CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 26

9K to 12K   out of 76.5K words

zaunawa tayi, tadafe chicks dinta, shima zaman yayi yana fadin "Ina sauraronki" tace "I'm in trouble inhar brother dinka bezoba" sannan takwashe duk yadda sukayi jiya tafada masa, wata irin dariya usman yakece dashi harda hawaye, kallonshi tatsaya yi kafin tace "ok kamaidani sokuwa ko?" Ya tsagaita dariyarsa sannan yace "I wonder wlh, Ashe abinda ke faruwa kenan" tace "menene yake faruwa?" Yace "kinsan Yaya bayason kawoni ko daukoni a makaranta, wlh nayita mamakin yadda kwana biyunnan yadage dazuwa daukata Ashe ga dalili" wata dariyar yayi "jiya bayan anty Raliya tashigo gida, Ina tayata hada Kaya, bayan minti biyu se inga tayi dariya ko murmushi, na tambayeta Amma taki fadamin dalili, can Kuma sega Yaya rai a 6ace yashigo, ko amsa gaisuwata beyiba yawuce daki, senaga anty Raliya yasake sakin dariya, Ashe abinda yafaru kenan" Sofiyya tace "niduk bawannan ne yadameni ba, please kikirashi a wayanka" yace "haaaa'an to Wai case din naku bekare bane?" Dago kan dazatayi kawai taganshi yafito daga cikin mota, dalilin ganin wani friend dinsa da yayi, oh God tunda suka fito taga wannan motan, but batasan shine a cikiba da tuntuni daje ta amsa jakanta, mikewa tayi dasauri tace "friend Gashi canma Ashe yazo, but wannan ba motan jiya bane" Usman yace "may be ai yadaukp miki" tace "Allah yasa, muje to" suka karasa Usman yabude front door yazauna, itakuma tatsaya tana jiran dawowarsa, bewani dadeba segashi yadawo, be kulataba yabude motan yashiga, sedai be rufe kofanba, kamar dai yadda Usman yayi, ran Sofiyya yasake 6aci, look at him, kamar beta6a ganinta ba, zagawa tayi ta gefenshi tace "morning" batareda tajira amsarshi ba tace "am jiya na manta jakana cikin motanka, I hope kadaukomin?" Dago Kai yayi caraf suka hada Ido, tamke fuska tasakeyi, tareda dauke Kai, shiko kallonta yake babu kiftawa, bayan wasu seconni yace "a Ina Kika ajiye?" Tace "ba ajiyewa nayiba mantawa nayi" yace "shiga kiduba to" tace "bafa a wannan motan bane" Usman dai kanshi da kafarshi na waje ta wancan side din but kunnuwansa duka a cikin motan yake, Yana nazarin conversation din nasu, shiko gogan kafada yadaga yace "then jakanki Yana gida" kamar zatayi kuka tace "yanzu fisabilillah kadaukomin ne kakasa iyawa, innalillahi Ni yanzu mezance ma mommy?" Dariya taso bashi, da alama tanada tsoro, wayarsa yafara dannawa Dan kuma besan mezece ba, haushi yagama cikata, tarasa yazatayi, juyawan dazatayi ta hango motan gidansu, dasauri tashiga motansu Usman tace "let's go there indau jakana, inyaso se incewa mommy nawuce shagonne da nagama exam dawuri" wani murmushi yayi yagyara zama, Usman ma gyaran zaman yayi yajawo kofa yarufe, tayar da motan yayi sukadau hanya, tunda suka Fara tafiya Babu Wanda yayi magana, ita magananniyar ranta a 6ace yake, shikuma Usman tsoron magana yake, shiko gogan dama ba maganar yakeba seta Kama.
kamar jiya, yauma a kusa da gate din gidan yayi parking ya kalli Usman yace "sauka kashiga gida, and be quite as usual" wani munafikin murmushi Usman yayi yace "tom" sannan yajuya yace "friend byee" ko kallonshi batayiba har yawuce, Abdul yajuyo yace "kidawo gaba I'm not a driver" fita tayi tatsaya gabanshi tace "why? Nace kakaini wani wurinne? Jakana kawai zaka bani, in wuce," batareda ya kalleta ba yace "you back will be given to you inhar kindawo nan kinzauna" yacigaba da dannan wayanshi as if bashine yayi maganar ba, Babu irin 6aci daranta beyiba a wannan lokacin, wannan wani irin wulakanci ne, batada wani choice saboda mommy zata iya cin ubanta inhar tasan ba'a shagon saloon tabar jakanba, and she don't want to loose mommy's trust danhaka tabude inda Usman yafita tashiga, tayar da motan yayi, ya juya, batadai cemai komai ba Dan tayi alkawarin bazata sake cewa komaiba harse yabata jakanta, seda suka fita a unguwar sannan yanemi gefen titi yayi parking, yajuyo yana kallonta yace "me nayi Miki jiya?" Cuno Baki tayi tace "Ni nace kamin wani abune?" Yace "bakice ba, but meyasa kikatafi ko sallama babu?" Tace "bakomai" kura Mata idanu yayi yana karemata kallo, itakuma ta sunkuyar dakai tana Wasa da purse dinta, "she's more than cute" maganar zuciyarsa tafito batareda yasaniba, dago Kai tayi tace "me kace?" Kautar dakai yayi yace "allow me to drop you home" dasauri tace "no no thank you" jingina da kujeran motan yayi yace "ok then your back will remain here with me" yafada yana zakulo jakan ya nuna mata, kokarin fizgewa tayi, yamayar dayan hannun yana murmushi, tace "Dan Allah kabani, wlh mommy zatamin fada Inka maidani gida" yace "ai a waje zanyi parking bazata ganmu ba" hakadai yayita lalla6ata harta yarda tafada masa address dinta, and that's exactly what he need, suna hanya yace "why silent" Dan murmushi tayi tace "u don't like talking" yace "but I like your's" tace "really" yace "yes" tace "but why?" Yace "because you talk majestically, slowly, it won't give me headache" haka suke Dan ta6a hira harsuka kusa gidan, tace "saukeni a nan" parking yayi a gefe, yaciro jakanta ya mikamata sannan yace "can I call you cutie? Since you don't want to tell me your name?" Yar dariya tayi tace "you're cutie, not me, my name is Sofiyya" fita tayi a motan tace thank you" sannan tawuce, yananan zaune a motan har yaga shiganta gidan tukunna ya tada motan yawuce office.

Munnir dashine yaje daukota yau a school yagama jiranta har aka watse, ya tabbatar batanan, yakoma gida yaga Bata dawoba, kinbari yayi mommy taganshi, yafito gate yazauna akan bench Yana jiran yaga ta Ina zata 6ullo, kamar ance yadago, yaga mota tayi parking a gefe, kasa dauke idonshi yayi, harseda yaga fitowarta, gabanshi yafadi, dasauri yakoma cikin gidan yala6e, tana bude kofan gidan tashiga ya cakumota, yayi hanyar bq da ita yadda megadi ko masu aiki bazasu gansuba, fincike kanta tayi tana fadin "what nonesense is this, ya munnir are you alright?" Kallonta yake da jajayen idonshi yace "wani Dan iskan ne ya ajiyeki yanzu? U know naje school daukoki bakyanan, so there you are? Yawon iskanci kikafara zuwa baby? Wato kin balaga ko? Kega candidate huh" a fusace take kallonshi da wani irin expression, daurewa tayi tace "yes na balaga tunda Zan iya zaman aure kuma in haihu insha Allah, then meyarage, kaga Yaya munnir kafita hanyata" ra6awa tayi ta gefensa zata wuce, yariko hannunta yadawo da ita Yana Mata wani mugun kallo, yayi murmushi yace "ok that's what I have been waiting for, tunda Zaki iya zaman aure harki haihu fine, kishiryawa zaman aure dani, hope u can satisfy me" yawu ta tofar hadeda fizge hannunta tace "Allah yakiyaye inyi zaman aure dakai, aikai kamin kadan, Ni matar manyace, masu jini ajiki, marasa basir" tana gama fadin haka tawuceshi da sauri zuciyarta na bugawa da sauri sauri, Dan ta tsorata da yanayinsa, anashi bangaren kuwa mamakine yahanashi kwakwkwaran motsi, tagaya Masa maganar da Dole yadau mataki wlh kozata mutu seya aureta yanuna mata shiba yarobane, sannan shi basir bata cinyeshi ba,.

Allah ya taimaketa tashiga parlor bakowa, ta haura sama dasauri, sukaci karo da ikee tace "ya sofy kingadai mommy taje anguwa badani ba" wata ajiyar zuciya tasauke ta rungumota tace "sorry ikeena nizanje dake kinji" dahaka suka wuce daki.

Zuly dake kwance daki tana barchi wayanta yafara ringing, tajawo tadauka, daga dayan bangaren munnir yace "u bitch, Babu abinda Kika iya sebin maza, u no what, kibar aikin, nahakura, and yes karkisake tunanin ganina balle kiyi tunanin zan kashe dare dake, stupid" kit yakashe wayar, hawaye ne kawai ke saukowa idonta, me kuma tayi, wannan kaddara, dame tayi kama? .

Yinin ranar mutum hudu sunyishi sokoko, bangaren Abdul farinciki ne yayi Masa yawa harya kasa aikata komai a office se murmushi, Bangaren Sofiyya abubuwa biyune suka tsaya mata arai, idan tatuno maganganun munnir dakuma amsar data bashi gabanta faduwa yake, saboda batasan mezeje yazoba, sannan idan tatuna Wanda yajawo mata hakan, a maimakon taji haushi, setaji sanyi harda murmushi. Bangaren munnir kuwa zuciyarsa tafarfasa take harya kasa hakuri seda yakira zuly ya zazzageta sannan yadan huce, yakumayi kudirin samun daddy da zancen, sannan bangaren zuly tayi data sanin tarayyarta da munnir, Kuma tayi alkawarin rabuwa dashi Koda hakan ze jawo mata ciwon zuciyane.

Shin me kuke tunani?
Kuyi sharhi please domin karamin karfin gwiwa
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Join my watsaap group mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Wannan shafin na sadaukar dashi gareku, Aisha Sadees, Hajarat Ibrahim, and Mom Nabeehat (Sa'adat) nagode da nuna kaunar littafina da kukeyi, Allah yabar zumunci.

Episode 9
Yau kam duk dalibin daka kalla acikin Golden High School zakaga farinciki tattare dashi dalilin kammala jarrabawar WAEC dasukayi, candidate sunyi jike-jike, wasu harda yage uniform dinsu alamun sungama sakawa, a bangaren Usman kuwa shima Yana daya daga cikin student din dasuka yage uniform, Sofiyya kuwa dukda rokonsu data dingayi kan karsu jikata da ruwan sanyi hakan yagagara, domin kamarma zugasu takeyi seda suka mata sharkaf da ruwan sanyi har diga takeyi tsabar jikewa, aikuwa da mugun sauri harda hadawa da gudu tafito tana fatan taradda driver kasancewar tasan matsalarta da sanyi, amma Koda tafito driver dinsu bezoba, dakalin dasuke Zama taje tazauna tana rawar sanyi, hakoranta suna haduwa, ta dunkule guri daya,.
Tunda tafito yake binta da kallo harta gama dube dubenta taje tazauna, and she's alone, to Ina Usman din yau?, da ganinta kasan she's not okay, bude motan yayi yafito yanufi inda take, batasan ma yazo kusa da ita ba saboda ta kulle idonta gam, addu'ar ta shine Allah yakawo me daukarta yanzu, sunkuyowa yayi gab da ita, kamshin turaren dataji yasata bude idonta, karaf suka hada Ido, a hankali yace "cutie" kallonshi tacigaba dayi batareda ta amsa ba, yasake cewa "what happened to you? Duk kin jike da ruwa, garin Yaya?" Bata iya bashi amsa ba, duk kokarinta na ganin tayi mishi magana Amma takasa, seta bude baki sekuma ta rufe, a haka Usman yazo gurin dasauri yake cewa "Yaya what happened to her?" Be iya amsashi ba duk hankalinsa yatashi, yakuma rasa abinyi, neman rikota yake, Amma yakasa ta6ata, Usman ne yakoma cikin school din da gudu, segashi da friend dinta sunfito sunzo wajen, da taimakomta Sofiyya ta iya mikewa suka sakata a mota, bayan yarufe motan yataho daidai ze bude gaban motan, idon munnir yasauka a kanshi, zuwanshi kenan domin daukarta, but it seems yauma tashiga motan wancan Dan iskan, saurin bude motanshi yayi yafito Amma kafin yazo har Abdul yaja motanshi yayi gaba, hakan yasa shima dasauri yakoma yatada motan nashi yabi bayansa, saying "duk inda suke zuwa yau asirinsu yatonu, an indai ya tabbatar da abinda yake zargi wlh agurin seya kakkarya koma wanene Dan iskan dayake daukanta" ahaka suketa tafiya, duk bayan yan mintuna se Abdul yajuyo yana mata sannu har yadoshi hanyar gidansu, Usman yace "Yaya dama kasan gidansu ne?" Ko kallonshi beyiba balle ya amsa mishi,
Daidai inda yayi parking the other day daya kawota yauma anan yayi parking, yajuyo yana kallonta duk tabashi tausai yace "cutie can you walk?" Daga mishi Kai tayi alamun eh, domin taji dan dama dama, fitowa yayi yabude mata kofan, daidai lokacin da motan munnir takaraso wurin, parking yayi yafito dasauri yazago wajen Sofiyya a lokacin da itakuma tafito, tadafa motan, be kula kowaba ya nufeta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, ganin halin datake ciki yasa yamika hannu da nufin tallafa Mata, daga Masa hannu tayi tace "don't you dare touch me" Usman da Abdul kam kallon ikon Allah suke, shiko munnir bejiba yasake mika hannu ze tabata, ji yayi anbuge hannunshi, sannan yaji ance "cutie go" kafin yarufe baki munnir ya damko hannunta yana kallonshi yace "idan ka Isa kasake ganganci rabani da ita" itadai Sofiyya kokarin kwace hannunta take, Usman ko ido yazuba musu, wani naushi Abdul yakaiwa hannun munnir Wanda ya rike hannun Sofiyya, harseda hannun yasage, danko ita Sofiyya seda taji a hannunta, dunkule hannushi yayi zesake kaimai naushi Sofiyya tayi saurin cewa "yayanane please don't punch him" sauke hannunsa yayi, sekuma yadanji Babu Dadi, kawai seya juya yashige mota, ganin haka yasa Usman ma yayi saurin shiga motan, ya tayar suka bar wurin.
Batareda Sofiyya tace mishi komai ba, tayi hanyar gida, a hankali take tafiya dan duk jikinta Babu kwari, Kuma haryanzu rawar sanyin take, munnir Kam motanshi yashiga ya tayar a fusace yabar unguwar.

Haka Sofiyya tawuni da zazza6i gashi mommy batanan, ana bikin yar kawarta,two days dinnan Bata wani Zama, seda yamma bayan la'asar tadanji dama dama.

Wuraren 5pm munnir yashiga gidan hajiya, tana zaune a parlor tana sauraron labarai a tv, ko sallamarsa bata amsa ba, yanemi guri kusada ita ya zauna Yana gaidata Amma kota kanshi batabiba, ita labarai kawai take sauraro, ganin haka yasa yadau remote yakashe tvn "innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun, yau Naga tanbadadden da, wannan tvn muhammadu ne yasaimin shifa ba salisu ba, nikam kaga kawai ka tattaro kayanka kazo kakoma gidan ubanka wlh bazan iya jaraba ba" fadin hajiya data Mike tsaye, shiko munnir murmushi yayi yace "nazo Miki da albishir amma nafasa fada" komawa tayi ta zauna tana fadin "aike bawuya kasaya mutum farinciki, shiyasa ma nakejin dadin zama taredakai, Dan albarka jikan muhammadu, bani labarin inji" dariya yayi yace "sonake kishigemin gaba hajjaju na, jikarki nakeso abani" kallonshi tayi baki a hangame sannan tace "wacce daga ciki?" Kai tsaye yace "Sofiyya" aikuwa Babu shiri hajjaju tasauko kasa tayi zaman dirshan sannan tace "astagfirullah, yoni inba haukacewa nayiba aibazanga hakaba, yanzu ma yana kare, balle Kuma ka auri wannan yarinya me ido a tsakar ka, ai Aisha bata yiwa wannan yaran tarbiyya ba, meyasa kaga bana shiga shirginta, to garama kaje kanemo yar mutunci" kallonta kawai munnir yake sannan yace "tonidai ita nakeso Kuma koki yarda kokar ki yarda Sena aureta" Yana Gama fadin haka yamike yayi dakinsa, itako Baki tarike tana fadin "nidai ba bakiciki nake makaba, yo bakincikin mezan maka, tundadai kyauma ai Ni tagado bawaniba, kawai dai Allah yakyauta"

Abdul sam yakasa samun sukuni yakuma kasa nutsuwa, rashin sanin halinda Sofiyya ke ciki abin yadameshi sosai, har yakasa zaman office yadawo gida yakwanta.

Munnir nashiga daki yakira abokinshi Salim Yana fadin "guy shawararka fa batayiba, Dan tsohuwar nan Taki fahimta ta Sam" daga dayan bangaren Salim yace "to ba ending of this month zakaje kaduna ba, kawai kabari inkaje kasanar da abbanka, I know he will be happy Kuma kamar kasamu sofy" Dan jimmm yayi sannan yace "this weekend ma zanje, I can't wait any longer" dahaka sukayi sallama.

A wurin dinner Abba yakalli Abdul yace "Abdullah inason magana dakai after dinner," umma ma tayi saurin cewa "nimako sonake inyi magana daku biyun," Abba yace "ok Bari mugama to".
After dinner Usman yawuce dakinsa, umma da Abba suna zaune kan kujera yayinda Abdul kezaune a kasa ya sunkuyar dakai, Abba yayi gyaran murya sannan yace "meyake damunka kwana biyu bakasan zama a office?" Dimm yaji tambayar dan harga Allah beyi tsammanin wannance maganar daza'a masaba, sosakai yafarayi, shikam mezece ne? "Kayi shiru Kuma nima tambayar da nakeso inmaka kenan" inji umma,,, a hankii yadago yace "bakomai" murmushi Abba yayi yace "Kinga danki Yana kokarin boye Mana" umma tayi murmushi batadai ce komai ba, tuni Abdul ya tsargu Amma seya dake shima bece komai ba "Abba yace tashi kaje to" yatashi ya musu sallama yatafi.
Umma na kallon Abba tace "meka gano taredashi?" Yayi murmushi yace "may be watace tafara wasa da zuciyarsa" Umma tazaro Ido tace "Aiko danayi farinciki wlh" Abba yace "Allah ya tabbatar da alkhairi" umma ta amsa da Amieen.

Gidan daddy ma yau munnir bezoba, dan dagaske harya fara Jin nauyin daddy a matsayin surkinsa, balle Kuma mommy,. Sofiyya dai jiki yayi kyau sosai, dama ita haka take indai taji sanyi koyaya bawuya zazza6i yarufeta amma dazaran ta Sanya kayan sanyi tadanji dumi shikenan zata dawo normal.
Kamar yadda daddy yayi Mata alkawari haka yacika Mata, domin be manta cewa yau suka rubuta last paper dinsu ba, Dan haka yataho Mata da wayanta babba kirar Samsung, sannan yace Mata laptop Kuma se result yafito inyaga tayi kokari.
Yaufa ansamu freedom, Baki harkunne, su Sofiyya anzama yan Mata, Nan da Nan tadau wayar mommy tafara kwasan numbers din wadanda takeso, tayi takaici dabata amshi number din ko mutum daya cikin friends dinta ba, da yanzu ansakata watsapp group ai inta bude. Daki taje tahau bude app din Facebook da watsapp dama burinta kenan.
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Join my watsaap group mata zallah please =?O?=?O?

Episode 10
Weekend, munnir yasauka kd lafiya, sedai beyi sa'a ba, Dan babanshi baya gari, Yana Abuja, takaicin hakan yasa ko kwana betsaya yiba yajuyo.

Sofiyya kam kullum tana daki, watsapp da Facebook sun 6oyeta, wata cousin sister dinta tasanyata a groups dayawa harda na Matan aure, lokaci zuwa lokaci dai takan tuno da Abdul, setayi murmushi kawai, ko a Ina zata sake ganinshi oho. Tana cikin wannan tunanin taga Kiran mommy, ajiye wayan tayi tasauko domin amsa Kiran,,, mommy dake zaune tana rubutu ga laptop a gabanta tadago tace "zauna" Zama tayi, bayan mommy ta kammala ta rufe laptop din, takalleta tace "this week nakeso kuje suleja keda ikram" wani tsalle ta doka kamar karamar yarinya sannan ta rungume mommy tana fadin "mommy like no other, I love you,,, wlh nayi missing Inna sosai, gasu siddika dasu ayman, dukdama muna chat dasu, oh my god, mommy is like I'm....." Katseta mommy tayi tace "narasa wakika gado a zance wlh, sakeni karki samin jiki yayi tsami da Allah, kedai bakya girma, ko ikram batayi abinda kikeyi ba" cuno Baki tayi takoma gefe, mommy tace "kishirya keda ikram kuje kusiyo tsaraba, gobe sekuje saloon, may be jibi ko gata kuwuce" dasauri ta mike tayi sama tana wakenta na murna.

Abdul kam abin duniya yadameshi, yayi iya kokarinsa na ganin ya kaucewa tunaninta Amma kamar kara zuga zuciyarsa yake,

4 / 26