Chapter 24 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 26

69K to 72K   out of 76.5K words

tayi tace "mehali dai baya fasawa" kallonta Abdul yayi yace "kakar kike fadawa haka" tace "bakasan wacece hajja ba wlh"

Mikewa Abdul yayi dasauri yana fadin "listen kamar fa kuka takeyi" Sofiyya tadago kai tana daga zaune tace "and so? Kaga you should n't go there Dan wlh zaginka ma zatayi", inaaa Abdul betsaya jin ta Sofiyya ba yanufi inda hajjaju take dasaurinshi, itama Sofiyya mikewa tayi tabi bayansa.

Kusan atare su Abdul da munnir suka iso gurin kallon kallon aka fara tsakanin Abdul da munnir gakuma zuly da Sofiyya sunyiwa hajja zobe sun sakata a tsakiya........................
'

07046767662 Maryam-Ashner CE
[9/12, 9:43 AM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 49


Kallonsu take daya bayan daya, Abdul kuma munnir yake kallo sannan yamaida kallonshi kan zuly yace "ke me kikeyi anan da daren nan?" Sofiyya ta kalleshi da mamakin yadda yayi magana cike da tsare gida, adole ga babban yaya, munnir yayi dariya yace "sahunku mukebi ai yaya" shima Abdul din dariya yayi, zuly tace "ni sanyima nakeji wlh, sis mutafi gida ko?" Kafin Sofiyya tayi magana Abdul yarigata yace "tare kukazo? To koma tare kukazo batare zaku koma ba, I will take her hoom my self" kafin kowa yayi magana hajjaju tasanya salati, se a lokacin kowa ya ankare da ita sannan duk suka tuno abinda yakawosu wajen, it seems sunma manta da ita.
Abdul ne yamatsa kusa da ita cikin lallashi yace "inna meyafaru, duk kukanki mukaji muka taho"

"Kuka taho daga ina?me kukeyi da din? Yo da ina zaka kaimun jika? Wlh kaji tsoron Allah Dan ma'azu nidama can baka kwantamin ba" hajja tafada a hasale kamar zata kaimasa duka.

Munnir yace "kekam bazaki canza haliba hajjaju"
Tace "ina zan canza kuwa, kullum ina cikin bautar ubangiji na, lazimi da sadaka sune manyan halayeni yo aini bakamar uwarka bace wadda batada aiki se tusa" takare tana kallon Abdul tacigaba "kaga uwar manniru billahillazi bazaka iya zama da ita ba, lutiya CE kuma kasan lutaye da aukin tusa, ince dai uwarka ba lutiya bace? Danma karkace dakai nakeyi" duk dariya sukayi, munnir kuwa yacika yayi fam jiyaje kamar yakai mata duka.

Sofiyya tace "kaii hajja agaban budurwasa kike irin wannan bakyau fa" hajja tace "yoni ina ruwana, duk inda gaskiya take nan nake, banajin kunyar kowa, aigarama tasan gaskiya" tafada tana gyara daurin zaninta, kamar wadda aka tsikara kuma tajuyo tana kallon zuly tace "me kikace safiya? Wannan CE budurwar manniru jikana tilo?"

Sofiyya tace "gashi kingani" zuly nason yin magana amma hajja tahau masifa "in an isa ba tsatson muntari nafito ba, kullum cikin yin salatin annabi nake, tokuwa bazanga hakaba, ni DaDa zata cuta tun ban mutuba?" Tafada tana bangaje Abdul dake gabanta takoma cikin gidan tana sababi.

Dariya Abdul yayi yace "she is too funny" munnir yace "funny? She is mad" Dan yau tagama 6ata masa rai, badon yakai zuciya nesaba tabbas daze iya dukanta ma.
Hakanan suka karasa soyewarsu sukayi sallama suka koma gida.

Bugun duniya siddika taki bude kofar nan, wayarta take hankali kwance, mama CE tafito daga dakin aunty hafsat tagansu a tsaye suna buga kofa, wayarta tadauko taduba time 10:12pm karasawa tayi kusa dasu tace "daga ina kuke kukuma?" Inda inda suka farayi sunkasa bada amsa, siddika da dama jiran hakan take takatse wayar datakeyi tabude kofar tana mutstsike ido kamar me barchi tace "au seyanzu kuka dawo, sorry nikam tuni nayi barchi yanzu ma fitsari naji shine na taso," kallon mama tayi tace "ai mama ashe tare kuke"

Mama tace "ina sukaje? Niba tare mukeba yanzu suka shigo gidannan" siddika tace "infada?" Tana kallonsu, Sofiyya tasan makirci siddika ta shiryo Dan haka ma batako kulata ba, mama tace "au tambayarsu ma kikeyi tukunna, just tell me tundasu sunzama kurame" siddika tace "gurin samarinsu sukaje mama" tana fadin haka tayi wucewarta.

Sosai mama tayimusu fada, Sofiyya harda kukanta don batason fada sam, daga karshe tayimusu nasiha sannan tatafi gurin DaDa.

Koda siddika tadawo kin kulata sukayi, itama ko ajikinta tadau wayarta suka daura ita da masoyinta bashir.

Washegari dasafe Alhj salisu ya bukaci ganin mama, shimadai kamar Abba yazo da neman aurenta, amsar data bawa abba shita mayarwa baban munnir, don duk abubuwan dasuka faru subiyun nan sune sila, don haka ayanzu batako son hada hanya dasu balle zancen aure, gara kawai suyi zumunci.

Daya tabbatar yarasa ta seya ke nemawa munnir auren zuly, mama tace "indai sun daidaita Kansu nibani da matsala da wannan" duk dacewa yarasata amma burinshi zecika nahada zuri'a da ita.

A gurin Karin kumallo baban munnir ke nemawa munnir auren zuly gurin Abba, bamusu Abba ya amince, atake kuma daddy yabiya sadaki, Abdul ne ya kar6a sadakin sannan suka tsaida rana daidai dana Sofiyya.

Tuni zance yabazu a gidan, cewar za'a hada bikin Sofiyya dana zuly, koda hajja tasamu labari zuwa tayi har inda zuly take, takamo hannunta suka taho dakin DaDa tace "aminiya nifa saboda yawan salatin manzon dakikeyi wlh nakeson hada zuri'a dake, yanzu kinga yadda nayi ruwa nayi tsaki harseda na tabbatar an kar6i sadakin jikana manniru akan wannan yarinyar, duk dacewa bata hanyar aure aka sameta ba amma aibazamu iya canza kaddara ba, balle kuma indai tayo halinki na istigfari da hailala aisedai Alhamdulillahi" sosai zuly tayi mamakin hajja, kamar ba itace jiya tagama zagesu ba.


Sungama magana kan cewa mama da zuly zasu zauna anan bayan wani Dan lokaci se zuly tadawo gurin mahaifinta amma tunda mommy taji zancen aurensu tace baze yiwu ba, dole zata tafi da zuly domin tagyarasu itada sofiyya,.

Hakan kuwa akayi, guraren 11am duk sun shirya sundau hanya, a inda akabar mama itakadai, harta fara kewar diyarta zuly. aunty hafsat kuwa bakaramin dadin zaman mama tajiba, tun a jiya tafarajin damuwarta taragu sosai yaukuma data tabbatar mama nanan setaji damuwarta takare ma duka.


Kowa yasauka a gidanshi lafiya Lou, sedai fatan huta gajiya.

A ranar dasuka dawo da daddare akayi sallama da daddy, he isn't expecting anyone hakadai yafita, mijin aunty zee yagani wato mansir, da mamaki yakarasa suka gaisa, yace yashigo amma yaki yarda yace maganar bame tsayi bace, nan dai mansir ya shaidawa daddy bukatarsa na auren mama, dagaske yakeyi, duk irin hakurin da daddy yabashi kan cewa yabari yayi magana da ita kin yarda yayi, shidai abashi number ta, haka dole daddy yakira mommy taturo masa da numbern mama yabashi sannan suka daidaita, sukayi sallama yawuce.

Koda daddy yakoma yake sanar da mommy abinda yafaru itadinma mamaki sosai tayi tace "zulai ta farinjini duk da tsufarta" dariya sukayi dukansu.

A daren ranar mansur yayita kiran mama, data ganeshine setadena dauka, amma yaki dena kiran nata, daga karshe ma kashe wayar tayi tana fadin "I'm not like that niba butulu bace"


Tundaga ranar sedai in mama bata kunna wayarta ba amma setaci karo da sakonnin shi, damunta dayayi ne yasa tayi kiransa tace "we are not children don Allah kadenamin childishness ka kyaleni I'm not interested in you"

Murmushi yayi yana kwaikwayonta yace "we are adult I know baby" wata kunyace tarufe mama babu Wanda yata6a kiranta da baby, kodacan datayi soyayya ankikkirata da sunayen masoya amma ba'a ta6a kiranta da baby ba.

Ganin yafara cin nasara yasashi kara dagewa akan manufarsa na aurenta, ba'a rufa sati ba yasamu gurbi a zuciyarta domin yazo da salon datake muradi sedai wani 6angaren na zuciyarta na sanar da ita rashin dacewar hakan don aunty zee mutum ce bekamata ba sam ta aure mata miji ba.

She is confused hakan yasa takara dagewa da addu'ar neman za6in ubangiji amma kullum sonshi take karayi.


Tunda yaga yasamu gurbi da amincewarta yake neman hanyar daze Sanar da aunty zee manufarsa amma yarasa courage don matarsa yar halal CE, duk inda ake neman mace tagari aunty zee takai, babbar matsalarshi ma itace yasan zatace don yaga basu haihu bane shiyasa zekara auren.

Tunjiya yaketa zarya, yanason yasanar da ita amma yakasa, yau bayan yadawo daga masallaci yazo yasameta kan darduma yazauna gefenta, bayan tashafa addu'o'inta tajuyo tagaidashi ya amsa kanshi a sunkuya kamar wata sabuwar amarya.

Can dai yafara yimata wa'azi yajawo nan yasake yakama can, a karshe dai yafito yasanar da ita zekara aure, kuma mama yakeson aura.

Tabbas tun bayan kwana biyu dasuka wuce takula da canzawarshi kuma tagano cewar aure yake nema, amma bata ta6a tsammanin mama CE matar dayake so ba, kishi ne yataso mata, don tasan mama na haihuwa, idan har matsalar haihuwa daga gurinta yake aita shiga ukun ta.

Sosai take kuka tarasa meke yimata dadi, hakadai yayita lallashinta dabata baki da kwantar mata da hankali, don har cikin zuciyarsa yanaji da matarsa, dakyar yasamu yashawo kanta ta amince.

Kullum yana dada jawota ajiki dasanar da ita dukkanin shirinsa domin yasamu tasaki jikinta kamar da.

Bayan kwana biyu yashirya zuwa suleja domin tattaunawa da mama, ranar daya tafi itama aunty zee tashirya tayo gidan umma.

Nan take sanar da ita cewa mijinta zekara aure kuma mama ze aura yanzu haka ma yatafi gurinta.

Sosai umma tayi mamaki in the other hand kuma tayi murnan sanin cewa mijinta baze auro mama ba don dama abinda yahanata sake masa kenan, kallon aunty zee tayi tace "kinga irinta ba, keda kalen dangi kowa nakine aigashinan zata aure miki miji" umma macece me kishi sosai don haka amemakon ta lallashi aunty zee setake tayata kishi dazugata akan karta yarda.

Mansur yaje suleja rana daya da iyayen bashir sukaje nemawa bashir auren siddika, Alhajin kano shine yazo domin tarbansu anan Alhj Mansur yayi tsalle yayi kane kane seda aka amince aka kar6i kudin aurenshi sannan aka tsaida rana wata biyu da bikinsu zuly.

Yadawo da farinciki yasanar da aunty zee sosai ranar yaga tashin hankali domin aunty zee tadau zugar umma amma daga karshe ta watsar don tadada fahimtar soyayyar mijinta akanta, tadau auren dazeyi a matsayin kaddara.

Aure se matsowa yakeyi ayau saura sati biyu bikinsu Sofiyya, sosai 6angarori uku suke shiri, gidansu Abdul, gidansu Sofiyya dakuma gidan hajjaju don cewa tayi lallai sedai maman munnir dazo gidanta ayi taro.

Anshirya programs sosai amma Abdul ya ruguje yace vazeyi kodaya ba, babu yadda munnir beyiba amma yaki amincewa dakyar sofiyya ta lallabashi ya amince ayi dinner only.

Shirye shirye akeyi sosai, anata gyara amare tako ina, ga dinkuna dasuketa uban dunkawa sekace masu hada lefe.

Biki yarage saura sati daya, ankawo lefen Abdul akwatuna set uku nagani nafada, ankawo na zuly ma set biyu abudai yayi kyau se godiya.

Ranar ne kuma yan suleja suka taho, dukka gidan ba'a bar kowa ba, DaDa kuwa gidan aminiyarta tasauka, maman munnir ma babu yadda ta iya da masifar hajja hakanan ta taho domin ayi bikin danta da ita, don tun bayan data fahimci zuly yar Gallafi CE ta amince da auren batare da 6ata wani lokaci ba...............
'


07046767662 Maryam-Ashner CE
[9/14, 8:03 AM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 50

Maman munnir tariga su DaDa isowa tana zaune a kujera a parlo tana cin dumamen tuwo don da yunwa ta karaso, tabude baki zatakai loman tuwa DaDa tayi sallama, "innalillahi" tafurta tana komawa baya tasake labulen, hajjaju data dawo daga makobta, ta riske DaDa zaune ta6as a tsakar gida tanata tasbihi "la'ilaha illallah, la'ilaha illallah" abinda taketa maimaitawa kenan, Hajjaju takaraso dasauri tana fadin "aminiya lafiya, saukar yaushe?"

"Duba dakinki hajja, gamo nayi wlh" dasauri hajja taje tadaga labulen itama dasauri tasauke tana fadin "a'uzubillahi nikam nashiga ukuna"

DaDa tace "kinganta ko hajja kije kinemo me ruqya afitar miki da ita wlh inba hakaba ni gidansu Mardiyya zantafi se infasa sauka anan din aiba dole" hajja tazauna gefen DaDa tace "bafa aljana bace, wannan itace bodara matar salisu danake fada miki"
Aiba shiri DaDa tamike tana fadin "ah haba don Allah, bari inje inmata kallon tsab" wucewa gaba tayi Hajja nabinta abaya suka shiga cikin dakin.

Itako maman munnir lomarta take zubawa don bata wssa daciki, takai loma bakinta tace "imawuni baabs"

DaDa tace "inawuni bodara, aigaradai in ingaidaki, bana bari kigaisheni ba anjima ki isheni da tusa" tajuya tana kallon hajja race "anya zan zauna nan gidan hajja? Yo inbanda tasbihi da salatin ma'aiki Aida ganin farko suma zanyi"

Hajja tace "Nima nan dakiganni istigfari CE tarikeni, ai billahillazi abinci zan dinga kiyasta mata don bazata kashemu da tusa ba"

DaDa tace "kekam hajja bakida kara sam wlh, Wanda yazo kunga ai karramashi ake, musamman idan sirikinka ne, indai kana koyi da ma'aiki ai baka wulakanta bakonka" takarasa tana zama kusa da maman munnir tace "kiyi hakuri bodara wlh aminiya haka take kingadai kawata CE nima kaina hakuri nake da ita, kedai kawai kirageyin tusa don bakyau kinji"
Itadai maman munnir mamakin cin fuska irin tasu take takasa cewa komai.

Hajja tace "ni aibana tsoron Iowa, don haka gaskiya nake fada akan kowa sannan incika da hailala da salatin manzo" tana gama fadin haka tayi bedroom dinta, DaDa tamike tabimata baya sukabar maman munnir dasakakken baki.

Biki yarage saura 3days, ayau ne kuma akeyiwa amare gyaran gashi, basa fita ko ina tun bayan dasuka gama rabon minti wa kawayensu shikenan kuma aka hanasu fita domin gyaran jikin da ake musu, yau dinma a gida me gyaran tazo takeyi musu.

Masha Allah daka gansu zakasan cewa sune amaren batareda kayi tambaya ba, yadda suke daukar ido kadai ya isa ka fahimta, balle kuma kamshin dayake fita a jikinsu wannan kam sedai idan basu gifta ba, sunsamu ingantaccen gyara daga gurin me gyaran jiki da gashi, hakanan sunsamu ingantaccen hadin humra na amare sedai muce masha Allah, yo dama inda kudinka fa lol.

Dinkunan su duk sun iso sedai jiran ranar biki, Washegari me lalle tazo ta tsantsara musu.

Yau ake sa lalle sosai amare suka cancare

24 / 26