Chapter 21 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 26

60K to 63K   out of 76.5K words

tonikam ina anfanin rayuwata" haka yayita tafiya yana zancen zuci.



Tunda tashiga dakin take kuka tana fadin "why Abba why? You shouldn't have done that yanzu kaga abinda kajawo ko? Babu ruwan handsome fa amma kajawo mana" takarasa tana kuka, wayar ta tadauko ta lalubo numbern sa kokarin kira take sekuma ta dakata thinking of what to say idan takirashi "what should i tell him? Sorry handsome" tafada tana ajiye wayar tayi kwanciyarta tana hawaye.

Daddy ne yayi kiran dan uwansa Alhj salisu ya shaida masa duk abunda yafaru, tabbas Alhj salisu yayi mamakin jin cewa Gallafi shine ma'azu ashe, beyi gangancin sanar dasu munnir faruwan hakan ba, amma a ransa yanajin cewa ankusa ganin Zulaikha insha Allah.


A ranar Abdul a titi yakwana, Sofiyya kam batayi gigin kiranshi ba tadai raba dare tana yimusu addu'a, mommy kuwa 6atan 'yar uwarta yadawo mata sabo don haka itama damuwa fal ranta ta kwana, umma kuwa tunda tashiga daki take kuka tayi harta dena hawaye, Abba kuwa shima salloli da addu'o'i yayitayi yanayi yana kuka har gari ya waye.


Yaune Aunty zee take dawowa, murna gurin zuly ba'a magana, mama kam mamakin yadda zuly tabi tadamu kanta da dawowar aunty zee take, harsu girki akeyi mata itadai mama idanu kawai tazuba mata.

Bayan azahar Aunty zee tasauka kuma dashigarta gida zuly tabi bayanta da abincin data girka, sosai Aunty zee taji dadin tarbar da zuly tayi mata hakanan taji tana kaunarta a ranta, sosai sukasha hirarsu, sannan zuly ta tafi gida.

Bayan anyi la'asar ne mama tace bari taje tayiwa aunty zee sannu dazuwa, a rashin sani ashe mijin aunty zee yadawo gida, don haka tana shiga sukaci karo a zaure, da kallo yaketa binta, tunani yadanyi inda yasanta, tabbas yaganeta a kano yasanta kuma yaketa binta taki sauraronsa, gaisheshi tayi ya amsa, tabi ta gefenshi tawuce, sarai ta dade da sanin shidinne mijin aunty zes shiyasa bata ta6a bari tashigo gidan idan yananan, yau dinma datasan yananan dabata zoba wlh.

Hakadai takarasa shiga tayima aunty barka da dawowa sannan tayi fitowarta gudun karma yadawo yasameta a gidan.

Koda tafito a kofar gida tasameshi yana tsaye, yitayi kamar bata ganshi ba tana kokarin wucewa yace "don girman Allah da darajar manzon Allah kitsaya ki saurareni"
Girman Allah da manzon Allah ne kadai yayi nasarar tsaidata don haka tace "nima don girman Allah da darajar manzon Allah ka takaita abinda zaka fadamin kuma daga yau kadena bibiyata"

Murmushi yayi sannan yace "masha Allah, tambayarki kawai nakeson inyi, kuma inason ki fadamin gaskiya tsakaninki da Allah"

"Inajinka" tace mishi

"Don Allah inason sanin tarihinki a takaice in babu damuwa"

Wani kallon banza tayi masa sannan tace "akwai damuwa don haka leave me alone" tagama fadin haka tayi wucewarta tabarshi tsaye a gurin, bewani 6ata lokaci ba yabita harseda yaga gidan data shiga sannan yajuya.


Har magriba Abdul be waiwayi gida ba, yanacan yana garari a gari, duk ya fice hayyacinsa, rabonsa da abinci tun jiya a asibity, idan yagaji seya nemi gefen titi yazauna, idan barchi yazo mishi yayi barchin idan yatashi yadaura daga inda yatsaya, sallah ce kawai ke tsaidashi inyaji ankira yakan tsaya yayi sallar sannan yawuce, shi anashi burin ahaka ne zesamu mutuwa ta daukeshi ya huta, ya galabaita iya galabaituwa, ya wahala iya wahaluwa, ya yunwatu cikinsa babu komai se qugin yunwa dayake masa, gajiya tasashi yanke jiki yafadi agefen wani shagon provision, mutumin shagon ne yafito dasauri yana fadin "subhanallah malam lafiya"

Dakyar Abdul yabude baki yace mishi "ruwa" dasauri mutumin yadauko pure water yakawo yafasa yabashi, tunda yakafa kai becire ba seda yaga babu komai cikin ledar sannan ya yar da ledar yana sauke numfashi.

Mutumin kam se binshi da kallo yakeyi daga bisani yace "bawan Allah daga ina kake haka kuma meya sameka"

Kokarin tashi yayi, da taimakon mutumin yatashi yafara kokarin fafiya batare da yabawa me shagon amsa ba, tangadi yakeyi kamar matsayi, shidai mutumin da ido yabishi sannan yace "Allah yakawo mafita"........................
'

07046767662 Maryam-Ashner ce
[9/4, 9:49 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 44

Bakin titi yakebi yana tangal tangal, saura kiris mota tabitakanshi dasauri bashir daje tuki yataka birki yayi parking yafito zuwa ga Abdul "innalillahi" yafirta ganin Abdul cikin wannan yanayin "Abdul menene haka? Meya sameka?" Be kulashi ba, shima kuma dama besa rai dasamun amsar sa ba, da taimakon bashir Abdul yashiga mota, kai tsaye asibity yawuce dashi aka saka masa drip, zuwa yamma harya fara dawowa hayyacinsa sannan suka baro asibityn, a mota bashir yace "friend meya sameka haka?" Shiru yamishi kuma daman yasan shirun zemishi, can yasake cewa "what ever happened please try to calm yourself know how to control your anger amma wannan ai neman kashe kai ne" nan ma shirun yayi masa, seda yaga sunyi hanyar gida sannan a hankali yace "gidanku zanje"

Bashir ya kalleshi yace "gidanmu kuma? Yin me?"

Besake cemishi komai ba, to dama yaya balle kuma ga dalili, shidai Bashir a ransa cewa yake "Allah da yasa bada Sofiyya kayi fada ba" .


Bayan kwana uku.
Cikin kwanaki ukunnan zuciyoyi da dama sun azabtu matuka, umma, Abba, Mommy, Sofiyya uwa uba Abdul dahar yau bekoma gidaba.

Usman da Raliya sun zama masu bada baki wa iyayen nasu, a 6angare guda kuma suna tunanin inda Abdul yashiga, Abba dai nasane dacewa Abdul natare da bashir, umma kuma duk tunanin ta shima yana dakine bayason fitowa kamar yadda itama take zaman daki tun faruwar lamarin.

Yaune bakincikin abin yadan ragu a zuciyar umma, dacin datake ji a ranta shima ya ragu sosai, don haka dakanta tashiga kitchen as usual tahada breakfast, babu wanda yakaj Abba farincikin ganin hakan followed by Raliya and Usman.

Yau dai gidan yadan fara dawowa daidai, tunda umma tafito, batadai kula kowa ba, bayan amsa gaisuwarsu datayi, dama can ita ba ma'abociyar magana sosai bace.

Bayan anzo yin breakfast bataga Abdul yafito ba, dakanta tatashi taje duboshi, amma seta s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????amu kofarsa a rufe da key, da mamaki tadawo parlon tadau wayarta tahau kiranshi, surprisingly taji ringing din wayar akan kujera, that means Abdul baya gidan? Kallon Raliya da Usman tayi tace "ina yayanku" kafin subata amsa Abba yace "suna tare da bashir" bata sake cewa komai ba tazauna suka hauyin breakfast.

Bayan sun kammala tawuce dakine Abba yabita, lallashi da rokonta gafara ya dungayi, tsakanin mata da miji, a karshe dai yaci nasara ta hakura tayafe mishi.


Sofiyya kam yau takasa hakura da rashin jin muryar handsome don haka bayan tayi sallar azahar ne tafara kokarin kiran wayarsa, hartagama ringing ba'a dauka ba, ajiye wayar tayi don dama batasan mezata cemishi ba koda yadauka din.

Yau yakama sati kenan da faruwar lamarin, cikin satin kuwa abubuwa sun dan daidaita bakamar farko ba, mommy tagama fushinta da daddy don a tunaninta yagane ma'azu tun a haduwarsu ta farko amma yaki sanar da ita, seda ya rantse mata cewar befa ganeshi ba sannan ta yarda tadena fushin datakeyi dashi amma tanakan bakarta nacewa Sofiyya bazata auri Abdul ba gara ta auri munnir in auren yazama dole.


Abdul ma yadawo gida sakamakon umma datayi kiran bashir yabashi wayar tayita lallashinsa da kwantar da hankalinsa, dakuma nunar masa matsayin yadda da kaddara, har tasamu shawo kansa ya yarda yadawo gida, amma bayan gaisuwa ba abinda ke hadasu da Abba, bayama yarda yazauna inda yake don shi gani yakeyi yarasa Cutie har abada don haka bashida sauran farinciki kuma.


Yauma kamar kullum sun kammala yin breakfast kamar yadda suka saba, Abdul yamike zewuce Abba yace "kajirani a mota"

Dakyar ya amsa da "to" sannan yafice, banda cewa shidin mahaifinsa ne aida har karshen rayuwarsa baze kara sauraronshi ba, sedai matsayinsa na mahaifinsa baze bari ya iya wulakantashi ba, duk kuwa girman laifin dayayi masa, hakan yasa yabude motar yazauna ya zuro kafafunsa a waje yakuma tamke fuska kamar wanda be ta6ayin dariya ba.

Koda Abba yafito yaganshi sosai yakejin tausayinsa a ransa, inama se bayan da akayi aurensa da Sofiyya ne asirin nan yatonu? Karasowa yayi yaje dayan 6angaren yazauna a nutse yace "nazo neman yafiyarka ne kan abinda na aikata, wanda a yau kafi kowa kar6an hukuncin laifin nawa, nasan na cuceka, bama kai kadai ba dukanku na cuceku nabar muku tabon da baze goge ba har abada" yakarasa yana goge hawayen takaici"

Duk irin yadda yakejin hAushin abinda Abba yayi amma tabbas yana kaunarsa sosai don haka seyaji tausayinsa yajuyo yace "Abba nayafe maka, Allah yakiyaye gaba"

Da murmushi kan fuskar Abba yace "nagode Allah yayi maka albarka, nayimaka alkawari kota halin yaya zan shawo kan familyn Sofiyya suyarda subaks ita koda yakama in durkusa gabansu in nemi yafiyarsu ne"


Girgiza kai Abdul yayi yace "bazaka durkusa musu ba saboda ni Abba, kuma suma nasan bazasu hakura ba, kawai mubar wannan maganar ni na hakura da ita kawai Abba karka damu dani"


Yafada yana dakewa don can kasan zuciyarsa wani daci da radadi yakeji, Murmushi kawai Abba yayi yafice a motar yakoma cikin gidan.


Yau sati guda kenan Sofiyya bataji muryar Abdul ba balle tasaka ran ganinsa, ada idan takira wayarsa tana shiga amma ba'a dauka, yanzu kuwa kullum switched off takejinta, duk tarasa nutsuwarta, gashi babu wanda zata iya sanarwa damuwarta, don mommy sosai taja mata kunne kan sanar dakowa abinda yafaru, kuma tahanata kiran Abdul kwata kwata jinedai batayiba.
Tun tana danne damuwarta har tafara kasa dannewa damuwar tafara bayyana kan fuskarta dakuma movement dinta na cikin gida.

Mommy tana lura daduk motsinta amma bata ko kalleta ba balle ta kulata, itadai ko maza sunkare bazata ta6a barin Sofiyya ta auri dan ma'azu ba.

Yau Aunty zee take shirin zuwa gidansu Abdul don yimusu Allah yasanya alkhairy don haka tun jiya taroki mama kan cewa tanaso zulaikha tayimata rakiya, bamusu mama ta amince, zuly kam rai yayi fari tasss kamar wadda akace insunje za'a daura aurenta da Abdul ne tsabar farincikin datake ciki.

Sungama shiryawa sunfito sunhau adaidaita yasaukesu a kofar gidan, sun kwankwasa megadi ya leko domin ganin kosuwaye, ganin aunty zee ce yasa yafara gaidata yana matsawa gefe domin yabata damar shigewa, karaf idanunsa yasauka kan zuly, aida gudu yakwasa zuwa cikin gidan yana ihu yana cewa "mayyar nan tadawo zata cinyeni kutaimakeni"

Kowa na gidan seda yafito dayaje weekend ne babu aiki, Abba, Abdul da usman duk sunanan, Raliya ma tananan akan anjima mijinta zezo yadauketa sutafi.

Duk kallo sukebin megadi dashi, shiko se tsalle yakeyi yana fadin "ku taimakeni ga mayyar can wlh"


Acan waje kuwa tsoro ne yakama zuly don tabbas bata mance da abinda yafaru a wancen zuwan datayi ba, jikinta harya fara 6ari tace "Aunty kije kawai nizan koma gida karsu dukeni"

Da mamaki Aunty tace "au wai dama dake yakeyi kenan? Meya hadaku to dahar yasanki kuma yake kiranki da mayya?"


Kafin tabata amsa tajiyo muryoyinsu usman suna cewa "muje muga mayyar kodai gamo kayine"

Jin haka yasa zuly juyawa tanajin faduwar gaba me tsananin gaske.

Dukansu sun fito sukaga Aunty zee tsaye da baki asake tana kallon zuly data juya baya.

Abba dashima yaji sauyin yanayi, yadaure yace "zainab cefa, ko itance baka ganeba yau?"

Megadi yace "wlh ba itakadai bace ga mayyar nan tajuya baya"

Tsaki Raliya tayi tana kokarin juyawa taji aunty zee tace "zulaikha meye hakane wai, kiwuce muje mana"

A hankali zuly tajuyo karaf idonta yasauka akan Abba, shima kuma idonshi akan fuskarta...............................
'


07046767662 Maryam-Ashner ce
[9/6, 6:00 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 45

Gaban zuly ne yafadi bayan hada ido da Abba datayi jikintane yafara rawa aranta kuwa cewa take "nashiga uku wlh shine mutumin ranar ashe anan gidan yake, yau nakowa kaina inda za'a kasheni ni zuly innalillahi nashiga uku"

Abba da kwalla tacika mishi idanu saboda kara tabbatar da zarginsa dayaji Aunty zee ta kirata da zulaikha, a hankali yake tahowa gareta, itakuma tayi saranda kawai tana jiran ganin hukuncin dazeyi mata, gab yakusa zuwa inda take itakuma ta damke idanuwanta caf ya rungumeta a jikinshi a razane ta bude idanunta tana zazzarosu, tarasa metakeji a ranta, she feel comfortable a jikinsa but zuciyarta dai bugu kawai takeyi dub dub dub, Raliya da ranta yakara 6aci kam juyawa tayi takoma ciki abinta, umma da takaici ya dabaibaye itama bin bayan Raliya tayi, Usman dai ba yabo ba fallasa yagyara tsayuwarsa yana cigaba da kallon ikon Allah, Abdul kuwa zuciyarsa fal tausayi, tausayin irin rayuwar sa zuly tayi batare da mahaifi ba.

Aunty zee dabatasan komai ba mamaki duk ya cikata tadubi Abba tace "Alhaji lafiya?"

Sake zuly yayi ya kalli Aunty zee yace "muje ciki zainab" yafada yana riko hannun zuly datake binshi da kallo kamar doluwa .

Sune suka fara shigewa Abdul da Usman nabinsu a baya, a parlon suka tadda umma da Raliya zaune akan kujera 3 seater, Aunty zee tazauna kusa da umma, Usman yaje one seater Abdul ma haka, Abba dayake rike da hannun zuly har lokacin yajata suka zauna a two seater sannan a hankali yafara magana "nasan duk nan zuwa yanzu kunsan wacece zulaikha a wajena dakuma matsayinta a gidannan, sedai ita da zainab basusan hakan ba," yamaida kallonshi kan zuly sannan yacigaba "nine mahaifinki zulaikha"

a kidime take binshi da kallo, nan yafara basu labarin duk abinda yafaru, har karshe be 6oye musu komai ba, yakare yana kuka itama zulaikhan kukan take, kukane mecike da bakinciki dakuma farinciki.


Tadade tanason sanin wanene mahaifinta, yau gata gashi amma tayi bakincikin jin cewar bata hanyar aure aka haifeta ba, kukan datake abin tausayi, babu Wanda yayi kokarin lallashinta seda tayi me isarta

21 / 26