Chapter 7 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 26

18K to 21K   out of 76.5K words

jin muryar ta, but zuciyarsa ce tahanasa kiranta.
Seda yakusa katsewa sannan yadauka yakumayi shiru.

Jin andauka yasa Sofiyya cewa
"Yaukam lafiya? Kodai an manta danine?"

Kamar Wanda akayiwa dole yabude Baki yace
"Nop kodaya"

Jin yanayinda ya amsa Mata yasata sanin cewa tabbas akwai abunda ke damunshi Dan haka tace
"Ingaya maka, wata sister na taga photonka Wai tana sonka"

Zunbur yamike yazauna yace
"Then sekekuma kikace Mata me?"

Murmushi tayi Jin yadda yagyara muryarsa one time, tace
"Cemata nayi bazata iya dakaiba"

Yace "why?"
Tace "because sometimes haka kawai zaka dingajin haushinta, and sometimes hakanan zaka Dena kiranta a waya and lastly you may not like her"

Gimtse fuska yayi yace
"Malama you don't know me haryanzu so don't judge me"

Tace "Really? Then explain to me"

Yace "I don't have that time"

Tace "is ok zansanka very well with time ai, but now lokacin cika alkawarine, labarin 10 minutes dakace zaka bani I'm all ears"

Dafe kai yayi, danshi harga Allah fada kawai yayi, kumama yamanta, toshi yanzu ta inama zefara?

Jin shiru yasa tace
"Inajinka fa"

Yace "ok duba agogo kiga karfe nawane"

Dubawa tayi taga 10;15 tafada masa, yace
"Ok listen now, Bari indan Baki taqaitaccen tarihina
Farko dai abbana asalinshi Dan niger ne, ummana Kuma asalinta 'yar Kano ce, sau daya muka ta6a zuwa niger, lokacinda kakanmu yarasu, dama shikadai yaragewa abbanmu so tunda yarasu shikenan we don't have anything to do with niger kuma., Ummanmu Kuma 'yar bauchice aurene yakawota Jos, so bamuda kowa a Jos se abokan arziki sekuma kanwar ummana dake aure anan jos so that's it. Uhmmm 10 minutes yawucema Aiko?"

Sofiyya data nutsu tana sararonshi taduba agogon taga 10:19 tace
"Minti 4 fa kawai kayi"

Yadan hade rai yace
"Minti 4 kuma kamarya?"

Tace "yes 10:15 kafara and now 10:19"

Caraf yayi yace "no no this is cheating 10:00 dai-dai nafara malama, wato harma 19 minutes nayi inata zuba Miki surutu"

Cuno Baki tayi tace
"You cheated me, ah swear 4 minutes kayi" takarasa kamar zatayi kuka

Murmushi yayi yace
"'yar karama dake zakimin wayau"

Itama murmushin tayi, hakadai sukayita hirarsu har ma yamanta da haushinta dayakeji, anan take sanardashi cewa gobe zasu dawo, yayi matukar farinciki dajin labarin. Domin yashirya ranar graduation party dinsu ze proposing mata,.

Washegari kamar yadda mama tashaidawa zulaikha hakan akayi, tadauketa suka tafi gidan antyn yara kamar yadda suke Kiran matar, bayan sunyi sallama ta amsa, da fara'arta
"Kune dasafe haka? Zulai zulai jelar mama"

Duk dariya sukayi sannan suka shiga daki.

Bayan sungaisa ne mama tace
"Dama wata 'yar tafiyace takamani ta kwana daya takamani, shine nazo rokon alfarma"

Anty tace
"Ayya Allah yakiyaye hanya,"

Mama tace
"Amieen, sonake Dan Allah inbar zulaikha Nan gurinki har zuwa gobe in Allah yadawo Dani lafiya"

Anty tace
"Allah sarki bakomai wlh, aisemu zauna, Kinga nasamu 'yar taya Hira ai, dama yasayyad yayi tafiya shima se goben zedawo"

Mama tayi murmushi hade dayimata godiya, sannan tayi musu sallama tawuce.
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa* >?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Yawan comment, yawan typing da posting. qarancin comment, qarancin typing da posting.

Episode 15
Munnir abun duniya duk yataru yayimasa yawa, harwata 'yar rama yayi, tako Ina Babu Dadi.
Tunda yadau number din Sofiyya a daren ranar yakira but switched off Kuma kullum inya dialing numbern amsar dayake samu kenan, kasancewar tun a wancan ranar bayan ya mayarmata da wayar tacire simcard din, Dan dama bawani anfani dashi takeba, tafi anfani da dayan, shikuma beyi dabarar daukan duka numbers dinba.
Yaje gidan yasamu labarin tafiyarta, hakan yasa yake ganin may be ko garin ba network ne, aikuwa dai suleja tasha tsinuwa gurin munnir, Dan har Wanda yakirkiro garin seda yazaga.
A dayan bangaren kuma, yayita kokarin ganin babanshi yazo yasamu daddy Amma hakan besamuba, dalilin aika baban nashi aiki da'akayi a wurin aikinshi, Wanda seyanzu yasamu dawowa, shima Kam aikin da ogan baban nashi sunsamu rabonsu na zagi Babu adadi.
Yaune kuma baban munnir ke tahowa domin ganawa da mahaifiyar shi dakuma daddy Kan zancen munnir da Sofiyya, hakan ba karamin farinciki yasanya zuciyar munnir ba, harma yakasa 6oyewa, abinda yaba hajiya mamaki kenan harseda ta tanka "manniru nace anya ba aljanune suka shigeka ba? Garafa insani dawuri domin inkira ubannaka yataho da malamai ayi maka rukiyya" kallonta yayi Yana murmushi yace "hajjaju tawa, toni shikenan bazanyi farinciki dazuwan mahaifina ba? Wata nawa bansashi idanuna ba"
Hajjaju tace "la'ilaha illallahu, Amma Allah wadaran halin munafunci, yo wani lokacin basema yafi haka dadewa bezoba, inzezo ko ajikinka, Amma harkake fadin haka" tafada tana rike ha6a, munnir yabude Baki zeyi magana hajjaju tayi saurin katseshi tana tufarda yawu "tuf tuf, Allah kayimana tsari da makirai Kuma munafukai" tafada tana wucewa abinta.

Shiko munnir ko a jikinsa, Dan Sam maganganun hajiya basa damunsa, shiyanzu burinsa babanshi yazo ayita takare,.

Agidan Alhaji salisu bayan yashirya domin tafiya garin Jos mahaifarsa, yaje yiwa Ammi sallama Amma besamu Koda arzikin Allah yakiyaye hanya ba, sedai kashedi datake yimasa "karka sake kace musu akwai maganar shegiyar yarinyar nan, Dan wallahi koma meye zefaru Dana baze auri yarinyar nan ba" shidai be kulataba yayi wucewarsa.

Bayan zuwan baban munnir, gidan hajiya yasauka inda yasamu tarba ta musamman kamar dai yadda yasaba.

Zuly abin duniya duk yadameta, itadai tunda tayi hankali Bata ta6a ganin Wanda tasoshi kamar Abdullah ba, ita kanta son da take masa har mamaki yake Bata, tayaya za'a ce daga ganin mutum sau daya tak takamu da matsananciyar soyayya haka? Yanzune ta tabbatar dacewa munnir bawani sonsa takeba, is like kamar sha'awarsa kawai take, domin Abdullah bata ta6a Jin tanason kwanciya dashi ba, zallar soyayya kawai take masa, Amma munnir jitake kawai tadinga rungumarsa kozataji Dadi.

Dukda cewa haryanzu bawai tadena tunanin munnir bane, but tunanin yayi kasa sosai bakamar daba.

Yanzu haka zaune take, tazuba uban tagumin da ayanzu za'a ce yazame Mata kamar jiki, tayi zurfi sosai cikin tunanin data saba, wato tunanin Abdullah.

"Zulaikha, bansan Kuma mekikeso inyi miki yanzuba, duk wani gata nayi mikishi a rayuwa saboda farincikinki narabu da iyayena da 'yan uwana, Amma Gashi ke sokike ki kashe kanki saboda wani can Wanda na tabbata baze ta6a sauraronki ba" cewar mama data Dade kanta Amma Bata saniba.

hawayene shar yazubo ma zuly, tasa hannu tashare, sannan tamike tayi hanyar daki,

Fizgota mama tayi hadeda wanka Mata mari sannan tace "Dan ubanki Dani zakiyi gaba zulaikha? Ni mahaifiyar ki?"
Kuka zuly tafashe dashi tana durkushewa a gurin, jikin mama yayi sanyi sosai itama tanemi gefen dakalin kofar dakinsu tazauna, bayan 'yan mintuna zuly batabar kukanda takeba, mama tasunkuya ta dagota ta kwantar da kanta akan cinyarta tana fadin
"Kiyi hakuri zulaikha, ba'ason Raina naza6a Miki wannan rayuwar ba, dukdacewa laifina yafi yawa ciki Amma ki yafemin kinji" cikin sheshshekar kuka zuly tace "mama kimin alfarma kisanar dani waye mahaifina Dan Allah" mama tashare guntun hawayen daya zubo Mata tace
"Fadama bashida anfani, yadda muka Fara rayuwar mu batareda kinsaniba, mucigaba da rayuwa a haka kawai"
Shiru tadanyi, sannan tacr
"Tashi kije kici abincinki, inaso da gobe inje kano, tunda Kinga wayata ta 6ata yanzu banida number din malam shehu, kuma ga graduation party dinku nata matsowa Babu wasu isassun kudi cikin account dina, zanje yabani kudadena kawai nahakura da business din" kallonta zuly tayi tace
"To mama tare zamuje ko?"
Mama tace "yaza'ayi intafi dake, nadai yanke hukunci Zan ajiyeki Nan gidan maman yara, tunda befi inkwana dayaba zandawo, nasan zata rikeki se inkulle gidan, inbata makulli" cuno Baki zulu tayi, tamike tanufi daki domin cin abinci.

A office Abdullah yagama shagala da wayar dasukeyi shida cutienshi, harma beji nocking da aketayi Masa ba, ganin Bashir yayi kawai akansa.
Harararsa yayi, yacigaba da wayarsa cikin low voice dinsa yake fadin "jekici abinci please, you talk too much baby" kasake Bashir yayi Yana kallonshi cike da mamaki, kasa Zama yayi yadaura hannaye akai kamar Wanda ze kurma ihu.
Can suleja kuwa, Sofiyya ta daddage tana zuba mishi labarin abinda siddiqa ke Mata, Jin abinda yace yasa cikeda shagwa6a take fadin
"Yanzu korata kakeyi ma?"
Shiko bebi takan Bashir dake kallonshi cikin zare idanu ba, yakara kashe murya yana fadin
"Baby rigima, banso kizauna da yunwa nefa, go go go, anjima nizan baki labari"
Cikeda nishadi tace "oh my God, ok ok ok tell me na mintuna nawa zaka bani"
Murmushi yayi yace "10 minutes"
Dariya tayi tace
"Ok promise?"
Yace "promise, now go"
Tace "ok you take care, byeee"

Duk suka ajiye wayar, ita tamike tayi hanyar kitchen tana kwala Kiran siddiqa.

Shikuma dagowa yayi Yana kallon Bashir dahar yanzu yake a tsaye, hannaye akai.
Yace "dafatan badaga gidan sarki aka turokaba, Dan Naga kazama dogari" se sannan Bashir yaja kujera yazauna yana karema Abdul kallo as if yaga sabon mutum, dakyar ya hadiye yawun bakinshi sannan yayi gyaran murya yace
"Abdullahiii" yaja sunan Yana kara zare idanu.
Abdullah Kam ko kallonshi besake yiba, yaja file din gabanshi yafara rubutu, Dan yaga kamar ba'acikin hayyacinsa yakeba.
Bashir ya canye file din Yana fadin
"Yanzu kagama labari da mace Amma nizaka komamin miskili"
Kallonshi kawai Abdullah keyi bece komai ba.
Bashir yace "mutumina bani labarinta Mana, yaushe akayi wuff dakai haka?"
Murmushi Abdullah yayi yace
"Labarin uwarme Zan baka, munafiki kawai"
Bashir ya kyalkyale da dariya yace "tofah! Wayaga manya na love, oh wlh zanso inga babyn Nan"
Bata fuska Abdullah yayi yace "kaga mema yakawoka Nan?"
Bashir ya gyara Zama yanason Jin gulma, Amma Abdullah iyayen kishi yaki sanar dashi komai, daga karshema shiru yayi Masa Dole yahakura da zancen, yadawo Kan batunda yakawoshi.
"Nifa numbern wannan beautiful nazo kar6a, kokuma kabani address nata please"
Tuni yanayin Abdullah yafara canzawa, mikewa tsaye yayi Yana fadin
"Bakajin Kiran sallah ne, malam niba kafiri bane"
Yayi hanyar barin office din.
Bin bayanshi Bashir yayi danba abin mamaki bane a wulakancin Abdullah kadan kenan.
Koda suka idar da sallan iya magiya da roko Babu Wanda Bashir beyiwa Abdullah ba Amma yakima ya saurareshi balle har ya samu abinda yakeso, daga karshe kuwa kamar zasuyi fada, Dan ran Bashir yasoma 6aci da wulakancin da Abdullah kemashi, hakadai suka rabu kowa rai Babu Dadi......................................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn
Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Nadawo bayan kusan wata biyu danayi offline, alhamdulillah yanzu zamu daura, sedai ina rokonku daku dinga bada hadin kai wurin comment da sharhi please.

Episode 17
A parlor bayan sungama breakfast Umma tadubi Abdul tace
"ina tunanin yau Abbanku zedawo"
usman yayi saurin mikewa yace "thank god he will be present agurin partyna"
Abdul ya harareshi yace "kuma seme? "
Usman yayi dariya yace "yaya you forgot Abba yamin alkawarin mota on my graduation day "
Mikewa Abdul yayi yana tafiya hanyar waje Yace "inkayi abin arziki Kenan" sannan yakuma cewa "Umma nawuce office "
Umma tace "adawo lpy Allah yatsare"

Harya shiga mota yatayar yahango usman dagudu yana daga masa hannu, tsayawa yayi harya karaso yana haki yamika masa envelope yana fadin "invitation card inji Umma kakaiwa Anty zainab"

Kar6a yayi shikuma yajuya yakoma cikin gida.

A suleja 11am su sofiyya duk sungama shirin tafiya, sofiyya tafaki idon inna tanufi sashinsu siddiqa, dazuwanta bata yi side din Maman siddiqa ba tanufi side din amaryar baban siddiqa,
"Assalamu Alaikum Anty"
Sofiyya tafadi daga kofa

Daga ciki Anty hafsa tamike dakyar sakamakon cikinta dayayi girma sosai, tataho tabude mata kofar takoma tazauna.

Sofiyya tace "sannu Anty Allah yasaukeki lpy"

Murmushi Anty hafsa tayi tace "Amin sofyn inna"

Itama murmushin tayi sannan suka gaisa tace "yaufa zamu wuce"

6ata fuska Anty hafsa tayi tace "shine seyanzun kike fadamin"

Sofiyya ta sunkuyar dakai tace "sorry Anty kinsan dokar inna tahanani zuwa nan sashin, yanzu hakama batasan nazoba"

Jim Anty hafsa tayi sannan tace "hakane Aidan azauna lpy ne shiyasa"

Sofiyya tace "sekin haihu insha Allah zandawo" tamike tana fadin "Bari inje kartafara nemana"

Anty hafsa tayi saurin cewa "dan jirani I'm coming "

Komawa tayi tazauna, Jim kadan segatanan tafito da Leda ta mika mata tace "bansan cewa yau zaku tafiba, gashi kuma bazan samu damar zuwa partyn nakuba"

Kar6an ledan tayi tana fadin "harda dawainiya haka Anty"

Zungure mata kai tayi tana cewa "har Yaushe muka fara haka dake"

Murmushi sofiyya tayi tace "sorry, bari inwuce, tunda yanzu inada number dinki zamuyi waya"

Anty hafsa tace "to Allah yatsare hanya, semunyi waya"

Dahaka tafito dasauri tayi hanyar sashin inna, tana zuwa ta tarar itakadai ake jira, duk Yan gidan sunfito yimata sallama, ta girgiza kai a ranta tace "wato kowa yasan yau zantafi amma banda Anty hafsa"

Dahaka dai duk sukayi sallama babansu siddiqa yajasu dayake harda siddiqa suka tafi.


yau a gidan hajjaju daddy yayi breakfast, taredasu munnir da babanshi, cikin nishadi.

Bayan sungamane sunadan ta6a hira, munnir yakafa yatsare yana jiran yaji ansako batunshi, daddy yadubi munnir yace "dan Hajiya bamu wuri mu tattauna ko"

Cike da bakin ciki yatashi yanufi waje, don shi soyayi ayi komai a gabanshi, inyaji an kuskure yayi gyara.

Alhaji salisu yace "gara dakasa yayi waje ai"

Hajiyama mikewa tayi tace "kafin korar tabiyi takaina nima bari nayi waje"

Duk dariya sukayi, daddy tace "Aida kintsaya dan kinsan komai se ansanar dake"

Hajiya tace "zanje in runtsa, daga baya naji koma menene"

Duk atare sukace "afito lpy"

Tace "amin"

Daga nan Alhaji salis ya fuskanci daddy yana fadin "danka fa aure yakeso"

Da tsantsar farin ciki daddy yace "masha Allah hankali yazo, girma kuma yakamamu"

Dariya Alhj yayi yace "sosai kam"

Daddy yace "a Ina yake neman auren".
Alhj yace "ai inaga yar gida za'ayi, shiyasa ma nataso nataho dakaina"

Gyara zama yayi sannan yacigaba da fadin "Wai sofiyya yakeso, yadameni da waya akan lallai inzo insameka"

Da matukar murna daddy ya mike ya rungume dan uwansa yana fadin "masha Allah, nadade da Wannan tunankn amma nakasa furtawa ina jiran dayansu yafara furtawa alhamdulillah "

Shima Alhj murna yayi sosai sannan suka koma suka zauna, yagyara murya yace "amma kasan akwai alkawarin danayiwa zulaikha nacewa munnir shize auri diyarta insha Allah, inaso kataimakamin wurin cika alkawarina"

Daddy yayi jimm sannan yace "yanzu ina zaka samu zulaikha yaya? KO adanginta fa babu Wanda yakeda labarinta".

Alhj salis yace "zan nemota duk inda rake, shekaru biyunnan ne ta 6acemin, domin bandena bibiyarta ba"

Girgiza kai daddy yayi Cike da mamakin irin kaunar da dan uwansa kewa Wannan baiwar Allahn, amma taci amanarsa.
Ya numfasa sannan yace "yaya 'yar gurin zulaikha da sofiyya kamar 'Yan uwane, kana ganin hadasu kishi babu matsala? Kuma kana gani iyayensu mata zasu yarda? "

Alhj salis ya jjnjina sannan yace "kwarai nayi nazari akan Wannan batun kuma naga cewa babu wata matsala insha Allah, kaidai kayi kokarin shawo kan iyalinka, inhar ta amince tawurin zulaikha Indai nasameta mesaukine"
dasauri yasake fadin "ammafa akwai sharadi, tabbas inkowa yayarda sekuma sofiyya tayadda, dan bazan yiwa diyata auren doleba. "

Murmushi daddy yayi yace "diyarka ma nasan tanaso, da alama sunshirya kansu ai"

Hakadai sukayuta hirarsu ta Yan uwa.

12pm tayiwa Maman Zuly a kano, inda tasamu ganin Wanda taje gani suka gama tattaunawarsu wurin 3:40pm, taso takoma gida arana, amma ko hauka take batajin zatayi tafiyar dare, domin bata manta mummunar kaddarar data sameta sanadiyyar tafiyar dare ba, guntun hawayenta ta goge sannan tawuce tanufi hanyar wani hotel data sani.
Tabbas dataje wani guri neman taimakon gurin kwana, gara ta kwana a titi inhar batada halin Kama hotel,.

Shigarsa ta kamala da manyan kaya, malum-malum, dakuma hula, dukda yafara manyanta amma daka ganshi kaga kyakykyawan mutum. Alhaji Mu'az Gallafi kenan

Sauri yakeyi domin jirginsu yakusa tashi, mikawa Matar reception key yayi, da alama a hotel din yakwana.

Dasauri yamika mata key din yawuce, driver dinshi yabude mishi mota, cak yatsaya ganin fuskar dayake mafarki ta bayyana a gabanshi.

Maman zuly da saukarta Kenan daga adaidaita, kai tsaye tayi cikin hotel din,.

Dasauri yamatsa ya kauce dan baiso taganshi.

Bayan sungama magana da reception dinne, tamika mata key din da yanzu aka bata, kar6a tayi tanufi upstairs.

Alhj Gallafi da zuciyarshi taketa bugu, idonshi yaciko da hawaye kiris yarage yazubo,.
Driver dinsa ne yataho jinshi shiru, haryazo kusadashi besaniba, seda yayi masa magana sannan yace
"Anfasa tafiyar yau"

Jinjina kai yayi sannan yace "to yallabai, amma lpy kuwa naganka haka"

Girgiza kai alhj yayi yace "bakomai kaje kawai zan kiraka"

Amsawa yayi, sannan yajuya yayi wucewarsa.

Shiko alhj gallafi komawa gurin reception din yayi yana Tambayar bayani akan Matar data shigo yanzu, bayan tagama sanar dashi, sannan yakuma Kama wani dakin domin sanya mata idanu.

What do you think???
Wacece zulaikha da Alhj salis ke yawan fada?
Meya hada Alhj Gallafi da Maman zuly?

Kusanar dani abinda kuke tunani
Sannan kujira episode nagaba, Dan zata fasheeeeeeee.
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?

Episode 18

Saukarsu kenan cikin garin jos 2:pm, murna sosai Sofiyya tayi domin tayi missing mommy da daddy gakuma handsome, murmushi tadanyi a ranta tace "rigimamme"

Bayan sunyi parking suka fito suka shiga cikin gidan dagudu Ikram taje ta rungume mommy, Siddika ma kusa da mommy taje tazauna.

Cikin murnar ganinsu duka mommy tace "welcome mutanen suleja, kunsha hanya sannunku"

Baban Siddika yana zama yace "barka dai, dafatan munsa meku lafiya"

Gaishe-gaishe suka farayi na yaushe gamo,

Sofiyya ko abubuwa biyu zuwa ukune suke damunta a zuciya.

Na daya yadda tabaro Anty hafsa da katoton ciki gakuma halin da take ciki a gidan

Na biyu yadda haryanzu bata san matsayarta ba, gashi ranar graduation dinsu takusa

Na uku uwa uba handsome yayi kane-kane a zuciyarta koda yaushe cikin tunanin shi take.

Gani tayi sunata surutu bazama subarta

7 / 26