Chapter 22 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 26

63K to 66K   out of 76.5K words

sannan tafara goge hawayenta.


Aunty zee kuwa sakaroro tayi dajin bayyanar wannan sabon labarin, juyawa tayi 6angaren da umma take, suna hada ido umma ta makamata wata uwar harara sannan tamike tayi shigewarta daki, ranta duk a 6ace yake musamman yanzu da zuly ta bayyana a matsayin 'yar mijinta.

Abba kam hankalinshi nakan zuly yafara yimata tambayoyi akan mahaifiyarta dakuma rayuwar dasukayi, nan tafara bashi labarin irin wahalar da mama tayi da ita kafin tasamu aikinyi, dakuma irin gorin da kawayenta sukeyimata na rashin uba karshe ma yazama bata kawa ko daya.

Ganin Abba zuly sun shagalaw, wurin hirarsu yasa aunty zee tatashi tabi nayan umma, Raliya ma mikewa tayi tanufi dakin don't hirar tasu bai shafeta ba, shiko usman dama tuni yaciro wayarsa yana dannawa, Abdul ne kadai ya maids hankali kan hirar tasu harma In anyi abin dariya zhikuma yayi murmushi.

Aunty zee data zauna bakin gadon umma tadubi umma tace "kinga rabo ko anty? Wannan shi ake kira rabo wlh" takaicine ya hana umma yin magana, itako aunty zee tadage se magana takeyi, can dai abin ya ishi umma don haka tace "waini rabon uban me aka samune? Kinbi kin dameni dawani rabo, rabon banzanki da wofi, inbanda shegen jaye jayenki meze hadamu da wannan annobar, wlh tun farkon ganinta bata minba, ashe annoba ce"

Sake Baku aunty zee tayi tana kallon umma data hakikance tana masifa, can dai tace "Allah yabaki hakuri aunty amma Wlh abin fa ...." Bata bari takai karshen maganarta ba tace "bayan cutata dakikayi kuma mezaki fadamin, don Allah malama kije kidau annobar dakika kawo mana kutafi, abin ya isa hakanan kuma mungode"


A sanyaye aunty zee tamike tafice, duo setaji babu dadi data zama sanadin haduwar zuly da Abba, koda ta koma parlon ta tarar dasu suna tsaka da hirarsu a hankali takarasa kusa dash tace "to Alhaji muzamu wuce yaya za'ayi kenan?"

Mikewa Abba yayi rike da hannun zuly yace "ai kamata yayi mutafi tare, domin inyi magana da mahaifiyarta ko? Bari dai ina zuwa" yasake hannun zuly yayi hanyar dakin umma, koda yaje ya bukaci tazo suje gidansu zuly tare fafur taki yarda, babu irin rokon Dabe mata ba amma sam tace ita bazata jeba hakanan ya hakura ya kyaleta, Raliya ma cewa tayi kanta nayimata ciwo bazata iya zuwa ba don haka Abba, Abdul da usman ne suka bisu.

Abdul ne ke driven yayinda aunty zee ke gefensa a baya kuma usman da zuly na gefe da gefe yayinda Abba kezaune a tsakiyarsu, se hurarsu suke kamar sun saba don usman ma yasake dama sedai inbeji surutu ba.

Suna tsaka da tafiya Abba yace "kai son aiko yakamata mubiya tagidansu Sofiyya mu shaida musu bayyanar dota ko?"

Nan da nan Abdul ya tamke fuska, anta6o inda yake masa kaikayi, shiharga Allah soyake ya manta da Sofiyya duk kuwa dacewar hakan yagagara amma yasan yariga yarasa Sofiyya har abada. Batare da yayi magana ba yajuyar da akalar motar zuwa layinsu Sofiyya.

Aunty zee da kanta yakuma daurewa da lamarin tace "meya hada gidansu Sofiyya da wannan maganar kuma?" Zuly ma kunne takasa domin jin hadinsu dasu Sofiyya.

Nan Abba yabasu labarin komai, aunty zee se girgiza kai take tana mamakin wannan lamarin a fili tace "ikon Allah" zuly kam tausayin kanta ne ya mamayeta, jin duk wata wahala da kokarin raba tsakanin Abdul da Sofiyya na banzane tundama gashi a karshe babu aure tsakaninta da Abdul din, sannan Sofiyya 'yar uwarta CE, har kwalla seda tashare .


Koda sukaje gidan bamusu megadi yabude musu don yashaida Alhj Gallafi kuma besan abinda yafaru tsakaninsu da yan gidan ba recently, bayan sunyi parking ne Abba yace "Zainab kezaki taimaka kushiga ciki tare da dota kuyi musu bayani inze yiwu duk semu tafi a tare"

Fitowa aunty zee tayi, zuly ma tafito suka nufi cikin parlon gidan.

Mommy tana kitchen taje ajiye cup, tajiyo motsi hade da sallama, fitowa tayi tana amsawa takaraso cikin parlon, nuna musu kujera tayi tana cewa "bismillah kuzauna sannunku dazuwa" tafada tana kokarin zama kuma tana karewa zuly kallo, itama zulyn idanunta na kan mommy har kasan zuciyarta taji cewa wannan itace mahaifiyar sofiyya kuma yayar mahaifiyarta.

Mommy kam cikin ranta tanajin kamar tasan zuly amma a fili setace "sannunku, ko ruwa ban bakuba, bari akawo muku ruwa" takarasa tana kokarin mikewa, aunty zee tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "laa kibarshi wlh wucewa zamuyi ma, sako nazo infada miki dama"

Komawa mommy tayi tazauna tana kallon aunty zee sannan tace "eyya to inajinki"

Aunty zee tace "sunana zainab kuma ni kanwar mahaifiyar Abdul CE, Dan gidan Alhaji......" Mikewa mommy tayi bata bari aunty zee takai karshe ba tace "nagane bama sekin karasa ba and you're not welcome over here so..." Tafada tana nuna musu hanyar kofa tace "can we have a space here?"

Murmushi aunty zee tayi sannan tace "dakin Dan dakata aunty" ta nuna zuly tace "kinganeta kuwa?" Batare da ta jira amsarta ba tacigaba "sunanta zulaikha 'yar wajen kanwarki zulaikha"

Zaro ido mommy tayi tana nuna zuly bakinta se rawa yakeyi amma takasayin magana, ganin haka yasa aunty zee mikewa ta zaunar da ita sannan tafara bata labarin abinda yafaru da safiyar yau agidansu Abdul.

Kuka sosai mommy tayi hakama zuly kukan takeyi.

Awaje kuwa Abdul yamatsu suyi sufito sutafi, don zuciyarsa a kuntace take ganinshi a harabar gidansu cutie amma baida halin ganinta idanma yaganta baida damar kiranta tashi, duk Abba na lura dashi a ransa kuwa addu'a yake Allah yasa bayyanar su zuly tacanzawa mommy ra'ayi kan batun aurensu Abdul din.

Sofiyya da yunwa tafito da ita tunda kafin takarasa gangarowa take jiyo sheshshekar kuka, hakan yasa takara saurin takunta ta karasa gangarowa, a hankali take kallon zuly da aunty zee tabbas taganesu duka don zuly kam haduwarsu ta uku kenan agurin saloon dagun graduation dakuma yau, aunty zee kuma haduwarsu ta biyu kenan, ganin mommy da zuly na kuka yasa kanta daurewa, can dai tace "what is happening here, can someone explain please?"

Mommy CE tagoge hawayenta cikin muryar kuka tace "she is your cousin sister yar zulaikha ce"

Zaro ido Sofiyya tayi tace "what! Oh my god so what are we waiting for? Oh sis come on let us huge you " tafada tana matsawa kusada zuly ta rungumota sannan tace "mommy join us now" dasauri mommy tamike taje gefen zuly itama ta rungomosu duk sekuma sabon kuka.


Dakyau aunty zee ta rabasu tace ana jiransu insun shirya sutafi tare kokuma sufara gaba su sazo data baya, harara momy tayiwa aunty zee tace "inkinga dota tabar nan to hannunta na cikin nawa ne" tafada tana Jan zuly zuwa dakinta sannan tace "sofy kikira daddynki kisanar dashi, sannan kidauko mayafinki muwuce shiyazo daga baya"

Momy na wucewa sofiyya takaraso tazauna kusa da aunty zee tace "aunty tare da shi kukazo don Allah?"

Murmushi aunty zee tayi tace "yana waje, kije dai kiyi abinda akace"

Sesannan taji kunya tamike tahaura da gudu..............
'

07046767662 Maryam-Ashner ce
[9/8, 8:35 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 46

Kiran daddy tayi a waya tamishi summary, cewa yayi suje shima gashinan zuwa.

Mommy kam baki yaki rufuwa after that long ashe darabon zasu sake haduwa da yar uwarta, hijabi tadauko har zuwa sannan tana rike da hannun zuly amma takasa cemata komai, sedai ta kalleta tayi murmushi, ahaka tasanyo hijabin suka fito, daidai lokacin da sofiyya ke gangarowa sanye da doguwar riga baka da adon stones maroon, ta yane kanta da karamin veil shima maroon sanna tasako takalmi sauciki baki, se wayarta dake rike a hannunta duk dacewa bawata kwalliya tayi ba amma sosai tayi kyau, gangarowa tayi tace "ready to go" batare da kowa yayi magana ba aunty zee tayi gaba sukuma suna biye da ita har zuwa wannan lokacin kuma mommy narike da hannun zuly takasa sakinta.

Tunda suka sako kai Abdul ya kurawa kofar kallo, bayan duk sunfito sannan Sofiyya tafito a karshe "Subhanallah" yafurta don shi harga Allah kullum idan suka hadu gani yake kamar ana canzata kullum kyawunta sake fitomishi yakeyi, bedauke idonshi a kanta ba itakuwa se rarraba idanuwa takeyi tana neman inda zata hangoshi, a yayin da mommy ke kiran drivern su itakuma aunty zee dake lura da motsin Sofiyya Jan hannunta tayi tabude gaban motar tajefata ciki tana fadin "gashinan fa" takare tana dariya.

Kunya sofiyya taji amma ganin handsome dinta yasata yin murmushi can kuma ta gimtse tana cuno baki tana harararsa, kallonta yake da murmushi a fuskarsa yace "me bawan Allah yayi ake harararsa?"

Kallonsa tayi cikin shagwa6a tace "bakai bane, wlh ka gyara hali" gabadaya ya shagala da kallonta cikin salon shagwa6arta me burgeshi yace "kinga karki kashemin jiki da wannan shagwa6ar taki inkasa tuki"

Usman dai sake baki yayi yana ganin ikon Allah, kamar ba Sofiyya parrot dayasani few month back ba, shikuwa Abba beta6a sanin cewa Abdul ya iya hira ba seyau, he was thinking tayaya ma akayi sofiyya takesonshi da rashin maganarsa ashe sune yakewa miskilancin ba itaba "ah lallai kuwa" Abba yafada a ranshi batare da yasaniba ashe maganar tashi tafito.

Wiki wiki Sofiyya tayi da idanu, kana da sauri tabude motar tafita, shiko Abdul harga Allah ganin cutie yasa yamanta cewar bashi kadai bane a mortar, don haka yawani sha mur kamar bashine yagama zance ba.

Usman ne yadubi Abba yace "Abba ka kwafsa wlh, video fa nakeshirin yimusu, Abdul yajuyo yawani makamishi harara yace " kaga sa'anka acikinmu he?"

Abba dai besake magana ba, shikuma usman a ransa yace wlh sofy sa'ata CE danma bawani zancen ince mata aunty kuma.

Fitowar sofiyya yayi daidai da karasowar su mommy daga kiran driver, wani kallo mommy tamata dayake nuna cewar zasu hadu, sannan tace "sekiwuce muje ai ko" gaba tayi zuwa gun motar dataga driver ya tayar, mommy dai har sannan narike da hannun zuly, duk a baya suka zauna.

Abba yanata jiran dawowar sofiyya aunty zee tashigo tacewa Abdul "son muje ko"

Kallonta Abba yayi yace "ina dotan?"

Murmushi aunty zee tayi tace "mamanta tariketa zasuje tare" Abba besake cewa komai ba Abdul yatada mota sukayi gaba mortar su mommy na binsu a baya.


Suna tafiya sofiyya se surutu takewa zuly, kamar damacan sun saba, itadai zuly se uhm da a, a take fada.

Ahaka har Abdul yayi parking daidai kofar gidansu zuly domin anan aunty zee tace yayi parking, drivern su mommy ma parking din yayi duk kowa yafito sun tsaya a kofar gidan .

Kowa yakasa motsawa mommy ta kalli zuly tace "nanne gidan?" Gyada kai kawai zuly tayi a hankali mommy tayi gaba zuw cikin gida rike da hannun zuly Sofiyya nabin bayanta, sannan aunty zee ma tabimusu baya, sukuma mazan suna jiran ayi musu izini, driver kumq yajuya zuwa dauko daddy.

Sunanan tsaye mijin aunty zee yafito daga gida, daman yana gari bekoma kano ba, hangosu yayi don haka yataho garesu. Dama sunjima basu haduba don haka da farinciki suka rungume juna nan Abba yake bashi labarin abinda yafaru, sosai mijin aunty zee yayi mamakin jin wannan batun, sannan yaji aranshi cewa yarasa maman zuly kenan don yaga alamun Abba nason kasancewa da tsohuwar budurwarsa, sunanan tsaye kuma daddy yakaraso.

Da sallama momy tashiga gidan sauran ma suka mara mata baya, maman zuly da fitowarta kenan a bayangida hannunta rike da buta batasan lokacin da butar ta su6uce a hannunta tafadi a kasa ba, kallon mommy take tana zare ido hawaye na zubowa jikinta na rawa bakinta na motsi amma takasa magana.

Mommy ma kwalla takeyi takarasa gabanta ta rungumeta tana fadin "nice sis nice 'yar uwata" fashewa da kuka duk su biyun sukayi suna kara kamkame juna, zuly ma durkushewa tayi a gurin tana yin nata kukan, Sofiyya kam jawo hannun aunty zee tayi zuwa wani Dan dakalin dake tsakar gidan tazaunar da ita sannan itama tazauna tana fadin "your leg will ich you if you keep standing wadancan yaufa se anyimusu uzuri"

Aunty zee tayi murmushi tace "I see"

Sunkusa minti 2 a haka Sofiyya tana danna waya tace "easy mana mommies karfa hawayenku yakare kurasa na shading ranar dazaku aurar damu" tamake kamar ba itace tayi maganar ba.

Da dariya da kuka maman zuly tasake mommy tana nufo inda su Sofiyya suke tace "so here is my elder dota" tafada tana durkusawa ta tallafo fuskar sofiyya, mikewa sofiyya tayi suka rungume juna.

Bayan dai sungama rungume rungumensu da koke kokensu ne tayimusu iso zuwa parlonta da babu komai se tabarmai.

Zama duk sukayi ta debomusu ruwa duk sukasha sannan suka fara zance, sunma mance dawasu na jiransu a waje, se aunty zee CE tatuno sannan tayimusu magana aka tura Sofiyya tayi musu iso....................
'

Kuyi hakuri anyimana rasuwa ne ba lokaci.

07046767662 Maryam-Ashner ce
[9/9, 8:58 AM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 47

Daddy ne yafara shigowa se mijin aunty zee, da mamaki mama ke binshi da kallo tana tunanin kome yakawoshi gidanta shikuma, bata gama mamakin ba Abba ya danno kai, mikewa tayi a razane tana nunashi da yatsa tanaja da baya lokaci guda kuma hawaye yana wanke mata fuska kokari take tayi magana tace yafita kar ya shigo amma maganar takasa fitowa jikinta yana rawa ta sulale a gurin tana gunjin kukan takaici, nadama dakuma danasani na haduwa da Abba, usman da Abdul ne suka shigo a karshe, tabarma daya aka shimfida musu can gefe duk suka zazzauna.

Aunty zee koda taga mijinta batawani yi mamaki ba tunda tasan yana gari kuma shidin abokin Abba ne sosai.

Nan fa mommy tahau lallashin mama har tasamu dawowa cikin nutsuwarta, daddy ne yafara yin magana bayan yayi addu'a sannan yace "shi ubangiji yakanyi ikonsa batare da ya shawarci kowa ba, yau kuma munga ikon sa, zulaikha kisauraremu don kowa anan

22 / 26