Chapter 13 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 26

36K to 39K   out of 76.5K words

hana Sofiyya ganin Abdul da akayi, damace dazakayi anfani da ita wurin shiga jikinta har ka mantar da ita wani Abdul"



Shiru munnir yayi yana nazari sannan yayi murmushi yace, "kumafa kinkawo shawara, dana bari ne kawai se randa aka kawomin ita gidana, don tun randa abin yafaru bansake zuwa gidan ba, sedai nakanji yadda ake cikine idan daddy yazo gaida hajjaju"


Zuly tace "aikuwa bahaka yadace kayiba, kagafa koda aka hanata fita akwai waya fa"


Yace "tabbas wayar itace zata lalata mana shiri"


Tace "to ai kaima kanada number dinta why not kadinga kiranta koda ma bakaje gidanba?"


Yace "nooo bahaka za'ayi ba, dabara zamu samo yadda za'ayi a kwace wayarta kawai"


Zuly tace "tabbas wannan shawara tayi amma tayaya za'ayi hakan?"


Shiru yayi yana tunani itama tunanin tahau yi.

Wayarta ne yafara ringing, ganin number din mama yasa tamike tana cewa "mama ce ke kirana, yamma tayi, munnir, yanzu dai kaje kayi tunanin yadda za'a 6ullowa lamarin, nima zanyi tunani zuwa gobe, semuga yaya zamuyi"



Dahaka suka rabu kowa yakama gabansa.



.................


Koda daddy yadawo daga masallaci a falon ya tadda mommy da itama fitowarta kenan, zama duk sukayi domin tattaunawa.


Daddy yace "dagaske yaronnan Abdul yakeyi ashe, wlh nadauka shirmensa ne kawai shiyasa ma ban nemeshi ba"


Mommy tace "ai kaga tabbas"


Yace "yanzu yazanyi da munnir? *


Mommy ta 6ata fuska tace "kamar yaya? Meye kuma munnir? "


Shima 6ata fuskar yayi yace "yakike hakane mardiyya, kamar ban sanar dake yadda mukayi da yaaya ba"


Ta6e baki mommy tayi tace "to amma dai kasan bazaka yiwa Sofiyya auren dole ba ko? "



Yace "ai matsalar kenan, tsakanin shi wannan yaron da munnir bansan waye Sofiyya keso ba"



Mommy tace "bama seka 6ata lokaci wurin tambaya ba, wlh nasan Sofiyya batason munnir, saboda haka karma kasawa ranka wannan"



Daddy ya kalleta da mamaki yace "don Allah meyasa bakyason ahada Sofiyya da dan uwanta aure ne"


Mommy tace "bawai banaso bane, idan itadin tace tanaso ai bazan hanaba"



Girgiza kai kawai daddy yayi, sannan yace "to nidai nacewa Alhaji Gallafi, sudawo bayan sati, kafinnan nasan abinyi, ni bansan yaushe Sofiyya tafara soyayya ba, ina mamaki wlh"



Murmushin jin dadi mommy tayi tace "bawai fa andau lokaci bane, don bayan tasamu wayar nan ne"



Daddy yace "wlh danasan haka wayar zata jawo daban bata ba"



Mommy ta ta6e baki tace "Allah dai yakaimu satin, kafinnan kaikuma sekayi kokarin sanin amsar dazaka basu". Tana kaiwa nan tamike tayi wucewarta.



Da kallo yabita harta shige, ya gurgiza kai yana"hmmm Allah kayi mana za6in alkhairy".......................
'?


Nidai nace amin

Kufa me kukace?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*

By

*Maryam-Ashner*


_*ina mikawa daukacin masoyan Cutie Naa novel gaisuwar sallah, Allahumma ya maimaita mana*_



inkinsan bazaki dingayin sharhi/comment me ma'ana ba kada kimin magana=?L? ba sticker da godiya nakeso ba' addu'a da sharhi/comments masu ma'ana nakeso' inkin shirya shiga group dina sekiyimin magana a 07046767662


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana ds kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Muna saida kowani network if needed=?L?
Call/WhatsApp 07046767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 30

Washe gari bayan sungama breakfast Daddy yawuce office, ikram kuma tatafi school.


Sofiyya na kokarin tashi tanufi daki, mommy tace "zauna muyi magana".

Komawa tayi tazauna

Mommy tace "nasan dai kinsan meya dace dake don yanzu keba yarinya bace, to daddynku ze iya kiranki a kowani lokaci, ze tambayeki waye za6inki tsakanin munnir da Abdul, kafinnan ni inason sanin waye kikeso a cikinsu "



Shiru tayi tana kara sunkuyar dakai kasa tana wasa da wayarta dake hannunta,


Mommy tace "Sofiyya nicefa, inzaki bude baki kimin magana kibude, inkuma shiru zakimin to se insanar dashi yabaki za6inshi kawai"



Tasan waye za6in daddy bewuce munnir ba kuma wlh da abata munnir gwamma tamutu.



Don haka kanta a kasa tace "yaaya Abdul"



Mommy tace "to Alhamdulillah, daga yanzu zuwa kowani lokaci daddynku ze iya zuwa domin tambayarki, dama karki yadda kimishi shiru kamar kurma, inkuwa ba hakaba zaki samu abinda bakyaso"
Takarasa tana mikewa tace "kigyara gurin kafin kitashi"




Murmushi Sofiyya tayi tace "SOFDUL" tana kaunar sunannan wlh fiye da kowani suna.


Mikewa tayi yagyara gurin sannan tawuce dakinta.

Kaitsaye toilet tanufa domin yin wanka, nan tatuna da kanta da yayi datti, tsawon wata guda kenan bata wanke ba.


Tsaki tayi tace "Allah ya isana munnir "


Dahaka tashirya tataho dakin mommy domin neman izinin zuwa saloon.............



................




Munnir daya gama samo hanyar dazebi yasa a kwacewa Sofiyya waya, da murmushi a fuskar sa yadau waya yahau kiran zuly domin sanar da ita.


Koda sukayi wayar tabbas zuly tayi amanna da wannan hanya da munnir yafito da ita, don haka takara masa kwarin gwiwa.



Fitowarsa kenan daga daki yanufo dinning domin yin breakfast, sedai kafin yakarasa yaji muryar daddy yana magana da hajjaju, hakan yasa yadan jabaya ya la6e, don dama haka yakeyi kullum indai yanason jin abinda zasuce.



"Hajiya wannan yaron Abdullahi jiya mahaifinshi yazo domin nema masa auren Sofiyya "



Gyara zama hajjaju tayi tana "a to ai Alhamdulillah, abu yayi kyau kuwa".



Daddy yace "banso hakanba wlh, don naso ace munnir shine wanda ze auri Sofiyya, duk dadai haryanzu bansan wanene za6inta ba, amma....... "



Katseshi hajjaju tayi da "dakata adamu, yanzu dama duk zaman dakukayi da dan uwanka salisu babu amana kenan? Tayaya zakace ahada munnir da Sofiyya aura? Bayan duk gantalin da wannan yaron yajata sukayi lalatarsu, sannan yanzu dan bakason zaman lafiya kakeson likawa jikana sauran wani? "


Tabbas zuciyar daddy ta sosu dajin mummunar furucin da hajjaju keyi, tayaya zata dinga jifan jikarta da mugun kalamai irin wannan? Dondai uwa uwace wlh da baze sake kawo mata zancen akan Sofiyya ba, amma babu yadda zeyi, dole komai seda saninta za'ayi. Kafin yasake magana takara cewa


"Nidai kai da matarka kurufamin asiri ku aurawa wancan yaron diyarku, don gsky bazan ta6a amincewa da wannan lalataccen shirin ba, shikuwa manniru nida kaina zan nemomasa matar aure yar gidan mutunci ahto" takarasa tana barin gurin.





Kukane kawai munnir beyi a gurin ba, iya kuluwa ya kulu, bakin cikine ya mamaye zuciyar sa, jiyake kamar yaje ya shake wuyan hajjaju tadena numfashi a duniya


*mekaratu anan yakamata kagane cewa duk wanda zegina ramin mugunta yagina daidai dashi, inko bahaka ba zefada a abinda yafi karfinsa, gadai munnir yayi sharrinsa yana ganin yaci riba wanda gashi yanzu sharrin dayayi yazame masa sanadin rasa abinda yake buri*




Daddy kam da yarasa abin cewa bayan wasu yan mintuna yamike yayi wuceqarsa.



Bayan yafitane munnir yafito yahau bige bige kamar sabon ta6a66e, yacika falon da karar haukarsa, hajjaju ce tafito a guje tana "nikam adamu kazamemin bala'i a rayuwata, to sokake incuci,,,, "


Tsit tayi ganin munnir a gabanta yana huci, yace "cemiki nayi banason ta dan munafurci zaki ce wani baza'a hadamu aureba? To inkece Allah seki hana mugani, wlh in kikazama sanadin rabuwata da Sofiyya wlh senayi sanadin barinki duniya"



Tabbas ta tsorata musamman furucin sa na karshe ya matukar firgitata, don haka jiki na rawa ta juya tashige daki ta kulle da makulli tana maida numfashi tace "wlh kaine mugun iri manniru, idan ka auremin jika ai zaka iya kasheta, kuma wlh bazaka aureta badin" takarasa gefen gado tazauna tazuba uban tagumi.




Bayan hajjaju tagudu shikuma munnir yadau key din mota tayi waje.

Yaukam ko office dinma bayajin ze iya zuwa, don haka yanufi shagon abokinsa kai tsaye,.


Mall ne Babba, irin namasu hannu da shuni, sam wanda betara kudade ba baze fara zuwa irin gurin nan ba, beta6a zuwa gurin ba, duk dacewa sabit abokinsa ne tun a kano.


Kasancewar Sabit nada fariya kan cewa su masu kudine, hakan yasa zumuncinsu baya daurewa dasun hadu sesunyi fada.

Amma kuma sabit akwai brain, don haka nema yakeda fans ko a school, duk wanda yashiga matsala yakan garzayo gun sabit domin neman solution.


Wani lokaci shawarwarin sabit sukanyi anfani dukda cewa daga baya abubuwa suna kwa6ewa.


Hakan yasa munnir tunkaro shi kai tsaye, domin a yanzu ba shawarar Salim ko zuly yake bukata ba, abin kam yafi karfinsu gaba daya.



..............


Koda Sofiyya takaraso dakin mommy fuskar tausayi tayi kafin tace "mommy kaina ciwo fa"


Kallonta mommy tayi sannan tace "to inzama panadol kenan? "


Girgiza kai tayi tana cire hular dake kanta tace "mommy look yadda kaina yayi datti dakyar nake iya barchi and yau kuma gashi harya fara yimin ciwo" takarasa kamar zatayi kuka.



Mommy tace "to yanzu yaya kikeson inmiki? Bana tunanin akwai shampoo a gidannan balle in wanke mk"



Sofiyya ta 6ata fuska tace "kaiiii mommy yaushe ma zan wani wanke kai a gida? Don Allah mommyna kimin uzuri inje saloon kinji"



Mommy tace "amma dai kinsan banice nasaka miki dokar fita bako? Don haka banice zan baki damar fita ba either'



Zama Sofiyya tayi tana dadayin kalar tausayi tace "mommy please kikirashi don Allah "



Dakyar ta lalla6a mommy takira daddy ta nema mata izini, cikin sa'a kuwa ya amince taje amma tadawo dawuri.



Mommy tace "kinga gashi driver bayanan, sekije kihau napep, kuma ki tabbatar azahar a gidannan tayi miki"



Godiya tayi sannan tafita cikin murna tasako hijab tafito tayiwa mommy sallama tafita.



Tunda yaje office babu abinda yakeyi se tunanin *Cutie*, yau kam dama da mafarkinta yatashi, yayi kewar ganin fuskarta, murmushinta, da shagwa6arta dukda cewa suna waya amma harga Allah shi wlh so yake yaganta ido da ido,.


Ganin yakasa ta6uka komai ne yasashi daukar waya ya kunna data domin suyi kida video call ne, may be yadanji dama-dama, unfortunately bata online, hakan yasa kai tsaye yayi kiran numbern ta.




Sofiyya da isarta shagon saloon kenan ko zama bata Riga tayi ba taji ring din wayarta, neman guri tayi tazauna sannan tabude purse dinta ta zaro wayar.


Murmushi ne ya bayyana kan fuskarta ganin Wanda ke kiranta, babu wani 6ata lokaci kuwa ta daga wayar da fadin.


"Yaayana"


Daga dayan bangaren Abdul ne ya kishingide kan kujerar office dinsa yana juyi hadi da lumshe idanu, najin dadin muryar ta.



" *Cutie Naa*" shima ya furta yana kwaikwayon irin muryar ta,


Dariya tayi sannan tace "ina kabaro aikin kazo kana waya?"


Yace "tunanin ki ta hanani aikin fa, please ki kunna data muyi video call kozan iya yin aikin"


Murmushin jin dadin kalamanshi tayi sannan tace "kaiiii yaaya, nikam bana ma gida fa"


Dasauri yabude ido yana fadin "ina kike yanzu inzo muyi Satan hanya"


Dariya sosai tayi sannan tace "lallai ma yaaya nidai ba ruwana"


Mikewa Yayi yana daukar key din motarshi yace "kinga malama just tell me"


Tace "okay ina wurin saloon nefa"


"Okay" kawai yace mata yakashe wayar. kulle office din yayi yafito yanufi motarshi.


Sabit dake hakimce kan kujera cikin dan office dinsa a mall din, yana danna wayarsa cikin kwanciyar hankali, gani yayi kira na shigowa, daga kai yayi yaduba, waro idanuwa yayi cike da mamakin ganin sunan munnir, dariya sosai yayi kafin ya daga kiran yana
"Dan iska dama baka mutu ba"



Tsaki munnir yayi yana fadin "bansani ba, shege inafa kofar mall dinka"


Mikewa sabit yayi yana cewa
"Kai haba dagaske kake ko wasa"


Munnir yace "wlh dagaske nakeyi, kafito please akwai magana ne"


Sabit yanufo hanyar kofa yana "dama ku ana ganinku ansan da matsala ai, to ganinan zuwa"



Bayan yafito ya taradda munnir a jikin motarshi, da murmushi yakarasa yana mika masa hannu.


Bayan sun gaisa ya jawoshi suka nufi office dinsa domin tattaunawa.


.................. Kai tsaye Abdul yanufi shagon saloon din da Sofiyya ke zuwa, tunda yasan cewa dama nan take zuwa yin saloon din.



Be kira ta ba, har seda ya kusan awa a gurin, sannan yadaga waya yahau kiranta.


Kiranshi yayi daidai da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sanya hijabin ta, domin yanzun aka gama mata.


"Harfa angama nashirya zan tafi" tafada kamar zatayi kuka domin a tunanin ta bezoba tukunna.


Shima yi yayi kamar zeyi kukan yace "Harfa nayi kusan awa ina zaman jiranki"



Dariya yake bata duk sanda ya kwaikwayi muryar ta,.

Katse kiran tayi sannan tayi sallama da yan shagon ta fito.


Tunda tafito yake kare mata kallo, duk da kuwa babu abinda yake gani se fuskarta, beta6a ganin ta da hijab ba, inba na makaranta ba, hakan yasa yakara ganin kyanta dakuma mutuncin ta fiye da kullum.



Da murmushi a fuskarta as usual, don shi ze iya cewa ma beta6a ganin fushinta ba.


Kafin takaraso ya fito ya zaga ya bude mata dayan gefen yana fadin "bismillah my ustaziya"


Dariya tayi sannan tawuce tashiga tazauna, shima zagowa yayi yazauna.



Batareda 6ata lokaci ba ya tada motar yanayi yana kallonta, itakam takasa hada idanu dashi, don tun randa furta yana sonta basu kara haduwa face to face ba seyau.

Duk da suna shan soyayya iya soyayya a waya amma yau data ganshi setaji wata sabuwar kunyarsa ta lullu6eta.



"Yau kuma ustazanci akeji kenan" ya breaking silent din da fadin hakan.


"Uhm dama fa ni ustaziya ce" tabashi amsa tana dada dukar da kanta kasa.


"Banta6a ganinki cikin hijab ba seyau, kuma kinfi kyau sosai a hijab din"


Sosai take murmushi amma takasa cewa komai

"Wai duk Ina maganarki ta tafine? Yau kinki yimin hira"


Cuno baki tayi tace "ni nadena surutu fa"


Ganin sundau wata hanyar daba gidaba yasa ta cewa " yaaya ina kuma zamu? "


Yace "sai daki zanyi"


Langwa6e kai tayi tana "don Allah yaaya muje gida, kaga fa dakyar mommy tabarni na fito wlh"



Yana cigaba da tuki yace "it will not take long time, please ikram kawai zan saiwa chocolate"


Shiru tayi suka cigaba da tafiya, itadai a ranta zata iya cewa duk randa ya daukota daga wani guri baya ajiyeta gida direct dole seya kaita gurin siyayya yajido mata kaya, but today kam baza ta yarda tadau kayan da za'a gane sun haduba, yadda yace chocolate to chocolate din kawai zata dauka.



Direct Mall din sabit ya wuce da ita...................
'?



Koyaya zasu kare?
Kozasu hadu da munnir?
To meze faru kuma?

Kubini sannu a hankali, gameson shiga group dina seya tuntu6eni a lamba kamar haka 07046767662 =?L?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*

By

*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana ds kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Call/WhatsApp 07046767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 32

Daddy na dawowa beshiga daki ba yazauna a parlo, duk gidan babu wadda yasan yadawo, har akayi magriba yafita masallaci, tunda yaje masallacin bedawo ba har seda akayi isha'i yadan jima a masallacin kafin yadawo.


Yasame su duka a dinning har sunfara dinner, kujera yaja yazauna, mommy ce tafara gaidashi sannan Sofiyya da ikram, duk ya amsa as usual sannan suka cigaba dacin abinci.


Bayan sungama ne sunkoma parlo daddy ya kalli Sofiyya tace "Sofiyya jeki kawomin wayar ki"


Dammm gabanta yafadi tadafa kirji tace "daddy wayata kuma"


Dagowa yayi ya kalleta silently yace "eh wayarki ki kawomin "


Jiki a sanyaye tamike ta haura ta dauko ta kawo mishi takoma tazauna tana jiran jin abinda zece.



Mommy ma batace komai tana sauraron karin bayani daga gurin daddy.


Tunda daddy ya kar6a wayar ya kashe ta becewa kowa komai ba, danne dannen wayarsa yake, bayan 'yan mintuna kuma yamike yayi musu sallama dacewa yau yagaji sosai don haka zeje ya watsa ruwa ya huta.



Yana tafiya Sofiyya ta matso kusa da mommy tana "mommy don Allah me nayi"



Ta6e baki mommy tayi tana mamakin dalilin dayasa daddy kwace wayar Sofiyya tace "oho ni ina nasani? "



Kuka tafashe da,

13 / 26