dakai kakiramin Adamu yanzun nan"


Aikuwa babu musu Munnir yahau Kiran daddy.

Mommy jitayi gaba daya munnir yasane mata, wata tsanarsa takeji har cikin ranta, barin gurin tayi taje can gefe tahau Kiran layin Sofiyya.


Daddy dabe dade da barin gurin graduation dinba yaji ringing wayarsa, ganin munnir yasashi yadauka.

"Daddy Hajjaju keson magana dakai"

Nan yabawa Hajjaju wayar

"Kaga Adamu indai ni Amina nice nahaifeka to kabar duk abinda kakeyi kazo nan makarantar kasameni" Hajjaju ta furta sannan ta mikawa munnir wayar batare da ta tsaya jin me Daddyn kecewa ba.


Hankali tashe daddy ya juyo kan motar dama bekai ga Isa inda yanufa ba.



Siddika dake rike da wayar Sofiyya taga Kiran mommy kin dauka tayi tace "mommy kibar yarki taji da handsome"


Ita da Bashir duk dariya sukayi,.

Cigaba da Kiran wayar mommy tayi har seda tayi missed call biyar.

Nan hankalinta yafara tashi sosai, layin Siddika takoma Kira.

Siddika ma ganin Kiran yayi yawa yasa tace "inaga fa mommy na bukatar ganin Sofiyya ne, baridai inje insan mezance mata"


Bashir yace "gsky kam to don Allah zan iya samun numbern ki don mudinga gaisawa"


Ba musu tafara karanto mishi, a gurguje takarasa Karanta mishi sakamakon sabon Kiran data gani a wayarta.


Sallama sukayi tayi saurin daga Kiran.


"Ina kuke ne? Ina Sofiyya bani ita inason magana da ita"


Rikicewa Siddika tayi, don tun awaya tagane akwai matsala, yanayin da mommy take tambayarta tasan ba lafiya.

"Mommy gamunan zuwa"

Abinda Tafada kenan takashe wayar,

Aranta take zance "Kodai hatsari su Sofiyya sukayi? "

Dasauri ta girgiza kai tace "insha Allah bahaka bane"

Wani Kiran tasake gani daga mommy, hakan yasa tayi saurin komawa cikin makarantar batareda tadau wayar ba.


Kaci6us sukayi a hanya mommy na kokarin fitowa


"Ina Sofiyya?"

Kalmar da mommy tafurta kenan bayan taga Siddika.

Gaban Siddika ne yafadi, amma tadaure tace "ta ta tafita ne taje... Uhm"

"Ina taje" mommy ta tambaya

"Taje raka bakinta ne yanzu ai zata shigo mommy lafiya kuwa? "

"Maza kibita kice tabar raka bakin tazo nan yanzu yanzu"

"To" tace tajuya tayi hanyar fita cike da fargaba.

To ita yanzu ina zata nemo Sofiyya?

.... Bashir daya fito yana ta murmushinsa, don Siddika ta nishadantar dashi ba kadanba, shi beso mommy takirata ba wlh.

Hangota yayi tafito hakan yasa shima yafito yanufo inda take.

"Yadai? " ya tambaya ganin yadda yanayinta duk ya sauya.

Nan tabashi labarin abinda yafaru.

Tayata jimami yakeyi, suka fara tunanin tayadda zasu 6ullowa lamarin.


Can dai ga Hajjaju, munnir sekara ingizata yake.


Daddy kuma na hanya hankalinsa duk ya tashi.


Sofiyya kam na mota cike da farinciki na shaukin sabuwar rayuwar soyayya.

Shikuma Abdul yana tuki cike da taraddadin amsar dazeji daga gareta.

Zuly takoma gunsu Anty Zainab cike da tunanin matakin daya kamata ta dauka aka Sofiyya.


..............


Har kusan la'asar babu wanda yazo asibitin duba halin da suke ciki.

Haka mustapha ya wuni besaka komai cikin bakinshi ba.

Bayan yadawo daga masallaci ya tarar har lokacin hafsat bata farkaba.
Ajiyar zuciya yasauke yajuya ya nufi gun likita.

"Likita zan iya tafiya inje indawo bazata farkaba"

"Eh amma karka wuce awa 3 don ina tsammanin nan da awa 3 zata iya farkawa" inji likita


"Ok tom nagode, insha Allah zan dawo dawuri"


Fitowa yayi yahau mota yanufi gida....................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?

Episode 25

Dashigarsa gidan bewuce ko inaba se sashin inna, yasameta zaune kan dardum ta idar da sallah tana jan carbi.

Neman guri yayi yazauna yana jiran takarasa.

Bayan 'yan mintuna ta ajiye carbin tajuyo tana kallonsa.

Sunkuyar dakai yayi sannan yace

"Barka da yamma inna"

"Barkanka, yanaganka anan a wannan lokacin? " inji inna


Cikeda ladabi yace "inna Dama yau banje kasuwa ba, sakamakon lalurar hafsat, yanzu haka tana can asibitin nabaro ta a can"


Cikin halin ko inkula inna tace "to yayi kyau"

Har cikin ransa bayajin dadin yadda inna keyiwa hafsat a gidannan, yanzu duk irin halin da take ciki ko damuwa da lamarinta batayiba, anya ko mutuwa hafsat tayi zata samu addu'ar inna kuwa?

Shikadai a ransa yake zancen, inna ce takatse shi da "to kuma zaman me kakemin anan? "

Mikewa yayi yanufi waje cike dajin zafin hali irin nata, Wai a hakama dasauki kenan.

Kai tsaye sashinsu yanufa, dashigar sa ya taradda Baraka na wanke-wanke, beko kulata ba yanufi dakinsa.


Baraka da tun bayan fitarsu babu abinda take illa addu'ar Allah ya amshi rayuwar hafsat, ganin yadda yashigo yanayin fuskarsa tanuna akwai matsala.


"Kodai bata mutuba nasan tana hanyar mutuwa" tafada tare da Mikewa tanufi dakinsa cike da farinciki.

Daidai kofar dakin ta tsaya ta daidaita nutsuwarta tayi kalar tashin hankali sannan a hanlali ta

10 / 26