CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 26

24K to 27K   out of 76.5K words

mata "wow" ya furta
Kallonshi tayi tace "what? "

Yace "lallen yayi kyau sosai"

Murmushin jin dadi tayi tace "thank you"

Yace "wacece tayi lallen?"

Tace "gatacan a bayan motanka"

Yace "she deserve to be paid, karfomin account number dinta"

Dadi taji sosai tace "aina biya fa"

Yace "she deserve more"

Juyawa tayi tace "farida kibada account number wai kudin lallenki yafi haka"

Siddika kuwa shewa tayi tace "haka mukeso ai, ke fariri yisauri kibada Account number yau kakarki ta yanke saqa"

Duk dariya sukayi banda Abdul dayayi murmushi sekuma zuly da ta gimtse fuska tun shigowarta motar.

Kallon zuly farida tayi tace "pleace kibasu Account number dinki don Allah kinsan banida Account "

Harta dago zatayi masifa sekuma tadanyi murmushi tabayar, domin hakan ma wata hanyar samun kusanci ne da handsome.

A take yayi mata transfer din 20k aikuwa murna agunta ba'a magana se godiya takeyi.


Suna tafiya suna hira amma su Siddika duk basajin abinda suke cewa, zuly har kara kunne take amma takasa jiyo komai, hakan kuwa yakara 6ata mata rai.


Ahaka suketa tafiya, Sofiyya ta juyo tace "address dinku fa"

Dasauri zuly tace "ai yasan gidanmu"

Da mamaki Sofiyya tadube shi tace "wai kasan gidansu".

Dan waigowa yayi yace "ta ina gidankun yake? "

Wata dariya Siddika tayi, bata dai ce komai ba.

Nan Zuly tasake qula tadai daure tace "Layinsu Anty zainab, filin sukuwa"

Se sannan Abdul yatuno inda yasanta, tabbas.

Tafiya sukeyi, zuciyar Sofiyya cike da tambayar inda yasan Zuly.

Seda suka ajiyesu sannan suka wuce, hanyar wani shoprite yayi dasu,.

Sofiyya tace "ina kuma zamuje? "

Yace "saidaku zanyi"

Tace "wane mutum"

A haka dai sunadan ta6a hirarsu har sukaje.

Tun tana dan tirjewa kan ita bazata shigaba, seda Siddika ta tilasta mata suka shiga.

Aikuwa anjido kaya kamar na siyarwa.

Sosai Siddika ke yiwa Sofiyya murna, don tanason mutum me sake hannu kamar dai Abdul.

Har yamaidasu gida sukayi sallama shaf Sofiyya ta manta da tambayar dazata yi masa, se bayan data nutsu tukun abun yadawo mata, tace "ai zamuyi waya anjima"


Alhaji Mu'az dai jiki yaki dadi, don wannan karon abin yafi na koyaushe.

Umma dai zuba mishi idanu tayi, don batama yarda suhadu, lokacin abincinsa zata tabbatar yafita masallaci kokuma yashiga toilet sannan take zuwa ta ajiye masa.

Hakan datake masa kuma bakaramin kara masa zafin halin dayake ciki takeyiba.

Abin yazame masa biyu
Ga damuwarsa gakuma ta umma.

Cikin yaran ma babu wanda yasan Abban yadawo, saboda Usman nata shirye-shiryen graduation sam baya nutsuwa a gida, duk dacewa kullum yana gwada Kiran Abban amma wayar a kashe.

A 6angaren Abdul ma hakanne takasance, sam besan cewa Abban nasu yadawo ba, yakan kira business line dinshi koda yaushe idan yakira drivern shine kedauka yace yana busy, don hakan Abba yace yadinga fada.

Yaune kuma Anty Raliya ke tafe, babu wanda yakai Usman murna at least zesamu abokiyar shawara dakuma hira

*

Ranar Asabar
Yakasance saura kwana daya graduation party dinsu, kowane 6angare ana shirye-shirye kamar na aure.



Da dare bayan angama dinner su Sofiyya anbaje kayayyakin da aka kar6o daga dinki se gwadawa akeyi.

Munnir ne ya sako kai cikin falon, tsayawa cak yayi ganin Sofiyya cikin wani gown maroon colour wanda yakara haska fatarta, tayi matukar kyau.

Besamu damar karasa sallamar daya farayi ba, babu wanda yakula dashi se mommy.

Itasam kwanakinnan bata gane irin kallon da munnir ke jifan Sofiyya dashiba.

Kuma ko kadan batason hakan,
Kallon Sofiyya tayi Tace "to aiseki cire tunda kingama gwadawa"


Sofy tace "mom wlh wannan duk tafi kyau, nifa inaga itakadai zansaka ma"

Siddika tayi dariya tace "kaji kauyis"

Tana kokarin cireewa ne (dayake akwai kaya a jikinta)
Munnir yayi saurin tareta dacewa
"A, a tsaya inmiki photo tukun"


Dan tsaki taja yacigaba da cirewa ta ninke ta mayar Leda.

Yaji babu dadi a ranshi amma dai yadaure.

Mommy kam batace uffan ba.

mikewa Sofiyya tayi tanajan hannun Siddika tace "kizo muje makarasa a can"


Dasauri yasha gabanta Yace "waini meyasa kikemin hakane iyee? "


Wata Uwar harara ta watsa mishi, sannan ta gittashi tawuce.

Dariya Siddika tayi tace "dan anace beyiba wlh hhhhhhhh"

Tazo zata wuce tagabanshi ya fizgo hannunta kafin tayi magana ya kifa mata Mari.


Ihunta kawai mommy da Sofiyya sukaji, tuni sukayo gurin.


Mommy tace "amma munnir ka kyauta kenan? "

Yana huci Yace "ashe kinajinmu seyanzu zakiyi magana saboda nayi hukunci."


"Lallai munnir bakada kunya mommyn kake yiwa magana haka? "
Sofiyya tafada tana gangarowa


Cikin 6acin rai Yace "Munnir munnir kike kira munnir Sofiyya? "


Wata Uwar harara tasake zuba masa taja hannun Siddika sukayi gaba.


Mommy ma bata sake cewa komai ba tayi wucewarta aka barshi shikadai yana cizon yatsa.


Anty Raliya ta iso lafiya, sun kammala duk shirinsu.


Munnir kai tsaye gida yanufa, ya tadda hajjaju harta kwanta barchi,

Buko kofar dakinta yayi da karfi, hakan yasa a firgice tamike tafito falon a guje tana
"a'uzubillahi nashiga uku ni Amina yanzu DaDa seda kikamin turen aljanu cikin dare? Manniru Manniru kana ina, kataho da alqur'ani"


Kallonta kawai yake tana juye-juye a falon tarasa inda zata nufa.

Seda tagama haukarta sannan ta kula dashi yana zaune kan kujera.

A hankali tazo tadan ta6ashi domin tabbatar wa koshidinne, ajiyar zuciya tasauke sannan tazauna gefenshi

"kasanfa DaDa bata mantuwa kuma bata yafiya, kagadai aminiya tace amma dole infadi gsky koda akainane, kasan fa..... "

Bata karasaba yamike cikin zafi Yace "dalla ni karki wani dameni da surkulle, kibarni inji da damuwata"

A firgice ta mike itama tana daga hannuwa sama tana saukewa

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'uuna Manniru shiyasa nake cewa kadinga addu'a yanzu gashi anturomin aljanun saboda karfin addu'a ta sun tsallakeni sunhau kanka"

Tayi hanyar dakinta tana magana
"Garadai intafi kafin kafara duka, Allah dai yakaimu gobe anemo maka me rukiyya"


Shikam zama yayi agurin yana tunanin yadda ze shawo kan Sofiyya su daidaita.


A suleja
Cikin dare Anty hafsat tafara nakuda gashi babansu Siddika ba'a dakinta yakeba, hakan yasa tadau waya tayi kiransa

A daidai lokacin shikuma yashiga toilet hakan yabawa Haj. Baraka (mamansu Siddika) damar daukar wayar.

Cikin yanayin rashin lafiya Anty hafsat tace "noory abinfa yazo wlh, nakasa daurewa kuma, don tun magriba nakejin badadi"

Wani wawan tsaki Baraka taja takuma katse kiran.

Tabbas Anty hafsat taji sautin tsakin datayi, amma hakan bedameta ba, tasake kira.


Ganin wani kiran nasake shigowa yasa ta kashe wayar gaba daya.

kiran wayar tacigaba dayi amma taji switched off.

Hankalinta yatashi don tasan aikin Baraka ne, duba wayar takeyi a ranta tace
"Towa ma zankira? Banida kowa a duniyar nan sekai"


Hawaye ne ya zubo mata, bawai na wahalar datake shaba, na tuno maraicin datake ciki.


Haka tayita murkususu kafin asubah kuwa tagama galabaita har bata motsi,.

Baban Siddika nafitowa domin zuwa masallaci yayi hanyar dakinta domin tashinta, tura kofar yayi kai tsaye, don dama ya hanata saka sakata saboda tsufan da cikinta Yayi, kada azo asamu matsala.

Tunkan yakarasa shiga falon ya hangota a kasa kamar gawa

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'iuun"
Yafurta kana yakarasa cikin dakin da hanzari ya hau jijjigata amma inaa babu alamun zata motsa.


Cicci6ota yayi a hannu yayi hanyar waje da ita.

Baraka da fitowarta kenan ta hangoshi, wani farinciki ne ya mamayeta a ranta tace "Allah dai yasa daga can se kabari badai gidannan ba amin"

Ko takan shashin Inna bebiba yayi waje dasauri yasata a mota yadau hanyar asibiti...........
'?


Nace muhadu a gun graduation ne kokuma a asibity ne>??
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?


Episode 21-22

Asibiti

Dazu wansu likitoci sukayi rubdugu akan hafsat, dafarko ma sun zata ta mutune, seda wani babban likita yazo sannan ya tabbatar dacewa bata mutu ba, hakan yasa aka tafi da'ita emergency.

Bayan Baraka ta idar da sallah ne tamike domin zuwa tasanar da inna abinda ke faruwa.

Sallama tayi amma inna bata amsaba, kuma sarai tajita.

Guri tasamu ta zauna tana "ina kwana Inna? "

Hannu kawai ta dago mata, don batason magana yau.

Zama Baraka tagyara sannan tace "dama hafsat ce haihuwa tazo mata"

"To" Inna tafada.

"Shine suka tafi asibiti dx baban.... "
Kafin takarasa Inna tayi saurin katseta da fadin

"Nace ni likitace? Kinga Baraka ki kiyayeni, to ina ruwana da haihuwar dazatayi, koni nayi mata cikin? "

Shiru Baraka tayi

Cikin tsawa Inna tace "kifice min anan kafin inyi bal dake"

Sum sum Baraka tayi waje.

...

Zuly tunda tayi sallar asuba bata koma barchi ba, tahau aikin duk datasan tasaba tagama.

Wanka tayi ta ca6a kwalliya, dayake ba ma'abociyar kwalliyar bace setayi kyau sosai.

Sabuwar Atamfar data dinka domin wannan ranar tasaka, se farinciki take, kamar itace zatayi graduation din.


Mama dai idanuwa tazuba mata, don tarasa farinciki da rawar kan da zuly keyi na menene?

Itakuwa a ranta ta kudiri niyyar bayyana soyayyarta ga Abdul a yau, domin taga alama idan tayi sake za'ayi wuff dashi.

Tarasa munnir amma bazata yarda tarasa Abdul ba kuma.

....

Su Usman da Sofiyya kam tuni sun tsufa a school anata Shirye-shirye.

Abdul kam kwana yayi yana tunanin ta inda zefara tunkara Cutie da zancen soyayya?

Har gari ya waye, besamo mafita ba, sedai yasaka ya warware yarasa makama.

Fitiwarsa daga wanka daure da towel a kugunsa, zama yayi bakin gado yayi tagumi a fili Yace "ni Abdul yaya zanyi? "

Mikewa yayi yafara shiri, sabon yadin daya dinka purposely saboda wannan ranar yadauko yasaka, dark ash, tayi matukar haskashi,.

Sabuwar hula yadauko yasaka, agogo da takalminsa duk sabbine,.

Tsayawa yayi a gaban mirror yana karewa kansa kallo, sosa keyarsa yayi yana murmushi.

Nan yafara kwatanta yadda zeje mata, dama already yasiyo gift din daze bata.

Ya gwada acting fin goma a karshe dai cewa yayi "komadai yaya ne, idan naje idea zataxo min"

Key din motarsa yadauka yafito falo,
Nan ya taradda su Raliya anata shiri kamar iyayen biki.

Raliya na hangoshi tahau guda, "ayyiririiii yaaya wlh kamar wani ango"

Murmushin jin dadi yayi, koba komai takara mishi hope din aiwatar da shirinsa.

Yarinyar Anty Raliya wato Tasleem tayi gudu tanufi gurin shi tace "uncle yau fa ba sallah bane, kuma naga kasaka kayan sallar ka"

Kafin yabata amsa Raliya tace "Hmmm su yaaya harda yin sabon dinki, gsky Usman yayi goshi, wama yata6a zaton zakaje, yadda bakason hayaniya"

A hankali Yace "to gashi kuma zanje ai"

Hakanan suketa hirarsu, shi yana zaune sukuma suna aiki.

Makobta ne suka fara shigowa hakan yasa yamike Yacewa Raliya "kawomin breakfast " yashige dakinsa.

....... Munnir kam bema tashi a barchi ba dalilin rashin barchin dabeyi jiya da wuri ba.

Hajjaju tagama shirinta tsab tanufi dakin munnir tahau knocking.


Bugu biyu yaji yafarka don baida nauyin barchi.

Fadi take "manniru Kodai ka mutune, inkira makobta suzo sumaka jana'iza? "

Bukawa tacigaba dayi, shikam munnir toilet ma yashiga yafara wanka.

Hajjaju kam hankalinta ne yafara tashi, jin ba'a bude kofar ba, kuka tafarayi tanufi Kofar gidan tana cewa "nidai Allah yatsine wannan gangetion din, sanadin wannan rana nake rasa jikana manniru"
Kara rushewa da wani kukan tayi, .


Munnir daya jiyo sautin kukan nata yayi saurin dauraye jikinsa ya daura towel yafito dagudu yakamo hannuta yana cewa
.
"Haba Hajiya don Allah meye haka".

Tsayawa tayi cak tazuba mishi idanu,
Janyo hannunta yafara yi tayi saurin fizgewa tana "nashiga uku kwarto, manniru kwarton aljani yashigeka innalillahi Allah kakawo mana agaji"

Cike da takaicin hali irinna hajjaju yajuya yawuce ciki.
Itama bayanshi tabi tanata sababi.

.....

Agidan daddy kam kowa yagama shirinsa, su Ikee ansha golden gown tafito tayi matukar kyau kamar flower girl.

Siddika ma ansha kyau leshi tasaka blue da fararen stones,

Mommy ma leshin tasaka Ash colour tasaka farin mayafi da farin takalmi.

Dukadai sunsha kyau, Hajjaju kawai suke jira da tuni suntafi.
dakin
......

Zuly kam tariga tagaji da jiran Anty zainab don haka tayiwa mama sallama tanufi gidan Anty zainab.


Dazuwanta tasamu Anty zainab tana kokarin kulle kofar dakinta don itama tagama shiryawa.

"Laaa zulyn mama kinkuwa zo a daidai don munkusa makara"

Murmushi zuly tayi tace "aikuwa semu wuce"

Nan suka gaisa sannan suka nufi gidan Abba.

.... Seda munnir yagama shirinsa yadau gift din daya saiwa Sofiyya yafito falo da keyn mota a hannu shi.

Hajjaju data zuba uban tagumi a zaune kan kujera tana hangoshi ta mike tana "sannu da fitowa manniru, nidai inkanayiwa Allah kada kata6ani kazubar min da mutuncina," takarasa tana ja da baya.


Dogon tsaki munnir yayi yanufi hanyar waje yana "inkin ga dama sekifo mutafi, inkuma Kika 6ata lokaci wlh sedai adaidaita ya kaiki"

Begama magana ba tayi gudu tawuce shi tafita taje gurin motar tatsaya se haki take tana numfarfashi.

Harararta yayi yabude mata gaban motar, ba musu tashiga ya rufe yazaga yashiga driver side yazauna yatada motar suka dau hanya.

...... Su Anty Zainab suna karasawa aka firfito domin dama ita suke jira.

Sungama fitowa harabar gidan umma tawaiga tace "to ina Abdul din kuma?"

Anty Raliya tace "bari inje inkirawo shi"

tana zuwa ta tura kofar, samunshi tayi ya zube abubuwa dayawa kan gado bemasan tashigo ba.

Wani frame ta kurawa ido, An rubuta I LOVE YOU CUTIE

batasan sanda wata dariya tazo mataba tama manta a inda take.

Juyowa yayi yaganta, wata Uwar harara ya zabga mata sannan yace "uban me kikazo min a daki"

Se sannan tatuno inda take, sum sum tayi hanyar waje, tana "dama umma ce tace mungama wai kazo mutafi"


Tattara duk shirgjn abubuwanshi yayi, cikin babbar leda ya kinkimo yafito.


Ganin jama'a dayawa yasa ransa dan 6aci, hakan yasa yakara tamke fuskarsa.

Batareda ya kula kowa ba yanufi motar ya bude yashiga yazauna.

Anty zainab ce takamo hannun zuly sukayi gurin motar.

Umma kam da harara tabisu, sannan tace "kwashe-kwashen zainab yayi yawa wlh, ko ina tasamo wannan yarinyar oho"

Kiran driver umma tayi, yafito da mota ta tura sauran yan uwa da makobta suka fara gaba.

Itakuma dasu Raliya duk motar Abdul suka shiga, Raliya tazauna a gaba.

A hanya Anty zainab tace "hala yau aljanun kin magana ne yashafeka Abdul"


"Kaiiiiiii" Yafurta yanadan waigowa Yace "toni wlh banma kura dakeba Anty kiyi hakuri please, ina yini"

Murmushi tayi tace "lpy Lou aina zata 'yan shirun ne suka motsa"

Zuly da tunda sukazo take sunsunne kai alamun dai tana gaban surukai lol
a hankali tace " ina yini yaya Abdul"

"Lafiya" kawai yace.

Umma ko sam yarinyar bata kwanta mata ba,.

Raliya kuwa juyowa tayi tana karewa Zuly kallo.

..... Koda su munnir suka kai gidan basu jira komai ba don dama su akejira, dan haka Hajjaju batama fito daga motar ba, sukadau hanya...


GOLDEN HIGH SCHOOL HALL

Kowani dalibi kagani murna yakeyi, sukuwa graduates kana ganinsu zaka ganesu sakamakon graduation gown din dasuka saka.

Antaru a gurin ba masaka tsinke anata gabatar da programs.

Yanzune kuma iyalai suketa zuwa, ciki kuwa harda Iyalan gidan Mu'az Gallafi dakuma na gidan Adam Muhammad.

Duk sun hallara a gurin anbasu masauki sun zazzauna.

Tunda suka shigo gurin Abdul idonshi akan graduates din yasauka, harsuka zauna kuma yanata rarraba idanun inda xe hango Cutie a cikin su amma haryanzu be gantaba.

Programs nacigaba da gudanawa, ankuma zo fannin da graduates zasu gabatar da kawunansu.

Lokacin da akazo kan Sofiyya har wani ajiyar zuciya Abdul yasauke sakamakon jin muryarta dayayi.

Zuly kuwa wani kulun bakin ciki taji, don bataso wannan yarinyar takasance anan ba, ashema 'yar makarantar ce.

Anzo gurin raba gift anan ne kuma Sofiyya tasamu gifts masu yawa best in chemistry, best in civic education, best in English, and best in performance.

Sunyi kunnen doki da Usman, shikuma best in physics, best in mathematics, best in IRS and best in neat ness.

Ihuuu filin yadauka aka hau tafi.

Nan aka bukaci graduates sufito fili sutaka rawa
Aka sake musu wakar Stand up stand up nan suka shiga fili suka hau rawa.

Cikinsu babu wadda betaka ba, daga karshe suka cire hulunan kansu suka wurga sama.

Nan aka sake wani ihun sannan kowani graduate yanufi gun da Iyalan gidan su suke cikin farinciki da annashwa.


Kafin Sofiyya takaraso gurin takwa6e graduation gown dinta a hanya, ta rikoshi a hannu, dasauri Munnir yamike yaje ze kar6a, kaucewa tayi tana harararsa tabi gefe tawuce abinta.


Wata irin kunya yaji, yadda ta kunyatashi a cikin mutane.

a kunyace yadawo gurin yazauna, mommy na kallon duk abinda ke faruwa amma tayi kamar bata ganiba.

Anshiga shagalin bikin graduation, dalibai duk sun caccanza kaya zuwa ankon dasukayi, maza sunsaka shadda brown colour mata kuma sunsaka leshi marron color, ansha hotunan iri-iri.

Duk wannan abubuwan da akeyi Abdul idonshi nakan Sofiyya, duk inda ta gifta binta yake da ido, itama zuly duk inda yake idonta nakanshi, kuma sarai ta lura da yadda yakebin Sofiyya da kallo, hakan yasa taji takara tsanarta.


Usman bayan sungama pic da yan ajinsu kusada Sofiyya yaje yace "Uwar rawar kai"

Harararshi tayi tace "Na'am uban rawar kai"

Dariya yayi yace "muje ku gaisa da fam Dina, don umma na harta gaji dajin labarinki"

Ba musu tabi bayan shi suka nufi inda su umma suke.

Tunda suka tunkarosu Abdull yake kallonta, Bakaramin kyau tayi masa ba,.

Itama a lokacin da ta kalli inda yake sakankancewa tayi wurin kallonsa, don harga

9 / 26