Chapter 14 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 26

39K to 42K   out of 76.5K words

tamike tayi dakinta, zuciyar ta nayi mata kuna, "meyake shirin faruwa dani haka," tafada cikin kuka "ya ilahi kakawo min dauki"


Bayan yan mintuna ne mommy tamike ta nufi dakin daddy.


Daddy da fitowar shi daga wanka kenan yana shafa mai, mommy tanemi bakin gado tazauna tana jiran ya karasa.


Bayan yagama ne shima yazo kusa da ita yazauna,

"Yau kuma ladan ne ba'a so insamu, akayi wankan ko sani banyi ba" mommy tafada tana gyarawa daddy kwalar rigar shi.



"Kodaya na hutar dake ne kawai yau" inji daddy


Mommy tace "okay"

Numfashi taja sanna ta daura da "wai menene yafaru Abu ikram? Meyasa ka kwace wayar first born?"


Cire hannunta yayi kan kafadarsa yace "nothing kawai dai naga hakanne yadace shiyasa"


Sarai mommy tasan halin daddy da taurin kai da kafiya, wanda gadonshi Sofiyya tayi na wannan halin.

Sure akwai abinda yafaru but tasan baze sanar da ita so easily ba, don haka tabar maganar ta dauko wani zancen daban.


................ 9pm Abdul yagama duk abubuwan daya sabayi kafin yayi barchi, bayan ya kwanta ne ya janyo wayarsa domin gabatar da aikin sa na karshe kafin barchi wato waya da *Cutie*.



Unfortunately for him kiran farko yaji switched off, ya mutsa fuska yayi yana "yau kuma network ni zaka ta6a"


Cigaba da kiran numbern yayi time without numbers but amsar dai bata canza ba.


Tun yana tunanin network ne har yafara tunanin babu lafiya, amma duk dahaka be fasa kira ba, cikin minti 20 yakira wayar yafi sau ashirin.



........... Sofiyya nagani 9pm tayi wato lokacin yin waya da Abdul ji tayi zuciyar ra nayi mata wani irin kuna, kai tsaye tanufi gadonta ta kwanta tafashe da kuka me ban tausayi.



Yadda Abdul yakusa raba dare yana kiran wayarta baya samu, itama haka takusa raba dare tana kuka.



Da safe.
Sofiyya bata fito ba harseda ta tabbatar daddy yafita, tunda tafito mommy ke binta da kallo ganin yadda fuskarta tayi ja, idanun ta sun kumbura, alamun dai tasha kuka daren jiya, watakila ma har da asubahin yau.



Bayan sun gaisa tawuce dinning tayi breakfast, bayan tagama ne taxo gaban mommy ta durkusa, tun kafin tafara magana hawaye yafara sauka kan fuskarta.



"Mommy dan girman Allah kibawa daddy hakuri yabani wayata don Allah "


Tabbas tabawa mommy tausayi amma koma me akayi mata ai ita tajawo dan haka mommy tace "wannan shine sakamakon duk yaron da yaci amanar iyayenshi ai, dakika rokeni nabaki damar zuwa wanke kai me nace miki? "




Kukanta ne yake karuwa ta sunkuyar dakai kasa tace "nayi kuskure mommy na bazan sake ba wlh nayi miki alkawari"



Tausayi matuka tabata don haka tace "kicire rai dasamun wayar ki nan kusa, don ran daddyn ki ya6aci sosai daganin ki tare da Abdul, sedai zan iya baki aron wayata kikira shi Abdul din and that two only for today saboda yasan halin da kuke ciki kar yaje yayita damuwa, sekuma kijira lokacin da daddy ze huce"




Mikewa tayi tana share hawayen ta tace "to mommy nagode".


......... Abdul ko breakfast besamu yi dakyau ba, har fitowarshi tafiya office befasa kiran wayar Sofiyya ba.


Umma ce kadai tadan fahimci sauyin sa, hakan ma don dai itace mahaifiyarshi, amma usman da Abba duk babu wanda yagane wani abun, kodon rashin fara'arsa kadai ya isa yahana su ganewa.




Har ya isa office bedena gwada kiran numbern ba, daga karshe kuma ya yanke hukunci kawai idan yatashi a office zebiyo ta gidan su yaduba ko lafiya.



Around 10am Sofiyya ke kiran wayar Abdul harta tsinke badaga ba don besan numbern ba, sake kira tayi, wannan karon yadauka duk da seda takusa yankewa.




"Yaaya nice"



Wata ajiyar zuciya ya sauke sannan yadan kwantar da kansa jikin kujerar dayake zaune yace

"Babyna laifin menayi haka don Allah, hukuncin yayi tsauri fa dayawa"


Itama ajiyar zuciya tayi tace "yaaya fitar da mukayi jiya yasa daddy ya kwace wayata"


"What to waye yaganmu? "


Tace "i dont know bansamu cikakken bayanin ba yanzu ms mommy ce tabani aron wayarta and that two only for now"



"Yasalam" yafurta yana dafa hannunshi kan goshinsa.

Shiru yayi don besan me zece mata ba, bemasan abinda yakamata yayi ba a daidai wannan lokacin.


Jin yayi shiru ne yasata cewa "karka damu yaaya Saura 3days Abban ku yadawo wurin daddy then everything will be fine"


Murmushi ya kakalo don yadda yasaba da hira da ita duk dare baya tunanin zejuri rashin magana da ita har na tsawon 3days.


Daurewa yayi yace "exactly, Allah yakaimu, but adan lalla6a mana mommy don Allah mudinga waya koda da rana ne mana"



Haka dai suka danyi hirarsu ta masoya sannan sukayi sallama akan Sofiyya zata nema musu alfarma gun mommy...........
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*

By

*Maryam-Ashner*



inkinsan bazaki dingayin sharhi/comment me ma'ana ba kada kice insaki a group=?L? ba sticker da godiya nakeso ba' addu'a da sharhi/comments masu ma'ana nakeso'
Meson shiga tamin magana a 07046767662


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana ds kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Muna saida kowani network if needed=?L?
Call/WhatsApp 07046767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 31


Sabit daya gama jin duk abinda munnir yagama fada masa ya sheke dawata shegiyar dariya irin ra basawa "hhhhhh wlh kai dakikine sam bakada kwakwalwa, Abba kam yayi asarar school fees hhhhhh"



Bakaramin 6ata mishi rai kalaman sabit yayi ba, shiyasa wlh bayason zuwa neman abu gurin shi, indai kanema zaka samu amma fa se anci maka mutunci tukun,.

Mikewa yayi yace "nine dakiki? Dan nazo gurin ka neman shawara shine nazama dakiki? Ba laifinka bane laifi nane danazo"

Yana kaiwa nan yayi wucewar sa, da gudu sabit yabishi yana bashi hakuri "haba friend kai bakasan wasa bane, ni wlh dani kasamu da tuntuni anyi aurenku ma ai, shiyasa nafada maka haka"

Beki ba yadawo suka shigo domin dama mafita yake nema

Bayan sun sake zama sabit yace "ai bama kai yakamata inkira dakiki ba, salim da zuly sune dakikan dasuke baka dakikiyar shawara"


Shidai munnir bece komai ba don duk ba wannan ne a gabanshi ba, muskutawa yayi yace "to yanzu meye solution? "



Sabit yace "karka damu har na hango andaura aurenku wlh, don nasamo hanyar daza'ayi hakan cikin sauki"


Washe baki munnir yayi dajin abinda sabit yace, wani murmushi-murmushi dariya-dariya yakeyi yana fadin "Alhamdulillah Alhamdulillah shiyasa bana jinka wlh, duk wulakancin ka indai mutum zeyi hakuri to zeyi nasara"


Duk dariya sukayi sannan sabit yafara daurashi kan shirin dayake ganin zasuci nasara.


............... Abdul ne yayi parking a daidai mall din, ya kalli) *Cutie* yace "muje ko baby"


Wata kunya taji, itafa gani take tunda suka fara soyayya Abdul yadena jin kunya, zuwan Abban su gidan su kuwa yasa shi kara zama marar kunya don kanshi rawa yakeyi taga alama.


Ba musu tafito suka shiga ciki, wannan karon kam duk yadda yaso tadau wani abu apart from chocolata ki tayi, seshine ya dau wasu abubuwan yan kadan shima, don tace mishi bataso mommy tasan sun hadu.




................ Wata shewa munnir yayi jin irin shawarar da sabit yakawo, tabbas wannan shine best solution, tafawa sukayi munnir yace "kai abokina wlh danine da wannan brain din dana tsula tsiya a duniya son raina"



Sabit yace "kaji dan iska, to angaya ma kowa irinka ne"


Mikewa munnir yayi yana "nasamu abinda yakawo ni, nizan wuce sekuma munyi waya, ko kuma ince senazo kawo maka invitation card"


Dariya sabit yayi shima yana mikewa domin yimasa rakiya, yace "inka gadama ma karka gayyaceni"


Munnir yace "nina isa, ai har kawo maka amarya zanyi ku gaisa"


Dariya sukayi duka suna fita daga office din.

Abdul da Sofiyya na tsaye wurin biyan kudi, su munnir suka biyo kwanar gurin, harsun wuce munnir yatsaya cak, sakamakon jin sautin murya kamar na Sofiyya da yayi.


Dawowa da baya yayi sabit na tambayarshi ko lafiya but Bema jishi ba, seda ya tabbatar cewa tabbas Sofiyya ce kuma tare da Abdul, wani huci zuciyarsa keyi masa, waige-waige yafara kamar me neman wani abun, ganin haka yasa sabit janshi sukayi waje, jikn motarsa sukaje sannan yatsayar dashi yace

"Kai kuma meye haka? "


Cikin huci yace "baka gansu ba? Shegen yaronnan ne fa da Sofiyya"


Murmushi sabit yayi yace "rashin basira ta kare a kwakwalwar ka wlh, shiga mota kajirani "


Duk dacewa beji dadin kalmar abokin nashiba, amma haka yawuce yabi umarnin sa, domin a yanzu bashi da wani za6i.



A tsaye jikin motar munnir sabit ya tsaya yadaga waya yana dannawa, tunda su Sofiyya suka fito yake daukarsu a photo, harda video har suka shige mota sannan yasauke wayar yana wani irin murmushin dashi kadai yasan ma'anar sa.




Hankali kwance yake driving suna hira cikin soyayya dajin dadi, ji suke kamar karsu rabu, a haka har yakawo ta unguwar su, can nesa da gidansu yayi parking ya kura mata idanu batare da yace komai ba.



Dagowa tayi suka hada idanu Dasauri ta sauke idanun ta kasa tana murmushi tace "yaaya bari intafi ko"


6ata fuska yayi yace "nidai banason yaayan nan wlh, please baby a canza min suna" yakarasa kamar zeyi kuka.


Dariya tayi tace "to ni yanzu mezan ce maka inba yaaya ba? "


Yace "nabaki assignment, kuma yau zakiyi submiting, jeki kar mommy tagano mu ko"


"To" tace tana bude motar, da gangan tabar mishi duk abinda ya siya mata a motar.


Shima fitowa yayi yana "wlh bangaji da ganin ki ba baby"


Kallonshi tayi taga yayi mata kalar tausayi, dariya yaso yabata amma tadan dake tace "to yaaya kayi hakuri nima hakurin nafika"



haka dai yadan taka mata suna yar hira sukayi sallama, seda ya tabbatar tashiga gida sannan yajuyo yanufo motarshi.


Tuki yake yana tuna tun farkon haduwarsu, zuwa fara sonta dakuma yadda yakejinta a ransa yanzu, "abin mamaki" ya furta a fili yana murmushi.





............... Shiga motar yayi yana karewa munnir kallo daya wani hade rai kamar wanda uwarsa ta mutu.


"Kalli nan" sabit yafada yana nunawa Munnir pictures din dayayi musu.


Kar6ar wayar yayi yana kallo yana huci, daga wayar yayi zeyi cilli da ita, sabit yayi hanzarin fizgewa yana "kaf danginku babu me iya siyamin wayar nan, wlh daka fasamin waya dakai da wannan akwalar motar taka zanrike harse anbiyani"




Takaici ne yakara kama munnir dan haka yace "dayake mu dangin matsiya tane ai, banda kai dan iskane miye na daukar su a photo kuma har kake nunamin? "



Harararshi sabit yayi yace "idan yanzu nace maka dakiki sekaji haushi bayan kai dakikin ne"


Munnir bece komai ba, kome sabit yafada masa shine yajawo, se jure koma menene har yasamu bukatarsa ta biya.


Numfasawa sabit yayi sannan yace "wannan photon zan tura maka ta whatsapp kai kuma ka tabbatar ka nunawa tsohon ta, kuma kada kabari yasan kaganta, kaje kafara janshi da hira, nikuma zan kiraka, idan kadauka kasaka a handsfree zance maka kahau whatsaap natura maka da abu, dazaran kahau sekayi salati ka nuna masa pictures din nasu, daganan zakaji sauran bayani"


Yana gama fadin haka yafice a motar yana "se munyi waya"


Wani shu@umin murmushi munnir yayi yana fadin "tabbas na cancanci kakirani dakiki domin a gabanka sam ni bame kwakwalwa bane sabit"


Kai tsaye ya tada motar yayi office domin aiwatar da aikinsa.




.................... Sofiyya nashiga gida tanufi dakin mommy tace ta dawo sannan tawuce dakinta.


Abdul ma kai tsaye office yanufa yakama aiki gadan-gadan domin yajishi da natural energy.


Kai tsaye munnir office din daddy yanufa yaci sa'a kuwa yasame shi shikadai don haka yaja kujera yazauna yana gaidashi.


Bayan sungama gaisuwar ne yafara kokarin bawa daddy labari, daman tun a kofar office din yakira sabit yasanar dashi cewa yanzu ze shiga.


Yana tsaka da bawa daddy labari kuwa kiran sabit yashigo, daukar wayar yayi abinda suka shirya hakan suka aiwatar dashi.



Yana hawa whatsaap kuwa mikewa yayi yana zaro idanuwa yace "daddy jo yaronnan yasake daukar Sofiyya sunfita, wlh yau koni koshi". Ya furta a hasale.



Mike hannu daddy yayi yana "menene wannan ingani"


Mika masa wayar yayi, ran daddy yakai kololuwa gurin 6axi, har yaushe Sofiyya tayi kwarin dazata dinga yin abubuwa son ranta?


"Zauna munnir ka saurareni tukun"


Babu musu munnir yazauna
Daddy yace "Sofiyya yar uwar kace, kusan ince a gabanka tataso, kasan abubuwa dayawa a kanta, meyasa bazakayi anfani da wannan ka lalla6ata ku sasanta junan ku ba? Bazan iya yimata auren dole ba, domin koda anyi auren kai kanka bazaka ta6a jin dadin auren ba"



Munnir yace "daddy wannan yaron shine me hure mata kunne, duk abinda zan mata wlh bazata saurareni ba matukar tana tare dashi, sedai in za'ayimin alfarma a kwace wayarta sannan a habata fita, nikuma cikin sati daya ko biyu zanyi kokarin janyo ra'ayinta daddy"



Shiru daddy yayi yana nazari, sannan yadago ya kalli munnir yace "nayarda zanyi maka wannan alfarmar, don dama ina tuntunin kwace wayar ne, to amma munnir karka bani kunya don Allah, don ni nafi kowa son inhadaku aure wlh"



Wani farinciki munnir yaji a ransa, murmushi yakasa barin fuskarsa, godiya yayi tayiwa daddy tare da alkawarin baze bashi kunya ba,.



Bayan yabar office din kai tsaye yakira sabit yasanar dashi abinda yafaru, sosai sabit yaji dadi sannan yakuma daura shi kan mataki nagaba domin samun nasara a zuciyar Sofiyya.................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*

By

*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana ds kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Call/WhatsApp 07046767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 33

Tun bayan azahar munnir yatashi a office, kai tsaye yanufi mall din sabit, yajido kaya na alfarma wanda duk sabit ne ya harhada masa domin yasamu damar siyan zuciyar Sofiyya.


Godiya yayi masa ba adadi, domin shine silar komai, gashi duk uban kayan daya tula mishi ko sisin shi bekar6a ba.


Bayan yatattaro komai kaii tsaye yanufi gidan daddy domin fara gabatar da soyayyar sa a gurin ta.



Parlon ba kowa dama yasan a wannan lokacin kam baze samu kowa a parlon ba.

Kai tsaye yanufi dakinta.


Sofiyya da take cikin kunci da takaicin rashin wayar ta, tayi kwanciyar tayi juyin amma barchin yakasa zuwa, tarasa mezatayi taji dadi don haka tadauko qur'ani tahau karatu har akayi kiran sallahr azahar.


Tunda ta idar da sallah bata tashi a gurin ba, har barchi yadan fara daukarta taji kamar ana knocking kofar ta.


Tashi tayi tazauna tana mitstsike idanu, jin ansake knocking dinne yasa tamike taje tabude.


Turus tayi ganin wanda ke tsaye a kofar, nan tafara jin sabon daci a zuciyar ta, sam batason kallon fuskar munnir wlh.



Kallonshi tayi sama zuwa kasa ta kautar da fuskarta tana "lafiya da tsakar ranar nan kazomin sekace wani aljani"



Murmushin dayakeyi befasa ba, don ko kadan kalaman ta basu bashi haushi ba.



"Haba 'yar uwata, koba komai ai kyacemin inshigo tukun, kiji meya kawoni tukunna"


Kallonshi tayi tana yamutsa fuska tace "kashigo Ina? Badai dakina ba, fadi duk abinda yakawo ka anan inzaka iya"



Shiru yayi sannan yace "bakomai dama wannan na kawo miki" yafada yana mika mata ledar hannunshi.



Ko sake kallonshi batayi balle kuma takalli ledar hannunshi tajuya ta banko kofar dakin harda murda key tana jan wani dogon tsaki.




Rasa abinyi munnir yayi yatsaya a gurin yakai monti 5 a tsaye a gurin, can dai ya yanke hukunci kawai ya ajiye mata ledar a kofar dakin sannan ya juya ya fita.



............ Koda

14 / 26