Chapter 11 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 26

30K to 33K   out of 76.5K words

daga labulen hade dayin sallama.


Mustapha dake zaune kan kujera, ya tallafe kansa da tafukan hannayensa, kansa a sunkuye, batare da yadago ba ya amsa sallamar ta.

Zuwa tayi ta zauna gefansa, dayake a two seater yazauna.

"Baban siddika meya faru da antynsu? Tunda najiku shiru nasan akwai matsala"



Dago da kanshi yayi yadubeta yace
"Hmmm lallai baraka harma kina iya tambayata, yanzu abinda kikeyi yadace, koda ace hafsat iyayenki ta kashe iyakacin hukuncin dazaki mata kenan, hmm amma bakomai duniya ce"



6ata fuska tayi tana " kaidai bakason zaman lafiya wlh, danma Ina tambayar jikinta shine har kake wani mita, to me kakeso inyi bayan abinda nayi"


Girgiza kai yayi yana mamakin bakin kishi irinna Baraka, can yace

"Girma da mutuncin da hafsat ke ganinki dashi yafi gaban wannan halin KO inkula da kika nuna a kanta, adaidai lokacin datake bukatar kulawa daga maku santanta"


Mikewa tsaye baraka tayi cikin masifa tace
"Wani mutunci da girma yarage wanda bata baniba, bayan tabi duk wata gur6atacciyar hanya wurin aurenka ai dole kace haka"


Girgiza kai kawai yayi, jin sallama sukayi hakan yasa baraka fitowa don jin wanene.


ganin Binta (kawar hafsat tilo a suleja) yasa taja dogon tsaki tana harararta tawuce tacigaba fa wanke-wanken ta.


Baban siddika ne yafito nan Binta tahau gaidashi.

Bayan sungama gaisawa ne kuma Binta tace "don Allah amarya batanan ne"


"Wlh tana asibiti" inji mustapha.


Zaro idanu tayi cike da damuwa tace "haihuwar ce? "

Yace "eh ta haihu Dan bezo darai ba"


"Allah sarki wani asibiti take"

Nan yasanar da ita tace "bari inkarasa girki zanje induba ta insha Allah"


Yace "to badamuwa"


Baraka dake wanke-wanke tanaji tace "munafika"


...........................................


Motan daddy tayo kwanan makarantar, daga dayan 6angaren kuma Motan su Abdul tayo kwanan makarantar.

Seya zama Motan daddy na gaba Motan su Abdul nabin bayanta.


Hajjaju da munnir yagama ingizawa tamike tace "wlh yau koni ko Mardiyya a wajennan, waishi Adamu Ina yatsaya ne, kai manniru zomuje can musameshi"


Gaba tayi munnir na mara mata baya.

Mommy jin siddika shiru haryanzu bata dawoba yasa tanufi waje itama, a hanya suka hadu da su munnir, hajjaju ta galla mata harara,.
Mommy dai batayi magana ba tayi wucewarta.



Siddika na magana da bashir ta hangosu mommy, rikicewa tayi tana "nashiga uku yau"

Bata rufe bakiba ta hango daddy na fitowa daga mota.


Kafin yataho har sunje gun motar sun tsaya, cikin tashin habkali daddy yace "meyake faruwa ne? "


Hajjaju tabude baki dashirin yin magana motar su Sofiyya tashigo gurin.



"Innalillahi wa inna ilaihir raji'uun, kungansu can yadawo da ita" inji hajjaju


Duk kallon inda hajjaju ke kallo sukayi


Tadaura da "dagani wannan ba mutumin kirki bane wlh"


Bayan Abdul yagama parking yadauko duk abubuwan daya kawo mata as a gift yabata, dafarko kin kar6a tayi, seda taga beji dadi ba sannan takar6a.


"Nagode" ta furta tana bude kofar motar.

Tana fitowa tayi tozali daduk familynsu, dummm gabanta yafadi.


Daurewa tayi tafara tunkarosu tana karewa fuskokinsu kallo.


Tabbas akwai matsala, zuciyarta tafada mata.


Bayan ta karasone Hajjaju tasaka kuka tace "yanzu Adamu har lalacewar yarka yakai tabi saurayi ya kashe mata kudi amma baka ta6a fadamin ba"


Daddy yasan halin Hajjaju sarai, yanzu seta tara musu jama'a agurin don haka yace


"Hajiya kiyi hakuri shiga mota muje gida ninasan mezanyi"


Bashir kam rike baki yayi yana mamakin furucin da Hajjaju tayi.


Duk shiga mota sukayi suka dau hanyar gida.

Bashir kuma yanufi gun motar Abdul..................
'?


Kuyi hakuri da wannan plzzz i will make it up to you next episode =?O?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By


*Maryam-Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Don ALLAH mata zallah=?O? kuma inkinsan bazaki dinga sharhi ba kada kishigo=?L? ba sticker da godiya nakeso ba' addu'a da sharhi me ma'ana nafi bukata'.


_*TALLA*_
akwai datan siyarwa mesauki kuma me lasting game bukata
MTN
500MB = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Call/WhatsApp 07046767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 28

Bugu biyu tadauka dasauri tana "Yaaya ina kake ne? Meya faru? Dawa kukayi fada?"

Seda yaciro wayar daga kunnensa yaduba ya tabbatar itadin yakira, a ransa yace "anya yarinyar nan nitake son kira kuwa, kodai mistake tayi? "

Maida wayar kunnensa Yayi yace "kinsan wa kika kira kuwa?"

Jin muryarsa lafiya lou yasa tasauke ajiyar zuciya sannan tace "yanzu dai kana inane yaaya? "


Yace "ina hanyar zuwa gida, don bazan koma makarantar ba ni, hope dai lafiya?"

Tace "toshikenan seka dawo, muma aituni muka dawo gidan"

Katse kiran yayi, sannan yahau kiran anty zainab, itama kamar jira take dasauri tadauka, yadda Raliya tajero mishi tambayoyi a rikice hakama anty zainab tajero mishi, abindai yafara bashi tsoro, to dama meze sameshi?

Begama bata amsaba Umma takwace wayar a hannun Anty zainab tana "Abdullah duk inda kake kazo gida yanzu inason ganin ka"


Nan zuly taji tsoron Abdul yadawo yasameta ace itace tabada labarin karya don haka tacewa Anty zainab "Anty naturawa Mama sako amma tayimin reply wai intaho gida yanzu inyi aiki don batajin dadi"


Anty Zainab, tace "Allah sarki toba komai ai, Allah yabata lafiya"
Tafada tana ciro kudi cikin jakarta, 500 tamika mata tace "gashi kihau napep kikoma yanzu, sannan kice ina gaidata sosai, idan nadawo dawuri zanshigo indubata, inkuma bandawo dawuri ba se da safe nashigo"


Kar6an kudi tayi tace "to anty skin dawo, Allah yadawo da yaaya lafiya"


"Amin" umma da Anty zainab suka fada.

Dahaka tawuce tafita tahau tare adaidaita, bayan tasamu tashigane tadau wayarta tahau kiran munnr.



Abba da fitowarshi kenan daga daki zashi masallaci. Yabisu da kallo daya bayan daya.



Ganin kamar akwai matsala ne yasashi zama kan kujera yana dada nazartan fuskokinsu.

Da mamaki usman ke kallon Abba, tasowa yayi yazo yazauna kusa dashi yace "Abba yaushe a gari? "


Kallon umma Abba yayi, itakam kautar da kanta tayi tana mikawa anty zainab wayarta tayi wucewarta daki.


"Ina yini Alhaji" inji anty zainab

"lafiya lou zainab, yagida ya megidan naki? Munjima bamu hadu ba wlh, harkoki sunyi yawa"


Anty Zainab, tace "wlh abinne se a hankali ba'a samun lokaci ne yanzun"


Abba yace "aikuwa se a hankali, wai meke faruwa ne a gidan"


Usman ne yace "Abba dukda kaki kulani amma zanfada, Yaya ne wlh yayi wani wawan tuki dazu da mugun gudu, to bamusan dai meyake faruwa dashiba shine muke zaman jiranshi"


Shikanshi Abban seda yaji damuwa tasaukar masa, duk da halin damuwar dayake ciki amma seda hankalin shi yatashi.


"Yanzu ina yake?"


Anty Zainab, tace "munyi waya dashi yanzu yana hanyar dawowa"


Abba yace "toshikenan bari inje masallaci indawo kafinnan yadawo"


"Adawo lafiya" anty zainab da usman suka fada a tare.


,..................


Suleja
Tunda ta farka take hawaye, ga bakin cikin rashin dangi da gatan datake ciki, gakuma rashin jaririnta, wanda taketa faman jiran zuwansa, don koba komai zedinga debe mata kewa, zezama aboki mafi kusa da ita, yanzu gashi shima tarasashi sanadin muguwar abokiyar zama.


Kuka tafashe dashi me ban tausayi, binta dake kusa da ita tanata faman lallashinta.


Shiko Mustapha kasa zama yayi a dakin don haka yayi ficewarsa.

Koda yafita wata kujera yasamu yazauna, tunanin yadda rayuwar hafsa take yafara, tundaga haduwarsu har zuwa auren su dakuma halin bakar rayuwar da ayau ta tsinci kanta.


Hawaye ya goge sannan yacigaba da tunanin yadda suka kwashe da Baraka, babu yadda beyi da ita ba akan tazo suje asibiti kememe taki yarda harda cewa "in inna tashirya zasuje tare" bayan tasan inna bazuwa zatayi ba.

Haka yayi juyin duniyar nan kan ta dafa musu abinci amma sam taki, "wannan wacce irin kiyayya ce? " banda Allah yakawo binta tataho da abinci da sedai yaje yasiya mata na siyarwa.


Baraka ba dadi, inna ba dadi "Allah sarki" a furta a fili


tunowa yayi da wayar da sukayi da yayanshi hakan yasa cikin hanzari ya lalubo wayarsa dake aljihunsa yahau kiransa yana fadin "Allahu yasa andace"



Harta katse be daukaba, beyi kasa a gwiwa ba yasake kira, Harta kusan katsewa sannan yadauka.


Bayan sun gaisane yace
"Yaya najika shiru kuma"



Shirun yayi sannan daga baya yace "mustapha kudai Kara hakuri tukunna, haryanzu dai ba'a dace ba"



"hmmm dama wlh banyi tsammanin za'a dace dinba, bakomai yaaya se anjima"


Wani ninkin tausayinta ne yakaru cikin zuciyarsa. "Allahumma kakawo dauki wa wannan baiwar taka" yafada a fili sannan yamike yakoma cikin dakin.


......................


shigorwa Abdul kenan da sallama a bakinshi bashir na binshi a baya, ganin Abba yasashi yin turus, a hankali yakarasa yannufi inda Abban yake yazauna a kasa, Bashir ma hakan yayi.



Gaishe da Abba sukayi ya amsa sannan yace "naji duk abinda yafaru, kuma na yanke hukuncin karabu da yarinyar nan"

Mamaki ne yakama Abdul dajin furucin da Abba yayi, to wacce yarinyar yake nufi?


Kafin yayi magana Anty zainab tace "kaga yaro munsan komai zuwa yanzu, ita wadda kakeso din yaudarar Dan uwan nata tayi kaga inkai aka yaudara aibaza kaji dadiba KO? "



Bashir ne yace "kuyi hakuri nashiga maganar family but muna bukatar Karin bayani akan abinda kuka fada please "



Anty zainab ce ta karanto musu duk abinda zuly tafada akan Sofiyya da munnir sannan takara dacewa "indai adalci za'ayi to bekamata kazama silar rabuwarsu ba"



Umma dai nazaune batace komai ba, itama Raliya da usman duk basuyi magana ba.


Abdul da mamaki ya baibayeshi yace "wannan duk karyane ai yanzu daga gidan nasu nake"


Bashir yakara dacewa "kuma harda daddyn ta munyi magana, da'ace dagaske ne aida yasanar damu"



Raliya dama haka takeson ji tace "wlh yaaya dagajin zancen kasan karya ne, dama ni banwani yarda ba"


Usman zeyi magana Umma tace "kumana shiru, dama su iyayenta indai suna sonta ai bayanta zasu bi, kawai ka hakura da ita tunkafin abun yayi nisa"



Abdul kanshi ya kulle, a ina zuly tasamo duk labarin nan?
Abinda ke zuciyar Bashir kenan don haka yace "to ita a ina tasan duk wannan labarin?"



Usman yace "waishi saurayin malamin Islamiyyarsu nefa"


Me Bashir zeyi inba dariya ba, yanayi yana dukan Abdul yana cewa "kajifa ashe rival din naka malamin Islamiyya ne hhhhhhhh"



Abba ne yace "kai Bashir banason shashanci meye abin dariya anan"



Gumtse dariyar tasa yayi sannan yace "yi hakuri Abba wlh wannan qagaggen labari ne, don idan kaga munnir zaka tabbatar da cewa shikanshi yana bukatar Islamiyyar a matsayin dalibine tukunna"



Abdul dai shiru yayi, tunanin sa yatafi kan zulyne, tabbas akwai bukatar ya nemota don yanason sanin dalilinta nayin hakan.



Abbs da kanshi yafara mishi ciwo dama bawai dadi yake jiba, yamike yace "bari dai zan bincika in tabbatar amma kafinnan kadakata da nemanta tukunna"



yana gama fadin haka yayi shigewarsa daki.


Shima Abdul dakinsa yanufa, Bashir kuma yayi musu sallama yatafi.


Anty Zainab ma sallama dasi tayi tatafi, yarage daga Raliya se Usman.


Usman yace "anty Raly akwai case fa, bansan ma yaushe Abba yadawo bafa"


Nan suka dasa gulmar Abdul da kuma halin da Abbansu ke ciki.




Koda munnir yadaga kiran zuly labarin abubuwan dasuka faru tabashi, hade da karyar data shirga musu ta rabasu, takara dacewa "ni yanzu yaaya Abdul nakeso shiyasa nakiraka muhada kai murabasu kowa yakama nashi"


Ba karamin dad munnir yaji da wannan labari, kwarin gwiwa ya kara mata, hadi da wasu hanyoyin dazasu bi don rabasu.


.
.
.
.
Kwanaki sunata tafiya gashi har Hafsa tayi kwana arba'in da haihuwa, kwananta hudu a asibitin aka sallamota suka dawo gida, duk wata kulawar da ake yiwa mejego tasamu ne gun kawarta Binta, don ko abinci a gidan ba bata akeba, sedai binta ta girko takawo mata.




Da mustapha 'yar aiki yaso dauko mata amma binta tace yabarshi insha Allah zata kula da ita.



Su mommy sunsamu labarin haihuwarta Sofiyya taso bin Siddika dazata tafi don zuwa yin barka amma daddy ya hanata, hakanan ta hakura don ba yadda zatayi.


Raliya ma tun bayan graduation da kwana uku ta tatrara ta koma gidanta.


A fannin Abdul kuwa babu abinda yaragu, sheke soyayyarsu suke kamar ba gobe.


Sunkara shakuwar da rabasu zeyi wuya, itakam Sofiyya harma jitake wani cigaba da karatu yafice a ranta, gara kawai ta nutsu wurin bawa handsome duk wata kulawar data dace.



Abba kam yadan warware yakoma harkokinsa kamar da, sedai radadin da zuciyar sa kemasa be raguba sam.



Zaune yake a dakinsa yana duba wasu littattafansa umma tashigo da sallama a bakinta.

Amsa mata yayi, yana cigaba da dubawa.


"Dama sonake muyi magana dakai Alhaji, inkana da lokaci" inji umma


"Okay bani mintuna 5 inkarasa then se inbaki hankalina duka ko? "


Zama tayi tana jiransa.


Bayan yagama yajuyo yana fuskantar ta yace "to bismillah ina jinki"



Umma tace "dama kan maganar yaron nan ne, naji kayi shiru kumafa bawai yadena nemanta bane, don nakanji suna waya, kaga kar abu yazo yayi nisa akasa tsaidasu"



Murmushi Abba yayi yace "to me kikeso ayi, ko kinji wani abun yasake faruwa me?"



Tace "a, a babu abinda yasake faruwa amma aibe kamata a zuba idanu ana kallonsu ba bayan ba'asan abinda ze biyo baya ba, kasan wlh banason tashin hankali"




"Ki kwantar da hankalinki babu wata matsala insha Allahu, naje na bincika ita yarinyar ba kawar usman bace ba!? Sonake ma insamu lokaci inje insamu mahaifin yarinyar muyi magana dashi" inji Abba




Umma tace "to Alhamdulillah garadai kaje ka sameshi"


"Sekuma magana ta biyu alhaji, wannan damuwar dakake shiga ciki lokaci bayan lokaci, ina ganin yakamata muje gurin masu maganin gargajiya muyi musu bayani, shekara da shekaru abu yakici yaki cinyewa, wata kila Allah yasa mudace"



Abba ya jinjina kai yace "harkin fara tunanin zuwa wurin wasu masu magani? Kenan kina tunanin aljanu ke damuna?"



Tace "alhaji to ai abunnne naga kamar bame karewa ba, kaga gara asamo mafita, don gsky nagaji da ganinka haka"



Yace "to kikara hakuri insha Allahu lokaci yakusa dazaki san menene matsalata, duk da kuwa hakan baze miki dadi ba"



Tace "to shikenan Allah yakaimu"

Daga haka tayi mishi sallama tafita...........................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*



Episode 26-27

Abdul ya nutse cikin tunanin yadda a lokaci kankani rayuwarsa ta canza,.

Haduwarsu da sofiyya ko wata biyu becikaba, abubuwa sunfaru kamar a mafarki.

Shidai fatanshi Allah yasa karta rejecting dinshi, jiyayi an kwankwasa masa glass.

Dagowa yayi yaga Bashir ne, dob haka ko kulashi ma beyiba yamaida hankalin shi kan tunanjn dayake yi.


Shik???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o bashir ko a jikinsa yabude motar yashiga yazauna.


"Dolema kakasa hada ido dani ai, tunda seda kayi kutun kutun karabani da beautiful kayimin snatching dinta"
Inji Bashir



Nan ma shiru Abdul yayi don besan mekuma yakeson yace masa ba.


"Mutumina wai ya akayi kafada soyayya haka ne? Kai ninaga kishi yau, kawai kawani figi yarinya ka yi gaba."


Nan ma dai Abdul be tanka ba.

"Gashinan kajawo mata matsala gun familynta"


Se sannan yadago ya kalli Bashir yace

"Wacce irin matsala kuma? "
Abdul yafada yana kallon Bashir don jin karin bayanu.


Tiryan tiryan Bashir yakaranto masa duk abinda yafaru ciki kuwa harda furucin dayaji Hajjaju tayi.


Jin maganar yayi kamar saukan tafasashshen ruwa a zuciyarsa,
Dukda cewa baya gurin abin yafaru, amma yanada tabbacin dasa hannun munnir cikin wannan al'amari.


Key yayi wa motar batareda yacewa Bashir komai ba, ya figi motar da shegen gudu.


Usman daya fito rakiyar bakinsa yayi tozali da tashin hankali, don saura kadan yarage ya bige usman din shi bema sani ba,.



Hankali tashe usman yakoma cikin makarantar yasanar dasu umma abibda yagani.

Mikewa umma tayi tana salati, anty zee ma salatin takeyi.



Umma tace "yanzu ina sukayi haka? "


Ganin irin yadda umma tadaga hankalinta se safa da marwa takeyi tasa Anty zee kiran usman


"Kaje kakirawo driver yazo yamaidamu, gara muje gidan ai"



Ciro kud dubu daya tayi ta mika masa tace "gashi nan katarewa wadanda muka zo tare adaidaita"


Karfan kudin yayi yajuya yafita

Dukkansu hankalinsu yatashine sakamakon sanin sanyin hali irin na Abdul, don indai kanason 6atawa kanka lokaci to kace Abdul yakaika anguwa.

Inda adaidaita zashi cikin mintuna 30 to shi seyayi 40 ko finhaka indai shiyake driving din.


Wani lokacin har a kan titi zakiji drivovi na korafi akan tukunshi, shikam haka yake, sam be iya tukun sauriba, hakanne kuma yasaka duk hankulansu tashi domin sun tabbatar ba lafiya ba.


Raliya kam harda 'yar kwallarta tace "Allah sarki yaaya"


Suna tsaitsaye usman yadawo yace "kuzo mutafi, suma suntafi"


Duk wucewa sukayi, anty zee ta kalli zuly tace "to zulaikha kozamuje kema intare miki adaidaitan ne kitafi, kar mamanki ta nemeki, ni kinga tafiya bata ganni ba tukun"



Cike da damuwa zuly tace "haba anty Zainab, munzo tare aibe kamata intafi inbarki ba, karki damu da mama zankirata a waya ai"


"Ti shikenan muje" inji anty zee.

............




Tunda sukadau hanya hajjaju keta faman sabani, babu dai wanda ya kulata cikinsu, har sukazo gida.


Sofiyya sam bata

11 / 26