Chapter 19 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 26

54K to 57K   out of 76.5K words

mishi, umma ta fizge key din tace "it won't help, mujira fitowar likitan tukunna"

Duk jugum sukayi kowa da tunanin dayake a zuciyarsa.............
'?


07046767662 inkinason shiga group dina kimin magana.
[8/28, 9:10 AM] Maryam-Ashner Jos: [8/26, 10:43 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 41
[8/27, 6:57 AM] Maryam-Ashner Jos: [8/26, 11:29 PM] Maryam-Ashner Jos: Kokari sosai doctors sukayi sannan suka gano matsalar, allurar barchi sukayi masa sannan aka fito dashi zuwa dakin hutu, duk bin bayansu sukayi har zuwa dakin da aka kaishi, bayan an kwantar dashine likita yadubi umma yace "kada kuyi hayaniyar dazata tasheshi" girgiza kai umma tayi, shikuma doctor yayi waje.

Kallon Raliya umma tayi tace "kidauki yarannan da usman driver yamaidaku gida, kiyi abinchi kibashi yakawo daduk abinda kikasan zamu bukata, nizan zauna anan harya farka, kaikuma Abdul kabi doctor kaji menene matsalar abban naku"

"Tom" duk sukace sannan kowa yamike yanufi aiken da akayimasa.

Sofiyya kai nata rawa kamar sabon kadangare, a kitchen take ko ina ka kalla kayane ba masaka tsinke cikin kitchen din duk tabaza shirgi kamar me girkin gidan biki, babu abinda yadameta tana aikinta tana wake-wakenta, momy ce ta leka kitchen din tace "yanzu Sofiyya bazaki dinga kokarin tsaftace gurin dakike aiki ba? See how you mess the kitchen, komai nazaune da duwawunsa, haka kikaga inayi kokuwa dai kazanta ce?"

Sunkuyar dakai Sofiyya tayi tana cigaba da 6are magin dake hannunta tace "momy i want to finish making the soup then i will......"
Katseta tayi da "you will what? Ahakan ne kike tunanin Abdul ze iya dunga cin girkin ki?common kitashi ki tattara duk wani abinda kika 6ata kisaka shi cikin sink dazaran kingama hada miyar seki wankesu kafin miyar tayi"

"Tom" tace tana kokarin harhada duk abinda ta6ata.
"Rubbish girl" mommy tafada tana juyawa takoma parlo.


Nishadin dake tare da ita sam beragu ba don haka tacigaba da rera wakarta tanayi tanadan girgiza kai, yo daman mezesa farincikinta gushewa bayan yau habibinta zezo, numfashi taja tasauke a fili tace "zezo a matsayin mijin dazan aura kuma sirikin mommy da daddy" kunya taji don haka tarufe fuskarta da tafin hannunta.
Cigaba da aikinta tayi tana wakarta, bayan kamar awa daya Sofiyya ta kammala ayyukanta tafara fito da abinci tana jerawa kan dinning, warmer ta farko white rice ne aciki, warmer ta biyu farfesun naman kai ne aciki, warmer ta uku miyan stew ne aciki dayaji kifi, sekuma karamar warmer me dauke da chips sannan wani vowl da aka saka vegetable salad, abin gwanin burgewa, seda tagama jerawa tanufi stairs domin watsa ruwa sannan tatuna bata hada juice ba, don haka dasauri ta dawo tashiga kitchen din, blender tadauko ta dauraye sannan ta dibo abubuwa kamar haka.
Cocumber
Danyen citta
Sugar
Flavour
Lemon tsami
Kanunfari (kwaya uku)

Ta wanke ta yayyanka cocumber tazuba cikin blender din, ta wanke citta ta yanka ta zuba sannan ta watsa kanunfari tazuba ruwa madaidaici sannan ta kunna ta markada, ta matse lemon tsami takawo rariya ta tace sannan tazuba sugar da flavour tajuya sosai tajuye cikin jug takai fridge tadawo tagyara gurin dagudu tahaura sama domin watsa ruwa.


Koda Abdul yfito daga dakin kiran Sofiyya yayi amma bata picking ba, sake kiranta yayi hartakusa yankewa sannan tadauka tana fadin "angona"
Duk da tarin damuwar da yake ciki naralshin sanin damuwar Abbanshi amma jin sautin muryarta dakuma sunan data kirashi dashi ya sanyaya zuciyarsa har yana sauke ajiyar zuciyaa kafin ya amsa da "amaryar Abdul'

Murmushi tayi tace " ka gaji sosai ko? Naji muryarka somehow tired"

"Hmmm wlh sosai ma, sedai godiya"


"Bazan dai yafe maka zuwa yauba duk gajiyar dakayi hakanan zakazo inganka konaji sanyi"

Yace "kamar kuwa kinsan bazan samu zuwaba"

Kukan shagwa6a tafara yimishi harda buga kafafuwa a kasa, shikuwa jin abinda zuciyarsa keso yasashi jin kamar ya kwanta a gurin yayi barchi, wani 6angaren jikinsa kuma yakejin kamar yaruga dagudu yaje gareta.

Kokarin dakatar da ita yake amma inaa se ta6ara take masa kamar a gabanshi take, dakyar yasamu ya lallal6ata sannan yayi mata bayanin halin dasuka samu Abba aciki don haka baze samu damar zuwa ba.

Taji haushin rashin zuwansa don ta 6ata lokaci wurin yimasa girki amma kuma ta tausaya masa na halin da Abbansa ke ciki, addu'a tayimasa sannan sukayi sallama. Daganan yanufi office din doctor.


Bayan sun gaisa ne yaja kujera yazauna yana jiran jin abinda doctor zefada masa, takarda doctor yamuko masa sannan yakara da "mr Abdul matsalar mahaifinka bawata babbar matsala bace, firgici da fargaba ne suka haifar masa da hakan a yayin da yayi gamo da abinda beyi tsammani ba, amma Alhamdulillah komai yalafa dalilin kawoshi asibity akan lokaci, ita wannan matsalar karama ce amma tana da matukar hadari, da abin yazo da tsautsayi ko kunyi jinkirin kawoshi asibity tabbas da ze iya rasa rayuwarsa gaba dayama, yanzu kafin yatashi kwakwalwarsa zata daidaita saboda allurar barchin danayi masa, idan ya farka ze iya mantawa da wancan abinda yagani, ze iya kuma tunawa, abindai da ba'aso shine kada ku takuramasa da maganar abin, idan kuka tambayesa yanuna bayaso to ku kyaleshi kawai"

Miko masa wata takardan yayi yace "wannan kuma kaje pharmacy kasiya, abashi yadunga sha akan lokaci kuma a tabbatar yaci abinci kafin yasha"
Godiya sosai Abdul yayiwa doctor sannan yamike yafito kaitsaye pharmacy din yanufa, bayan ya siya duk magungunan ne yadawo dakin, umma yasamu ta rafka uban tagumi seta bashi tausayi yace"umma kidena damuwa don damuwar Abba bawata babba bace" nan yakwashe duk yadda sukayi da doctor yafada mata, mamaki sosai umma tayi sannan tace "yasalam to kodai dagaske mayyar ce?"
Yace "zanyi bincike sosai ingano ko wacece insha Allah, sedai kawai umma akiyaye abinda doctor yace"
Tace "insha Allah"


Koda Raliya takoma gida jollof din couscous tayi wanda yaji ganda don tasan Abba dason ganda, nan da nan tagama tunda dama baida wuya, harhada duk kayan dazasu bukata tayi takirawo usman dayaje yin wanka , tabashi yadauko yayiwa driver magana suka taho asibityn.

Ganin sundawo yasa Abdul yimusu sallama domin komawa gida yasamu shima yayi wanka koya rage gajiyar daya kwaso.
[8/28, 9:09 AM] Maryam-Ashner Jos: Har magriba Sofiyya bata fito ba, ganin haka yasa mommy kwala mata kiran, bayan tafito mommy taganta da doguwar riga alamun dai bata shirya tarban kowa ba, "kekuma miye haka? Ko ahaka Abdul din zezo yasameki badan kwalliya" mommy tafada tana kare mata kallo.

Kumbura baki tayi tace "mommy fa yafasa bazezo ba"
Girgiza kai mommy tayi tace "i see, kema banda naci irin naki tayaya mutum yayi doguwar tafiya irin wannan kuma yadawo a ranar kice yazo"

Sake cuno bakin tayi tace "a, a fa mommy banice nace yazo ba shine yace zezo kuma wai sundawo sunsamu Abbansu baida lalfiya har anyi admitting dinshi a hospital"
Kafin mommy tayi magana daddy yashigo dawowarshi kenan daga masallaci yanemi guri yazauna, Sofiyya ta gaidashi sannan mommy tace "to Allah yabashi lafiya, kice ina gaidashi inkunyi waya"

Daddy ne yadubi mommy yace "waye ba lafiya?"
Mommy tace "Wai Abbansu Abdul ne ba lafiya harma anyi admitting di???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nshi a hospital"

Daddy yace "subhanallah, yaushe hakan tafaru"
Sofiyya tace "dazu ne daddy"

Numfasawa yayi sannan yace "to ai kamata yayi ace muje mudubshi in anyi isha'i ko, kawai ku shirya idan nadawo daga masallaci semuje"

"Tom daddy" sofiyya tafada tana mikewa, harcikin ranta taji dadin hakan, koba komai zataga handsome.


Seda akayi sallar magrib sannan Abdul yadawo asibityn yasamu umma na sallah, yanemi guri yazauna, kiran sofiyya ne yashigo wayar, kafin yadauka seda ya kalli side din umma dana Abba ya tabbatar bame kallonshi sannan yayi picking, sanar mishi tayi cewa zasuzo duba Abba anjima, shima yaji dadin hakan sosai atleast zega Cutien shi.

Suna gama waya Usman yashigo yadawo daga masallaci, shigowarshi tayi daidai da farkawar Abba, a hankali yake bude idonsa har yagama budewa, sannan yafara karewa dakin kallo idanunshi sun tabbatar mishi cewa a asibity yake, kwakwalwarsa kuma tafara tuno masa abubuwan dasuka faru dashi, wanda yakeda tabbacin sune sanadin zuwanshi asibityn nan, sake rufe idon yayi a hankali yana tunano wadda yagani, tabbas ko kaffara bazeyi ba idan ya rantse cewar wannan yarinyar yar zulaikha ce domin yaga kama, bama wannan ba, ko kokwanto bayayi cewar yanada alaka da yarinyar, tome hakan yake nufi? Kenan zulaikha bata zubar da cikin nan ba? "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun" yafurta a hankali, nan su Abdul suka fahimci cewar ya farka, dasauri suka matso kusa dashi suna masa sannu harda umma data sallame.

Bude idon yasakeyi akaro na biyu yana kare musu kallo, fuskar usman da Abdul sunyi kama sosai da fuskar daya gani dazun, amma yafi ganin kamar da Raliya, dube dube yafarayi inda zegano Raliyan amma beganta ba hakan yasa yace "ina Raliya".

Usman yace " tatafi gida"

Tundaga nan besake cewa komai ba, duk suma shirun sukayi sedai lokaci zuwa lokaci sukan yimasa sannu.


Bayan anyi isha'i Raliya tagama kimtsa yaranta duk sunyi barchi, tabarwa me aiki gadinsu sannan tadau keyn mota tanufi asibityn, a lokacin dataje tasamu andaga Abba yayi alwala har yana sallah, taji dadi sosai tanemi guri tazauna, zamanta ba wuya su Abdul da Usman suka dawo daga masallaci, se a lokacin je Abdul kecewa "umma su Sofiyya zasu zo duba Abba fa wai anjima" yana gama fada yaji kunya ta mamayeshi, wai shine yau yake maganar mace? Don haka yajuya yafice.

Usman da Raliya kam dariya suka hau yi kasa kasa, umma tayi murmushi tace "bakaji kunya ba tukun" Albba ya sallame duk sallolin dabeyi amma yakasa tashi daga kan sallayar se addu'o'i yakeyi akan zulaikha dakuma yarinyar daya gani.

Ba'afi minti biyar da fitan Abdul ba yadawo yana cewa "gasunan ma harsun zo fa"


Raliya tace "bari inje inshigo dasu tom" fita tayi ta hangosu adan nesa da dakin, zuwa tayi da murmushi a fuskarta ta rungumo Sofiyya tana cewa "gani ga matar yayana" Mommy da Daddy duk sukayi murmushi, Sofiyya kam kunya taji sosai itama murmushin takeyi tace "aunty raly inayini"

Bata amsa ba tasaketa sannan taruko hannuta kana tamaida kallonta kansu mommy tace "ina wunin ku" amsawa sukayi sannan tayi musu jagora zuwa dakin.


Bayan sun shiga gaisuwar mutunci sukayi sosai da umma, da usman shiko Abdul kai akasa ya gaidasu sewani nokewa yakeyi daddy yayi murmushi yace "kamar bakaine kaxo ka kalli kwayar idona kace kanason Sofiyya ba, yanzu kuma kana wani nokewa" duk dariya akayi Sofiyya kam janyo mayafinta tayi har yana rufe mata fuska, tacikin mayafin take karewa Abdul kallo tana murmushi, shima Abdul ta kasan ido yake kare mata kallo yanajin wani sabon yanayi tare dashi.

Tunda suka shigo gaban Abba yafadi, yanaji ajikinsa lokaci yayi da komai ze bayyana, yashafa addu'arshi tuntuni amma yakasa tasowa ko ya waigo, zuciyar sa se bugawa takeyi yana fargabar haduwa da Sofiyya da mahaifiyarta besan dalili ba.

Jin shiru yasa umma matsqwa kusa dashi tace "kadan takaita addu'ar dare nayi"

Daurewa yayi ya juyo yana gyara zama, gaisawa sukayi da daddy yalmishi yajiki, hakama Sofiyya kai a sunkuye ta gaidashi ya amsa gabanshi na faduwa, mommy data kare wayar datakeyi tajuyo domin gaisheshi harta bude baki zata gaidashi sekuma tamike tsaye cikin razana da ware idanu tanuna shi da yatsa tace "MA'AZU"

Kowa kallonta yakeyi da mamaki, Abba kam kwalla ce tafara zubo mishi, dakyar shima yamike tsaye yace "MARDIYYA"

A fusace tajuyo gun Sofiyya tace "kinsan wanene wannan dakika dau son duniya kika daurawa dansa" sannan tajuya ta kalli daddy tace "kasan wanene wannan dakake shirin hada mana zuri'a dashi?" Sannan tajuya kan Abdul tace "daga yau babu kai babu 'yata, kacireta a ranka don ko hauka nake bazan ta6a yarda inhada zuri'a da MA'AZU ba" tana kaiwa nan tafigi hannun sofiyya sukayi waje.


Mamaki sosai yakama duk sauran 'yan dakin, banda Abba daya durkushe a gurin yana kuka kamar bashi ba, daddy ma abin yadaure mishi kai, don haka yayi musu sallama tare da basu hakuri yafice..............
'

07046767662 domin karantawa complete
[9/1, 9:39 AM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 42

Kowa kallon Abba yakyi a dakin, suna jiran jin karin bayani daga wajensa amma yaki cewa komai se hawaye kawai yakeyi.

hanklin Abdul yafi na kowa tashi yashiga rudani yama rasa abin cewa, umma kam lamarin mamaki yabata matuka, tasan rabon da Abba ya amsa suna MA'Azu anjima tun kafin rasuwar me gidansu wato tun suna kano dazama tasan duk yadda akayi mommy tasan Abba ne lokaci me tsayi daya wuce to amma meya faru tsakanin su?

usman kam shima kukan yafara Raliya na kokarin danne kukan nata tana lallashin sa.

Abdul da tunaninsa ya hargitse yamike yaje gaban Abba ya durkusa yace "Abba inkanayiwa Allah da manzon sa kafitar damu cikin duhun damuka afkq yanzu, kasanar damu me wannan matar take nufi da kalamanta"



Raliya ta daura dacewa "tunda muka taso bamu ta6ajin wanda yafadi kalmaar 6atanci a kanka ba, kullum mutane yabonka suke amma yau gashi a gabanka a gaban mu anfadi kalmomin dasuka sanya shakku cikin zukatanmu, Abba ka fahimtar damu please"


Usman cikin kuka yace "Abba kodai ku yan biyu ne tazata wancan ne kai ko?"


haryanzu dai yananan a durkushe a gurin, kuma babu alamun zeyi magana a yanzu, ganin hakan yasa umma cewa "Abdul jeka kiramin doctor yazo ya sallamemu mukoma gida, maganar batanan bace"


batare da yace komai ba yamike yafita, Raliya tadubi umma tace "kenan umma kinsan meyake faruwa?"

umma tace "babu abinda nasani, nima sonake nasani amma koma menene ba'anan yadace a fada ba ai"

koda daddy yafito ya iske harsun shiga mota, mommy ta durkushe cikin motar se kuka takeyi, hankalin Sofiyya yatashi sosai, se hakuri take bata itama tana share nata hawayen, ganin hakan yasa daddy bece uffan ba yatada motar sukayi gida.
bayan zuwansu gida mommy a falo tazube

19 / 26