CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 26

12K to 15K   out of 76.5K words

sau uku kenan Yana barin office yataho kofar gidansu waiko zega tafito Amma shiru,, abokinshi Bashir ne yashigo office din, haryazo kusa dashi besaniba, seda yadan bugi table din sannan yadago adan firgice Yana sauke ajiyar zuciya,, Zama Bashir yayi Yana fadin "I never see you thinking deeply like this," Dan taaki yayi yace "is nothing serious, daga Ina kake haka?" Bashir yace " yau natashi da wurine nace Zan danyi ziyara," Abdul ya 6ata fuska yace "Wai ziyara, a hakan? During office" harararsa Bashir yayi yace "aigara ni, nakanzo office din kaifa?" Murmushi yayi yace "I'm busy ne shiyasa" hakadai sukadan ta6a hira daga karshe Abdul yarufe office suka wuce gidan wani abokinsu. Bayan sun fitone Bashir yaroki Abdul Kan yarakasa ShopRite, ze saiwa little sister dinsa Abu, dakyar yayarda yabishi suka tafi.

[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?

Episode 11
A ShopRite, fuskar ikram kya6e kamar zatayi kuka, Sofiyya ta harareta tace "kin ajiye kosena mareki?" Hawayen daya taru a idonta ne ya zubo, ta ajiye agogon data dauka Wai zata saiwa daddy, kamo hannunta Sofiyya tayi tajata suka wuce tana fadin "yarinya se uban iyayi, waike me daddy". A wurin biyan kudi bayan Bashir yagama anmiko mishi ledanshi, dago kan dazeyi, yayi tozali da fuskar Sofiyya, "wow" yafurta a fili, ganin takaraso gurin yasa yayi saurin fita yatsaya a waje Yana jiran fitowarta,.
Abdul dayayita Kiran wayar Bashir Amma baya dauka, saboda gaba daya hankalinshi yana kan kofan fitowa daga gurin, haushine yacika Abdul se tsaki yake Yana fadin "ko uban me yatsaidashi oho, may be ma wata yagana, mtssss na mamajo" gajiya yayi da jiransa yafito daga motan yanufi ShopRite din, kanshi nakan wayarsa dayake sake kiranshi.
Sofiyya tare da ikram sunfito suna tafiya, ikram tayi tsalle tace "laaa ga wannan uncle din daya saimun chocolate rannan" a hanzarce Sofiyya tadago Kai tana fadin "Ina yake" karaf idonta yasauka a kanshi "wow he looked more handsome today" tafurta a zuciyarta,.
Bashir daganin fitowar Sofiyya yayi saurin bin bayanta Yana Kiran "beautiful jimana" batako jiba, dan hankalinta nakan handsome,.
Sunzo gab da juna, ganin yana kokarin wuceta Dan hankalinshi nakan wayar hannunshi, saurin dakatar dashi tayi ta hanyar fadin "Mr Gallafi" kamar a mafarki yaji muryan dayake muradin ji fiye da komai, ba 6ata lokaci yadago kanshi yasauke manyan idanuwansa akanta, murmushi ne kwance a fuskarta, hakan yakara fito da kyawunta, "she's more than cute koba makeup" yafada a zuciyarsa, shima murmushin yayi Baki harkunne zeyi magana yaji ikram na fadin " uncle nizan rakaka" kafin yabata amsa Bashir yakaraso wurin Yana fadin "haba beautiful, koba komai ai kya tsaya ki saurareni" Abdul daransa yafara 6aci ganin Bashir dakuma jin abinda yake cewa yadago Kai ya kalli Sofiyya yagw itama shi take kallo, Bashir Kuma yakalli inda yaga tana kallo, da mamaki a fuskarsa yace "aboki dama kasan beautiful?" Ko kallonshi beyiba yajuya zekoma mota, da sauri Sofiyya tace "Wait please, kabani number din Usman Mana" ikram tayi tsulum tace "rh daddy jiya yasiyo Mata new phone" harararta Sofiyya tayi tace "magananniya" shidai Bashir shiru yayi, yasan Abdul ze iya kwafsa Masa, gara jnsun ke6e ya lalla6ashi yabashi address dinta kawai, dahaka yajuya yana fadin "since u don't want to talk, then byee" yawuce yashiga mota, Abdul yajuyo da kallonsa gareta Yana ciro wayanshi a aljihu, sekuma yaga ashe wayar office ce ajikinsa Babu number din Usman aciki, yace "ba number din Usman anan," ta mika hannu tana cewa "to kawo insa maka number na se idan kaje gida kabashi" ba musu yamika mata wayar, bayan tagama sakawa Tamika mishi tace "please kace yakirani I missed him wlh" wani daci yaji acikin zuciyarsa, wato she missed him, bama shi tayi missing ba "hmmmm" kawai yace yajuyo ko sallama beyimusu ba yawuce abinshi, aranshi Yana fadin "bazan Kuna bada numbern ba". Sofiyya tayi jimmm tana mamakinsa, yanzu yanzu yake murmushin daya kara Masa kyau, yanzu yanzu Kuma ya hade rai kamar wani saniya, a fili tace "masifaffe, Kuma miskili, anji jiki" taja hannun ikram sukayi hanyar motansu.....

A hanya Bashir na driving yake cewa "aboki kaga ikon Allah ko? Fitata tamin Rana wlh, tunda Gashi nayi gamo" ko kallonshi beyiba, yasake cewa "waikai meke damunka ne? Nalura duk sanda kaga mace ranka 6aci yake, anya kanada cikakkiyar lafiya? Mata abinso Amma Kai baka ta6a gane hakanba" nanma banza yayi dashi, yakuma ceww "to nidai Allah yabaka lafiya" ganin ba kulashi zeyiba yasashi yin shiru, harsun shigo unguwar su Abdul besake magana ba, sunkusa zuwa gate din gidansu yasake cewa "inkanawa Allah kabani address din yarinyar can" batareda ya kalleshi ba yace "drop me here" burki yatada yadanje gefe yayi parking yajuyo yace "naji I will drop you but seka bani address din beautiful" ko kallon inda yake beyiba yaciro wayarsa yafara danne dannensa, ganin dagaske baze kulashiba yasa yafara rokonsa, duk dahaka kin kulashi yayi, dayaga cewa tabbas baze saurareshi ba dole yabude mishi kofa yafito ko kallonshi beyiba yayi hanyar gida, Yana takunsa daidai, kwafa Bashir yayi yace "zamu hadu Koda tsiya senasan gidansu beautiful" dahaka yaja motanshi yayi gaba......

8:30 mommy takalli Sofiyya dake danna waya, takuma kalli ikram dake kallon tv tayi gyaran murya duk suka juyo suna kallonta tace "duk kutashi kuje ku kwanta, gobe zakuje wanke Kai sannan kuje Kuma hajiya sallama" murna ikram tahau yi dankuwa tasu tazo daya da hajjaju musamman dayake sunan hajiyan gareta, Sofiyya kuwa cuno Baki tayi, dankuwa sam basa shiri da ita, haka duk sukatashi sukayiwa mommy sallama suka haura dakinsu. Bayan sungama duk abinda suka sabayi kafin kwanciya barchi, kowa taje tahau bed dinta ta kwanta, , Sofiyya taduba agogon wayarta taga 9:00pm tamayar da wayar kasan filow tayi addu'a takwanta, Nan da nan barchi yafara daukarta,.
Abdul na kwance se juye juye yake akan gado, yagagara yin barchi, damashi ba gwanin barchi dawuri bane, sedai aiki, toyau aikinma ya gagareshi, Banda tsaki Babu abinda yake, gabadaya ranshi Babu Dadi, wayarshi yadauka yayi dialing numbern Sofiyya, dayariga ya haddaceta danhaka beyi saving dinta ba, dasauri yakatse, yayi haka yafi sau a kirga, inya tuno da kalamanta se ranshi yakara baci, "I missed him" gakuna Bashir da kwlmarsa inyatuno yakejin daci Wai "beautiful" hmmm kawai yace yakara dialing numbern,..
Sofiyya da barchi yafara daukarta taji vibration din wayanta, da barchi fal idonta tazaro wayar taduba, ganin new number yasa tamayar ta ajiye, she can't pick new call at this time gaskiya, gyara kwanciyar ta tayi, sekuma tazaro wayar da sauri tunowa da tayi Usman ze iya kiranta, indai anbashi number dinta, Kiran numbern tashiga yi, yafara ringing tasa a kunne...
Abdul dayaga har wayar ya katse bata daukaba jiyayi ranshi yakara baci, yarasa dalilin dayasa zuciyarsa take azalzalarsa akan kiranta, gashi taki dauka, akan me ma zataki daukan wayarsa, bayan itace tayimasa laifi, jefar da wayar yayi can gefe, yaja barko yana faman tsaki, can yahango hasken wayar, alamun ana kiranshi domin a silent wayar take, kamar baze kula wayar ba, sekuma ya janyo yaduba, ganin Sofiyya ke kiranshi bejira komai ba yadauki wayar yasa a kunne.
Sofiyya tace "Assalamu alaikum" Abdul yace "wa'alakis salam" jimmm tadanyi jin ba muryan Usman bane, but sure tagane me muryan Amma setace "please wake magana" a hankali yace "yanzu har muryata bazaki iya ganewa ba?" Dan murmushi tayi tace "yes bangane ba" yace "guess" shiru tayi nadan wani lokaci kafin tace "ammm banganoba gaskiya just tell me" a dake yace "Wanda kika bawa number dazu if you can remember" dariya ce taso zuwa Mata, Dan tabbas tagano ranshi yafara 6aci, Dan dakewa itama tayi tace "I can't recall because ba mutum daya naba number ba" a tsawace yace "what?" Harseda tacire wayar a kunne, Bata amsa mishiba yasake cewa "uhmm wa da wa kikaba number?" Tace "sunada yawa gaskiya, duk Wanda yace Yana son number na ai kamar masoyinane" tsaki yayi yakatse Kiran, Yana furzar da iska me zafi, "what kind of nonesense is this mtsssss" yafada a fili, sannan yamike yashiga toilet danyin alwala, Dan yasan yau barchi sedai 6arawo.
Sofiyya anata bangaren dariya tayi tace "i like it inga fushinka mr handsome" da nishadinta takwanta, barchi me Dadi yayi awun gaba da ita.
Washegari suka shirya sukaje saloon, dagacan Kuma suka wuce gidan hajiya domin yimata sallama kamar yadda mommy tace suyi.....................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 12
A gidan hajiya, sallama su Sofiyya keyi amma ko kallonsu batayiba tanata sauraron radio dinta tana salati Jin abinda ake fadi cikin radio din.
Ikram ce tawuce taje kan tabarmar da hajiya ke zaune, tazauna itama tana dalewa kan hajiya "innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun, wannan wacce masuface, godai godai dake ki hayane? Wannan sangarta dame tayi kama?" Inji hajiya, Dariya ikram tahauyi, Dan dama sunsaba hakan da ita, Sofiyya ma karasawa tayi tazauna agefe tana gaida hajiyan, "yo ainazata bazaki gaisheni bane, aidani se ingaidaki, kintsayamin kamar soja, waike ga 'yar fari, itakuma 'yar auta" ikram dai dariyar tacigaba dayi, itakuma Sofiyya batasake cewa komaiba, tadai ciro wayarta tana dannawa, "waiku wasu irin halittune Dan Allah, ke se dariya kikeyi kamar mahaukaciya, itakuma tahau Danna wannan abar, kamar ta6a66iya" duk Basu kulataba, basukuma Dena abinda sukeyiba, mikewa tayi tanufi daki tana fadin "tonidai kam nasan ciwon kaina, ahto Banga dalilin Zama da marasa hankaliba" ikram takalli Sofiyya tace "yays Sofiyya yunwa nakeji fa" batareda ta kalleta ba tace "Nan gidanane dazaki fadamin" mikewa tayi tabi bayan hajjaju, Sofiyya Kuma tamike kafafu tana cigaba da aikinta.
Bayan kusan awa guda, hajiya tafito daga daki tazo kusada Sofiyya tace "dadai kinkama hanya kinkoma gurin uwarki dayafi Miki ai, yo inbanda jawomin zagi me kikeyi anan tundazu? Kalan adamu yashigo yanzu yace banrike Masa Amana ba, Kinga taso muje kema ga abinci can na ajiyemiki, kamar nasan zakuzo nayi dambun nama dayawa wlh" takarasa tana riko hannun Sofiyya, suka wuce cikin palon.

Abdul da bakin ciki tukuru yatashi, ko breakfast din kirki beyiba yafita office, acan dinma babu katabus yatattara yanufi gidan kanwar umma, Dan yasan idan yakoma gida a wannan lokacin, zesha questions which he can't answer.
Unguwar tamasu rufin asirice wato talakawa, kallon gidajen yaketa famanyi domin yakasa tantance wannene gidan, kasancewar sabuwar unguwace sannan yajima bezoba, duk yaga gurin ya canza masa dayawa sakamakon sababbin gine gine da akayi,.
A hankali yatura kofan wani gida dayake tunanin nanne gidan, yatsaya daga farandan gidan yakwada sallama da muryanshi me taushi,.
Zuly dake kofar daki dukta rame, tunani yayi Mata yawa tajiyo sallama, kamar bazata amsaba, seta sakejin wata sallamar, zuciyarta tadan tsinke is like kamar tasan muryannan oh tasan mekama da muryan, mikewa tayi, dakwance dankwalinta tadan yafoshi yakawo mata kafada, sannan tanufi farandar, a tsaye taganshi, keys din mota a hannunshi, dayan hannun Kuma wayace yakara a kunne, yanata Kiran auntyn tashi Amma ba'a dauka, kallonshi take daga sama har kasa, yes Bata sanshiba, batama ta6a ganin mekama dashiba, but her heart is telling her he is someone she knows, a zuciyarta tace "handsome indeed" waigowa yayi ta side dinta, cire wayar yayi daga kunnensa yadanyi gyaran murya yace "am please aunty zainab nake nema" Dan murmushi tayi tace "anan gidan Kuma? Gaskiya Babu aunty zainab anan gidan" juyawa yayi yace "ok" yacigaba da Kiran aunty zainab awaya.
Tabbas yatafi dadukkan zuciyarta, tadade atsaye a gurin sannan tajuya takoma gida, tacigaba dazama inda take zaune, mama data fito daga daki, da alamu daga barchi tatashi, ganin zuly zaune inda tabarta tunda zata kwanta, tarike Baki cikeda mamaki tace "yanzu zulaikha kashe kanki kikeson yin akan wancan yaron?" Murmushi zuly tayi tace "mama bazan ta6a kashe kainaba, Dan bazan iya tafiya inbarki kekadai ba" Zama tayi kusada ita, tadan dafata tace "to tunanin me kikeyi tundazu zulaikha,? Kinsan ciwo wuri yake nema ko" zuly tace "mama kemadai kinsan dole indinga yawan tunani, koma badan munnir ba kodan halin rayuwar danake ciki, bazan ta6a samun cikar burinaba mama" mama tadanyi saurin share hawayen daya zubo Mata tace "inda rai da rabo ai" zuly tace "wani rabo Mana? Gadai ran Amma rabokam babushi, Dan Babu Wanda ze auri shegiya" tana gama fadin haka tawuce tashiga daki zuciyarta nakuna,. Mama kuwa kuka tafashe dashi tana fadin "Usman kacuceni, kacuci rayuwata, Allah ya Isa" dahaka tamike tanufi bandaki.
Abdul kuwa sa'a yasamu aunty zainab tadaga wayarsa, dan dama makobta tashiga, takuma bar wayar a gida.
Bayan yashiga gidan yazauna yasha ruwa, aunty zainab Fadi take "yaudai wace Rana? Abdullah agidana Ni zainabu" 'yar dariya yayi yace "haba aunty zainab, sekace Wanda baya zuwa" tace "kaiii dama zuwan kake? Kajimin yaro" dariya duk sukayi suka cigaba da hirarsu, sosai yakeson auntyn tashi, hargida yabata Amma taki amsa, tace mijinta Yana wadatata gwargwadon ikonsa, duk cikinsu umma itakadaice ta auri talaka me rufin asiri Kuma itakadaice Allah bebawa haihuwa ba, haka sukaita hirarsu har lokaci yaja sosai, sannan Abdul yayi Mata sallama yawuce.

A gidan hajiya kuwa Sofiyya barchinta tasha tagode Allah, harseda aka kira la'asar sannan hajiya ta tadata tayi sallah, Bata Dade da idarwaba munnir yayi sallama, tunda yaga ikram yasan tare suke da Sofiyya danhaka yayi saurin shigewa dakin hajiya, danyasan tanacan, aikuwa akan gado ya isketa tana chat se murmushi take, fizge wayar yayi Yana dubawa, murmushi yayi ganin da mace take chat din, bada na mijiba, mikewa tayi tazauna tahade rai tace "bani wayata, tunda bakaine kasiyamin ba" cigaba da dannawa yayi yace "idan irinta goma kikeso kinsan nime siya mikine, wato shine anbaki wayar koki amsa number na kikirani ko?" Shiru tamishi, Dan harga Allah Bata koson ganinshi balle magana dashi, zama yayi gefenta yace "haba mommy's girl, menene na gushin? Duk abinda yafaru ai yawuce ko?" Ko kallonshi batayiba balle tamishi magana, surutun shi yadunga yi, ganin Babu amsa yasa yadau number dinta yasaka mata nashi yamike yafice, karo sukayi da hajjaju zata shigo dakin "a'uzubikalimatillahi minash shaidanir rajiim, nidai Allah ya jarrabeni da jarrababben jika, yo inba dole aise kahado kayanka kakoma gaban uwarka" wuceta yayi yafito beko waigo ya kalleta ba, karasawa dakib tayi tana fadin "ke aini nayi kuskure, Kinga da'a ce nabar salisu ya auri waccer yarinya zaliha, Aida tahaifomin masu tarbiyya" Sofiyya dason Jin gulma tace "hajiya wacece Kuma zaliha" hajiya tace "ahff ki inazaki santa, ai lokacin ko cikinki uwarki batayiba balle a haifoki" 6ata fuska Sofiyya tayi Bata Kuma sake maganaba, hajjaju tacigaba "cikin shege zaliha tayi, sannan salisu yayarda ze aureta, bayan ta haihu, hardafa yimata alkawarin rike shegiyar yarinyar, Niko nayi tsalle nadire nace inya aureta Sena daga Masa nono, ke 'yar fari Kinga laifina ana? Tayaya Zan yarda akawomin karuwa?wacce ta ajiye shegiya?" Sofiyya dai taki magana amma kunnuwanta a bude suke, hajiya takuma cewa "nidai kirufamin asiri kada ki gayawa uwarki, dan zata iya zuwa ta dokeni, ko wancan lokacin ma dakyar ta kyaleni" dahaka ta mike tayi gaba abinta, "shirme kawai, to Ina ruwan mommy da wannan zancen?" Sofiyya tafada tana gyara kwanciyar ta.

Munnir nazaune tareda abokinsa Salim, sunata hirar yadda zasu 6ulloma lamarin Sofiyya, waya munnir tafara ringing, dubawa yayi yace "kaga popsy nakira, yadamu waise nagaya Masa menaje nemansa kd" Salim yace "tokai kagaya Masa Mana" munnir yace "noo ninafison muzauna nidashi zefi" Salim yace "kafara gayamasa a wayar, at least yasan topic of discussion din naku first" sake Kiran wayar yayi hakan yasa yadauka "hello baba" adayan bangaren alhaji salisu yace "munnir bazaka fadamin mekazoyi kd ba? Duk kadagawa maminka hankali, se tambaya ta take" munnir yace "oh Mami naface Mata bakomai Amma taki yarda" alhaji salisu yace "ko menene kafadamin ko hankalinta ze kwanta" gyaran murya munnir yayi sannan yace "dama maganar aurene, kuma Sofiyyan daddy ce nakeso" jimmmmm Alhaji salisu yayi sannan yace "ok bakomai kadai jira, cikin week dinnan zanshigo ingaida hajiya, daganan semuyi maganar" munnir ya kalli Salim dake kallonshi sannan yace "to baba, Amma lafiya kuwa? Naga kamar baka farinciki da za6ina" alhj salisu yace "a,a kodaya, aini zanfi kowa murna munnir, akwai wata maganar ce, kadai jirani senazo" dahaka sukayi sallama, kowa da tunanin dayake cikin zuciyarsa.

Dadare Abdul yakasa barchi, duk kokarinshi naganin ya mantar da kanshi tunanin Sofiyya Amma hakan yaki yiwuwa, kuma yayi alkawarin baze sake kirantaba, Dan zata iya sawa zuciyarsa tabuga in yacigaba da kiranta, hakan yasa ya kunna data dinshi yahau watsapp.
Anata bangaren itama bayan takwanta kamar jiya, tunanin hirarsu dashi ta dinga yi tana murmushi, da taga tunanin baze kaitaba tajanyo wayarta ta kunna data tahau watsapp, duba numbers dinta tayi, tahango number dinshi da tayi Saving da M.H, "woowwww" tafurta bayan gani picture dinsa datayi akan DP, a fili tace "gaskiya wannan gayen karshene wurin kyau, Masha Allah" ganinshi online yasa tatura mishi da sticker na rawa, dakuma na dariya.
Yana cigaba da chat yaga number anturo mishi message, Aida sauri yaduba, basan sanda dariya tazo mishiba, ganin abinda Sofiyya taturo mishi, reply yamata da message "wacece?"
Wata dariya Sofiyya tayi, tace "wato zerama" reply tamishi da "did I talk to you?"
Cikeda nishadi yamirgina sannan yamata reply "did I talk to you too" reply tamasa da "the man in your DP look very nice" pictures dinshi yaturamata kusan 5, aikuwa duk tayi saving dinsu sannan yamata message "kikashe data I will call you now" hakan kuwa akayi, kashe datan tayi, yakirata sukasha Hira, se wurin 11 sukayi sallama, ahakama dan tanada tafiya gobene shiyasa ,,,,,,,,,,,
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 13
Washegari kowa da nishadi dakuma farinciki yatashi tsakanin Abdul da Sofiyya, Dan Abdul nema yatasheta da asuba,

5 / 26