CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   25 / 26

72K to 75K   out of 76.5K words

cikin ankon lace anko sukayi, duk inda suka gifta hoto ne kawai akeyi musu. Bayan isha'i ne duk sun gaji sunma cire kayan su zuly nasanye da riga da top itakuma sofiyya night gown tasaka daidai gwiwa sunata kallon pictures din da siddika tayimusu ya hadu sosai, suna cikin kallon bashir yayi kiran wayar, Sofiyya ta jefa mata tana harararta tace "that maye is calling, kallon minti Goman ma baza'a barmu muyi ba" kar6an wayar Siddika tayi tana hararar Sofy tace "kingama kallon kuma ai narantse" picking call din tayi suka gaisa, sekuma ta kalli Sofiyya takalli zuly tace okay I will try.

Bayan ta katse kiran ne ta kallesu tace "guys albishirinku" sofiyya dai kallon ta take tana ta6e baki, zuly kuma tace "goro whats up" siddika tace "ina kilishin ranar da tsire?"
Matsowa kusa da ita Sofiyya tayi tana cewa "kawowa aka sakeyi? Don Allah jeki kar6o mana sis wlh yau tun safe banci abinci ba ko yar uwa?" Takarasa tana kallon zuly a marairaice, zuly tace "please kiyi sauri wlh bamuci abinci ba"

Siddika tace "lallai wato infita nikadai da daddaren nan, ai wlh sedai kar aci kowama ya hakura"

Duk shiru sukayi Sofiyya tace "sis kije kirakata Ku kar6o mana please" siddika tayimata kallon kin rainamu sannan tace "aiba mubiyu zamuci ba, don haka inbazamuce mu duka tare ba wlh sedai a hakura" babu yadda Sofiyya ta iya don kwadayi kam jinshi take kamar sabuwar meciki, haka tatashi tadaura kimoni kan kayan jikinta sannan ta zumbula hijab harkasa, itama zuly hijab ta zumbula, itakuwa siddika dama bata cire atamfar jikinta ba, so mayafi kawai tayafa suka fita.

Koda sukaje mota suka gani guda biyu a wajen gidan, Sofiyya takalli siddika batadai CE komai ba, suka karasa Bashir ne yafito yana tafa hannu yace "aikinki nakyau sweetheart" dariya siddika tayi tace "anything you want habibi"

Bude baki Sofiyya tayi kafin tayi magana munnir yafito daga dayar motar yana karewa zuly kallo, da mamaki sofiyya ke kallonshi sannan tajuya ta kalli siddika, gwalo siddika tayi mata, kafin tayi magana Abdul ya iso gabanta da smilling face sokoko tatsaya kallonshi, duk dadai tayi missing dinshi don tunda suka dawo daga suleja batasake ganinshi ba.

Ba zato taji ya damke hannunta, salolo tabishi har cikin mota, bayan tazauna yarufe yazaga shima yazauna yarufe, kallonta yake ko kifta ido bayayi, itako ranta ne ya6aci, how dare siddika deceived them in such manner, gashi nan tasa yakama mata hannu, dagowa tayi tace "how many times do you want to commit a sin? I'm not yet your wife fa" takarasa kamar zatayi kuka.

Abdul yahade hannayenshi guri daya yace "I'm sorry gajen hakurine wlh, it won't repeat it self I promise"

Zuly ma nacan munnir yajata mota suna zantawa, siddika dai tacewa bashir yataimaka yaje yasiyo musu kilishi da tsire kafin sugama, ita zataje gida tayi musu CID idan yadawo yakirata, hakan kuwa akayi.

Tun tana kumbure kumbure harta sake suke hirarsu tama mance gobe zata amarce, cikin hirar tasune Abdul kece mata "Nifa inaga zamufasa yin dinner dinnan kawai dakun gama event dinku kitaho gidana" wani kallo tayi mishi tace "as how?"
Yace "as I said, u konw I can't afford to see you there with too much men looking at you? Inaaa please afasa kawai hankalin kowa a kwance"

Hirar daba'a gama cikin dadi ba kenan, sukarabu ko sallamar arziki babu, ita fushi shima fushi haka tadawo gida tabar zuly, aikuwa siddika tasha zaki karshema da akakawo kilishin ko kallonshi batayi ba tayi shirinta ta kwanta expecting a call from handsome but shiru har barchi ya kwasheta.

Washegari daurin aure 11am saturday aka daura auren daya samu halartan baki manya manya daga wurare daban daban a fadin nigeria da kasashen ketare, nera tayi kuka gurin bawa mawaka da maroka, angwaye se washe bakuna sukeyi.

Mijin aunty zee ma yasamu halarta domin baya gari a ranar yadawo domin yasamu zuwa daurin auren, dadin dadawa kuma yasamu ganin mama Karin sukoma suleja.

Sofiyya suna daki angama shiryasu cikin wani lallausan material, dakudu siddika tazo tana makalawa zuly waya a kunne domin duk wayoyinsu na hannunta, munnir ne yakirata yana fadin "an daura fa, you're now mine Alhamdulillah"
Hawaye ne yazubo mata, Sofiyya taji duk abinda aka fada don a handsfree akasaka wayar, itama jira take amiko mata wayar but shiru, can dai tace was siddika tabata wayarta, mika mata tayi tanayin fuskar tausayi tace "kidai kara hakuri" naushi takai mata takauce tana dariya.

Tun 11, take juya wayar har yanzu azahar bataga kiran Abdul ba, se message datagani "Alhamdulillah kinzama mallakina yau, anjima se kwanan gidana Cutie Naa" tsaki tayi ta jefar da wayar.

Me makeup CE tazo tace suje suyi alwala suyi sallah sannan a fara.

Amare sun hadu iya haduwa, 3:30pm akace suje susakeyin alwala za'a sake gyara musu makeup din Idan sunyi sallah.

Bayan sunyi sallah suka fara shirin zuwa event na parents day dasu amare dakansu suka shirya domin karrama iyayensu, kuma sun gayyaci both gidan angwaye, hall suka kama akayi decorating dinshi sosai yayi kyau.

4pm an hallara cikin hall din, Abinci kala daban daban aka ajiye serve yourself kadiba Wanda kakeso kawai, angayyaci mommy domin tafito tayiwa yarta nasiha, bayan ta kar6i mick ne aka fito da Sofiyya cikin lafaya maroon da bakar longslive, anyimata light makeup tasaka takalminta half cover, tayi matukar kyau, wayoyi da camera ne kawai suke aikin daukarta photo, dukda dai tadan kare fuskarta amma hakan behana angan kyawun nata ba, mommy na tsaye itakuma sofiyya na zaune kan wata lallausar dardauma a gefen mommy, kanta a sunkuye.

Mommy tafara magana "yake yata zanbarki da kalmomi kadan amma idan kika fahimcesu tabbas sune zaman auren, dafarko kisawa ranki cewa ibada zakijeyi ba jin dadi ba bakuma neman kudi ba kamar yadda wasu kedaukar aure, sannan kafin kifara aiwatar da komai kinutsu ki fahimci wanene mijinki domin kisan abubuwan dazaki applying dakuma Wanda zaki avoiding, a karshe kisakawa zuciyarki hakuri, hakuri, hakuri" *(zan fadada wadannan maganganu a littafina nagaba insha Allah, bear with me lovers)*
Kabbara akayimata, Umman su Abdul hakanan taji mommy ta burgeta sosai, Sofiyya kanta a kasa amma hawaye takeyi jitake inama karta tafi tabar mommynta.

Dafa kanta mommy tayi tace "as banida matsala dake, duk yadda akeson diya tagari tazama tabbas kinzama Allahu ya albarkaci aurenki da zuri'a dayyiba" amin yan hall din suka amsa, itama sofiyya aranta amin din ta amsa.

Durkusawa tayi tadago sofiyya ta rungumeta itama takasa tsaida hawayenta, anan ne kuma mc takira umma da Aunty zee domin suzo su kar6i 'yarsu domin a yanzu tazama tasu, maman Zuly ma tataso tazo gurin tatsaya kusa da mommy. Takar6a mic tace "ga diyarmu amana a gurinku, a yau tatashi daga tamu tazama taku mu sedai zumunci kuma" dakyar mama ta 6an6are Sofiyya a jikin mommy su umma suka rungumota suka tafi da ita zuwa sit dinsu, kuka take sosai Aunty zee da mardiyya da ita kanta umma se lallashinta suke.

Hajja dake gefe itada aminiyarta tace "kinga wata sabuwar bidi'a da iyayi ko DaDa?" DaDa tace "bawaninan kedai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bakyason harkar zaman lafiya da nishadi" Hajja tace "kedama addiniki ai sunane, inbanda ma salatin ma'aiki dakikeyi aida tuni munraba hanya, don ni bana harka da yan bidi'a wlh" DaDa dai batace komai ba, tacigaba da kallon abinda ke wakana.

Maman zuly aka kira, tare da zuly, dakyar ta iyayiwa zuly yar nasiha daga karshe itada zulyn duk suka fashe da kuka, mommy CE tazo tahau lallashi kana aka kira maman munnir itadawata kawarta domin su amshi amarya.

Tunda maman munnir tamike take tahowa hajja da DaDa suka dariya suna fadin bodara wai yarinya zakisha tusa wlh, natausaya miki.

Suma sunkar6i zuly hannu bibbiyu sunkoma sunzauna suna lallashinta.

Ahaka taro ya watse, iyayen angwaye suntafi da amare gidajensu, inda anan ne za'a shiryasu zuwa gurin dinner daga can kuma awuce dasu gidajensu.

Bayan kowa yakoma gida, zuly dai gidan hajja suka wuce da ita, tunda suka shiga gidan hajja ke nan nan da ita ina za'a saka ina za'a ajiye ganin idon DaDa.

Sofiyya kam taga gata, don sosai suke jida ita, Raliya na manne da ita, anyi isha'i Abdul yashigo gidan se leke leke yake yakasa gano amaryarshi, aunty zee nalura dashi sarai tadai yimasa shiru ne, can dai yakira Raliya gefe yace "ina takene wai" Raliya tace "wa?" Kafin yayi magana Aunty zee tace "kafita kabamu guri rasai, inkayi hakuri nan da yan awanni ne seyadda kayi da ita ai" sum sum yawuce yana Sosa keya.

Shirin zuwa dinner akewa amare, suma angwayen shiri suke, Abdul dai bayadda zeyi ne amma shifa kishin matarshi yake, da cune cune, da kumbure kumbure haka bashir yataya shi shiryawa, (fans nace muhadu Turin dinner) lol............................
'

07046767662 Maryam-Ashner CE
[9/15, 2:06 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 51

Haduwa iya haduwa amaren nan da angwaye sunyi so masha Allah.

Sofiyya cikin wedding gown golden purs and shoe also golden, wannan shirin aunty zee ne, domin kayanma itace tazo mata dasu.

Abdul ansha shadda brown da babbar riga, yana zaune a bayan mota ya jiran fitowar amaryarsa, bashir yana driver sit magana yaketa yiwa Abdul amma yayi banza dashi, Raliya CE tarako Sofiyya har kofar motar da dama a bude yake yana jiranta.

Zaunar da ita tayi sannan ta sunkuya tace "yaya inshigo muwuce ne please?" Wani kallon zakici ubanki Idan nafito yayimata, tuni tabar gurin tana tura kofar motar.

Kanta a sunkuye tunda tazauna bata dago ba, shikuwa tun shigowarta motar kamshin turarenta ya bugi hancinsa, jikinsa ya mutu, kallonta yake kamar tsohon maye sannan slowly yakamo hannunta ya damke cikin nashi a hankali ya matso kusa da ita tayadda suna iya jiyo numfashin juna yace "no complain today u are mine"

Kokarin janye hannunta take, don ta fahimci ya sauko daga fushin nashi itakuma yanzu tahau nata fushin, sam taki yarda suhada ido.


Duk wani kokarinshi na ganin fuskarta dakyau abin yacitura don sam taki bashi damar hakan.

Masu tafiya dinner kam duk sun tafi, don su zuly ma tuni sun isa, SOFDUL ne kawai suka rage, gogan yaki cewa a tafi, shikuwa bashir jiran order kawai yakeyi amma yaji shiru.

Abdul fa yamatsa lallai shine zefara karewa kwalliyar matarsa kallo amma itakuma tasha mur, daga karshe dai yace sutafi, bashir yatada mota sukadau hanya.

Bayan sunyi parking bashir yafito yabude musu mota yace "bismillah" fitowa Sofiyya tayi Abdul ma yafito yazago tagefenta suka fara tafiya yana rike da hannunta, dashigarsu hall din aka dau tafi, ganin duk idon kowa nakansu kuma shi gani yakema kamar duk mazan gurin sofy kadai suke kallo, haushi sosai yaji a ranshi yace "that's why banso abinnan ba wlh" ba zato ba tsammani taji an cicci6eta kamar wata baby haka yadauketa, aikuwa nan hall yadau tafi dagudu akazo akafara yimusu ruwan kudi.

Zaro ido tayi ta waresu gaba daya tana kallonshi da mamaki, with a smilling face yake kallonta a hankali ya whispering dinta dacewa "I will never let you fall so don't be scared a hannun mijinki kike"

She never thought that Abdul is such, da sakakken ido da baki kawai take binshi har yakai mazauninsu yadireta sannan yazaunar da ita shima yazauna, ita duk kunya tagama rufeta don haka kanta a kasa takasa dagowa takalli mutane.

DaDa da Hajja da suka nace seda aka taho dasu kuwa tun sanda sukaji tafi suka juyo sukaga yadda Abdul yadauki sofy hankalinsu yatashi suka tsaya da sakakken baki harseda ya direta tukunna suka kalli juna, Hajja tace "A'uzubillahi minash shaidanin rajim" DaDa tace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'uun" Hajja tace "kinga abinda nagani kuwa?" DaDa tace "ni aibansan haka akeyi a gurinba wlh dabazan zo ba" hajja tace "to ai yanzu ma bazama zamuyi anan ba, ai nan gurin yafi karfinmu, yaushe ruhin dayake salatin manzon Allah zezauna gurin yan iska" tafada tana jawo hannun DaDa.

Kai tsaye tanufi gurinsu munnir, mutanene suka fara tareta tana fadin "ni wlh ba yar iska bace, bakina kullum da salaltin manzo don haka bazan zauna anan ba, manniru zan kira" DaDa tana "kumatsa mana Dan ubanku" munnir ne ya hango abinda ke faruwa yataso yataho gurin yakamo hannunta yayo waje da ita, DaDa na biye dasu.

Bayan sun fitone yace "meya kawoki nan gurin hajja" Hajja tafara kuka tana cewa "aikaga dai iskancin da akeyi agurin ko manniru? Shiyasa nace kadauko matarka mutafi tunda muba yan iska bane bakinmu akwai salati"

Wani tsaki munnir yaja yace "kinsan Allah sedai kuta jira har agama taron nan kuma anan gurin don nidaga nan gidana zan wuce wlh kuma zanfada ma masu gadi karsu yadda subarku kushigo" yana gama fadin haka yajuya yakoma kuma yafada kar abarsu sushiga din.

Zaune sukayi agun suka fara istigfari don dama kobece ahanasu shigaba suma bazasu komaba.


Munnir ba mutunci lol

Sosai iskar wajen ke kadasu don haka suka fice don samun adaidaita Allah ya taimakesu dare beyi canba suka samu adaidaita yadaukesu.
Cikin napep dinma se mita suke, idan sukayi sukayi se sucewa me napep "kaida malam karike istigfari da salatin manzo karka zama Dan iska" ahaka dai yakaisu kofar gidan hajja gashi basuda ko sisi, bayan sun sauka hajja tadubeshi tace "mungode malam Allah dai yayi albarka" takama hannun DaDa zasu wuce me napep yace "kudin fa?"

DaDa ta waigo tace "yanzu duk wa'azin damuka maka semun biya kudi?" Hajja tace "lallai wai kai dama kazata a banza muka maka wa'azin? Kai inbanda ma darajar manzon Allah yaushe zamu maka wa'azi kyauta?" DaDa tace "kyaleshi hajja inbeyarda ba yabiyamu abinda muka sanar dashi wanda ko miliyan nata isa siyanshi ba"

Me napep dai kallonsu yake yana hararo irin rashin kirkin daze musu, Allah yataimakesu Su Daddy suka karaso gurin akasamu aka sallami me napep yayi tafiyarsu sukuma suka wuce gidan suna sababi.

A gurin dinner kuwa sha'ani yayi sha'ani,can na hango su little da faty anata selfie, su jidda kuwa andage anayiwa amare video, su mama auwal da maman mubeenart kuwa se rawa ake itako Asma'u nacan anacin kaza, masu turare se feshewa ake lol

Sofiyya dai har akayi aka gama taki sakin jiki da Abdul, se wuraren 12 aka tashi, aka maida kowa gida, abokan angwaye kuma suka kwashe angwaye da amare zuwa gidajensu.

Anwatse anbar angwaye da amarensu, bari muleka gidansu SOFDUL. Sofiyya dai se noke noke take da cune cune, Abdul nalura da ita, murmushi kawai yake, cire babbar rigarshi yayi ya ajiye kan kujera, yacire agogonsa da hura ya ajiye, Sofiyya dai na zaune kasan carpet tana kallonshi ta gefen ido, kallonta yayi yace "muje muyi alwala ko Mrs Cuna" kin kulashi tayi aikuwa shime besake maimaitawa ba ya sunkuceta, ihu tasa tana wurwurga kafa tana fadin "put me down I can walk I will go please" bekulata ba sedai ya dangantata da toilet ya direta yace "maza kiyi alwala kifito, inazuwa" yajuya yafito.

Ajiyar zuciya tasauke sannan tafara yin alwalan, shikuwa sama ya haura yashiga wani dakin yafada toilet ya watsa ruwa sannan ya dauro alwalan yasaka farar jallabiya sabuwa kal sannan yafito yasameta zaune kan kujera tana jiranshi.

Batasan yakaraso ba seda ya hura mata iska a keyarta, juyowa tayi tasake cuno baki sannan tamike tana ware ido tace "wanka kayi?" Yace "yap" buga jafa tafarayi a kasa tana fadin "wlh niban yardaba ni banyi wanka ba sekai" yace "wifey nifa warin gumi nakeyi" harararshi tayi tace "tonidin fa?" Matsowa yayi daf da ita a hankali cikin rada yake "ke kamshi kike and I love the scent"

Batasake magana ba, hijab din daya dauko ya mika mata yace "lets pray now if you want daga baya sekiyi wankan I can even help you"

Sulum ta saka hijabin bcos yau taga tabbas kan handsone rawa yake, as he don't even know what exactly he is saying. Sallah yajasu raka'a biyu sannan yagabatar da addu'o'i.

Daganan akazo cin kaza lol

Dakyar Sofy takar6a yanka daya sannan tadansha yo kadan tace takoshi, dama dai aunty tacika mata ciki da kwakwa

25 / 26