CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 26

45K to 48K   out of 76.5K words

bugu irin bugun dabe ta6a jiba a tsawon rayuwarsa.



Har suka kai gurin da akayi decorating da sunan Sofiyya sannan munnir yaja mata kujera tazauna kafin yace tabude ido.



"Wow" tayi karfin halin furtawa duk da yadda takejin zuciyar ta na mata wani irin zugi.


Tabbas gurin ya 'kayatu matu'kar kayatuwa amma ita sam bataga kyawun gurin ba, hasalima takaicin ganin abinda yayi tayi, amma sam bata nuna ba, sedai tayitayin murmushin yake.



Duk wani abun ci a gurin Sofiyya taki ci, duk kuwa kokarin ta naganin taci din amma jitake kamar idan tasaka a baki zatayi amai ne.



Duk wani kokarin munnir na ganin Sofiyya tasaki jiki taci wani abu abun ya citura, daga karshe ma cewa tayi kanta ciwo yake sukoma gida kawai.




Tunda suka wuce idonshi na kansu, kuma haryanzu dasuka mike domin tafiya bedauke idonshi a kansu ba.


Yazama kamar mutum mutumi, he is shock to the extend da bayama fahimtar komai,.



Tunda suka tashi tafiya idon Sofiyya a kasa yake, tarasa dalili tunda suka zauna takeji a ranta inhar tajuya abinda zata gani ze iya karasa tarwatsa sauran nutauwar data rage a tare da ita.



A yanzun ma suna tafiya domin fitowa taki yarda ta dago idonta domin abinda takeji besauya ba.



Sunzo Daidai inda Abdul yake taja tatsaya kamar wadda aka riketa, zuciyar ta, na bugawa da sauri da sauri, damke idonta tasakeyi sosai, yayinda hawaye ke zubowa zuwa kan kumatunta.




Abdul da idonshi yacika da kwalla, yaji kamar wani abu yata6a shi daya sashi dawowa cikin hayyacinsa, bakinsa na rawa ya ambaci sunanta "SOFIYYA"



ambaton sunan nata yayi daidai da zubowar hawayen dake makale cikin idanun shi.



Itakuwa a razane tabude idonta, sakamakon sunanta dataji an ambata, tunkafin taji muryarsa zuciyar ta ta dade da sanar da ita cewa yana gurin, amma jin muryarsa ya dada tabbatar mata da abinda take tunani.



Tunda take dashi bata ta6aji ya ambaci sunanta ba seyau, kuma sunan seyafi fita dakyau da dadi duk da cewa bawai da farinciki yafadi sunan ba.



A hankali tasauke idonta kasa akan Abdul, ido suka kurawa juna duk suna hawaye.


Munnir kuwa tunda yaga Sofiyya ta tsaya a gaban Abdul yake jiran yaji ta zazzaga mishi rashin mutunci amma seyaji shiru, matsowa yayi domin ganin metakeyi, ganin duk su biyun sun kurawa juna idanu gakuma hawaye a idanun su duka yasa jikinshi yin sanyi.



Gyaran murya munnir yayi sannan yace "muje ko"


Babu musu Sofiyya tawuce Abdul batare da ta waiwayeshi ba, shima haka yabita da idanu kamar wawa harya dena ganin su.




Tunda suka dau hanya babu wanda yayi magana a cikinsu, itadai hankalinta baya jikinta gaba daya, burinta suje gida tasamu tayi kuka kozataji dadi.



Shikuma munnir ya rasa meke yimasa dadi, a ransa ko fadi yake "kenan har yanzu tana son yaronnan " tambayar daya dinga yima kansa kenan har sukazo gida.



Ko gidan beshiga ba yana sauketa yajuya yabar gidan, a parlo ta iske mommy zaune kan kujera.



Da isarta ta durkusa gaban mommy tana "mommy dan girman Allah kibani aron wayarki koda 5minutes ne inyi don Allah "


Kallonta mommy take cike da tsoro, domin a zatonta sunyi fada ne da munnir tazo tanason ta kirashi tabashi hakuri, gashi duk taga babu nutsuwa a tare da ita, don haka tace "tashi kibani guri bazan bayar ba"



Babu musu tamike jiki a sanyaye tanufi dakinta.


Mommy kuwa hankalinta yafara tashi da al'amarin Sofiyya da munnir, ta tabbatar akwai wani abu don yadda akalar Soyayyar Sofiyya tajuya lokaci daya daga kan Abdul tadawo kan munnir abin baze zama haka kawai ba.



Tabbas akwai bukatar ta tsaya sosai da addu'a, inta kama tanemi taimakon malamai ma zatayi, koda sauka ne ayi domin a kubutar da Sofiyya.



Tunda tashiga dakin take tikar kuka kamar ranta ze fita, safa da marwa takeyi tana sambatu "wlh tallahi banason munnir har cikin zuciya ta na tsaneshi, yaaya don Allah yazanyi ka fahimce nj, nashiga uku ni Sofiyya"



Haka tayitayi har seda taji kiran sallahr magriba sannan dagudu ta nufi toilet don se a lokacin ta tuna cewa rokon Allah yakamata tayi don neman mafita...................
'?




Gameson shiga group dina seya yimin magana ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_



_*TALLA*_
Akwai turaren humra me kamshin kwantar da hankali dakuma kama jiki. Muna maraba da masu siyan daya daya ko sari. Dakuma masu talla ta online abasu a farashin sari sukuma sukara nasu akai, in ansamu me siya sucire ribarsu=?L?
Mace seda kamshi, game bukata yayi magana ta 07046767662 kokuma chat ta Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 36




Tunda yake beta6a mummunan gani irin wanda yayi a yau ba, yadda suka tafi suka barshi idanun shi na zubda hawaye, haka nan yayi ta zama yana hawaye harma hawayen ya kafe yadena zubowa sedai kukan zuci.




Zaune yake kamar wanda aka dasashi a gurin, babu abinda ke yawo a zuciyar sa se photon Sofiyya da munnir, abun se dawo mishi yakeyi tundaga shigowar su, har zamansu a gurin dakuma tasowarsu da tsayuwar Sofiyya a gabanshi.


Zuciyar sa se bugu takeyi kamar ganga, yakasa motsawa balle yatashi yatafi, har aka fara kiraye kirayen sallahr magriba yananan zaune kunnuwansa babu abinda suke jiyo masa se sautin muryar munnir a lokacin da yake kiran Sofiyya "sweetheart"



magriba tayi har gari yafara duhu, wadanda suke zazzaune a park din duk sun watse, me gyara gurin ne yazo domin yin aikinsa, yagama gyara gurin yazo futa yaga Abdul kamar yadda yashigo yasa meshi, haryayi gaba, sekuma yadawo baya ganin kamar mutumin baya motsi, tsugunawa yayi a gabanshi sannan yace "hey are you okay "



Firgit Abdul yadawo daga duniyar daya tafi girgiza mishi kai kawai Abdul yayi batare da yayi magana ba.



Mutumin wanda cristian ne yasake cewa "are you waiting for someone"

Nan ma Abdul girgiza kan yasake yi, kafada mutumin ya dage alamun kai kasani. wayarsa ce tafara ringing har seda ta katse bedauka ba, juyawa yayi yadauko wayar "subhanallah" ya furta ganin har karfe 7:30pm har ankusa yin isha'i bude idonshi yayi yaga gari yayi duhu.



Dasauri yamike domin tafiya amma seyaji kanshi ya sara mishi, jiri yana kokarin yar dashi kasa, dasauri yasake komawa yazauna dafe da kanshi yana furta "innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun"



Ganin lokaci naci gaba da tafiya yasashi mikewa yana dafe da kanshi a hankali yafara takawa idan yaji jiri seya tsuguna inya danji dama-dama seya cigaba da tafiya.



A haka harya kai motarshi yabude yashiga yakife kanshi jikin staring motar , yafi minti 10 ahaka sannan dakyar ya tada motar a slowly yafara tuki.




Tun wuraren 6:30 umma taga Abdul bedawo ba tafara daluwa amma dai ta daure, bayan ta idar da sallahr magriba ne tadau waya domin kira taji ko lafiya amma ba, a dauka ba, cigaba da kiran wayar tayi amma ba'a amsawa.



Hankali tashe takira Abba tasanar dashi domin Abdul baya ta6a wuce magriba bedawo ba, inma akwai inda zashi to tabbas zefara sanar da umma kafin yatafi koda a waya ne.



Abba ma kokarin kiran sa yadingayi amma ba'a amsawa, hakan yasa kai tsaye yadawo gida yafasa zuwa anguwar dayayi niyyar zuwa.



Tuki yake very slowly dama yaya bare kuma ga dalili, se wuraren 8:30 yasamu damar karasowa gida, bayan yayi parking ma yafi mintuna 10 kafin yafito yana takawa a hankali yashiga cikin gidan, kamar wanda aka sallamo daga gadon asibity begama warkewa ba haka yake takowa harya shigo cikin parlon.



Da hanzari umma ta mike tazo gareshi tana rike hannunshi tana "innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun dama nasan ba kalau ba wlh"



Abba da dama ba a zaune yake ba yana tsaye ne yana kaiwa da komowa, ya taho dasauri shima yakama dayan hannunshi yana fadin "meya farune Abdullah? Hatsari kukayi ne? "



Besamu amsar tambayar sa ba har suka dangana shi da kujera suka zaunar dashi, Usman dake zaune yamike yaje yakawo masa ruwa, babu musu yakar6a ruwan yafarasha. Yassha dayawa saura kadan ya shanye sannan yacire kofin a bakinsa usman ya kar6a ya ajiye.



Yadanji sanyin ruwan har cikin zuciyar, lumshe idanunsa yayi, a lokaci daya kuma ya bude idon domin babu abinda ke bayyan inba hoton su Sofiyya da munnir ba.



......,. Daren ranar dai mutane dayawa barchin beyi musu dadi ba, wasu kuwa basuma samu damar yin barchin ba kamar Sofiyya da Abdul dasuka kwana addu'a, ita tanayi tana kuka, shikuma yanayi kanshi na sarawa.



Munnir kuwa tunane-tunane yadinga yi yarasa wanne ze dauka cikin tunanin dayake yi, tabbas yasan Sofiyya har yanzu tanason Abdul amma zeyiwa daddy magana tunda dai tahakura da Abdul din zece kawai ayi ayi auren nan inyaso shizesan yadda zeyi ya mantar da ita kowa ma ba Abdul, da wannan tunanin dakuma murmushi a fuskarsa yasamu yayi barchi.



Abdul kam da zazza6i mezafi yatashi, sannan sam yaki sanar da kowa damuwarsa yabarwa zuciyar sa komai sedai addu'a. Dayake yi kawai, dakyar ya lalla6a yayi sallah a gurin kuma yadan kwanta nan barchi yayi awon gaba dashi.



Itama Sofiyya bayan tayi sallah ciwon kai yasakota a gaba don haka tasha magani ta kwanta nan barchi yayi awon gaba da ita.





............. Yau kwana 3 kenan da faruwar duk wannan abun, tsawon kwanaki ukunnan sam Abdul baya fitowa ko parlo kullum a daki yake wuni, abinci ma sedai abishi dashi daki, kuma ko ankai mishi se umma tayi da gaske kafin yake samu yaci.



Duk tunanin shi Sofiyya ta canza, harma beso yau din tayi ba don yana ganin idan Abba yaje daddy zece abawa Abdul hakuri don Sofiyya bata sonshi Munnir takeso.



A tsorace yake yau din, yana shakkar jin amsar da Abba zezo da ita don haka tun safe yaketa addu'o'i da karatun kur'ani.



Sofiyya kam da farinciki ta tashi domin tasan yau Abban Abdul zezo, kuma insha Allah yau ne za'a dawo mata da wayarta.



Daddy na shirin fitowa domin yin breakfast mommy tace "Daddy yau nefa bakinka zasu dawo ko?"


Murmushi yayi yace "eh yaune, sedai amsar dazasu samu bazata yimusu dadi ba banji dadi ba don mr Gallafi mutumin kirki ne wlh"

Mommy tace "kamarya yalla6ai? Wace amsa zaka basu haka"


Daddy ya kalleta yace "a mtsayinki na mahaifiyar Sofiyya baki karanci sauyinta ba? Dan gidan hajiya yayi nasara ai yanzu kam shi takeso" yakarasa yana 'yar dariya



Mommy tace "hmmmm daddy kenan duk da haka dai bekamata a yanke hukunci batare da anji ta bakinta ba, kasan sha'anin yara kada tazo tayi kuka damu"



6ata fuska daddy yayi yace "wani irin kuka kuma mardiyya, naji zanji ta bakin nata, duk dai rashin sonki da hadinnan da ikon Allah se anyi" yana kai nan yayi gaba abinshi.


Mommy ma binshi tayi da tarin tunane-tunane a ranta dakuma fargabar amsar da Sofiyya zata bayar.





Munnir ma da farinciki ya tashi, domin 2days back yasamu daddy da maganar ayi ayi aurensu, amma daddy yace mishi yayi hakuri tukunna ya sallami iyayen Abdul sannan zekira babanshi suyi magana.


Yanzu kam yarage zuwa gidan domin tunda yaje washegarin ranar da suka fita Sofiyya taki sakewa dashi tace kanta ke ciwo yadena zuwa da safe sedai da yamma sukeyin dinner tare.



Bayan sungama breakfast daddy yadubi Sofiyya yace "first born inaso ki nutsu zan miki wata tambaya"



Da murmushi a fuskarta tace "ok daddy" don koba'a fada mata ba tasan meza'a tambayeta.



Kallon mommy yayi yace "kidan bamu guri domin ganinki ze iya sa positive yazama negative"



Sam bataji dadin yadda daddy ke yimata magana babu dadi akan munnir ba, amma haka ta mike tanufi dakinta.


Ko Sofiyya bataji dadin kalaman daddy ba, amma dai bata nuna ba................
'?



Gameson shiga group dina setayi min magana ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_



_*TALLA*_
Akwai turaren humra me kamshin kwantar da hankali dakuma kama jiki. Muna maraba da masu siyan daya daya ko sari. Dakuma masu talla ta online abasu a farashin sari sukuma sukara nasu akai, in ansamu me siya sucire ribarsu=?L?
Mace seda kamshi, game bukata yayi magana ta 07046767662 kokuma chat ta Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 37

Daddy ya kalli Sofiyya da kanta ke sunkuye yace "first born kinsan babu wani abinda iyaye zasusowa ''ya'yansu yazama ba mekyau ba, karki biyewq mommynki duk abinda ke ranki shizaki fada min idan na tambayeki kinji"



Girgiza mishi kai tayi aranta kuwa fadi take "daddy i'm sorry but i hate munnir wlh"



"Tsakanin munnir da wancen yaron Abdul wa kikeson kasancewa dashi? "


Kai tsaye batare da ta dago ba tace "Abdul"



Wani banzan kallo daddy ya watso mata sannan yace "kinga banason shashanci, munnir fa dan uwanki ne Sofiyya meye laifin yaronnan, tunda yataso yake dawainiya da sonki amma tashi daya kiwani ce Abdul, yaushe kika sanshi harda zaki wani like mishi haka? Zanbaki last chance kije kiyi tunani dakyau kiga wayafi dacewa dake, don kar ki cuci kanki, inma zugaki akeyi ki ajiye wannan zugar a gefe idan nadawo zan sake tambayar ki ". Yana kaiwa nan yamike yanufi kofa yana mita.




Itama Sofiyya mikewa tayi tanufi dakinta harda dan tsallenta take fadin "kayi kadawo daddy ayita takare wlh amsata bazata canza ba Abdul zankuma cewa" ta karasa maganar ta tana shigewa daki.




Abdul sam yarasa nutsuwarsa, yau harwani karfi yasamu se kaiwa da komowa yake acikin dakin, zuciyar sa se bugu takeyi domin besan amsar da Abba zedawo da itaba, tun asuba bekoma barchi ba se left right yake kamar sabon soja.



Knocking akayi yabada izinin shigowa, usman ne yashigo ya gaidashi bayan ya amsa ya masa yajiki sannan yace "Abba yace kaje yanzu don yayi lattin fita yana jiranka a parlo"



Gyada mishi kai kawai yayi sannan yamike dama jallabiya ce a jikinshi yasanya takalmansa kawai yabi bayan usman.


A parlo ya tadda Abba tsaye yana waya, umma kuma tana zaune kan kujera shikuwa usman nacan dinning yana zuri na biyu ba wasa da ciki lol.



Gefen da Abba ke tsaye yaje yazauna a kasa yana gaidashi, bayan ya amsa sannan yajuya yagaida umma duk sukayi masa yajiki yace dasauki.



Umma ce tafara cewa "Abdul ka fadamin gsky kodai irin ciwon mahaifin ka ne yasameka? Tunda naka yanayin ciwon naku iri dayane kaga indai hakqne yanzu yazama wajibi munemi magani"





Girgiza kai Abdul yayi yace "a, a umma nama farajin sauki fa gobe ma insha Allah zankoma office ".



Abba da gama wayar sa kenan yanemi guri yazauna, yace "nima dai nakusa warkewa inhuta, kuma ciwon ai badashi aka haifeni ba balle yagado, ke nifa bawani ciwo ma dake damuna"



Usman dake kai loma yace "Abba aikai kama warke ko insha Allah "



Abba yace "insha Allah kuwa yaron Abba "

Duban Abdul Abba yayi yace "yau zan koma gidansu budurwarka inji mezasu ce, inason daga office inwuce kuma sonake idan har sun amince kawai inbada sadaki don banason auren yadau wani dogon lokaci"


Nan take zuciyar Abdul tabada sautin dummmm a ranshi yace "intana sona haryanzu ba"


Numfasawa yayi sannan yace "to Abba Allah yasaka da alkhairi "



Amin yace yatashi yayi musu sallama yatafi office, umma ce tadubi Abdul tace "kuma haryanzu kanason yarinyar nan Abdul? "



Murmushi kawai yayi wanda hakan yabawa umma damar samun amsarta, itama murmushin tayi tace "to Allah yasanya alkhairi"..



"Amin" yafurta a hankali sannan yamike yanufi daki, da shigarsa yadaura alwala yahau karatun alqur'ani duk surah inyakai seya tsaya yayi addu'ar samun nasara a zuciyar Sofiyya.

Shi har mamaki yake yadda zuciyar sa ke masifar sonta subhanallah wai yama akayi yayi zurfi a kaunarta har yakeji inya rasata kamar rayuwarsa zata ruguje? Imagine don kawai yaganta da munnir yadda ya rikice harma baya iya fita office???.


Cigaba da addu'a yayi har seda yaji zuciyar sa tasanar dashi cewa da izinin Allah zeyi nasara yaji sanyi sannan fargabar dayakeyi taragu cikin zuciyar sa, a yanzu babu abinda yakeso illa yaji sallamar Abba.




Munnir kam yau duk wadda ya kalleshi seya fahimci farincikin dayake ciki, washe baki yadungayi dazaran yatuno da abinda daddy yafada masa sedai yaga yana dariya kamar sabon ta6a66e.



Ta 6angaren Sofiyya kuwa bayan tayi barchi tatashi tayi sallahr azahar nishadin datakeji yawuce misali don haka tasauka kasa tanemo tashar da ake saka wakoki ta kure volume tanayi tanadan takawa, ahaka mommy tafito tasameta tace "sannu yau kuma shedan kikeji"



Murmushi Sofiyya tayi tanemi guri tazauna tace "mommy bahaka bane fa kawai dai yaune"



Mommy tace "yaune me? Hmmmm nasan daddynki ya tambayeki kuma me kikace masa?"



Tana murmushi tace "Abdul nace mana mommy "



Tunda daddy yace tatafi taketa addu'a Allah yasa kar sofiyya tace munnir takeso Alhamdulillah Allah ya amsa rokona tafada cikin ranta.



Murnushi mommy tayi tace "to kin kyautawa kanki ai yayi kyau"


Sofiyya ta cuno baki tace "Amma daddy yace wai insake tunani kafin yadawo wai yabani last chance"



Wani murmushin mommy tayi tace "duk yadda za'ayi karki fadi abinda bahaka ne a zuciyar ki ba"


Itama cikin murmushi tace "insha Allah mommy".


Dahaka taci gaba da jin wakokin ta, mommy bata hanata ba tamike tanufi dakinta.


8:03 daddy yashigo gidan daga masallaci, duk fuskarsa a daure haka sukayi dinner, suna gamawa

16 / 26