Chapter 17 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 26

48K to 51K   out of 76.5K words

daddy cikin daure fuska yace "your final answer Sofiyya "

Babu wani tsoro Kanta a kasa tace "daddy Abdul"

Besake cewa komai ba yamike yanufi dakinshi.

Kaiwa da komowa yahau yi yana nazari, shin dawani idon ze kalli yayanshi? Kiri-kiri Sofiyya nason tabashi kunya, ga uwa uba yadda Munnir ya kwallafawa ransa son yarinyar nan, to gida bekoshi ba yabawa na waje? Haka dai yayita zarya yana tunane tunane, be ankaraba yaji sallamar mommy tana "bakinka sun karaso fa, anyi musu iso suna parlon baki" tana gama fadin haka tayi wucewarta.

Numfashi yasauke sannan yadau hularsa daya ajiye yanufi parlon.
Bayan sun gaggaisa ne daddy yace "to Alhamdulillah yarinya dai ta amince da Abdullah kuma muma mun amince babu wata matsala"

Bakaramin farinciki Abba yaji, don shi har cikin zuciyar sa yakeson Sofiyya tazama surkarsa duk da beta6a ganin ta ba, a wannan karon bashi kadai yazo tareda abokinsa suka zo don haka abokin Abba da daddy ne sukayi magana shi Abba yayi kawaici.

Maganar sadaki sukayi daddy beso kar6an kudinsu ba amma saboda yadda suka matsa kuma yana jin kunyar Abba matuka hakan yasa ya amince ya zari dubu hamsin cikin kudin yamayar musu da sauran da yakai dubu dari biyu ko sama da haka, sunyi-sunyi ya kar6i kudin duka amma yace albarkar abin ake nema ai karancin sadaki yafi albarka.
Nan sukayi sallama Abba baki yaki rufuwa zezama suriki, shikam daddy ba yabo ba fallasa yashiga yasanar da mommy yadda sukayi sannan yayi kiran Sofiyya ya damka mata sadakinta a hannunta yanufi dakimshi.

Jikin Sofiyya yayi sanyi sosai daganin yanayin daddy kamar beji dadi ba, amma wani 6arin na zuciyar ta farinciki takeyi sosai kamar tamike tataka rawa, sunanan zaune a parlon daddy yasake fitowa yamikawa Sofiyya wayatta daya kwace sannan yace "kidai kiyaye banda rawar kai, koyanzu kikayi abinda bedace ba zan sake kwace wayar "

"Nagode daddy insha Allah bazan sake ba" Sofiyya tafada kanta akasa.

Daddy na wicewa itama tamike ta ajiyewa mommy kudin a cinyarta da kudu tayi stairs tana kokarin kunna wayar.

Koda Abba yakoma gida babu wanda yasamu a parlon se Abdul, gabadaya ya rikice yakasa zaman dakin nashi, abinci kuwa tun safe rabon dayaci wani abun se ruwa dayake sha.

Abba na shigowa Abdul yamike yana "Abba sannu da dawowa" bakinshi har rawa yake..
Da kallo Abba yabishi sannan ya girgiza kai yana wucewa yaje yazauna, shima biyoshi yayi yazauna a kasa kusa dashi, kallonshi Abba yayi yace "kasan ba lallai ne akoda yaushe mutum yakecin nasara a rayuwa ba"

Dummm Abdul yaji sedai wani 6angaren na zuciyar sa kuma farinciki ne seya rasa wannene gaskiya.

Abba yaci gaba "to Alhamdulillah yauma dai kaaakeyin nasara har ankar6a sadaki"

Abdul mezeyi inba murmushi me hade da dariya ba, yanayi yana "Abba nagode Allah yasaka da alkhairi nagode nagodewa Allah nagode" kamar wanda ya zauce haka yaketa maimaita wa yamike yana tafiya yana maimaita wa harya shige daki.

Dashigarsa yayi sujudush-shukr sannan yashiga toilet yadauro alwala domin gabatar da nafilar godiya ga ubqngijin daya bashi nasara a karo na ba adadi a rayuwarsa.

Yana idarwa ko addu'a beyiba wayarsa dake gefensa tadau haske, lekawa yayi ganin numbern dabeyi zatoba wato numbern Sofiyya yasashi dauka da sauri har hannunshi na rawa yamike yanufi gado yana lumshe idanu kafin yayi picking...................
'?

Nace yau babu jan ajinne mr handsome>??.

Ftan alkhairi gareku kusake hakuri dani please =?O?

Masu yimin cinikin data ina matukar godiya Allah yabar zumunci=?
?

Gameson shiga group dina ga numberna 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_

_*TALLA*_
Akwai turaren humra me kamshin kwantar da hankali dakuma kama jiki. Muna maraba da masu siyan daya daya ko sari. Dakuma masu talla ta online abasu a farashin sari sukuma sukara nasu akai, in ansamu me siya sucire ribarsu=?L?
Mace seda kamshi, game bukata yayi magana ta 07046767662 kokuma chat ta Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman

Episode 38

Shiru duk sukayi se sauraron numfashin juna suke, sunkai minti 5 a haka sannan Sofiyya ta katse shirun da fadin "Assalamu alaika sahibina"

Ajiyar zuciya yasquke yana lumshe idanuwa sannan yabude a hankali cikin tausasa murya yace "wa'alaikis salaam habibtyna".

Har cikin tsakiyar kwakwalwar kanta taji sabon sunan nata, itama lumshe idanun tayi tana murmushi me hade da hawaye, tace "yaaya" cike da shagwa6a tayi maganar.

Jin sautin shagwa6ar datayi wadda yasa har seda tsigaar jikinshi yatashi yasashi saurin katse kiran yana kankame fillow.

Jin an katse kiran yasata dago wayar tana kare mata kallo tace "network uwaka" takarasa tana cuno baki, sannan tadau wayar tasake dialing numbern, but harya katse ba'a dauka ba, tunani tahauyi shin meya faru so suddenly? Bata kare tunanin ba taji alamar shigowan sako "i cant pick your call now babe, we will talk later"
Sake karanta sakon tayi tana mamaki, karshe kuma ta kunna data tahau online.

Abdul ya tsinci kanshi cikin sabon yanayin shaukin soyayya wanda beta6a jiba seyau, sosai yakejin wani yanayi wanda yake tunanin ada shisam bashida wannan ashe lokaci ne beyiba, yanayin na karuwa cikinshi na daukar zafi, kan kace me zazza6i ya rufe shi se rawar sanyi yakeyi, bargo ya janyo ya lullu6a ya damke idonshi nan hawaye suka fara zubo mishi, jiyake a wannan yanayin babu wani maganin daze mishi anfani *Cutie* ce kadai zatayi mishi magani, gashi tayi masa nisa, a ranshi yake dada godiya ga Allah daya bashi nasara sannan yake addu'ar Allah yasa bikinsu kar yadau lokaci me tsayi.

Ahaka barchi ya kwasheshi, itama Sofiyya ta karaci chat dinta har tasoma jin barchi bataga Abdul a online ba kuma bataji kiransa ba, agogo taduba taga 11 harta wuce, daga wayar tayi don tasake kiranshi sekuma ta ajiye wayar tana harararta tace "common Sofiyya you are classy okay, bazan kiraba till he call me ehe" takarasa tana murguda baki kamar a gabanshi take.
A haka da tunane-tunane barchi ya kwasheta.

Da asubah da message dinshi tafara tozali "barka da safiya amaryata, kiyi sallah kimana addu'a zuwa 6am zankiraki insha Allah" murmushi tayi tana rufe idonta da tafukan hannayenta tace "wai amarya awwwwn" ajiye wayar tayi tamike ta shige toilet domin dauro alwala.

Kamar yadda yayi mata alkawari 6am din daidai yakirata, hira suke na yaushe gamo nan suka fara labartawa juna abubuwan dasuka faru bayan rabuwarsu dakuma abubuwan dasuke shiryawa gobensu.

....,... Daddy dai se cika yake yana batsewa, adake yayi breakfast yafice, dama Sofiyya yau bata gangaro ba tana can tana soyewa kuma mommy ma batayi kiranta ba don tasan lafiya ce ta 6oyeta yau din.

Yau munnir sammakon zuwa office yayi don yama riga daddy zuwa office din, tubda yazo bezauna ba se zarya yakeyi yana kaiwa da komowa, karshe yama kasa zama cikin office din nashi, fitowa yayi yana ware ido, shigowar motar daddy yasashi sakar murmushin daya bayyanar da hakoransa yanayi yana tahowa.
Bayan daddy yayi parking yabude yafito dasauri ya kar6a jakarsa yana fadin "daddy barka da shigowa". Cike da tausayi daddy kebin munnir da kallo a yayin da yayi gaba shikuma yana binsa a baya beko amsa gaisuwar tashi ba.
Tundaga nan jikin Munnir yafara yin sanyi, a hankali kuma murmushin fuskarsa yafara disashewa zuwa damuwa.
Koda suka shiga office dinma zama daddy yayi fuskarsa cike da tausayin munnir yanuna ma munnir kujera alamun yazauna. Zama munnir din yayi a sanyaye yana kara gaida daddy, bayan sungama gaisawa ne daddy yahau yimishi takaitacciyar nasiha, wanda tunkafin yakarasa munnir yafara hawaye, bayan yagama yasanar dashi rashin nasarar dayayi sosai munnir yake kuka wiwi kamar karamin yaro, yanayi yana cewa "wlh inason ta sosai daddy ninasan mutuwa zanyi ka taimakamin don Allah kaceci raina" wani tari ne ya carke wuyanshi yafara yi ba kakkautawa, nan hankalin daddy yatashi, dasauri yayo kanshi ya jijjigashi, secretary din daddy ce tashigo dasauri tataimaka suka daukeshi suka nufi asibity dashi.

Sosai zuly tashiga damuwar rashin sanin gaskiyar maganar da munnir yayi mata, itadai haryanzu takasa gazgatashi sam, Gashi anty zee tayi tafiya balle tadan samu information, yau dai anty zee saura sati tadawo, hakanan zatayi hakuri har tadawo tukun.

Hankalin hajjaju yafi nakowa tashi dajin labarin halin da munnir ke ciki, don haka babu 6ata lokaci sukayi asibity.

Mommy, Sofiyya, Ikram, Hajjaju dakuma Daddy, duk suna zazzaune a dakin asibityn da munnir yake.

Hajjaju harda guntun hawayen ta se addu'o'i takeyi tana tofa masa.
Sofiyya kam chatting takeyi hankali kwance sema murmushi datake famanyi, mommy kam hira take da yar autarta, daddy kuma tagumi yayi yarasa mezeyi akan wannan matsalar.
Kowa jiran tashin Munnir suke daga barchin dayakeyi, suna cikin haka Doctor yashigo hannunshi da takarda dakuma abin gwaji, koda nadaga kai induba kowaye Doctor din senayi tozali da SABIT! Yes sabit abokin munnir?

Bayan yagama abubuwan dazeyi yajuyo fuskarsa dauke da glass yace "wannan bawan Allah saura kiris zuciyar sa tabuga, nayi mamakin ganin duk ku familynshi amma ya akayi kukabar matsalarsa tayi girma haka? To nidai banson akan me ya kwallafa ransa har zuciyar sa take kokarin bugawa ba" yakare maganar yana kallom Sofiyya da batama san me akeyi ba don hankalinta nakan wayarta.

Juyo da kallonshi yayi kan Abba yace "baba don Allah kuyi kokarin bashi abinda yake bukata nasan bewuce ko mota ba don naga samarin yanzu abinda suke buri kenan, idan har yafarka yasakejin mummunan labari zaku iya rasashi" yana kaiwa nan yayi musu sallama yayi ficewarsa.

Mommy kam mamaki tayi sosai kuma tayi kudirin cewa sedai duk abinda zefaru yafaru, wanda yamutu kwanansa ne yakare amma baza'a kashe 'yarta don a raya Munnir ba.

Hankalin daddy yatashi sosai tunanin abinyi yafarayi, shidai bayason matsawa Sofiyya kan auren munnir amma tunda wannan abun yafaru babu yadda zeyi dolene tayi hakuri ta ceci ran dan uwanta.

Hajjaju kan hankalinta yakai kololuwa gurin tashi, cikin kuka tace "Adamu me manniru keso kakasa yimasa, so kake yamutu koyaya, duk cikin jikokina babu namiji seshi kuma shinafi so, kodai bakin ciki kakeyi ne adamu? Yo inba bakinciki ba tayaya bazaka sai masa mota kota dubu nawa bace? To wlh indai akan motane ka tabbatar dazaran ya farfado duk kalar motar dayace yanaso se ansiya masa koda duka kudinka bazasu isaba sekaci bashi billahillazi se ansai masa mota"

Hakuri daddy yayita bawa Hajjaju yana tausar ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????don bayama son tasan akan me Munnir yashiga wannan halin, don haka bazema bari munnir ya farka a gabanta ba.

......... Ganin yadda Abdul yafito yayi breakfast sannan yatafi office cike da walwala yasanya umma da Abba fahimtar abinda ke damunsa kwana biyun can, bakaramin mamaki hakan yabawa umma ba, "tabdijam lallai Sofiyya taci gari" umma tafada tana murmushi.

Abba yace "banfada masa ba ai, next week zankoma a tsaida ranar aurensu insha Allah, kuma ina fatan hakan baze dau lokaci ba"

Cikin murmushi umma tace "Allah yakaimu"
"Amin" abba yace yana mikewa yace "bari inkoma dama wannan file din nazo dauka".

Umma nazaune anan tayi kiran anty zainab ta shaida mata duk abinda ke faruwa sosai anty zainab tayi murna dajin labarin takuma yi addu'ar Allah yasanya alkhairi.,.............,
'?

Ko yaushe Sabit yazama Doctor???

Gameson shiga group dina seya tuntu6emu ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_

_*TALLA*_
Akwai turaren humra me kamshin kwantar da hankali dakuma kama jiki. Muna maraba da masu siyan daya daya ko sari. Dakuma masu talla ta online abasu a farashin sari sukuma sukara nasu akai, in ansamu me siya sucire ribarsu=?L?
Mace seda kamshi, game bukata yayi magana ta 07046767662 kokuma chat ta Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman

Episode 38

Shiru duk sukayi se sauraron numfashin juna suke, sunkai minti 5 a haka sannan Sofiyya ta katse shirun da fadin "Assalamu alaika sahibina"

Ajiyar zuciya yasquke yana lumshe idanuwa sannan yabude a hankali cikin tausasa murya yace "wa'alaikis salaam habibtyna".

Har cikin tsakiyar kwakwalwar kanta taji sabon sunan nata, itama lumshe idanun tayi tana murmushi me hade da hawaye, tace "yaaya" cike da shagwa6a tayi maganar.

Jin sautin shagwa6ar datayi wadda yasa har seda tsigaar jikinshi yatashi yasashi saurin katse kiran yana kankame fillow.

Jin an katse kiran yasata dago wayar tana kare mata kallo tace "network uwaka" takarasa tana cuno baki, sannan tadau wayar tasake dialing numbern, but harya katse ba'a dauka ba, tunani tahauyi shin meya faru so suddenly? Bata kare tunanin ba taji alamar shigowan sako "i cant pick your call now babe, we will talk later"
Sake karanta sakon tayi tana mamaki, karshe kuma ta kunna data tahau online.

Abdul ya tsinci kanshi cikin sabon yanayin shaukin soyayya wanda beta6a jiba seyau, sosai yakejin wani yanayi wanda yake tunanin ada shisam bashida wannan ashe lokaci ne beyiba, yanayin na karuwa cikinshi na daukar zafi, kan kace me zazza6i ya rufe shi se rawar sanyi yakeyi, bargo ya janyo ya lullu6a ya damke idonshi nan hawaye suka fara zubo mishi, jiyake a wannan yanayin babu wani maganin daze mishi anfani *Cutie* ce kadai zatayi mishi magani, gashi tayi masa nisa, a ranshi yake dada godiya ga Allah daya bashi nasara sannan yake addu'ar Allah yasa bikinsu kar yadau lokaci me tsayi.

Ahaka barchi ya kwasheshi, itama Sofiyya ta karaci chat dinta har tasoma jin barchi bataga Abdul a online ba kuma bataji kiransa ba, agogo taduba taga 11 harta wuce, daga wayar tayi don tasake kiranshi sekuma ta ajiye wayar tana harararta tace "common Sofiyya you are classy okay, bazan kiraba till he call me ehe" takarasa tana murguda baki kamar a gabanshi take.
A haka da tunane-tunane barchi ya kwasheta.

Da asubah da message dinshi tafara tozali "barka da safiya amaryata, kiyi sallah kimana addu'a zuwa 6am zankiraki insha Allah" murmushi tayi tana rufe idonta da tafukan hannayenta tace "wai amarya awwwwn" ajiye wayar tayi tamike ta shige toilet domin dauro alwala.

Kamar yadda yayi mata alkawari 6am din daidai yakirata, hira suke na yaushe gamo nan suka fara labartawa juna abubuwan dasuka faru bayan rabuwarsu dakuma abubuwan dasuke shiryawa gobensu.

....,... Daddy dai se cika yake yana batsewa, adake yayi breakfast yafice, dama Sofiyya yau bata gangaro ba tana can tana soyewa kuma mommy ma batayi kiranta ba don tasan lafiya ce ta 6oyeta yau din.

Yau munnir sammakon zuwa office yayi don yama riga daddy zuwa office din, tubda yazo bezauna ba se zarya yakeyi yana kaiwa da komowa, karshe yama kasa zama cikin office din nashi, fitowa yayi yana ware ido, shigowar motar daddy yasashi sakar murmushin daya bayyanar da hakoransa yanayi yana tahowa.
Bayan daddy yayi parking yabude yafito dasauri ya kar6a jakarsa yana fadin "daddy barka da shigowa". Cike da tausayi daddy kebin munnir da kallo a yayin da yayi gaba shikuma yana binsa a baya beko amsa gaisuwar tashi ba.
Tundaga nan jikin Munnir yafara yin sanyi, a hankali kuma murmushin fuskarsa yafara disashewa zuwa damuwa.
Koda suka shiga office dinma zama daddy yayi fuskarsa cike da tausayin munnir yanuna ma munnir kujera alamun yazauna. Zama munnir din yayi a sanyaye yana kara gaida daddy, bayan sungama gaisawa ne daddy yahau yimishi takaitacciyar nasiha, wanda tunkafin yakarasa munnir yafara hawaye, bayan yagama yasanar dashi rashin nasarar dayayi sosai munnir yake kuka wiwi kamar karamin yaro, yanayi yana cewa "wlh inason ta sosai daddy ninasan mutuwa zanyi ka taimakamin don Allah kaceci raina" wani tari ne ya carke wuyanshi yafara yi ba kakkautawa, nan hankalin daddy yatashi, dasauri yayo kanshi ya jijjigashi, secretary din daddy ce tashigo dasauri tataimaka suka daukeshi suka nufi asibity dashi.

Sosai zuly tashiga damuwar rashin sanin gaskiyar maganar da munnir yayi mata, itadai haryanzu takasa gazgatashi sam, Gashi anty zee tayi tafiya balle tadan samu information, yau dai anty zee saura sati tadawo, hakanan zatayi hakuri har tadawo tukun.

Hankalin hajjaju yafi nakowa tashi dajin labarin halin da munnir ke ciki, don haka babu 6ata lokaci sukayi asibity.

Mommy, Sofiyya, Ikram, Hajjaju dakuma Daddy, duk suna zazzaune a dakin asibityn da munnir yake.

Hajjaju harda guntun hawayen ta se addu'o'i takeyi tana tofa masa.
Sofiyya kam chatting takeyi hankali kwance sema murmushi datake famanyi, mommy kam hira take da yar autarta, daddy kuma tagumi yayi yarasa mezeyi akan wannan matsalar.
Kowa jiran tashin Munnir suke daga barchin dayakeyi, suna cikin haka Doctor yashigo hannunshi da takarda dakuma abin gwaji, koda nadaga kai induba kowaye Doctor din senayi tozali da SABIT! Yes sabit abokin munnir?

Bayan yagama abubuwan dazeyi yajuyo fuskarsa dauke da glass yace "wannan bawan Allah saura kiris zuciyar sa tabuga, nayi mamakin ganin duk ku familynshi amma ya akayi kukabar matsalarsa tayi girma haka? To nidai banson akan me ya kwallafa ransa har zuciyar sa take kokarin bugawa ba" yakare maganar yana kallom Sofiyya da batama san me akeyi ba don hankalinta nakan wayarta.

Juyo da kallonshi yayi kan Abba yace "baba don Allah kuyi kokarin bashi abinda yake bukata nasan bewuce ko mota ba don naga samarin yanzu abinda suke buri kenan, idan har yafarka yasakejin mummunan labari zaku iya

17 / 26