Chapter 3 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 26

6K to 9K   out of 76.5K words

tajq ikram tana mita "Satan yara har agurin shopping" Sofiyya tadago Kai caraf suka hada Ido, dummmm zuciyarsu tabuga a lokaci daya, kafeta yayi da ido ko kyaftawa Babu, itama kallonshi take kafin tayi karfin halin cewa "laaaa yayan Usman hello" tayi kirkiro murmushi tana daga Masa hannu, kokarin saita kansa yayi, shima murmushin yayi kafin yace "you here" tace "yes narako kawata shopping ne" yayi murmushi yace"that's good" tace "kaifa mekazo siya?" Yace "yara nazo sayawa chocolates" tace "kawai chocolates? Ke bazaka sai komaiba kenan kayi zuwan banza? Lallai bakada wayo Sam" murmushi yayi yace "really? Then help me find something for me" tace "ai bansan sumeye favorite dinka ba" yace "nibanida favorite" tsayawa kallonshi tayi tace "wait wait" ta 6ata fuska sannan tace "that day in our school, baka min maganaba I thought baka iya maganane ashe akwai ranar dabaka magana, ok wato yau ranar yin maganane a gurinka shiyasa kaketamin magana, ammafa nayi mamaki" murmushi yadingayi yana mamaki sure she's talkertive parrot, Jin bece komai ba tace "oh I'm sorry I remembered" yace "what" tace "namanta Ashe kirga maganar dazakayi arana kakeyi, may be yau nasaka ka karya dokarka" yayi murmushi yace "who told you" kaitsaye tace "Usman of course" sekuma tajuyo dasauri tace "au not Usman not him, I know it myself" wannan karan murmushin dayayi harseda hakoransa suka fito, Maryam ce tatahi wurin ta kalli basket din Sofiyya tadago ta kalleta batareda ta kalli wadda suke magana ba tace "kekam kinji jiki, tun dazu abinda Kika dauka kenan? Kitsaya se surutu kikeyi mara dalili, tajuyo tana duban mutumin caraf taga Abdul tace "ke Sofiyya wannan fa yakusa sace ikram dazu, shine kike bashi labari" da mamaki Sofiyya ke kallonta tace "wannan yayan friend dinane fa Maryam" Maryam tace "au haba? Sekuma ta kalleshi tace "I'm sorry yayanmu" murmushi kawai yamata yaja hannun ikram sukayi gaba, su Sofiyya nabinsu abaya. Ahaka aka gaba shopping din, inda Abdul yadage lallai seda Sofiyya taza6a mishi wani agogon hannu, sannan shikuma yasiya mata perfume yasaima Maryam takalmi ikram Kuma yahadata da ice cream.

Yaukam da farinciki yakeyi bakadanba, yana driving yakunna wata wakae India yanaji Yana girgiza Kai ahaka haryaje gida, yazauna a parlor Yana rabawa kowa tsarabarsa umma dai da ido take binshi tana studying dinshi, kowa na mamakin yadda yasake a cikinsu kamar bashiba, Usman dai kasa hakuri yayi yace " Yaya yaukam kanata happy" agogon hannunsa ya kalla yayi murmushi bedaice komai ba, Dan tunda yafito daga ShopRite din yaga wani almajiri yacire agogon hannunsa me tsada yabashi kyauta sannan ya daura Wanda Sofiyya taza6a mishi, har Abba yadawo betashi agun ba, se Hira su Tasleem suke masa, shidai nashi girgiza Kai sekuma murmushi har aka watse kowa yatafi sannnan shima ya suce daki.

Da daddare bayan su Sofiyya sungama dinner bata yarda sun hada Ido da munnir ba tace kanta na ciyo tayi gaba, daddy yace "Dan gidan hajiya, ince dai lafiya jiya bakazoba Kuma ance kadawo gida dawuri" yasosa Kai yace "daddy kaina ke ciwo, Dana bar nan Sena koma gida nasha magani shine kawai nakwanta" daddy yace "hajiya ko cemin tayi bakanan danaje da daddare" yace "Aiko itama batasan Ina cikiba" mommy tace "Allah ya sawwake" yace "amieen" sukadan ta6a hira daddy yawuce dakinsa mommy tayi parlor tana kallo, yarage daga ikram se munnir ne a gurin, munnir yace "ikeena glutton acici" cuno Baki tayi tace "aidai yau abinci kadan naci, saboda uncle yasaimin ice cream" yace "wani uncle?" Tace "munje shopping da ya sofy mukaga wani uncle yasaimin ice cream yasaima yaa perfume" tamike tace "Bari inkar6o maka ma kaga" tayi upstairs dagudu, ranshi yayi mugun 6aci, wato wanine ke hure Mata kunne? Mikewa yayi dasauri yacewa mommy seda safe yafita, Yana shiga mota yayi dialing numbern zuly, tana dauka yace "kisameni a fiddy restaurant" Yana fadin haka yakatse Kiran yatada motan yafice a guje.
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Join my watsaap group mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 6
Zuly ce zaune tareda munnir, mikamata wayan hannunshi yayi yace "kitura photon nan a wayanki" kar6a tayi tatura, sannan tamika masa wayarsa, tace "what about her?" Yace "she is Sofiyya Adam Muhammad by name, a candidate of waec and neco, a very perfect student in both school and madrasa, but very slow writer indeed" yayi shiru Yana murmushi sannan yacigaba "gentle, very cute looking, fear skin colour, she likes tea and snacks more than food, she's 17 years old, she likes watching cartoons movie then followed by Indian movie, she has plenty friends because she's very talkative, but she has only one best friend that's Maryam" shiry yayi sannan yace "abinda nakeso kiyi nafarko shine, kisan yadda zakiyi tazama friend dinki at any cost, sannan seki samin ido akanta, I mean watch her every move, inaso indinga samun information akan komai datakeyi, when I say komai ina nufin komai" murmushi takeyi tace "consider it done" murmushi yayi yace "gobe kifito by 11 inkaiki kiga gidansu" tace "ok, but what about me?" Yadan 6ata fuska sannan yace "yanzu dai try your best kiga kunzama friends then nikuma zan miki abinda kikeso kafin kikarasa aikin" tace "ok kabani nan da three days angama, tundadai she talk alot zama friend dinta bazeban wahala ba" yace "ok then let's see" tayi murmushi tamike tace "see you then" bayan fitarta yadade zaune a gurin kafin shima yamike yabiya kudin order din dayayi yafita.

Mami nazaune tsakar gida tana Shan iska, kasancewar yau garin badai zafiba, tajiyo sheshshekar kuka, mikewa tayi dasauri tanufi dakin, ganin zuly tayi takwanta ruf daciki se kuka takeyi, mami tazauna gefen gadon tayi shiru tana kallont, can kuma tace "zulaikha" dago Kai tayi fuska duk hawaye, mami tadafata tace "meyafaru ?" Tagyara zama tace "mami munnir will never love me" sekuma tasake fashewa da kuka, Mami ta girgiza Kai tana fadin "meya faru?" Tadago tajayo wayanta ta nuno picture din daya tura Mata ta mikawa mami tace "look at her Mami, her beauty is beyond explaining, Kuma they are rich" Mami takurawa picture din ido takasa janye idonta kan picture din, tatafi duniyar tunani harma batajin me zuly kecewa "mamiii" firgit tajuyo tace "yeah she's, kawai kifita hanyarsa tunda dai kinga batake yakeba" da mamaki zuly kebin Mami da kallo, Bata ta6a kawo mata zancen munnir tasace Mata gwiwa ba seyau tace "mami yanzu kan tafini kyau shikenan nazama looser? Can't I fight for my love" Mami tatashi tayi hanyar barin dakin tace "nadai gaya miki kifita harkar yaronnan" mamaki yahana zuly motsawa a inda take.

Washegari Tuesday basuda exam se Wednesday and Friday, bayan tagama duk abinda yakamata 11:30 tafito cikin shirinta na doguwar Riga, purple color, taji manyan stones, tayi rolling da mayafin rigar tadau wata 'yar fashion back milk colour ta zuwa takalminta flat shoe, shima milk colour, ta feshe jikinta da turaren dake kan dressing mirror din gurin, tatsaya gaban mirror din tana karema kanta kallo, tayi murmushi kafin tayi hanyar ficewa a dakin, harta fita tafara sauka, tayi saurin dawowa, bedside drawer tabude, nan taga turaren da Abdullah yasaimata tadauko ta fesashi a hannunta takai hancinta lumshe idanuwanta tayi kana tahau fesawa duk jikinta, kana tasauka zuwa dakin mommy, tasameta zaune da laptop agabanta tace " mommy I'm going" tadago tazare medicated glass dinta tace "going where? Dama munyi dake zakije wani wurinne?" Tace "yes Mana mommy jiya banace miki zanje saloon ba" kya6e Baki mommy tayi tace "nama manta wlh, Gashi na aiki driver," tamika mata wayarta tace "you call munnir seyazo yakaiki" girgiza Kai tayi tace "intasoshi yana office? No zanshiga adaidaita kawai" mommy tace "kyadaiji da gulmarki, dacan dakike kiranshi ai bakya tunanin office" itadai batace komai ba salim alim tayi gaba.

Yagama shirin office yafito yanama umma sallama, Anty Raliya tafito cikin shirinta tace "laa Yaya seyanzu zaka office koka dawone" yace "zandai tafi" takalli agogon wayanta tace "11:30 fa, bakayi lattiba" yace "ai Abbane ya aikeni seyanzu nadawo, kuma banson karashe yinin agida doing nothing" tace "aikuwa gara katafi, but please indauko mayafina ka ajiyeni gurin saloon din Mana" yace "ok kiyi sauri" dahaka ta haura tataso keyar Tasleem, dama Qasim bayanan sunfita da Usman, bayan sunfito suka shiga kitchen duk sukayi umma sallama sannan suka fice, a motan haka sukayi zaman kurame har suka isa gurin.

11:40 motar munnir tayi parking daidai kofar gidansu, munnir yakalli zuly yace "this house me milk din fenti" ta girgiza Kai tace "ok" dahaka suka juya ya maidata gida.

Daidai yagama parking, Raliya na kokarin fita daga motan ya hangota tasauka a napep, kallonta yake ko kyaftawa babu, harta sallami me napep din kafin tatako a hankali tashige saloon din, a zuciyarsa yace "komai nata so slowly, the way she writes the way she talk, they way she walk even the way she looks" Raliya tayi sokoko tana binshi da kallo kafin tabi Sofiyya da kallo ganin inda idonshi yayi kenan, seda tai masa tafi tace "oh so she's the luckiest girl" dauke kanshi yayi yace "zaku gama yanzune kokuma zaku dade?" Raliya tace "I don't know seyadda takaya, kawai katafi kada mu 6ata maka time" shiru yayi sannan yace "you just go, I will wait for you to finish" daga haka yazaro wayarsa yahau danne danne, Raliya tawuce tana murmushi.
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Join my Watsaap group mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 7
A cikin shagon saloon kuwa, Sofiyya tashiga tagaisa da mutanen gurin sannan tanemi wuri tazauna, watace ta taso tana fadin "meza'ayi Miki?" Sofiyya tace "no karki damu bari sister nancy takarasa" (saboda ita duk intazo bata yarda kowa yata6a mata kai se Nancy domin tafi yarda da aikinta) a zuciyarta fadi take 'daddy please kayi ka yayeni,kowa na danna phone niko se kallo' sallamar su Raliya ne yakatse mata tunanin nata, bayan sunshigo sun nemi guri sun zauna, aka gaggaisa, Raliya ko idonta akan Sofiyya, matar dazuce tazo tacewa Raliya "madam meza'ayi Miki?" Raliya takalli Sofiyya tace "sister na tarigani zuwa, kifara da ita I will wait" murmushi Sofiyya tayi tace "no nice nace tabarshi, inajiran waccer takarasa ne setayimin" Raliya ma murmushin tayi tana daga Tasleem tace "gata afara yimata" matar taja hannun Tasleem sukayi gaba, Raliya tadubi Sofiyya tasake cewa "da alamu nan kika saba zuwa saloon" gyada Kai Sofiyya tayi tana murmushi, Raliya tasake fadin "muko kinga bakine a garin, duk dadai cewa nanne asalina" Sofiyya tace "eyya, kunzo ziyara kenan" Raliya tace "eh wlh, saboda gobe zamu wuce, a abuja muke da zama" Sofiyya tagyara zama, ansamu abunda akeso, nan hira ta 6arke tsakaninsu abinka da masu surutu nan da nan suka saba sosai har aka gamawa Tasleem aka fara yima Sofiyya da Raliya kusan a tare aka gama musu, suka fito tare sunata hirarsu tamkar sun dade dasanin juna, yananan zaune yanata danna wayarsa harsuka fito suka tsaya a gefen titi, ganin tana kokarin tare adaidaita yasa Raliya cewa "kizo muje murage miki hanya mana" Sofiyya tace "no sister bari kawai intare karmu takurwa baban Tasleem" Raliya tayi murmushi tace "bafa dashi mukazoba" Sofiyya taki yarda amma Raliya tanace, adolenta ta yarda suka wuce zuwa inda Abdul yayi parking, yanata danna waya bemasan sunzo wajenba, Raliya tabude ma Sofiyya baya tana fadin "sister shiga" Tasleem tabude dayan gefen tashiga, itakuma Raliya tabude gaba tashiga, se sannan yadago ya kalli Raliya sannan yakalli mirror karaf suka hada ido, dummmmmm suka sakejin bugun zuciyarsu a lokaci daya, Sofiyya tayi saurin janye idonta takoma gyarawa Tasleem hulanta, kamar wacce tatuna da abu tasake dago Kai dasauri, still suka sake hada ido, wannan karon murmushi tasakar mai tace "cutie yayan friend hello, ashe kaine" murmushin shima yayi yana gyda Kai yace "uhmm how are you?" Nodding kai tayi tace "fine, sister ashema kece antyn Usman, yana yawan bani labarinki, dan banma san yana brother na mijiba, koda yake yace is like...." Tunowa tayi agaban Abdul take kuma usman gulman Abdul yakawo mata that day, seta hau girgiza Kai tana fadin "is like nothing because there's nothing" me Raliya zatayi inba dariya ba, shiko gogan murmushi kawai yayi yana tayar da mota, ahaka sukadau hanya, Sofiyya da Raliya se zuba suke, shidai se murmushi kawai yakeyi, se insun sakoshi cikin zancen yace uhm ko hmmm sun danyi tafiya kadan yadan juyo yadan kalleta yace "address" cigaba da bada labarinta tayi dan batama jishiba kwata kwata, Raliya ko tajishi sarai tayi kamar batajiba, ganin haka yasa yadan bude murya yace "your address" shiru tayi sekuma tata6o Raliya tace "sister tell him your address" nanma dariya Raliya tahau yi harda sunkuyawa, neman gefen titi yayi ya Parker motan, Sofiyya ta kalleshi tace "why?" Sekuma tasa hannu tarufe bakinta sannan tabude tace "I'm really sorry wlh nazata motan gidanmu ne muka dauko wata zamu rage mata hanya" me Raliya zatayi inba dariya ba harda kwarewa tahau tari, suna cikin haka wayan Raliya yahau ringing, harta katse bata samu daman daukaba, wani kiranne yasake shigowa tayi kokari tatsaida dariyar tadau wayar "yes, ok ok just 5 minutes please," tagama wayar tajuyo tana kallon Abdul tace "Yaya daddyn Tasleem ne yazo wlh, gashi wai jirgin 3 zamubi, Dan Allah kafara, ajiyeni gida tukun ka karasa da ita,. Sofiyya tace "no just drop me here" duk suka juyo suna kallonta, tadaga kafadanta tace "I just say drop me here, is there anything new in my word?" Raliya zatayi magana taji Abdul yaja motan fewwwww, tsit Raliya tayi dan tasan ransa ya6aci, ita tamayi mamakin duk surutun dasukayi bece zasu samishi headache ba, ok wato abin nashi 'yar warayyace, itama Sofiyya shiru tayi tanata kumbure kumbure, yo Banda kaddara meze kaita hawa motarshi, tundazhi besan wasaba.
A bakin gate yayi parking yajuyo yana kallon Raliya wadda sum sum tabude tafice tazaga tadau Tasleem tana yiwa Sofiyya byeebyee, fita yayi shima a motan yaje kusada Raliya yace "don't say word" sannan yajuyo yashiga motan ya zauna yatayar yana jira tadawo gaba amma yaji shiru, juyawa yayi yaga tawani 6ata fuska, mamakine yakamashi, tome aka Mata? Daurewa yayi yace "there's no driver here if I'm not mistaken, banza tayi dashi, taki yarda ta kalli inda yake, kashe motan yayi yajawo wayarsa yahau danne danne, ganin dagaske batafiya zeyiba yasa a fusace ta bude motan tafita tahau tafiya batareda tasake kallon inda motan yakeba. da mugun mamaki yake binta da kallo, yakasa koda kwakwkwaran motsi balle Kuma yabita, wannan anya lafiyanta kuwa, no did he even look like a driver? Oh female, anan yayita zama yana tunani kozega dalilin dayasa ta fushi but yakasa, Jin kanshi yafara ciwone yasashi tayarda motan yayi horn domin shiga gida.

Gaba daya ranta ya lalace, Wannan wani irin mutum ne? Jifa tace ya sauketa tahau napep ya ignoring dinta yaja mota yatafi da ita can gidansu, who cares to see their home? Harta manta yaushe rabonda ranta ya6aci haka, mtsssss mess.. dahaka tayita tafiya harta fita daga unguwan gashi duk bataga masu napep ba, gashi unguwar da nisa da gidansu, gashi ta6ata lokaci dayawa tasan dole mommy ta questioning dinta, oh God, tsayawa tayi ganin tagaji da tafiyar, takyar tasamu napep zuwa gida a naira 1000, bata damuba tashiga, seda ya ajiyeta kofan gate din gidansu tafito, sannan tanemi jakarta tarasa, yaa ilahee, yau ake wata sega wata, rokon me napep din tayi tashiga tayiwa megadi magana yafito yakawo masa kudin.
A gajiye, rai a 6ace tashiga parlor tabaje kan kujera, mommy da shigarta kitchen kenan tafito tana karemata kallo kafin tace "nadauka ai bazaki dawoba can Zaki kwana" kamar zatayi kuka tace "bazan dawoba Kuma mommy, a shagon saloon din zan kwana?" Tace "oho nasani, aida kinbari nagama shan cornflakes dinnan dasedai kiganni a shagon, inga abinda yatsaidake" tace "mommy layinefa a shagon" mommy tana zama kan kujera tace "shi shagonsu Nancy ne da layi? Karki yadda kimin karya yanzu intashi inje, kindai san halina" kus Sofiyya tayi da bakinta Jin abinda mommy tace, domin tasan mommy yanzu ba abin wahala bane tace suje "karyar banza da wofi, damadai bansanki da shegen surutu ba, zaki fadamin layi" sum sum tamike tace "mommy can I go " banza mommy tamata seda takusa gama shanye cornflakes dinta sannan tace "6acemin anan magananniya kawai" dama jira take a hanzarce tayi upstairs, mommy tabita da kallo can tace "ke dawo" tadawo tana kallonta tace "gani mommy" "Ina jakanki naga kindawo haka? Koba dajaka kika fita bane?" Inda inda tafarayi tace "am.. oh inaga nabarta a can, zankoma inkar6o" wata harara mommy tayi mata tace "wuce kibani guri, banda surutu babu abinda kika iya" dasauri tahaura dan zuciyarta girgiza taketayi, kadan yarage jikinta yadau girgizan shima, tana shiga daki tasauke nannauyar ajiyar zuciya "hmmmmmm Allah nagode maka".
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Join my watsaap group mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Ina yiwa kowa barka da sallah, fatan kowa yayi sallah lafiya, Allah ya maimaita Mana.

Episode 8
A Golden High School after exam, as usual Sofiyya tareda Usman suna hanyar fitowa tace "hope yauma brother dinkane zezo daukarka?" Kallonta yayi da mamaki yace "why?" Tace "why what?" Yace "why asking for him?" 6ata fuska tayi tace "I'm not asking for him I just asked you a question malam" dage kafada yayi yace "to I don't know, may be shizezo may be Kuma no" dasauri tace "please kiramin shi a wayanka" wani kallo yake mata na alamun tambaya kafin yace "wait,, what really happened? Kibani details inji tukun" yafadi hakan daidai lokacin da suka karaso dakalin dasuke Zama,

3 / 26